Showing 1 words to 3000 words out of 33733 words
Chapter 1 - BAYAN GANGAMI Part1 Complete by Ummu Heebah.pdf
*BAYAN GANGAMI*
*NA UMMU HEEBBAT*
*MANAZARTA WRITES ASSOCIATION*
PG 1
Duk da irin tsohon cikin da yake jikina, bai sa na fa sa gudun da nake ba. Saboda ina yin sa ne
domin ceto rayuwata wajen ganin na tse-rewa mugayen y'an ta'addarta da suka cimma garin
mu. Hannuna rike da hannun yarona na biyu. Mutanen da muke gudu da su da yawa sun
tsaya. Saboda wahala yasa na dakata da gudun da na ke yi a wannan dajin da muka kusa
cimma wani kauye. Tsayuwata ke nan Yarima yarona ya fara kukan ƙishirwa saboda zazzafan
zazzaɓin da yake jikin sa! Ganin babu wani sarki sai Allah ya sa ban nemi shawarar a bokan
tafiyar ta wa ba, na sake daukar hanya domin na ƙarasa ƙaramin kauyen da nake hango wa ko
zan samu ruwan da zan bawa yarima ya sha a wannan halin, tunda na san bani da ko biyar a
irin wannan lokacin da muka riski kan mu. Kuma koda ina da ma ba mai sayar da ruwa a
wannan yankin da muke ciki. Haka na ƙarasa bakin ƙauyen da yake dauke da gidajen da ba su
wuce na ƙidaye su ba. Amma a binda na riska na bakin ciki sai da ya sa na ji cewa da ma ban
bar garin mu ba na zauna a chan y'an bindiga sun hallaka ni. Saboda kowanne gida na shiga na
nemi alfarma da su bani ruwa na bawa yarona sai su haɗe min rai su juya yare sannan suce ba
suda shi. Tun ina ganin abin kamar wa sa har na kusa karaɗe garin dai amma amsa ɗaya ce.
Jikin yarima na sha fa naji yadda ya sa ke dau kar zafi ga kuma yadda yake ta faman mai-maita
ruwa a bakin sa, tuni ruwan hawayen da ke cikin na mujiyata ya fara tunbatsowa zuwa kan
dan-damalin fuskata! Tashin hankalin shine ina za ni ? Baya zan koma da nake jin sautin
bindiga har yanzu ko kuwa gaba zan ƙara na nemi ruwa ? Shin idan na yi gaba zan samu ruwan
ko kuwa zan ta tafiya ne cikin daji har mu mutu a hanya da ni da shi? Tambayar da zuciyata
take ta faman je fo min ke nan. Amma sai na dauki kawai na yi gaba a bina tunda Allah yana
tare dani. Da wannan tunani na ɗaga ƙafata da ta yi min tsami na fara tafiya ina jan yarima
yana biye da ni cikin ƙarfin hali saboda ƙarancin shekarun sa basu kai ya yi wannan tafiyar ba
tunda gaba ki ɗaya shekarar sa shidda ne. Tafiya mai nisa mukayi har muka riski wani kauye
na gangara cikin sa domin gwada sa a ta wajen neman taimakon ruwa ko zan samu. Cikin iko
na Ubangiji matar ta bani ruwa na bawa yarima ya sha, wanda galabaita duka ta sanya shi ya
ke la amai a ta ke a wurin, domin cikin sa ba komai. Cike da jarumta na zauna daɓas a wurin
na janyo shi jikina na ce; " Yarima Allah ya ba ka lafiya, rayuwa tana cike da tashin hankali kai
ma har Allah ya nuna maka yadda duniya ta sauya ina kuma wannan abin cikina da bai zo
duniya ba, shi kuma ko ya zai sami duniya idan mun rayu." Na karashe maganar ina matsar
kwalla.
Matar da ta ba mu ruwa ta ce, "Baiwar Allah kuyi hakuri daman kowanne ɗan Adam da tashi
ƙaddarar sa a rayuwa."
Murmushin ƙarfin hali na yi kawai bance komai ba na kishin giɗe a wurin na kalli yadda yarima
ya ke fidda wani irin numfashi mai tururi, zuciyata kuma tana tunanin ko ina su mamana suka
fake a wannan lokacin .
Kallona matar ta yi kamar ta san abinda yake zuciyata ta ce, " Ina maihaifiyar ki da sauran 'yan
uwan ki?"
Murmushin ya ƙe na yi wanda ya fi kuka ciwo na ce "Ban saniba wallahi na rasa su na rasa
kowa na wa a wannan lokacin, kawai fatana abinnan ya lafa na koma gida na ga halin da kowa
ya ke ciki. Hatta babban yarona da karamar ɗiyata ban san a wacce duniya suke ba, saboda
sun fita makaranta abin ya faru, shi ma wannan da kike gani rashin lafiyar sa ne ya sa bai ta fi
ba.
Na kai ƙarshen zancen ina wani irin kuka mai tsuma zuciya .
"Kiyi hakuri in sha Allahu komai zai dai-dai ta ki koma gida.
Da irin wannan kalaman ta samu na daina kuka na samu nutsuwa harma ina tunanin tunda
ƙarar harbe-harben ya lafa an jima zan iya ko ma wa cikin garin mu.
Sai dai wani abun mamaki ko awa ɗaya ba a yi da yin shirun namu ba abu ya sake tashi
sabo fil! Domin wannan karon harda irin manyan roket ɗinnan ake harbawa wanda kararsu
kamar ta aradu, domin har haske suke bayarwa kafin su faɗi inda a ka je fa su.
Ga kuma yadda abin ya ke sake tun karo ƙauyen da nake, ganin Mutane da na bari a baya
yuyu guda sun zo suna wucewa ya sa na gane cewa tabbas baya ba lafiya abin ya sake
barkewa, da kyar wata mace ta na rike da yaronta ta tsaya ta min bayanin cewa ai 'yan ta'addan
sun ce kowa ya bar yankin wurin zasu sanya bom saboda 'yan ta'adda shine ake ƙara yin gaba
dan kaucewa wannan lama..... Bata ƙarashe min batun ba a ka saki wani harbin da sai da
dukkan mu muka zube gurin durƙushe! Wani irin murdawar da cikina ya yi a wannan lokaci sai
da na zaci ko haihuwa ce zanyi.
Bamuga ta zama ba dan haka har ba fullatanar muka dauki hanya ta daukamin yarona wanda
a wancan lokacin ma wallahi bani da tabbacin halin da yake ciki kawai dai ina ta fama da abin
cikina yadda na ƙuda ta ke taso min a cikin dokar dajin da muke tafiyar kurame .
Jin ƙafafuwan nawa sun riƙe ya sanya min tilas na tsaya a wurin tuni na durkushe bisa
guiwata ina numfar- fashin wahala. Kadan daga ciki suka tsaya saboda tausayin halin da nake
ciki wasu kuma sukayi gaba.
Mun tsaya ke nan wani jirgi ya zo yana faman shawagi a kan mu ga shi kuma zumbutun sa
wuta ce jajir ya ke shirin fiddawa! Ganin haka yasa wasu suka kwashi gudu, na dubi
bafullatanar da ta ke dauke da yarima na ce ku gudu ku barni kar su kashe ku dan Allah!
Wanda hakan ya yi daidai ta fashewar fayar haihuwa ga kuma jini ya yanko saboda abinda ya
ke cikina yake son fita duniya..........
PG 2.
Ganin ba wani sarki sai Allah ya sa na sa ke bajewa a wurin domin bawa yaron cikina damar
fitowa duniya. Ya yin da su yarima suka yi nisa da gani na, haka kuma ya yi daidai da wannan
jirgi ya fara shan manya manyan harbi da ga yan ta'addan Da ke gefe da mu.
Ba zan iya cewa na mutu ko ina ra ye ba! Saboda tsantsar firgici da kuma a zabar ciwon na
ƙudar da ya ka ma ni. Amma duk da haka Sha wuya bai fasa zuwa duniya ba, sunan da na
laƙabawa yaron cikina ke nan tun kafin ya zo duniya! Daidai haihuwar shi dai dai isowar yan
bindiga wurina, cike da izza guda daga cikin su ya dube ni ya ce, " Ke ba ki tsorata ba ne da
baki gudu ba?"
Cike da firgici na ɗago na mujiyata na dube shi, na rasa ma wacce irin amsa zan bashi,
saboda na fahimci ba makaho ba ne kuma ya ga halin da na ke ciki, shin to kuma mai ya ke son
na ce masa? Jin ƙarar wani abu mai kama da aradu cikin kunnuwana shine ya sani jin ina
neman ma na fita a hayyaci na. Ya yin da shawuya yake ta faman zabga uban kuka jiki duk jini
ga kuma cibiyar da ba ta samu Alfarmar rabuwa da shi ba. Ni kuwa daga wannan lokacin na
zama sumammiya.
Ban san ya ta kaya ba na farka da ga doguwar sumar da na yi na ganni gefe guda kuma
shawuya an raba shi da cibiyar . Ya yin da wata mata ke ta faman sa ke naɗe shi cikin tsumma
take saboda yadda iska ta ke ƙaɗawa mai sanyi, kallon na tashi ya sa ta ce da ni "Sannu da
zuwa wannan yanƙin na mu, muna farin ciki da samun yar'uwa, Allah ya raya mana tukur domin
wannan shine sunan da shugaba ya ce na sanar Miki an saka masa."
Wani irin mashi naji ya chaki zuciyata da na ga no inda na ke, tuni na zabura daga kwanciyar da
na yi duk da irin wani irin a zaba da na ke ji daga ƙasa na amma bai hana ni zama ba! Shin
yan'ta'adda ne suka ta ho da ni? Ina yarima da ba fulatana? Ina mijina da zulfa'u ɗiyata ? Ina
mamata da Abbana da sauran yan'uwana? Shin a wanne hali su ke idan sun koma gida sun
rasani? Irin wannan tambayoyin na yi ta jifan zuciyata da su wanda bani da mai amsa min su,
na sake cewa, Lalle BAYAN GANGAMI a kwai wata ƙura!!!
Domin ko ya ya ne tabbas a kwai wani tashin hankali da yake faruwa a baya. Ga kuma wanda
zai faru a nan! Dan ko giyar wa ke na sha ba zan ra yu a wannan dajin ba ! Na ƙarashe
maganar zuci tare da zubar wasu azababbun hawaye Masu zafi.
"Idan kin gama tunani zuci zaki iya kar ɓar Tukur ki ba shi nono ya sha kafin ya illata da
yunwa."
Sautin matar ke nan da ya riski kunnuwana, ƙuru na mata ina ƙare mata kallo. Dan haka sai ta
yi murmushi ta ce, " Na san kina mamaki ne a kan ya a kayi na san tunani kike ko, na sani
tabbas! Saboda ko wa idan ya zo sai ya yi wannan tunani ka fin magana. Amma ke na fi jin
tausayin ki saboda ɗanyan jegon da ya ke gare ki.
"Tofa!" Ita ce kalmar da na furta a lokacin da ta gama kwararon zancen na ta. A fili kuma na ce,
"Bani shi nan." Na faɗa ina miƙa mata hannuna.
Miƙomin shi ta yi na ƙarɓeshi ganin yadda ya ke tsula kukan wahala!
Cike da tashin hankali na San ya shi a nono ina jin ɓakin ciki idan na tuna na haihu ba a cikin
ɗangina ba! Kuma ba wani na wa kusa! Saboda yadda muka ci burin shan suna nida yan
uwana.
Yadda ya ke shan nonon yana zuƙarsa ya sani na ji wani mugun tausayi sa ya kamani, idan na
tuna a gida ina haihuwa tun a asibiti na ke bawa yaro nono ya sha. Amma wai yau nice da
haihuwa ban san ma adadin a wannin da na haihu ba tare da na kalli jaririn ba, bare a yi zancen
shan nono. Allah kaine gatana a wannan wurin da na fa ɗo, Allah ka taimake ni na kufce zuwa ga ahalina!
Na karashe maganar zucin da zuƙar majina.
"Ya sunan ki."
Ita ce kalmar da ta faso cikin kunnena."
Kallon matar na yi na ce, "Sunana Kubra."
"Madallah Kubra ina Miki fatan alheri a wannan kwangon da zamu rayu abin da na ke son na ja
hankalin ki shine, kawai kiyi biyayya a zauna lafiya . Saboda gidan nan a kwai mata dayawa da
maza kuma kowa da mijin auren ta! Kuma ke ma na san kwanan nan zakiyi sabon miji."
Cike da fargaba da taraddadi na bude baki da hanci da idanu duka ina kallon ta! "Sabon miji
kuma."
Na watsa mata wannan tambayar.
Murmushin ta yi ta ce "Tabbas! Kuwa domin mutum baya sati ake daura masa aure."
"To ai ni ina da miji kuma bamu rabu ba."
"Ke ki ka san haka, abinda na sani kawai ko wa ye mijin ki idan har kika zo gidan nan to kin
gama auren sa!"
Tashin hankali wanda ba shida rana!!! Shine abinda na iya furta wa a zahiri.
"Na shiga uku ni Kubra ta ya zan auri wani bayan Nasir yana da rai kuma bai sake ni ba?"
Bata bani amsa ba jin motsin tafiyar mutum zai shigo cikin ɗan ke wayen.
Dan haka daga ita har ni mukayi gum da bakin mu, har ya shigo yana rike da wata zungureriyar
bindiga wanda da za'a gwada tsayin ta da yaro ɗan shekara goma, to da tabbas zasuyi ɗaya!
Dogo ne kakkaura, mai ƙaton hanci da kuma wargajejen baki, ga shi ba fara'a. Cikin wata irin
hausar sa kwaɓaɓɓiya wacce ba zan ma iya ga ne ainahin yaren sa ba ya ce, "Kausar! Ka
sener masa da dokokin gida ko ya ya."
Matar da ya kira da Kausar wannan wacce ke tare da ni na duba yadda na ga tana ta faman
karkarwar amsa masa kamar haka, " O..oo OGA yanzu na ke ..na ke shirin sanar mata
sabo......."
Bai bata damar ƙarasawa ba saboda wata uwar tsawar da ya daka mata, ba ita bama ni kaina
sai da na yi dan karamin suman zaune, dan lokacin da na dawo hayyaci na na fuskanci
shawuya bisa ƙasa abin sa, a she wai firgitar da na yi ce ta sanya shi ya wantsalo daga cinyata.
Amma da ke ya ci sunan sa sha wuya ko kuka bayyi ba. Ya ce , "Keeee mahaukaciyar ina ce!!!!!! Zaman me kike da ita tun ɗazun? To maza ki sa ta
sanya ɗanta a inda zata San ya shi cikin jikin ta ki Kai ta gurin OGA gaba ɗaya."
Da to ta amsa masa cikin in ina har ta na yi tana russuna wa kamar zata hantsila.
Cike da mamaki na ke tambayar kaina " Wato bayan wannan ma a kwai wani OGA gaba daya?
To shi OGA gaba dayan kuma da wacce siffa zan ganshi? Yau na shiga uku na lalace ga shi ya
ce na sanya dana a inda zan sa shi, shin ba zan tafi da shi ba ne ko ya?.
Ashe duka maganar tawa ta fito fili,sai ji na yi Kausar ta ce, "Yana nufin ki sanya shi cikin
hijabin ki ki ɓoye saboda ai ya tausaya miki ma, domin idan wani ko wata daga yankin nan suka
ganshi to zasu iya cewa ya yi musu ki basu, kuma tilas ki bayar ɗin, domin gidan duk abinda ka
ne ma kana samun shi."
Kamar wata so kuwa na zama a gaban ta na ce "Ban gane ba! Shin wai kina nufin shawuyan
zan bayar wanda ko suna ba'ayi ba?"
"Tabbas haka ne maganar amma idan kina ganin wasa ne to ki gwada ki ga ko zaki dawo da shi
idan bayyi wasu iya ye ba."
Ta mayar min da amsa tare da miƙamin wata hijabi mai kauri da girma.
Tsabar mamaki ma ban iya cewa komai ba, sai kuma na tuna maganar ta ta karshe na ce, " Na
ji kince komai mutum ya ne ma yana samu ko?"
Kallona ta yi ta ce"tabbas haka ne."
Cike da jin daɗin amsar ta harwani saukar ƙaramin wani dutse na ji daga ire-iren duwatsun da
suka sanya zuciyata ta yi min nauyi wani ya sauƙa da ga ciki. Cikin karsashi da zumudi harda
wani karya murya na ce "To dan girman Allah idan muka je shi wa jen OGA gaba ɗayan ki nai
mamin Alfarma a barni na koma gida."
Wata irin dariya ta bushe da ita wanda sai da na dauka ma ko tana da iska ne ko kuma iskar ce
kanta sannan ta ce "Da ana iya samun wannan damar da baki zo kin samu kowa ba. Dan haka
wuce muje kawai kuma kar ki kalli kowa bare wani ya yi yunkurin rabaki da yaron ki."
Tana gama fadar haka ta kama hannu na ɗaya muka fita ya yin da hannuna ɗayan ya ke rike da
shawuya cikin hijabin.
Mutane iri iri ne zaune tanti tanti maza da mata kowa yana harkarasa da manyan bindiga,
mazan basu da kyan gani ko kusa. Tunawa da na yi da maganar ta na cewa kar na kalli kowa
ya sanya na yi saurin kai kaina ƙasa.
Amma jikina yana bani ana kallon mu ko ina saboda yadda idanun jama'a suke yawo cikin
jikina kuma daidai lokacin shawuya ya fasa wani irin kuka wanda ya ja hankalin jama'ar wurin
duka suka dube mu har wani daga cikin su mai rike bindiga ya yi wani murmushi ya mike tsaye
ya zuba min na mujiyar sa.
Cike da halin ni y'atsu na tsaya kamar wanda ƙwai ya fashe min a ciki ya yin da Kausar ma ta
kasa gaba ta kasa baya. A zuciya ta na ce yau na shiga uku idan suka karbi shawuya kuwa
tabbas zan mutu a gunnan!!!! Saboda shine kawai na ke da tabbas din cewa zan kallah a
gabana tunda sauran ban ma san halin da suke ciki ba........ Wanda ya yi dai dai da sake
hautsinawar sa a cikin shijabin.............
PG 3
Duk da irin tsoran da ya riski zuciyata bai sa