Showing 21001 words to 24000 words out of 33733 words

Chapter 8 - BAYAN GANGAMI Part1 Complete by Ummu Heebah.pdf

27 Apr 2025

2101

"Me ya haɗa ka da Kubra? Wa ya
kawo ta nan? "
Ta jera masa duka tambayoyin.

Sanin cewa Hajiya mace ce mai kishi Dan haka tuni ya shirya irin ƙaryar da zai mata.

"Ban san ya akayi ta zo ba, kuma abinda ya ban mamaki shine yadda ta hanani ta fiya gare ki
jiya ban san irin ƙarfin asirin ta ba."

Ya faɗa cikin muryar kuka wacce tuni Hajiya ta ruɗe duka tunanin ta ka sa gane mata wannan
shiryayyiyar magana ce, wanda dukkan mai hankali ya kamata ya gane ƙarya ce domin idan ba
rami mai ya kawo rami? Amma saboda tsantsar kishi irin na Hajiya ga shi ta ji ya ambaci asiri
da son rabashi da shi ai bata yi wani tunani ba ta nufi kubra cikin damuwa, ita kuwa Kubra bata
ce da ita komai ba saboda ya riga da ya ɗaure ta da jijjiyar jikintaTa na zuwa wurin kubra bata
ɓata lokaci ba ta wanke ta da mari hagu da dama.
Wanda ya sanya kubra zubar wasu hawaye Masu zafi, amma kuma bata da bakin magana.
Hajiya ta fara mata masifa, "Lalle tsintacciyar mage bata mage! Ni kubra! Ni zakiwa haka? Duka
alherin da na miki, da kar ɓar da na miki na baki wurin kwana sutura abinci! Duka da abinda
zaki saka min ke nan."
Jin kalaman ta duka sai suka sanyawa zuciyata damuwa na ji kamar da gaske na aikata
mata laifi, cikin ƙarfin hali na bude baki na fara mata magana cikin dusa shewar murya.
"Hajiya dan Allah ina son ki saurare ni, bazan yi ƙoƙarin ka re kaina ba a gare ki domin ba
lalle ne ki fahimta ba. Amma sai dai yadda na same ki mai taimako na ji matukar baƙin ciki da

kika kasan ce mai watsar da ladan ki tun ba ayi nisa ba. Dukkan wanda ya yi abu domin Allah
koda anbi shi da sharri ba zayyi go ri ba. Idan har domin Allah a kayi , amma duk da haka ina
roƙon Allah da ya bar miki ladan ki, saboda tunda na faɗa halin da na shiga ba wanda ya min
abinda kika min na alheri kamar ki. Dama mu mata muna da wannan raunin duk yadda muka kasan ce da saurin tausayi amma
ba mu da wuyar zubar da ladan sai mu fara da ba gori ba.

Amma ina roƙon ki dan girman Allah taimakon na karshe da zakiyi min ki fitar da ni cikin
gidannan, sannan ki tuhumi mai gidan ki domin bai kamata yadda kike da hali na gari kin zaune
da wanda baki san ko waye ba."

Na karashe maganar cikin kuka ina zuƙe majinar wahala.
Tunda na fara magana Hajiya bata ce komai ba kuma duk jikin ta ya mutu da magan ganu na
dan haka shiru ta yi tana nazarin kalamai na. Ganin haka ya sanya Alhaji zabura min da cewa.

"Muna fuka wato har kina da bakin wa'azi? Ke ce fa kika zo da kanki har kina cewa a nuna
miki hanya? Ai daga nan sai gidan gyran hali."
Hajiya wuce muje idan munje Chan ta faɗa Miki yadda ta shigo .

Ita dai Hajiya kasa magana ta yi, har sai da ta jinjina lamarin a zuciyar ta sannan ta ce , "Ko ma
me ne ne yanzu ta bar mana gida bana son sake ganin ta bare ma mu yi zaman shari'ar har ta
samu damar rabani da kai ɗin. Dan haka kawai yanzu ta bar gidan! Ta faɗa cikin faɗa da masifa
. Ganin haka Alhaji ya yi kanta ya fara faɗin "To muna fuka a yi gaba maza yallah ! Allah ya so ki
da kin shiga uku! "
Ita kuwa kubra ba ƙaramin daɗin ta ji ba da jin kalaman Hajiya dan haka ta goya shawuya ta
fara shirin ta fiya sai dai kuma kash! Bata san hanyaa ba . Ganin ta tsaya ne Hajiya ta du be ta
ta ce "Me kike jira kuma."
"Hajiya wallahi ban san hanya ba ."

Hajiya ta juya ta kalli Alhaji, kafin ta yi magana ya yi zuruf ya ce, "Hajiya ba zaki fita hanyar
munafukar nan ba wai ?"
Kallon sa ta yi har sai da ya tsargu da kallon da ta ke masa sannan ta ce da kubra bi yo ni.
Ta yi gaba kubra ta bi bayanta ta na hamdala a zuciyar ta. Har bakin ƙofar gidan ta raka ta tace,
"Allah ya ki ya ye hanya Allah ya rabani da ke har abada! Idan ma kina da gaskiya ke ta sha fa !
Idan ma baki da na barki da Allah."

Duk kalaman ta sun fa ɗa cikin zuciyata na ce da ita ba tare da ja juya ba. "Allah ya biya ki da
gidan aljanna."

Na wuce na kama hanyar wani babban titi da ba abin hawa da yawa kasan cewar birnin Nijar
daman bai cika cin ƙo so da yawa kamar irin su Kano ba, tafiya mai nisa na yi na tare mai abin
hawa na ce ya kaini tashar difa. Kai tsaye ya dauki hanya ya kaini ina zuwa tasha kuwa na

samu mota mutun guda ya rage dan haka na afka cikin farin ciki. Hanya muka ɗauka ina
hamdala Allah ya kaimu lafiya.

Ta fiya muke cike da kwanciyar hankali amma Ni kuwa bani da wani burin da ya wuce a ce na
ganni gida. Dan gaba daya zuciyata sai bugawa ta ke ban san dalili ba! Amma kuma sai na ga
wani mutum mai siffar buzaye ya kalli na kusa da shi sunyi murmushi. Nidai na ce Allah ya fi ku
idan ma wani abu ne .....


PG 20

Har mun kusa kai wa maini kawai muka ji wani hayaki ya tur nuƙe mu.
Kowa ya kama tari, shawuya kuwa har da suma tuni direba ya tsaida motar dan haka kowa ya
fita .
Amma mai zai faru! Kawai wadanna mutane guda biyu suka cire wasu manyan wuƙake suka
ce kowa ya bada kudi ko kuma wani kayan kuɗi, amma kaf ɗin mu suka ce ba kudi a jikin su,
dan haka nima daman kudin nawa yana cikin dan kan faina ban masa ruƙo na wasa ba saboda
na san zai min amfani. Ganin zamu ɓata musu lokacin ne yasa ɗaya daga cikin su ya fizge shawuya ya ɗaura masa
wuƙa a wuya ya ce kowa ya fito da kudin jikin sa ko kuma mu yanka yaron nan a gaban ku
kuma kuma mu yanka ku. Ganin haka tuni na tsare har lumfashina yana sarƙewa na saka
hannu cikin jikina na cire duka kudin da Hajiya ta bani na bashi ina karkarwa, dariyar mugunta
ya yi sosai ya ce, "Allah ya so ki munafuka karɓi ɗanki!"
Ai kuwa hannu yana rawa na karbi shawuya ya yin da kowa ya cire abin da ya ke jikin sa ya
mika masu. Abu guda ne ya bani haushi yadda mutum biyu rak suka tsare duka motar saboda
wuƙar da ta ke hannun su .

Kuma yawancin motar maza ne masu yawa amma saboda tsoran mutuwa ba wanda ya yi
wani yunƙurin ceton mu! Bayan mutuwa dole ce idan lokacin ya cika ba makawa sai an mutu
ɗin, to amma kowa tsoran ta ya ke .
Idan ba haka ba ai Sarkin yawa ya fi Sarkin ƙarfi, a tunani na mai bindiga shine abin tsoro tunda
zai iya harbin ka! Amma mai wuƙa za'a iya cin masu ta dabara idan an so yin hakan.


Ganin na shagala da tunani wata da ke kusa da ni ta ce min " kiyi hakuri kin tsorata ko? Sun
gudu fa muje mu shiga mota."

Ban ce komai ba muka dauki hanya kai tsaye direba bai tsaya da mu ko ina ba sai gaidam.
Sauka kowa ya yi ya fara kama hanyar gidan su masu shiga motar wucewa suna shiga
amma Ni kuma bani da ko biyar da zan shiga motar kananma.

Sai na yi tunani na je wani gida kawai na nemi aron waya tunda dai ban mance lambar wayar

mijina ba sai na kira shi na sanar da shi ina gaidam tunda ba nisa ya zo ya tafi dani.



Dan haka na yan ke shawarar shiga gidajen da suke bayan ta shar maini domin na ga ko zan
samu wayar.

Amma kowanne gida na je ma na lura kamar gudu na suke kawai sai na mike da ta fiya saboda
mun taɓa zuwa gaidam so ɗaya da wata makwafciyar mu na ra kota suna amma kuma gidan
yana chan a ƙarshen gari ne.
Sai na fara gwada tafiya ko Allah zai sa na gane gidan duk da cewa na san akwai nisa tsakanin
tashar maini da anguwar kudu a kwai nisa gaskiya. To amma ba yanda zanyi nan ne kaɗai
zanje na samu wayar ƙiran.

Duk da kasancewar gaidam gari ne da kowa ya san shi da girmama baƙo da bashi kulawa
amma yau na ga saɓanin haka a gare su, ina tafe ina mamakin chanjawar ta su.
Ashe dai na tarar da su suna cikin ruɗin shaidan ne domin kuwa zuwana unguwar na tarar
gidan a kulle ba ko a lamun mutum yana rayuwa acikin sa wata ce ta sanar min da ai ta yi
balaguro.
Tsawan lokacin na dauka ina tunanin mafita sai na ji ana kiran sallar la'asar ga yunwa ga ba
kudi dan haka na yanke shawara nai man taimakon abinci, wani gida da naga yara suna wasa.
Koda zuwa kofar gidan kawai yaran suka watse suna gudu suna faɗin kar mu je ta kwashe
mana.
Mamaki ya sa na kalle su na ce ikon Allah wato har yanzu ban dawo kamar mutane ba ke nan
tunda yara ma suna guduna!
Wata maina na samu na zauna na kira wani yaro da yazo wucewa na sanya shi ya karɓomin
ruwa a wani gida na yi alwala na yi sallar azahar da la'asar sannan kuma na ce dan Allah ya
maida butar ya ce su aramin wayar su zanyi ƙira .

Cike da sa'a sai ga matar ta fito ita da yaron ta ke ce masa ya bani wayar amma ya yi a hankali
kar na kwashe masa dan ita tsoro na take . Mamaki ya kama zuciyata fal, har sai da raina ya
sosu duk da cewa na san yadda na ke a bushe dole ne na chanja kama.

Amma kuma bai kamata ana guduna ba tunda dai lalura ce.
Yaro yana bani waya naga ya buga tsalle ya min gwalo, sai matar ta ce masa lafiya kuwa?
Aikuwa yaro yana jin haka sai ya fasa ihu ya fara faɗin ta kwashe min su! Mamaki fal zuciyata
na ce yau zan ga ikon Allah.
Kafin na ce wani abu wuri ya cika makil da jama'a an fara narko min manyan zagi.
Wayar suka warche suna ja da baya maza suna cukume wandon su mata kuma suna
rungume ƙirgin su, na ce " Ikon Allah ! To nidai gaskiya abin da fari dariya ya bani har sai da na
dara na ce wai lafiya kuke kuwa.

Ai kuwa wata tana jin abin da na ce ta ce "Zaki ci ubaki yau kuwa idan baki dawo masa da
kayan sa ba."

Na ce, "Wai wana kaya ne haka bayin Allah ni fa baƙuwa ce wata na zo nema ban sa me ta ba."


"Yawwa munafuka daman ai baƙin ne suke haka dan dai mu kam kaf! Garin nan ba mai
wannan halin! Aha! A mayar masa kayan sa."

Mamaki ya sake lunke min zuciya na haɗiye wani miyau mai shegen zafi na ce,

"Na ce yanzu kun duba kayan na shi ne kunga babu?"

Duka suka yi kaina suna faɗin ba za'a duba ba ba ɗin kalan ki haɗa da sauran ko to ki yi maza
ki maida masi
Wata cikin su ta sa ke cewa, kuma idan zaki mai da mushi ki maida mishi na shi! Sai ku dau
abin mutum na yaro ku sanya masa na babba, shekaran jiya ma haka wata ta yi a chan layin.

Haka suka dinga jifana da miyagun kalamai har ta kai ga sun fara duka na tukunna wata babba
cikin su tace su daina duka na kar su ƙarasa gawar da ba ta su ba garin ne man gira a rasa
idanu.

Dan haka sai na samu rangwame aka ne mo mai nafef aka tusa kai na ciki na ji suna cewa aje
gidan kangar! Chab ! Duk da ban san ina ne ba amma ina jin makwafciyar mu tana bada labarin
wani wurin horo ne da ake kai mai laifi duk girman sa a bashi kashi.
To ni ba wannan ne damuwa ta ba, a'a ta ya ya zan maida abin da ban dauƙa ba tunda na san
shine abinda za'a tuhume ni da shi.Muna zuwa gidan kuwa wasu zaratan sojojin suka sakani
gaba da tambaya suna cewa ina na kai masa kayan sa, amsa ɗaya na ke bayarwa ita ce "
Bansan me suke nufi ba."
Ya sake cewa "Idan baki mayar masa ba wallahi har oga ya dawo daga kananma zaki sha
wahala."


Sunkuyar da kaina na yi bance komai ba. Saboda kalmar kananma da yace yasa naji farin ciki,
kuma Allah ya kawo ogan ko Allah zai sa ya taimaka min.


Ɗaya a cikin su yace da mai tambaya ta " Wai mutanen garin kanamma duka sun koma ne?"
Amsa ya bashe cewa duka sun koma wanda basu koma ba ma yau zasu koma saboda gobe
gwamna zaije ya basu kyauta.

Ni dai shiru na yi bance komai ba har sai da shawuya ya fasa ihu tukunna na tallafo shi.

Sojan ya zura min idanu kamar ya sanni yana ta faman kallona.....
PG 21
Ranar da su basma da su mama fedo Maryam hadiza da su yarima haidar zulfa'u duka suka
dawo daga gashu'wa saboda jin labarin sanarwar koma war kowa garin komai ya lafa.
Shi kuma Nasir cewa ya yi suje amma shi kam ba zai koma ba har sai anji labarin kubra. Dan
haka duka suka dawo gida ba su zauna ba, suka zo suka tarar garin su ya cika taf da jama'ar
garin hamdala suka yi da addu'ar Allah ya sa sun samu zaman lafiya mai ɗaurewa.


Captain Kamal ne ya dubi Captain jamil ya ce, "Wai duk dan basma ta tafi ne ka zama wani
salihi ne haka?"

Murmushi ya yi ya ce, "Kai fa baka da kirki wallahi, daman Chan ni salihi ne ai."

"Haka ne kam amma a wurin basma ne ka ke salihin tunda na ga har wani tsoran ta ka ke ji."

"Kai malam ka gane fa ba tsoro ba ne kawai tsntsar love ne."

Dariya sosai kamal ya yi ya dubi Jamil har ya na nuna shi, "To yanzu ina love ɗin? Yarin yar da
har ta wuce garin su."


"Wai kana tunanin zan barta ne? Ta turamin hoton yayarta fa, ka ga kuwa duk ranar da Allah
ya sa na same ta zan kai mata ita har gida da ga nan sai mu jone."
Ya faɗa yana masa gwalo kamar wasu yara. Sukuma sauran sojojin suna nan suna har ko kin
su ba wanda ya sanya musu baki.
Sai Chan wani babba cikin su ya ce "Yau zamu wuce gaidam sai mu jira gwamna da ta wagar
sa sai mu wuce kananma."

"Ok sir ba damuwa."

Kallon sa ya maida ga kamal ya ce "Ka ga rabon haɗuwa ya sa ke faruwa ko."


Kamal ya ce "To gaskiya abokina ina maka fatan alheri domin na tabbata kana ƙaunar
yarinyar nan fa, gani ɗaya ka mata ka susuce har da jin tsoro kamar wani so ko."

Naushi Jamil ya kai masa , "Wallahi baka da kirki ni ne sokon ko? Ba damuwa zan kamaka
wataran kai ma ."

"Kai haba ai tsoran mace sai dai kai ɗin amma bani ba kam."

Haka suka yi ta zuba zance har lokacin tafiyar su gaidam ya yi suka dauki hanya .



Ita kuwa kubra ganin irin kallon da yake mata ne ya sanya ta sunkuyar da kanta ƙasa,
Kamar dirar mikiya haka ta ji maganar sa. "Yanzu ke kina da wannan ɗan ƙaramin yaron kike
aikata irin wannan laifin haka? Bakya tsoron su cutar miki da yaron ki? Ki mayar musu idan har
kin ɗauka musu kayan su kawai dan yau idan OGA ya zo zai wuce zai Miki illah saboda baya
barin irin wannan lamarin da sauƙi tunda ya yi fama da irin masu rigimar ki ba sa mayarwa sai
dai a gaji abarsu."

Kallon sa na yi kamar ha zan yi magana ba na ce " To taya za su mayar da abinda ba su da
masaniya a kai, bayan basu ɗauka ba."

Shiru ya yi ya kalle ni ya jinjina kai irin zaki sani ɗin nan.


Misalin shida na magrib su Jamil suka shigo gaidam suna zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login