Showing 15001 words to 18000 words out of 27433 words
yana
kallon yusuf, kotu tabashi daman yayi
tambayarsa dayakesonyi wa yusuf “Malam
yusuf kamar yadda kace amira itace farkon
wacce kake so, sannan nadiya kuma tana
sonka, idan na fahimci maganar kana nufin
nadiya tana son maso wani kenan ko?”
Yusuf yace “ae hakane” “Ita amiran tana
sonka ko bata sonka, sannan kai ko ita
wayake bin wani” “Gaskiya amira tana sona
fiye da yadda nake tunani,sannan kuma ni
nake binta ba ita take bina ba” “Toh amma
acikin yanmatan dakace nadiya ta rabaka
dasu akwai wacce aka taba cewa ta kashe?
Su wancan din dasuke sonka, duk nadiya
tafisune?” “Gaskiya bansan dalilintaba,
saboda nadiya nake kafa tsaro wa amira ina
ganin kaman zata mata illa,” “Anma kasan
kishin mata haka yake, kanason abu dole
kayi kishinsa nadiya tana kishinka ne
shiyasa tayi haka” Yayi godiya wa kotu
yakoma yazauna, su inna dasauran mutanen
sunfara murmushi gani sukeyi ai anfara
samun nasara ganin cewa farzan bai xurfafa
tambayansa, saidai daidaikun lawyern cikin
kotun tare da yusuf shikanshi dakuma ramlat
didnt find it funny, absolutely sunsan cewa
hes up to something, alfarma yanema agun
kotu dazai mika diary din nadiya wacce take
rubuce rubucenta kullum aciki, tundaga ran
haduwarsu da amira ta rubuta, har randa
suka rabu na karshe alkali yasa aka karba
sannan yace kotu taduba, bata boye komi
ba, illa nakarshen shi yajawo hankalin
mutane akai inda take cewa “No matter how
i hate her, how i dnt want to see her exist
she has gone nd left me with a burden i cnt
unleash myself, shes a very good person to
be with, i have learnt a lesson been with her.
May you continue to rest in peace amira. Ill
remember you for d rest of my life, nd ill tek
kia of d person u wish to cherish foreva, (M
sorry bazan samu postn ba sai thursday
insha Allah, inada test a skul, but if nasamu
sarari zanturo muku insha Allah)
5⃣ HANNU DAYA BAYA DAUKAN JINKA NA
BENAXIR OMAR Court tayi shiru kowa da
abinda yake sakawa aransa, masu tausayin
nads nayi, masu Allah shi kara nayi, duniya
budurwar wawa, nads tadawo abun tausayi,
alokacin barr.ramlat ta nemi izinin kotu don
gabatar da shaidanta na gaba,kotu tabata
dama, inda wata budurwa mai kyau tafito ta
tsaya, tayi rantsuwar fadar gaskiyanta
sannan aka fara mata tambaya Ramlat
tanemi tasan sunanta, dakuma alakanta da
nadiya “Sunana hauwa mudi, nadiya kuma
nasanta ne sanadin yusuf, alokacin dana fara
soyayya da yusuf gurin aikinmu daya, anma
nads ita tajawo nadena aiki hatta zaman
bauchi ya gagareni,” “Saboda mefa? Metake
miki haka?” “Kullum cikin razana ni take,
tana barazanan kasheni, saudayawa tasha
so ta kadeni acikin mota, wani lokacin kuma
har gyda take biyoni tacimin mutunci, dalilin
barin aikina kuwa shine nadiya tadauramin
sharrin sata a office, bansan ya akayi ba
nashiga office naga ana binciken jakana
saiga gwal aciki, naji kunya don har kuka
nayi kowa yaki yarda dani, bansan ita tayiba
saidaga baya takirani awaya tacemin kadan
daga aikinta, lakanin sata ba abu mai kyau
bane don office dinmu tuni suka fara kaffa
kaffa dani ana ganina zaafara tattara kaya,
har yanzu illan da nads tamin yana bina, don
dazaran wani yafara nemana zaiji batun
sata” tana fada tana share hawaye, kotun
kowa yafara guna guni, ramlat tayi godiya
sannan tace wa nads ” shin haka yafaru
kokuma baifaruba?” “Yafaru, duk abunda
tafada gaskiya ne” “Amma nads tun farkon
case alkali ya bukaci you should plea guilty,
kinki yarda meyasa kikeson bawa court
matsala bayan kinsan ke kika kashe ta?
Kinrabata da ranta? Ki amsa laifinki kawai
mana” Cikin tsananin bacin rai Farzan
yamike dakarfi yace “objection my lord,
barrister ramlat is forcing d accuse which is
against the law,” Alkali ya nemi da ramlat ta
dakata inda tanemi afuwa takoma tazauna,
farzan yafito yakarewa hauwa mudi kallo
sannan yace Kinason yusuf ko bakisonshi?”
“Ae, na soshi a lokacin” 6⃣ HANNU DAYA
BAYA DAUKAN JINKA NA BENAXIR OMAR
“Da nads tamiki wannan sharrin? Kekuma
mekika shirya mata? Mekika aikata mata?”
“Kawai fadawa yusuf nayi, yakirata yamata
magana a waya,anma batajiba, ” Farzan
yafito da wani takarda sannam yamikawa
court, yace “wannan wasika ce da hauwa ta
turawa nadiya, ina rokon court data karanta
wannan wasikan, ” Aka karba alokacin
hauwa tahada ido da ramlat wacce take
mata alamun meye? Idonta yafito guli guli,
Wasikar ga abunda tace “Nadiya Azzam
Dahar, yakamata kisan duk haukanki, duk
yarintarki, duk rashin hankalinki, bazaki taba
kamoni ba, banda kirki ko kadan,
kindauramin sharrin sata and kina expectn
nashareki natafi? Bantafiba, ina kula dake.
Sannan zakiga sakamako watarana,
zakigane Ruwa bata tsami banza, dankalin
hausa ba saan ta bature bane, yellow fool.”
Court tayi shiru inda barrister farzan yace
“wannan shaidam kadai zatasa court tasan
cewa nadiya tayi laifi anma batayi kisannan
ba, akwai mutanen dasukeson ganin
bayanta, ga daya daga ciki, inason kotu
taduba tagani” Sannan ya matso kusa da
hauwa mudi yace “wasikar taki ce ko baki
takiba?” “Hauwa ta girgiza kai sannan tace
banawa bane, bantaba mata wasika ba”
ramlat wacce ta gane kan maganam tadafe
kanta tarufe fuskanta. Shikenan mudi ta
dama musu alamari Nadiya kuwa wacce take
zaune jin mudi tace bahaka bane yasa
tamike tama buga table din gabanta da karfi
tana kara wanda yaja hankalin kotu kanta
tana cewa “Hauwa y r u lying? F*** ass
bitch , ill kill u!!!!!, munafuka marar mutunci”
rikota akayi kotu tuni ta hargitse Wayyomu,
hauwa mudi is now a suspect
[12/4, 9:15 AM] Adda Bena: 7⃣ HANNU
DAYA BAYA DAUKAN JINKA NA BENAXIR
OMAR Alkali wato shuraim shi yabuga
gudumarsa da karfi wanda yajawo hankalin
court gaba daya kowa ya nutsu, inda ya
tuhume nadiya da simple offence na
distractn masa court, hauwa mudi kuwa fita
da ita akayi, ramlat ta kara bawa alkali
hakuri sannan ta gabatar da shaidanta wato
nanatu gidado, tafito tayi rantsuwa sannan
ramlat tamata tambayoyi “Menene cikakken
sunanki dakuma alakarki da wacce ta
rasu,?” “Sunana zainab gidado, amira
kawatace saboda tun yara muke school
daya!,” “Mekika sani dake tsakaninsu da
nadiya?” “Tundaga ran haduwarsu har ran
mutuwarta nasan komi, nakuma san nadiya
bata sonta, nema takeyi ta hallakata, harta
text da nadiya take mata da barazanar
dauke ranta duk agaba ne.nadiya tayi
alkawarin kashe amira a gabana, kuma
amira bata amsa mata ba, ana saura
kwanaki da mutuwan kuma tazo gida tasami
amira, tace mata tanaso su sasanta anma
amira bata amince ba, don tana tsoronta
kuma tana tunanin wani makircin tashirya, ”
“Nagode” sannan tajuya kan alkali tace
“Dafatan wannan kotu mai basira da adalci
zata dubi wannan alamarin da idon basira
tayi adalci,” Takoma tazauna alokacin kuma
farzan yafito yana murmushi, nanatu bata
kulashiba, illa haushi dayabata, ita yanzu
wanda yake kusanci da nadiya ta tsaneshi
[12/4, 9:43 AM] Adda Bena: 8⃣ HANNU
DAYA BAYA DAUKAN JINKA NA BENAXIR
OMAR Batason abunda zai hadasu, hakan
yasa takejin haushin shi; shikuwa tambaya
yafara mata “Sannunki hajiya zainab, wato
lokacin da nadiya tazo su shirya, kamar
yadda kikace tazone kenan cikin sanyi da
lumana, meyasa kikace tazo da wani
munafurcin, bayan kuma bakisani ba,?”
“Abunda nasani kenan, nadiya bata taba
zuwa da alheri ba,kullum sharri ne” “Akwai
wanda kika sani yake gaba da amira bayan
nadiya? “Babu , amira mutum ce mai
mutunci tana shiri da kowa batada abokin
gaba,” Farzan yayi murmushi sannan yace
“anma adan binciken danayi nasamo cewa
kin So yusuf” ba itaba hatta mutanen dake
gurin saida suka tada surutu, kowa da
abunda yake fada , tayi murmushi sannan
tace “Sosaima, dani tafara ganin yusuf a hall
ana wani training, tun lokacin nafara sonshi,
anma ban bari tasani ba, saboda son da
take masa yayi yawa, zan iya hakura nabar
mata, tafini sonshi, kuma tun alokacin nabar
sonshi din, bankuma kullaceta ba” Farzan
yakalli alkali sannan yace “ah gaskiya, kotu
ya kamata tadubi wannan shaidar dakyau,
itama tanasonshi, sannan kawarta ne, kuma
kunsan karin hausa da akecewa makashinka
na kasanka, baikamata kotu tadau shedanta
da muhimmanci ba, saboda itama yakamata
tashiga sahun wanda zaa zarga” inaso kotu
tabani dama nakara bincike game da ita da
shaida ta biyu, Yakoma yazauna, inda alkali
ya amince da bukatunsa, sannan yace zaa
dawo da sati uku, meanwhile yanaso a tsare
hauwa mudi, don bincike akanta, anan kotu
ta watse, nadiya tamike cikin kuka anma
haka aka wuce da ita, abdullahi ne yaje gun
yusuf don masa godiya alokacin farzan yazo
wucewa, yamika musu hannu sannan yace
“Yayan amira rgt?” “Ae” “I hope zaka zama
shaida don inada dan tambayoyi na” ramlat
ne ta katse shi tahanyan cewa ” dat depends
on me ” Yajuyo yana murmushi sannan yace
“i see. I just hope you dnt use your emotions
on your client, we shall meet
HANNU DAYA BAYA DAUKAN JINKA NA
BENAXIR OMAR Shiru tayi, tabbas yasan da
maganan son datakewa yusuf, Allah yasa kar
yayi amfani da wannan daman akanta, kowa
hanyansa yanufa, yayinda abdullahi yaja
inna sukayi gyda, inna mamaki yagagara
barinta, duk tunaninta ya kare, ahaka bata
daina kuka yar lelenta tarasu, tanacikin
tashin hankali, suna isa gyda, abdullahi yayi
wanka ya kwara bacci ta kwasheshi, Ramlat
tayi wanka tadauko abincinta rike da cokali
babu tunanin dabatayiba, tasan duk hujja
suna hannunta, amma da alamu akwai
abubuwan dake boye dabatasaniba, tana
dama cokalin tagagara hadiye wanda ta sa
abaki, jitayi anyi sallama,tadago kanta
ahankali sannan tamayar, yana tsaye bai
zaunaba yana kare mata kallo, jikinta a
sanyaye take. Kuma yasan matsalarta saidai
bayason abinda zai dameta ayanzu ko
abunda zai hadasu fada, shi damuwanshi
abdullahi yakara masa maganan yana sonta,
donhaka zama yayi agefen kujeranta, sannan
yagyra murya yana cewa “Sannunki da aiki,
thnk u soo much nd God bless” Bata
amsashiba, itadai tasan cewa tafara
regreting abunda tayi, duk iya kokarinta na
danne Zuciyanta, kishine yake neman
turnuketa, amira dai tamitu anma kishinta na
cinta, ga wai nanatu , dat small gel, itace
wai take sonshi, wani zuciyar yace mata
“saikingama taimakonshi kinrufa masa asiri,
yazo yace yanason wata,” dafa kafadarta
yayi dasauri tajuyo, “Ina magana kinyi shiru,
watz wrong?” Janyeshi tayi ajikinta, tareda
cewa “tek note! Niba muharammarka bace”
shiru yayi ya janye jiki. Sannan yamike “Ull
not regret helping me, and abdullahi yace na
isar miki da sakonshi, he has a crush on u”
HANNU DAYA BAYA DAUKAN JINKA NA
BENAXIR OMAR Mikewa tayi ta ture plate din
gabanta , ranta abace tace “well, tell him
tnx,” tafice tabarshi agun. Daki tashiga
tazauna ta sha kukanta, tari ya turnuketa,
tuni tamike tayi hanyan toilet, jini ne yafara
fito mata, hankalinta yatashi, tawanke
bakinta tadawo tazauna akam gadon, she
just wished , just once in her life yusuf yace
yana sonta, bata taba tsanan soyayya irin na
yanzu ba, data kasance very close da yusuf,
soyayya bata dadi, inhar kai kake kidanka
kake rawanka kai kadai, tadauko wayamta
tana kallon hotonsa, yusuf yahadu iya namiji,
da ace amira na raye, itace zata samu
daman aurenshi tunda ita yakeso, anma
Allah baiyiba, kuma baida alamun niyyan
canjata da wata, soyayyan shi naneman
hanata numfashi, Rike da wayan tayi bacci,
mahaifiyarta ce tashigo, takalleta, ganin
bacci takeyi ta gyra mata kwanciya harzata
juya taga gefen bakinta da jini, nan da nan
tagane, arazane tafito tadauko wayanta,
likita takira tareda cewa “nikam dr.ciwonnan
fa inaga haryanzu wlh” tanayi kaman zatayi
kuka, yace “Ramlat tana da taurin kai, tana
nema ta hallaka kanta da damuwa, namata
magana taki, treatments dinma ba complete
takeyiba, don Allah kitaimaka tasamu
abunda takeso” Shiru tayi takashe wayan,
hawaye nabin idonta, ko kadan bataso tafara
case dinnanba, saboda tasan halin yarta,
anma tadaure tadanne tace saitayi, meye
amfanin farantawa wanda kasan bazai
faranta maka ba? Wanda baima san
tanayiba, Itadai da ramlat zata yarda ta auri
dan uwanta muhd wanda suke kira da Aju,
anma taki yarda, aju yayi iya kokarinsa
anma ramlat ta kafe itakam sai yusuf
Shikuwa koda yafito daga gidan bai nufi ko
inaba sai office dinsa. Gaba daya kanshi
tadaure, damuwansa adaure nadiya ko
hankalinsa zai kwanta wayansa ce tayi ruri
yaduba sannan yaga baigane numbar ba
“Don Allah da yusuf nake magana?” “Ae”
“Ok, toh , maganan rasuwan amira ne, inaso
ne nagayamaka wani abu dabaka saniba,
akwai kudi da aka saka da sunan amira na
miliyan 25 na gadonta, kuma babu kudin
yanzu , nagayama ne ko zaka nemo
lawyernka kuzo kuji kundin labarin”
[12/8, 9:18 AM] Bee: 1⃣ HANNU DAYA
BAYA DAUKAN JINKA NA BENAXIR OMAR A
Firgice yamike sannan yace “wake magana?”
“Daga company din babanta” “Gani zuwa,
text me address” Keyn motanshi yaja, wani
horn dayayi saida maigadi yayi saurin
budewa, yanakan tafiya yaga msg tashigo
masa, yaduba abun mamaki kuma yaga kobi
theatre, yadaisan company na old gra, meya
kaishi theatre. Nan da nan yacanja akalarsa
zuwa kobi theatre da zummar son ganin
meya faru, gurin babu haske ko kadan,
hasken wayansa yakunna, yaringa dube dube
, takardu yagani a zube, hankerchief yaciro
yasa yadauka, hanyan motansa yanufa
yashiga ciki yazauna yafara budewa, tabbas
gashi account din anbude twenty years back,
anasa kudi kowani wata,,da sunan Amira aka
bude, wani abun mamaki shine baataba cire
ko sisi daga ciki ba, sai kwana hudu daya
wuce, yaduba yaga ancire dubu dari, jikinsa
na bari yajuya hanyan gyda, ramlat yadauka
yakira, baa daukaba don lokacin tana gaban
likita, hakan yasa yanufi gyda gun abdullahi
da inna don jin bayani, abdullahi yayi
mamaki sosai inda yace “Amira ce kadai
takeda access da account dinnan, saboda
kafin ta mutu dakaina nakirata tayi sighning
din takardun suka fita daga hannuna, naje
namata applyn atm, ” Yusuf yaja numfashi
sannan yace “Definately wanda suka saceta
suka kashe su suka cire kudin, ko hala sun
tattarata dashi duba dakinta mana” Inna ta
girgiza kai sannan tace “anya dakin zai shigu
kuwa?, saboda hatta kayan sawanta na
wardrobe nabayar komi na ajiye yadda yake,
kuje kudubu dai” Dakin suka nufa, sukahau
bincike, abun daya matukar basu mamaki
shine duk wani personal abu da mutum
zaidauka babushi, babu documents din bank,
hatta credentials dinta dake ajiye adakin
abbansu daya rasu abdullahi yaje yaduba
babu!, Tashin hankali!, nan da nan yusuf
yasha jinin jikinsa, yakalli inna yace “hajiya,
acikin gidannan akwai assasinate, wanda
aka hada baki dashi, kuhado kan masu
aikinku kaf!, barinje nadawo” Dare yarufa
aamma ahaka yadebo sojoji a barrack dirka
dirka guda hudu, kafin yazo masu aiki tunda
kan mai shara har maigadi, su takwas,
yazaunar dasu yafara magana cikin tsigan
lallami “Acikinku waye aka bashi kudi. Yaje
yakwaso wasu takardu adakin marigayiyan?
Da dakin mahaifin?” Kowa tsit yayi hakan
yasa yusuf maimaita tambayansa, saidai
yaga ko kadan basuda niyyan magana,
hakan yayi magana wa sojojin yace su
matso daga kusa, Masu aikinnan sunbugu
anma bawanda yayi magana donhaka yace
duk gobe police station zaakaisu, jin haka
dasauri saudat, wacce take share share tace
“inada magana” Kowa hankalinshi yayi
kanta, tana zubar da kwalla tace “Bayan
rasuwar ranan nashiga dakin naga mutum,
kuma tsiffan macece, ina shiga aka rufe
idona sannan ahankali akayi magana akan
idan nayi ihu ko nagayawa wani zaakasheni
nima shiyasa nayi tsit da bakina, kuma abu
aka diba, don harda akwati” yusuf a tsaye
yamike tareda cewa “nadiyan nan batada
kai, wakuma tasamu?, zan kwakulota, duk
wanda taturo ai zansani” [12/8, 10:34 AM]
Bee: 2⃣ HANNU DAYA BAYA DAUKAN JINKA
NA BENAXIR OMAR Mikewa yayi a tsaye
sannan yace “inna kike ki kwanta, zanje bank
din gobe, zasumin bayanin komi agunsu
zansamu, sannan wannan wanda yamin text
din yanunamin gun, nakira numban akashe
shima zanje mtn office subincikomin,
abdullahi ne yayi godiya, yarako shi har
motansa, yashiga yayinda sojojin ma suka
shiga tasu sukayi gaba, Yana isa gyda
yarinkabin takardun daya bayan daya,wani
matsanancin son amira nashigansa, yayi
nadama sosai, nadaman rashin gayamata,
nadaman rashin sanar da ita son dayake
mata, duk don gudun wannan ranan gashi
ranan tasameshi, tashin hankali tamishi
yawa, tunda tafadi tamitu bai kwanta yayi
baccin sama da awa uku ba, hankalinsa yaki
nutsuwa, zama yayi a kofar gyda kafin yayi
horn ya sunkuyar dakansa. Yashaa kukansa,
(y d fyn guy dey cry now?, ) idonshi tayi jaa
maigadi ne yaleko ganin motan dasauri
yabude gate. Hakan yasa yakunna motan
yashiga ciki. Saidaya kimtsa kansa don kar
kannensa sugane halin dayake ciki sannan
yanufi cikin gidan, kazrat na zaune tana
ganinsa tamike dasauri don karban jakan
dake hannunsa, baiyi maganaba haka itama
tabishi. Ta ajiye masa a saman reading table
dinsa sannan tajuya zata fita, yana daga
zaune akan gado yace “kazrat” Cak ta tsaya,
tajuyo sannan takoma tanemi gu agefensa
tazauna,don tagane magana yakeson mata,
tana balain son yayan nata cikin sanyin
murya yafara magana “Kintaba son mutum
yadda kowani numfashi saikinji shi aranki?,
kintaba son mutum yadda kowani juyin bacci
saikin yi tunaninsa, infact bakya iya bacci
akanshi?,” Shiru tayi don ta fahimci inda
magananshi ta dosa, “Yaya kayi hakuri,
duniyan nawa take balle abunda ke cikinta,
Allah yajikanta yamata rahama, abu daya
zaka iya mata yanzu a matsayin mai sonta
kamata addua, don Allah yaya kadena sa
damuwa aranka” juyowan dazatayi taga
hawaye fal a idonsa abunda bata taba
ganiba sai akan amira, lalle yana sonta, toh
shima inbandashi yazaayi kanason mutum
baka nuna masa, saida batanan zaifara
haukan so, itadai lallabashi tayi tamike
tafice, ranan kwana tayi tana tunanin hanyan
ceto yayan nata, tassn yanzu mata biyu ke
sonsa kuma zasu iya taimakonsa, nadiya da
ramlat, toh bawan Allahn nan ya tsani
nadiya dongani yake ita tayi kisan, alhali ita
jikinta na bata ba itabane, akwai boyeyyen
alamari a maganan nann, donhaka ramlat ce
last option, shima yusuf baiyi bacciba
yakwana da fargaban son sanin wayene? He
just hope nadiya ce tasa akayi ko itama zata
dauwama a prison taji yadda yakeji aransa,
Karfe goma nasafe yafice daga
gydan,Zuwansa mtn office suka ce saiya
hado da yansanda, hakan kuwa yayi , suka
masa tracing layi last usage a kobi theatre,
sannan registrrn layin na mace ne, itama yar
tsohuwa haka, agarin bajoga gombe, nan da
nan yusuf yagane cewa karban layi sukayi,
yaji haushi donhaka yasallami yan sandan
yanufi bank, don dubawa, sunbasa assurance
cewa ae lallai, ancire dubu dari thru bank
withdrawal, yabukaci information