Showing 18001 words to 21000 words out of 27433 words

Chapter 7 - HANNUNKA MAI SANDA COMPLT-1.pdf

03 Apr 2025

2189

suma sunki
bayarwa, nan yakara hado yan sandan, aka
cika files yayi komi, donma yanada dan
matsayi ne abun yake zuwa masa da sauki,
donhaka suka basu duk abunda suke bukata
Date of withdrawal 3rd may Time: 11:34am
Self withdrawal , location :abuja, Yace suyi
requesting footage din , sunyi requesting
anma sunce masa zaikai awa biyu donhaka
yajira aturo, gagara zama yayi ya zauna ya
tsaya, har aka turo gabadaya suka duba
time din dawanda yayi transactions din
“Innalilah wainna ilaihi rajiun,” Abunda yake
furtawa kenan don mamakin ganim waye
HANNU DAYA BAYA DAUKAN JINKA NA
BENAXIR OMAR Hannunsa yasa yana nuna
screen din, kalmomin bakinsa duk sun kafe
yana kokarin furtasa “A-A-AMII-RA” wani
gumi yaketo masa, mutumin yakara masa
playing don yagani da kyau,Amira ce
arayuwan duniya ko hauka yayi bazai manta
da fuskar ba, itace, fadi yayi agun, atake
suka tallafoshi, yamike agigice yadauko
wayansa gumi yana keto masa,hannunsa na
rawa yayi dialing numban abdullahi,
“Kaaaaaaazzzzzoooo zenith bank, inajiranka
yanzunnan” baisaurari mezaice ba yakashe
wayan, shikuwa abdullahi mikewa yayi yafito
dasauri dama bayada nisa da gun, cikin
mintina kadan ya iso, kiran yusuf yayi
dasauri yusuf ya amsa tareda masa
kwatancen inda yake, yana shigowa yusuf
yakirashi yamasa playing yagani, tabbas
amirace donkuwa da zata karbi kudin har
zoben hannun hagunta yagani, yayi
murmushi sannan yace “i knw kana sonta
and kana missing dinta. But kazo annemo
maka abunda yadade kana replaying,karfa
kasami problem fa, don alamun mental
sickness ke damunka” Yusuf tsaki yaja,
yajawo kan mouse din yamasa zooming date
nd time, tareda cewa “duba date and

time,abunnan ko sati baiyiba, donhaka amira
tanada rai,kuma fa it says self withdrawal,
dakanta tacire kudinnan, common abdullahi
dix is reality” Abdullahi yazura masa ido
sannan yace “basai nayi dogon surutu ba,
dakanka kaga gawan amira, anwanketa
sannan ankaita” “No nidai naga gawanta
ajini, tunda har fuskanta jinine. For wat she
suffered for, anma banganta bayan anmata
wanka ba, hey!! Abdullahi dnt tell me u r
involve in dix in anyway !” Wani takaici ya
gulli abdullahi, duk da shima zufan keto
masa take sannan yace “bamu saba wasa
dakai ba, i hav nfn to do wit dix, nd blv me
not , dix aint my sister” yana fadan haka
yafice yabar abdullahi a tsaye, a gigice
yakira wayan ramlat, tadauka cikin magagin
ciwo anma yadda ya furta mata maganan
bakinsa batasan lokacin data mike ta dafa
kirji ba, cemata yayi “amira is alive!!” “Wat?”
“Yesss!!” “You crazy” “Wateva, yanxu dai
help a broda, kizo zenith m waitn for u der”
Bai saurari mezatace ba yakashe wayansa
HANNU DAYA BAYA DAUKAN JINKA NA
BENAXIR OMAR Suna tsaye suna jira da yan
sandan tashigo cikin gurin sanye takeda
abaya, doguwa , fuskanta na nuna alamun
tsoro, dasauri yusuf yakunna mata tagani,
batasan lokacin data zauna akan kujeran ba,
tsantsan rikicewa, gumi yafito mata, takalli
yusuf wanda bakinshi har wuya , aranta tace
“dix person must be crazy!, antaba mutuwa
aka dawone?” “Yhto ramlat kinyadda?” “No
banyarda ba, mai kama da itane” “Bangane
mai kama da itaba. How can mai kama da
ita zata zama tana usn account dinta” Shiru
tayi, its a food for thought, duk basiranta
tafiya yayi, kallon mutumin tayi tareda cewa
“can we have a copy plx?” Saidata sighing
takardu hukuma suka sa hannu, donma suna
da karfine, da zaibasu wahalar shaani,
tadauka suka fito, shidai murmushi yakeyi,
can yagagara hakura yace “zanje abuja yau”

Juyowa tayi takalleshi tareda cewa, afadin
abuja ta ina zaka fara ganinta? Do u knw
dat u r falling into a trap?, someone might
do dix to hurt u” “Koma meye, ill be going , ”
bata saurareshiba, takunna motarta shima
kunna nasa yayi kowa yayi gaba, gabanta
sai tsananta fadi yake, yusuf gidan inna
yawuce yasamu batanan donhaka yanufi
asibiti, yaci saa bata da aiki sosai, donhaka
ya isa gunta suka zauna, ya gyra murya
sannan yace “Inna maganan kudin danaga
ancire a bank, naje bank nabukaci sumin
bayani naga details, toh kuma abunda yafaru
shine sun nunamin videon wanda yakarbi
kudin” Tazaro ido tareda cewa “yan fashi ne
ko?” Ya girgiza kai tareda cewa “Inna, amira
ce, takarbi kudin” Batagane meyake nufi ba,
saidaya kara maimaita mata Sannan tace
“Bangane wacce amira ba” “Amira dai,
amiran gydannan” Tayi murmushi tareda
cewa, “Yusuf kaga kasa damuwa aranka
gashi har kafara gane gane,” “Wlh inna
lafiyata lao, amira nagani, amiranki, itace,
bata mutuba” Inna ta girgiza kai donta fara
tsorata tace “kamanta nina mata wanka
kafin akaita?, yata nayiwa wanka , kuma baa
taba mutuwa andawo ba” Yayi shiru don
yaga bazata yatda dashi ba sannan yace
“barin nuna miki kiga” Flash yaciro a
aljihunsa, yadauko laptop dayagani akan
table din office din, yajona, yasa mata play,
sannan yaja baya ya tsaya Idonta kur akai
daga farko har karshe. Idonta tuni yaciko da
ruwa, tana cewa “ba amira bane, wannan ba
amira bane, amirana fa tamutu, gizau ne
kawai, innalilahi wainna ilaihi rajiun,” fadi
tayi a kasa
[12/11, 8:40 AM] Benaxir Omar: HANNU
DAYA BAYA DAUKAN JINKA NA BENAXIR
OMAR Dasauri yanemo agaji aka farkar da
ita, wayansa yasa yakira abdullahi. Cikin
mintuna kadan ya bayyana a asibitin yana
shigowa alokacin yusuf ya tallabo inna

wacce suka bata bedrest, dasauri ya isa
gareta sannan yagaydata da jikin, juyowan
dazaiyi yatsaya cak yana kallon yusuf.
Wanda ke kokarin bayanin meya faru,
abdullahi yasa hannu yatareshi alamun yayi
shiru sannan yace “do u knw wat? I dnt get
it, kazo kana dagawa mahaifiyata hankali,
kasan cewa fa da hannunta tayi wanka wa
amira, karamin hauka ne ke damunka ko
meye? Kataba ganin mamaci yadawo, its
high time u respect urself plx!,” Yusuf yayi
murmushi sannan yace “inna kiyi hakuri, but
tunanina wannan abun farin cikine shiyasa
nagayamiki, anma tunda baa yarda ba,
nizance nemanta, kuma zansamota, kuma
zan aureta!” Inna dasauri tace “tsaya” ya
tsaya donjin mezatace “kayi hkr, Allah
fargaba ne yacikani, babu maison yaga
amira da ranta irina, donAllah duk abunda ke
faruwa kasanar dani, abdullahi kozaka je
ne?” “Inje ina inna, bayan nasan ta mutu. Ba
inda zanje, kema yarda kikayi dashi kawai,
saiya dawo lfy Shidai yusuf yana mamakin
hali irinna abdullahi baka gane alkiblansa, if
not bcox ciki daya suka fito dayasashi acikin
black list yan hassadan amira, Gida yanufa
yahau tattara kaya, yana fitowa yaga
mammy yayi murmushi sannan yace “zanje
aiki abuja” “Saikuma yaushe?” “Saikunganni
kawai” Fitowanshi kazrat tabiyoshi, “yaya
kayi hakuri kana kula barr.ramlat” “Ita tace
bana kulata?” “A a, ni nalura, kaga rashin
amira ne yahawo haka” Murmushi yayi
sannan yariko kumatunta yace “dont worry
little sis, zandawo miki da labari mai dadi”
Jan motan yayi dakarfinsa, sai abuja, Yana
shiga yafara tunanin ina zaije, gidanshi
yanufa wanda ke lugbe, yayi parking yashiga
ya ajiye kayansa. Gidan tayi kura donhaka
wayansa yadauka yaddanna wa abokinsa
faruk waya, tareda cewa yataho da mai
aikinsa, aikuwa saigasu sunzo, ta gyra
gydan tsaf, shikuna yayi wanka suka

kinkima mota sukayi waje, [12/11, 8:56 AM]
Benaxir Omar: HANNU DAYA BAYA
DAUKAN JINKA NA BENAXIR OMAR Yana
rike da stiyerin mota,anma ranshi na tunanin
ina zaifara zuwa, duk fadin abuja ina zaije da
sunan nemanta, dafarko tunaninsa shine
wacce irin mutum ce amira, yasanta da son
zaman gyda kaman me, batason fita, kuma
zuwa wurin shakatawa ba idea dinta bane,
but yasan tana balain son shiga kasuwa,
aikuwa saidayafara tundaga lugbe, harsu
wuse market, yayi su gwagwalada, duba
agogon dazasuyi karfe goma, donhaka yaroki
faruk dasu kwana agydanshi, aikuwa hakan
sukayi baiyi bacciba, anma faruk kam harda
gwarti, map din abuja yanemo, yanata dube
dubenshi, dole nema yajesu manyan shaguna
washegari a mota suka karya, karfe sha daya
suka nufi shoprite, sai next, sunyi hanyan
grandsquare faruk yace “waini tsaya inmunje
nan sai ina?” “Sai sahad” “You must to be
stupid, ji yadda kake yawo damu, daga
grandsquare kadawo damu sahad, wani irin
baya ne haka, ni da Allah muje bank din,”
Zenith bank sukaje, sukayi confirming tape
din, tabbas itane, kuma self withdrawal,
which means babu photocopy dinta, ita ce
dakanta takarbi kudin, Numbansa yabayar
wa managern incase ko zaa sami wani trace,
harsun fito managern yakirasu tareda cewa
“tunda withdrawal ne, y not kuyi stickn da
nan bank din, intana gari definately zata
dawo nan din” Faruk ne ya amince atake,
donshi yawahala sosai, hakan kuwa tafaru,
satinsu uku ajere kullum saisunzo dasafe har
arufe bank sunagun, wataran yusuf shikadai
ke zuwa faruk nazuwa gun aiki, haryafara
hakura, don yafara tunanin komawa bauchi
kawai, duk da tsananta adduanshi daya keyi,
ana gobe zaitafi bauchi yazauna a reception
din bank din wanda harsun saba sosai dasu,
wasukam ma sundauka staff ne, Karan
takalminta ne yajanyo hankalin daukakan

mutanen dake cikin bank din, tana sanye da
abaya, baka, tayi daurin turban, tayi kyau
sosai, yakalleta gabanshi yafadi kaman
yajuya da gudu anma yayita maza yanufeta
sannan yace ” AA–AMIRA” Cak ta tsaya
daga rubutun datakeyi akam withdrawal slip
dinta, hannunta yafara rawa, biron yafado
kasa, cikin zakuwa ya fizgota
[12/12, 10:12 AM] Benaxir Omar:
HANNU DAYA BAYA DAUKAN JINKA NA
BENAXIR OMAR Idonta manya manya tadire
akansa, wani nutsuwa yaji yasauko masa,
fizgotan dayayi rungumota yayi, tuni
hankalin kowa yayi kansu, kowa yayi jigum
tundaga masu layin saka kudi, har gurin
masu laying complain, rungumar dayayi
mata damkota yayi dakarfinsa, irin wanda
uwa taga danta da baya duniya tunda
jimawa, shikanshi yamanta cewa ashefa ta
haramta agareshi, haramun ne agareshi
yataba wani gaba na jikinta, anma inas
yaukam yamanta,Ya matseta don gani yake
zata gudu masa. Hawaye na bin layin
idonsa, sunfi minti biyar ahaka, batayi
magana ba, sannan batayi resistn ba,
yasaketa sannan yakare mata kallo, tabbas
itace, ba mafarki yakeyiba, hannunsa ya
laluma a aljihu yakira faruk tare da cemasa
yayi saurin zuwa ko yatafi yabarshi,
Mutanen bank kuwa juyawa yayi yana wage
hakori tareda cewa “y’all should jubilate with
me, i found my lost wife, we all thought shes
dead, ” Wani inyamuri daga gefe ya matso
kusa tareda cewa “congrats my frnd, you luk
cute together” Kowadai natofa albarkacin
bakinsa, hannunta yajawo suka fito tana
tsaye, yabude mata mota tashiga, anma ta
tsaya. Kallonta yayi alokacin nutsuwa tazo
masa nacewa ashefa tunda suka hadu batayi
magana ba, yace “amira akwai matsala ne?,
ko baki ganeni bane?” Hawaye na bin gefen
idonta tace “babu” Yadauko hankerchief a
aljihunta sannan yashare mata ido, yashigar

da ita motar yazauna [12/12, 10:39 AM]
Benaxir Omar: HANNU DAYA BAYA
DAUKAN JINKA NA BENAXIR OMAR Taana
zaune kanta akasa, wayarsa yadauka yakira
ramlat tana kallonsa, yana cewa ga amira ya
samu, anma shes not d lively amira he knws,
tayi jim sannan tace “kafadawa yan
gydansu?” “A a, am planning to”
“Karkafadawa kowa, keep her, nd bring her
back silently, accomodate her, feed her, nd
let us see wat will happen,nadiya is not
involve in any of these, i think mujanye
karan, on my investigation list na jiya,
abdullahi is my first suspect,” Mikewa yayi
acikin motan yafice don kartaji maganan,
Saida yabar gefen motan sannan yace “Meya
faru” “Abdullahi ne yajawo komi, nd it seems
ba amira ce kadai ba, dey r identical twins,
dax y dakacemin kaganta kuma itane banma
musu ba, subiyu ne, but kaman ita kanta
uwar batasan subiyu bane, right from birth
aka rabasu. Toh kaga wannan dogon zance
ne, u have to come back as soon as
possible,” Numfashinsa dakyar yake fita,
yakashe wayan sannan yajuyo, bata cikin
motan , tuni yanemi kwanciyan hankali
yarasa yafara dube dube. Can yaganta acikin
wata matrix, baka, tana zaune, gun yanufa
tareda cewa “Motarki kenan, kiyi driving
zanbiki abaya, kokuma bar motan nawa
anan muje tare karki subucemin” Shiga yayi
ta tuka su har maitama, wani kaftareren
gida ta shiga gates din dakansu suka budu,
tawuce first gate. Tanufi second gate, nanma
taje tayi parking gun motoccin, sannan
tafito, all dix while cikansa batace masaba,
Fitowansu kenan sukayi hanyar shiga gydan,
falon gydan tashiga, komai coffee colour,
shikanshi yasan wannan gida, sunanshi gida,
zama yayi itakuma ta haura sama, can
saigata tasauko da wani saurayi, shikam
ganin farko yazata balarabe ne, irin bakaken
larabawan nan, yamike suka gaysa sannan

yakoma yazauna, sunzauna alokacin yusuf
yagyra mirya sannan yaace “Naga amira ne,
shine nabiyota, mundade muna nemanta,
kowa yazata ta mutu” Bakin balaraben,
wanda gashin kanshi ta kwanto luff akansa
yace “wacce amira? Ko kana nufin ummi?
Awh. Gaskiya its a long story, but tunda
kazo alhamdulilah komi yazo cikin sauki,
dama har munshirya aurenmu nxt month”
Wani kwarewa da yusuf yayi idonshi awaje
yace “wayedin? Amiran? Toh matar aurece!,
kasan kuwa aure ya haramta ko!,” baitaba
shiga wannan yanayin ba, takaleshi wanda
tunda suka fara maganan batace komi ba,
sannan tace “Bangane matar aureba, wen
aka dauramin aure?, last i knew ko saurayi
bandashi, ” “Amira nidin fa?” ‘Ta ina kaidin,
akwai randa kataba furtamin so ne?,
kataba? If kataba den kazama saurayina,
you can talk but not wen uve neva tried”
Tunda yake arayuwansa baitaba nadaman
rashin furta mata kalmominsa irin na yauba,
yamazaayi ne wani kato daga sama yazo
yace aure, toh zaman lfy taci gidansu!, wata
babbar mata ce ta sauko , kana ganin
halittarta kasan cewa mahaifiyar balaraben
ne!
[12/14, 11:07 AM] Benaxir Omar:
HANNU DAYA BAYA DAUKAN JINKA NA
BENAXIR OMAR takalli balareben sannan
tace “man haza? Fi mushkila awh
mafish?”(waye wannan? Akwai matsala ne
ko babu?). Shidai yusuf yasan yanajin
larabci, hakan ya tabbatar masa da larabcin
yare takeyi. Tafdijam aina itakuma amira ta
nemosu, bai idar da tunaninsa ba balaraben
yamayar mata da amsa “Mafish, huwa aiz
ummi; huwa yuhibbuha (babu, ummi yake
nema, yana sonta), Gyran murya yusuf yayi
anan taxauna tadaga mai hannu tareda cewa
“Sannu sannu, sannu ko, barka!” Bata iya
hausaba, abunda ya ayyana aransa kenan,
don kame kame takeyi, amira ce taje gefenta

cikin harshen larabci taketa mata magana,
larabcinsa baiyi zurfi ba donhaka bai fahimci
bayaninta ba, saidata gama sannan bakin
balaraben yace “By the way sunana
Imran,asalina dan kuwait ne, zama
yakawomu nan saboda aikin mahaifina,
nikuma shine nakarasa makaranta na anan,
wannan kuma mamana ne, batajin hausa
sosai, gwara turanci, ” Yusuf ya gyada kai
sannan yace “bawannan bane damuwana,
nazo daukanta ne nakaita gydansu daga
inda tafito” Yayi murmushi sannan yace “toh
ai gatanan, saitabaka amsa” Amira kif
tabata rai tahade rai wanda baitaba gani
tayiba sannan tace ba inda zataje, yayi
mamaki sosai juyin duniya taki kulashi,
hakan yasa imran yajanyeshi suka fice,
bayanin duniya yusuf yaroki imran yamasa
akan yadda yahadu da amira yaki, acewarsa
amira tahana, Gashi bayason kiran inna,
yatuna abunda ramlat tafada masa. Faruk
yanemo suka tsaya akofar gydan jira suke
tafito su tareta anma kim taki fitowa,
Kwanansa uku ajere yanason tafito sumata
magana, amira taki fitowa gashi saura
kwana shida akoma kotu, dole tayi
collaborating saboda susamu su janye kara,
don shi jikinsa nabasa amira ce tunda
hartaganeshi tace baitaba furta mata kalman
so ba, yayinda ramlat tace zai iya yiwuwa
ba amira bace, twin sistern ta ne, damuwan
shine su rikota komi zaixo dasauki anma
baiwar Allahn nan taki futuk tafito Rana
tahudu suna gefe a mota , sukaga tafito
dasauri yabita. Gudu take kaman zata tashi
sama anma haka yabita, bai bartaba itakuwa
datagane ana binta saitafara canja hanya
[12/14, 12:59 PM] Benaxir Omar:
HANNU DAYA BAYA DAUKAN JINKA NA
BENAXIR OMAR Bin ta yayi ganin zasu
kureta yasa takara gudu, dasauri yasha
gabanta wanda yasa tayi mummunan
tsayawa, itakanta ta zata tamutu, gabanta

yayi mummunan faduwa, dasauri yafito har
ya nufa kanta, bata dago ba ya bude kofan,
a tsorace takalleshi idonta yaciko da hawaye
, yacirota yaciro mukullin motan sannan
yarufe, fizganta yayi yanufi motarsa da ita,
faruq na gaba wajen tukawa yabude gidan
baya yacusata, sannan yashiga yarufo, tana
cewa “mota na fa” bai kulataba haka suka
wuce, can hanyar fita agari suka nufa da ita,
itakam tarasa mezatace , hanyan bauchi
suka nufa, dataga a zahiri bauchi zai nufa da
ita tafara kuka, kokari yayi yadanne ransa
donkar tagane yana tausayinta, kuka take
sosai bawanda yakulata, can dai faruq yaja
wawan birki tareda cewa “meye matsalar
ki?” “Kuyi hakuri ku mayar dani, don Allah
karku maidani bauchi, wallah zaa kasheni
nima yadda aka kashe yaruwata!” Shiru
sukayi musamman yusuf da yarasa yazaiyi
daransa yace “duk lokacin dakika shirya bani
labarin meya faru, meya sameki, sannan ta
ina kuka zama biyu aka kashe daya, anan
zanbarki!, kifadamin wadannan larabawan
daga ina kika samosu” Tayi shiru can tace,
zanfada muku, kuyi hakuri mukoma don
girman Allah” “Bazai motsa anan ba, harsai
kinfadamin komi” Tayi shiru kanta a kasa
sannan tace “Tun some months back, yayah
yazo gida da files yace nayi sighining na
kudi ne, danayi agefe dana karanta naga
Bayanin mutane uku ne aka kasa, 50%
saikuma 25% guda biyu, nadai san nikadai ce
mace daga ni sai yayah, toh yayi saurin
karba don alokacin har matsifa yamin basai
nakaranta ba, sighning kawai zanyi na miko
mishi, dana mika mishi, naje nasamu kawata
mrym maleka dama tana karanta economies
natambayeta ko zata iya min bayani akan
yadda zaa raba mana kudin mubiyu, nafada
mata total dinshi, tamin bayani cewa tunda
shi namiji ne akalla zai dau 75% ni nadau
25%, nazauna nafara bincikena aboye, ta
office dinsu yaya nabi, dafarko nagane mu

uku ne, saidai bansan dayan waye ba, nayi
kokarin nagane nagagara ganewa, saida
ranan dare dare naje office din nafitar da
takardun daya bayan daya, naga ta ukun
sunanta adiya, certificate of birth dinmu mu
biyu, ga kuma muna kama, komi ya
tsayamin, naciresu zanfito dasu, don na
nunawa inna dasafe, harna fita naga wani
yana bina, dasauri nadau mota nadawo,
maigadi yabudemin nashigo, na so gayawa
inna anma saboda wasu dalilai nakasa,
harna kwanta banyi bacci ba inajira safiya
tayi, inna tatashen azatonta nayi bacci tace
narufo kofa, natashi narufe, Can dare naji
anbuga kofan azatona inna ne, sai nabude,
ina budewa naga yayah dawani baki a
gefenshi, sukasamin abu a hanci, nan nafita
hayyacina
[12/15, 10:58 AM] Benaxir Omar:
HANNU DAYA BAYA DAUKAN JINKA NA
BENAXIR OMAR Shidai yusuf yana mamaki,
abun duniya ta isheshi, duk ya tsorata,
tacigaba da bayani yayinda suke sauraronta
“Bansan takamaiman inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login