Showing 12001 words to 15000 words out of 33733 words

Chapter 5 - BAYAN GANGAMI Part1 Complete by Ummu Heebah.pdf

27 Apr 2025

2102

aljana ba ce.

Sai na ce masa "Ba ruwan ifriti da maganar ka!!! Abun da ya ke bukata kawai shine ka kaini
cikin garin ku da ya ke kusa wanda diyar godiya ta bayana ba zata gaji ba a ya yin ta fiyar.
Kuma kar ka bari wani bil'adama ya ganmu haka yana da ga cikin abinda zai jawo ka rasa ranka
!!!!! "
Sunkuyar da kai ya yi ya ce cikin in ina "in in Allah ya ya yarda ba zasu gan mu ba ."

"Ka tsira!! ." Na furta haka cikin ƙaraji.

Juyawa ya yi domin mu tafi na fakaice shi na cire yalo uku na boye cikin kaya na. Muka dauki
hanya ta cikin wasu lunguna da motoci ma baza su iya bi ba kuma mutum ma da kyar yake
kutsawa. Lallai irin hanyar nan sai wanda ya santa kaɗai ne zai ga ne ta.

Munyi tafiya mai nisa na fara hango bakin titi kuma da wani gari chan gefen sa sai na ga kuma
ya tsaya ya ce "To ya ke bil jinnu anan matsalar ta ke kuma. Saboda anan kam dole bil'adama
zasu ganni.Ya faɗa yana russunawa.
Na ce da shi " Babu wata matsala! Muje kawai ...."
Koda muka fara shiga garin sai na fuskanci cewa garin ba babban gari ba ne ƙauye ne kuma
ba shida wani girma.
Dan haka muna kaiwa wajen gidaje na ce da shi "Dakata! Anan zamu rabu, dan haka ka juya ka
koma kar kuma ka sake ka wai wa yo! Yin hakan yana nufin kana wasa da rayuwar ka ne."
Da to ya amsa min ya kama hanyar dajin da muka baro ba ko waiwaye dariya na ji ta kubce
min wanda rabon da na yi ta inda ta nutsuwa ce na irin wacce na yi da sunan aljana ba tun
ranar da zamu rabu da mijina. Ba zan mance ranar ba kam tabbas.

Yana kishin gide ya ce dani. " Ƙurraty na, na ɗago idanuna na dube shi na yi masa kyakkyawan
murmushi na ce "Na'am hubby."

"Ƙurraty wallahi ina sonki ɗayawa ranar da zaki haihu kawai na ke tunawa idan na tuna da
yadda mata suke shan wuya a wajen haihuwa, wallahi ƙurraty sai na ji kamar na karɓa miki
saboda bana son na ganki kina shan wuya." Ya ƙarashe maganar tashi yana langwabar da kai .

Murmushin na yi na kalleshi na bude baki " Allah sarki mijin ƙurrat haka Allah ya tsara mana mu
mata karka damuwa muyi ta addu'a Allah ya kawo ta da sauki ."

"Haka ne ƙurraty amma gaskiya ba zan iya tsayawa a asibiti ba wannan karan dan haihuwar
zulfa'u kusan kuka na yi , ke na yi ma saboda bayan kin haihuwa na dunga hawayen da ban

san na me ne ba."

Murmushin sosai na sake masa ƙasan zuciyata kuma ina farin ciki da alfaharin irin yadda na
samu miji mai sona har tsawon wannan lokaci da na haifa masa yara uku zan yi na hudu bai
rage wani abu da yake na soyayya ta a zuciyar sa ba.

" Karka damu hubby in sha Allahu zan haihu lafiya lau kana bacci sai dai na tashe ka ka ga
yaron ka ko yarin ya ......


Wuri na samu na zauna bayan dawo wa daga duniyar tunanin da na afka ciki tabbas na san
yanzu mijina yana cikin wani hali. Haihuwar da yake mata fargaba yau ta zo min cikin wani halin
da ko ni ba zan iya cewa ga irin yadda na sha a zabar ba. Saboda sawun Giwa ya take na
Raƙumi.
Ganin zaman ma ba shida amfani ya sanya na ta shi na dauki hanya na sake kutsawa cikin
kauyen ina tambaya har na isa gidan mai gari .

Na nemi na gana da shi aka ce min sai zuwa sallar Ishaa na dare zai dawo .

Haka na zauna na ci yalo da tumatir na bawa shawuya nono ya sha bawan Allah duk ya rame
sai yanzu na ga asalin ramar da ya yi har sai da na yi ƙwalla saboda dukkan wani ƙashi na
jikinsa kana ganin sa za ne, har wani ƙaton kai ya yi . Lulluɓe shi na yi na rungume shi acikin
jikina ina faman sana'ar da ta zamo min abin yi wato kuka. Sai naji an dafa kafaɗa ta baya,
saurin juyawa na yi na kalli wata baiwar Allah ta ce min kije fada mai gari ya na neman ki.
Tsabar damuwa ban san ma sanda daren ya yi ba har suka yi sallah da yake ina cikin halin jego
ba ni da damuwa a kan sallah amma fa ina bukatar kama ruwa domin duk jini ya ɓata min jikina
har ya bushe idan ban da ƙarni ba abinda na ke yi.

Alfarma na ne ma wurin matar ta kuma amin ce min na shiga daga cikin gidan ta na wanke
jikina na kama dukkan inda na san ya ɓaci na wanke na baza zanin ya ɗan sha sannan na
daura shi may fito muka dauki hanyar fadar garin koda na je wurin a cike ya ke da jama'a kamar
za'ayi wani taron, shiga ta ke nan na hangi wannan bawan Allan da ya taimaka min ya shigo
dani gari . Yana ganin fuska ta ya mike ya na nuna ni, luuuu ya zuɓe kasa sumamme!

"Tashin hankali!" Shine abinda na furta a bakina ya yin da sauran jama'ar wurin duka suka yo
kaina suna faman salati da salallami suna faɗin mai kika masa baiwar Allah?

Daga zuwa wuri .

Nidai na yi zuru zuru na kasa cewa uffan ga kowa....

PG 12



Wani irin kallo jama'ar wurin suka bi ni da shi dukan su,hankali na ya yi matukar tashi na fara
ƙokarin yin magana domin na kare kaina.
Mai gari ya ce da ni " Ke baiwar Allah! Daga zuwa har kin fara jefo mana masifa! Wacece
ke? Daman kune irin tsofin Mayun nan na cikin daji da kuke bibiyar al'umma kuna lamushewa?
To ahir ɗinki tabbas kin zo wurin da zaki karɓi hukunci dai dai da abinda kika aikata.

Tunda kalaman bakin sa suka fara furzuwa zuwa masarrafin jina tuni hantar cikina ta yi
muguwar kaɗawa, har wani jiri na ji yana neman ɗi ba na.
Na so ace mutuwa ta zo min nida shawuya a wannan lokacin ko zamu huta da wadannan tashin
hankalin .
Kuma da na san cewa haka zata faru da mu to da kawai zan bayyana kaina a lokacin da y'an
ta'addan suka bayyana a wurin bishiyar nan .

Amma sai dai kash! Bakin alƙalami ya bushe baya bata dawo wa.
Durƙushewa na yi duka a ƙasa na ce.

"Wallahi ban san wannan maganar da kake yi ba, kuma bani da alaƙa da ita.

Hasali ma da zaka ji labarina da zaka......." Tsawar da ya daka min ce ta sani tilas na shanye
sauran maganganun bakina. Sai ya ce,

"Muna fuka bamu nemi jin komai daga gare ki ba, dan haka ki kama bakin ki sake yin wata
magana anan wurin tamkar ƙara wa kanki laifi ne.

Shirun dole ce ta riske ni bani da wata mafita sai wacce Allah ya kawo min.




Yarima ne zaune ya haɗe kai da guiwa yana tunanin mahaifiyar sa. Fedo mahaifiyar Kubra ta
dube Maryam ta ce Kinga Maryam lamarin yaron nan kullum damuna ya ke wallahi, kar ya je
wata cuta ta kama shi. Damuwar da ya yi ko yayan sa bayyi ba.

Maryam ta yi murmushin da ya fi kuka ciwo ta ce " Mama dole ya ka sa mancewa saboda waya
san a irin yanayin da ya ganta , kuma mama tunda kika ga ƙarancin shekaru irin na yarima ya
kasa mance wa da wannan lamarin wallahi mama aunty Kubra ta shiga wani mummunan
yanayi kafin su rabu..... Ta ƙarashe maganar cikin kuka saboda daman neman kukan ta ke yi.

"Haba Maryam yanzu mene ne abin kuka saboda Allah bayan kuma ke ce wacce zaki
rarrashe shi. Amma kuma kina yi a gaban sa ta ya shi kuma zai samu sauki a cikin zuciyar sa?"

"Mama zan kiya ye." Ta furta a chan ƙasan maƙoshin ta.
Miƙewa ta yi jiki ba ƙwari ta nufi inda yarima ya ke ta ɗago da kansa ta rungume shi ta ce
"Yarima yarona kayi hakuri in sha Allah mommy zata dawo kuma ba abin da zai faru da ita."
Ɗago rinannun idanun sa ya yi ya ce ; "Aunty Maryam sunyi mata rashin adalci kuma sai na je
na ƙarbo ta! Aunty Maryam ki taimaka ki sani a ajin sojoji dan Allah na koyi yaƙi na je na ga ni
ko sun kashe min mommy ko tana wurin su." Ya faɗa yana durƙusawa a gaban ta.

Cikin raunin zuciya ta dube shi tace ; "Tashi yarima zan kai ka in sha Allahu kaji, amma ina son
ka de na sanya damuwa sosai a ranka saboda idan ka kamu da cuta to bazasu kar ɓe ka ba
suma sojojin a wurin aikin na su.

Jin ta ambaci ba zasu ɗauke shi ba tuni ya ɗan saki fuska ya ce "To aunty indai zasu dau ke ni
na je na dawo da mommy na daina daga yau."
Murmushin ta yi ta kalle shi "Yawwa yarona haka na ke son ji."

Suna tsaka da hirar sai ga zulfa'u ta shigo da gudu hannun ta dauke da Sweet tana tsalle ta ce
cikin gwarancinta, "Atti na, baba ya bani Sweet ba jan baki ba mommy zan ajjiyewa."
Dariya Maryam ta yi ta ce "Shike nan ɗiyar mommy wato ni bazaki bani ba ko? Ai bazan Miki
wanka ba gobe ."

Tsalle ta fara yi tana shirin kuka tana cewa "Bana sho ni wanka zaki mun gobe na je ba mommy
sweet!" Ta faɗa tana maƙe kafaɗa.

Janyo ta Maryam ta yi jikin ta ta rungume su duka su biyun .

Yayin da mama ta ke gefe tana kallon su cikin tausayawa har sai da ƙwalla ta fito mata ta yi
saurin goge wa..........


PG 13

Suna rungume jikin ta Nasir ya shigo gidan, kallo ɗaya ya yi masu ya gane halin da suke ciki
dan haka cikin sauri ya saki hannun yayan yarima wato haidar ya juya waje saboda tabbas idan
ya tsaya sai yaji hawaye zai zubo masa .

Haidar yaro mai Shekara goma sha huɗu. Ya dube su ya ce "Aunty Maryam har yanzu ba su
dena kukan ba?"
Daga masa kai tayi a lamun basu dai na ba.

Kallon su ya yi ya ji wani mugun tausayin su ya kama zuciyar sa, sai dai ba yadda zayyi da

lamarin tunda haka Allah ya tsara musu sai ya ce da su. "Dukkan wanda ya sake mana kuka ko
mommy ta zo ɓoyeta zan yi nida daddy muna ganin ta bazan kawo ta wurin ku ba.
Jin ya ce haka duka suka ce "Yaya haidar mun daina ka yi hakuri."

"Yawwa yaran mommy to na ji, kuyi murmushi na gani ."

Murmushin suka yi suka kalle shi shi ma ya mayar musu ya ce "To kuje wurin kaka fedo ku
zauna ku bar aunty Maryam ta huta kunji ko."

Kai suka kaɗa suka wuce shi ma ya je ya gaida kakar su ya shige dakin sa.
Zama ya yi a bakin ƙaramin gadon da ya zama wurin kwanan sa tun ɓacewar mommyn su, duk
da cewa yarima ya ga halin da mommy ta ke amma bai kai shi damuwa ba saboda yadda
mahaifiyar su ta ke nuna musu so da ƙauna duka ba wariya farin ciki ya wanzu a familyn su a
lokacin da mommyn su ta ke nan. Saboda shine yaro na farko da suka haifa tunda ya ta shi bai
taɓa ganin faɗan su ba bare hayaniya, kuma kowanne a cikin su yana nuna masa so har ya kai
ya samu ƙanne mommy bata daina sa shi jikin ta ba kamar yadda daddy ya mai da shi abokin
sa . Saboda yana ganin hakan shine zai taimaka masa wajen kula da tarbiyyar sa.

Ko abinci na safe da dare dukan su suke haɗuwa su ci a babban faranti .


Jingina kansa ya yi da bango ya daki bangon yana wani irin kuka mai tsuma zuciya. Ya ce "
Allah ya wadaran sojojin garin mu da suke zaune kamar mata a zo a ci garin da kuke tsarewa
da yaki har a dauki ganima amma ku ka sa komai!!! Yau da ni soja ne a yau zan ɗibi zuga na
baza dajin da aka san suna nan muyi bata kashi na duba uwata!!
Mommy kina ina!!! Ina zamu ganki mommy kewarki ta kama mana zuciya mommy, idan kin
mutu mommy ko gawarki a kawo mana mugani!!!"

Ya faɗa cikin ƙaraji da ihu dan ya mance yanzu ya gama yiwa ƙannen sa faɗa.

Dukkan abinda ya ke faruwa baba Bala ya na bakin ƙofar ɗakin zama ya yi dur shan yana
hawaye ya kasa shiga dakin ya rarrashe shi.



Kubra ta since goyon ta ko zasu ga ƙaramin goyon su tausaya mata, amma da suka zo mai gari
yana ganin sawayen ta ba faratu ya kaɗa baki yana riƙe haɓa ya ce "Wato da maitar ki ta motsa
kika rasa abin ci sai kika cinye fara tanki.

Bari yanzu zamuyi maganin ki yana gama faɗa ya na ƙiran wani mai suna Yakubu da ya kawo
barko no da wuta a turare ta da shi .

Jin abinda ya ce yasa ta figita ta gigice ta ce cikin kuka " Dan girman Allah komai zaku mun
karku haɗa da wannan yaron da bai san komai ba a duniya ko baku tausaya min ba to ku
tausaya masa. Ku rike shi idan kun gama min hukun ci sai ku bani ."

Ina gama fadar hakan na ga duka sun ja da baya wata mace gajeruwa daya gefe ta ce , "Allah
Ya tsare mu riƙe yaron mayya, salon Ya je ya cinye mu wato mu rike shi shike nan kin samu
dama, to baki isa ba. Ai ke ba abin tausayi ba ce! Mayyar mace ai muguwa ce.

Dan haka me gari mafi sauki abin da zamu mata shine a bude ƙasan ta a watsa mata yajin zata
yi bayani da bakin ta ita mayya ce ko ba ita ba ce.

Kallon ta duka jama'ar da ke wurin suka yi suka ce tabbas wannan shawarar ta yi kuwa maza
kuyi mata aiki cikin gaggawa kafin ta ƙame mana bakuna da ƙafafu!

Ai kuwa suna jin haka suka afka kaina suka wangale min zanin ya yinda duka mazan wurin
suka juya baya suka watsa min wani yaji .

Wata irin ƙara na sake ta a zaba ga jego ga barkwano har suma sai da na yi domin azabtar da
Ni da suka yi sai dai Allah na yi ihu kamar zan zare shawuya yana na shi ihun ina ji amma ba
damar daukar sa .


Saboda na kasa zama na kasa tsayuwa kuma awannan halin suka yo kaina da tambaya suna
cewa mayya ce ke ko ba ita ba ce .

Tsabar azaba da masifar da na ke ciki na san idan na ƙaryata hakan wata azabar Zasuyi min na
ce "Mayya ce tabbas na jima ina cinye mutane!""


Salati suke baki dayan su suna tsine mun aka fara kawo ruwa ana kuzamin ina sake yin wani
ihun, ganin zasu cutar da Ni dayawa ya san ya na shiga haukar da gangan na dauki wani ita ce
cikin rumfar nan aikuwa na sauke wa wacce ta sanya min ya ji. Ganin haka suka yi baya na fara
bin su duka da duka ina faɗin duka yau sai na cinye ku ba mai kwana a duniya!! Sai da na tabbatar sun baje na dawo na dauki guntun jarkar ruwan da suka bari na dunga
wanke gabana da ruwan ina hawaye har na dan samu nutsuwa na dauki shawuya yana gefe a
ya she ga shi jikina duka ya jiki idan na sanya shi dole ya kamu da yaji ko mura ... ....



PG 14
Haka dole na tsaya har kayana su kaɗan sha na ɗan kara shawuya a gefen cikina na kama
hanya domin na bar wannan ƙauyen. Saboda ban san me zasu min gaba ba, gwanda na bar
wurin ko zan samu wata mafaka tunda dai na shigo gari na bar daji.

Da wannan tunanin na kama hanya tafiyar kilo mita guda da rabi ta kawo ni wani babban birni
wanda ban san sunan shi ba, amma bisa ga dukkan alamu garin na ta'alawa ne ko kuma
jama'ar Nijar. Saboda yadda na ke ganin yawancin su kayu kan su a naɗe kamar dai buza ye.


Haka na kutsa cikin garin tare da Bismillah domin neman tsari da ga dukkan sharri.

Kusan magrib na samu wata rumfa a cikin. Wata tasha na fake saboda ban san ina zan nufa ba,
sai kuma tsoro ya cika min zuciya, saboda na san halin mutanen da suke rayuwa a cikin tasha
yawancin su ba na gari ba ne.

Sai na chan ja shawara na fita na sake nausawa cikin garin ko zan samu mafaka.

Wani gida na hanga ga dukkan a lamu gidan na masu hannu da shuni ne dan haka na shiga ba
ko wani ɗar na fara doka sallama cike da sa'a kuwa wata mace kiwon madara da bota ta fito
cikin wani tsadadden leshi ta kalle ni ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login