Showing 18001 words to 21000 words out of 33733 words

Chapter 7 - BAYAN GANGAMI Part1 Complete by Ummu Heebah.pdf

27 Apr 2025

2098

faɗi ƙasa kamar gawa.........



PG 17

Ganin ya zube ƙasa ya sanya haidar ru gowa da gudu ya sanya hannun sa ya tallafi baban su
yana faɗin " Daddy dan Allah ka tashi Karka barmu yadda mommy ta barmu, ƙarya ya ke
mommy bata mutu ba. Daddy Please! Ya faɗa cikin wani irin kuka me sauti har sai da jama'ar
gidan suka fito. Baba Bala kuwa ya ka sa komai jikin sa sai mazari ya ke yana kaiwa da kawo wa, chan tukun
na ya ce da sojan, "Bawan Allah me ne ne gaskiyar lamarin maganar nan ta ka."

Soja ya gyara tsayuwar sa tamkar ba shi ya kawo tarzo mar ba.

Ya ce " Baba ina zato fa na ce tunda mun jefa musu wuta kuma sun ƙone, idan har ta na ciki ka
ga ai sai dai hakuri amma idan bata ciki to ƙila tana wurin su a raye ko wani wajen."


Baba ya yi shiru na wani lokaci Sannan ya ce, "Shike nan mun gode da ziyara Allah ya sa tana
raye."


"Amin baba. Amma ba shi kaɗai ya kawo ni ba idan ba damuwa ina son ganin yayar yarima
saboda akwai wata tambaya da zan mata ."

Badan dai soja ba ne da ba abinda zai hana baba Bala yi masa rashin daraja, amma ba yadda
zayyi tilas ya haɗa shi da basma ya yi da daidai da lokacin da Nasir ya farfaɗo da ga sumar da
ya yi. Sannu suka fara masa suka shiga da shi gida saboda har jama'a sun fara taruwa.

Basma kuwa ƙuru ta yi gaban soja tana jiran me zai ce mata.

"Ina son ki bani lambar wayar ki ko wata lambar da zan sa me ki. Saboda akwai wasu bayanai
da na ke nema a wurin ki amma yanzu na ga baki da nutsuwa sosai."

Shiru ta yi na wani lokaci dan harga Allah ta ji haushi da ya tsayar da ita a wannan lokacin da
suke cikin damuwa, kuma shine silar komai da ya faru a yanzu."

Lambar ta ambato masa ya sanya cikin wayar sa ya yi gaba ta shige gida.


Koda suka shiga jajan ta lamarin suka yi ya yinda mama ta kama kuka wiwi wai tunda yace
haka ta san zayyi wuya a ce Kubra na ra ye.

Haka su ka yi ta lalla shin ta har ta ɗan tsa gai ta.


Kubra zaune tana jiran zuwan Hajiya da yarima domin su Kaita ta sha, shawuya ta dauka ta
fara masa waƙa kamar haka.

Shawuya bawan Allah ne.

Shawuya ɗan gatan mama.

Allah ya so mu da nisan kwana yarona.

Zamu gida ka ga daddy da sauran yayye yarona.

Dariya ya ɗan ɓangala ai kuwa kubra ta yi da murna yau yaron ta ya yi dariya.

Lamari kamar wanda a kansa ne ta fara haihuwa.

Wajen sha biyu hajiya ta shigo ta ce ta zo su tafi dan haka da murna ta fito ta dauki shawuya ta
goya a bayan ta. Kayan da ta cire daman ta daure a leda dan bata son rabuwa da su ko dan
tarihi.

Suka kama hanyar fita zuwa gun motar yarima .

Tunda ta ga kallon da yarima ya ke mata sai ta ji hantar cikin ta ta ƙada saboda na kasa fassara
ya nayin kallon na sa. Har mun shiga Mota da Hajiya sai na ji ya ce. "Dear, ai ba sai kinje ba
kawai zan kaita. Saboda ta chan zan wuce sch ne."

Wani abu na ji ya chaki zuciyata kamar na yi ihu tun ban san me Hajiya zata ce ba.

"Yanzu kana nufin na sauƙa zaka yi koma yadda ya kamata?"

Tabbas kuwa dear zan kai ta mana badai Yobe zata je ba? zan sa ka ta motar difa daga nan sai
su kaita maini ko kuma ta shiga ta garin su darect kawai ."

"To yarima amma dan Allah kayi wa direba bayani sosai kar ya barta ta sha wuya ya yi ƙokari
ya sanya ta motar garin su da wuri da su ke difan."

"Ok Dear."

Kallon su na tsaya yi na ke kallon Hajiya. Kamar ta san ina cikin ta shin hankali ta ce, "ki
kwantar da hankalin ki wannan zaiyyi komai kamar ina nan kuma in sha Allahu zaki je gida a
yau ba sai gobe ba.

Ba dan ma ba ƙasa ɗaya muke ba ta kin sanar da zuwan ki a wayar jama'ar gidan ku.

Amma ga wannan ta faɗa ta na bani wasu ƙudi wanda zasu kai naira dubu ishirin. Hannu na
sanya na karba ina godiya ta re da share wata ƙwallar da ban san da zuwan ta ba sai ɗumin ta
da na ji kan fuskata.


Fita ta yi ta na ɗaga mana hannu har muka ɓace wa ganin ta . Kallo na na kai kan shawuya na
sha kansa a cikin zuciyata na ce "Allah ya raya min kai ya kaimu gida lafiya shawuya.

Jin sautin yana waya ne ya sanya ne ɗagowa da kaina domin na ji mai zai ce,

Kalmar da ya ambata ita ce ta yi sanadin daukewar lumfashina na wucin gaɗi. Bayan wani
lokaci na samu damar haɗiye wani mugun ya wu hannu na daura bisa kaina na furta " Na shiga
uku! Ya Salam! Haba dan Allah wannan wacce irin masifa ce..... Wawan birkin da yaci ne ya
sanya ni sake tabbatar da batun da na ji ya na yi ya zama gaskiya..

Shike nan nikam na shiga uku ina jin har abada bazan koma ga ahalina ba.......




PG 18


ganin yan ƙokarin chusa kan motar cikin wani wawa ke ken gida tuni na tuna da maganar da ya
yi a waya.

*Daddy ba wata matsala ga ta na kawo ta*
Wani hawaye na ji suna zubomin ya yinda ya yi dai dai da tsayuwar motar cikin rumfar ajjiyar
motocin gidan.

Fitowa ya yi ya bude inda na ke ya ce na fito fuska ba walwala.
Ba yadda zanyi haka dole na sa ƙafa na fito riƙe da shawuya a hannuna. "Bi yo ni .". Ita ce
kalmar da ya furta min wanda ta daki dukkan sassan jikina. Haka na dunga binsa a baya har
muka kai ga wasu manyan faluna na gani na faɗa kuma gidan yana da zurfi sosai mun wuce
manyan falo sun kai biyar, daga bisani muka bi wani korido muka kurda ta wata ƙaramar hanya
muka iske wani ƙaramin falo. Wani jibgegen mutum ne hakim ce a zaune kam wata kujera
fuskar sa dauke da murmushi, idan ka kalle shi ba zaka ce ya yi kala da mugayen mutane ba.
Saboda cikar zatin da Allah ya masa kuma ga shi da kwarjini a ido.

Hannu ya miƙawa wanda ya ke zaune tare da faɗin, "Daddy gata nan kuma ba wanda ya
ganmu mommy da kanta bata san ma ka ganta ba tunda tana ta mitar rashin tsayuwar ka ."

Dariya ya yi mai sauti sannan ya ce, "Ai shine da lilin da ya sa na ƙi tsyawar domin bana son ta
zargi wani abu ko daga baya amma kaga yanzu komai normal. Kai dai abinda zan ja maka
kunne ka tabbatar ka sake riƙe mana sirrin mu har zuwa lokacin da zamu fita cikin wannan
masifar."
Da to ya amsa masa ya fita ya barni zaune .

Duk jikina ya mutu na kasa ko da kwakkwaran motsi ne ga shi ruwan hawayena ya kasa dai na
zuba, sanadin magan-ganun su.
Na sallama wa rayuwa yau kam tabbas amma ma fi tausayin yaro na da zai kai shi gida ni ya
kashe da zan amince. Amma sai dai kash na san hakan bazata samu ba, damuwa ta ɗaya ce,
ko shakka babu wannan mutum idan ya haikemin kafin ya kai ga biyan buƙatar sa a wurina zan
mutu tabbas! Saboda bani da wani kwaliti jiki duk yunwa da gajiya. Ke nan idan na mutu
shawuya zai kai kaɗai a shanye wa jini. Zuciyata tana gama bani amsar ƙarshe na fashe da
wani uban kuka wanda zaka dauka duka na ake yi.


Ganin abinda na ke yi ne ya sanya Alhaji yin murmushi ya kalle Ni ya ce, "Sorry da kin bar
kukan haka dan ba zai Miki amfani ba kam. Ban so na Miki komai ba amma kuma ya zama dole
na yi hakan ko dan ceton rayuwar ahalina. Dan haka kiyi hakuri ki dauki wannan a matsayin
ƙaddarar ki."
Yana gama faɗar haka ya mike ya na fadin "Ki huta ga kaji chan da kayan more rayuwa ki ci ki
koshi zuwa dare sai mu haɗe."

Saman be ne ya haye abinsa, kallon dinning table ɗin na yi wanda ya ke cike da kayan more
rayuwa na dauke kaina, domin ba kaza ba ko ɗawisu a ka ban awannan lokacin ba zan iya ci
ba.

Yadda ya barni haka ya dawo ya wuce ni ko motsin kirki banyi ba har wajen Yamma ina zaune

in banda sallah da na yi ita ma da taimama na yi ta saboda a kwai wani lungu kafin mu shigo
ɗin na ga ƙasa dan haka chan na je na yi na dawo na yi sallah.

Na shiga tashin hankali matuka ainun ganin dare ya fara kawo kai ga kuma yunwa da ta ke
addabar cikina har ta shafi shawuya ya fara kuka saboda bai samun nono mai kyau a wuni yau
ɗin ba. Da yanzu ina Chan wurin dangina a na ta murna a na maraba da dawo wata, amma
wannan yarima bai kyauta wa mamar sa.
Ya Allah yadda ya ci amanar da maihaifiyar sa ta bashi Allah ka to ni asirin su ka ce ce ko da
yaro na ne....na hakura da rayuwar nikam koda na koma gida ba lalle na rayuwa tunda zuciyata
ta gama shaƙar bakin ciki na san da wuya na jima bata buga ba.... Na karshe maganar ina kuka
mai cin zuciya.



Basma ta na zaune ta ji wayar mama Fido ta na kukan neman taimako dan haka tuni ta dauka
saboda ba su cika barin ƙira ba ko za suyi katari da labarin Kubra.

Tana ɗagawa ta fara da Sallama. Shiru ta ji ba amsa kuma daga baya a ka ce, "Basma ce?"
"Eh ni ce wa ye ne?"
Ta mayar da amsa.
"Sojan ki ne." Ya faɗa cikin murmushi.

Wata faɗuwar gaba ce ta riske ta jin ya ambaci kalmar sojan ki ne, ta ya ya zama na ta? Ta
tambayi kanta.

"Kina jina kuwa basma?"

"Eh ina jinka soja." Ta faɗa cikin ƙosawa da wayar, saboda haushin ko wanne jami'i ta ke ji da
shugabanni, suna ji a na kwashe jama'a basa bin ka du da wuri har sai rayuka sun salwanta.

"Basma ina son idan kin samu nutsuwa muyi wata maga na ne."

Ya faɗa cikin sauti ƙasa ƙasa kamar mai raɗa.

"Ina jin ka ko yaushe zaka iya faɗa saboda bani ba samun tsuwa har sai ranar da aunty Kubra
ta dawo gida."

Shiru ya yi na wani lokaci Sannan ya ce , "Karki damu zata dawo in sha Allahu."

"Kai da ka ce ta mutu."

Ta jefa masa tambayar.

"Ina tsammani fa na ce basma." Ya faɗa cikin sanyin murya har sai da ya sa ta ɗan dara
Jin sautin darawar ta ta ne ya sanya shi yin murmushi ya ce "Shike nan ki huta zuwa wani lokaci
zan dawo idan kun samu nutsuwa. Amma ki sani wallahi da na san inda aunty Kubra ta ke to
da tabbas zanje na dawo da ita har gida kodan farin cikin ki."

Ajiyar zuciya ta sauƙe tana jinjina masa duk da ta san ƙila da wata manufar ya ke haka, amma
zan ba shi lokacin na ji ƙarshen gudun ruwan sa .


Sallama ya yi mata ta ajjiye wayar ta kwanta tana na zarin kalaman sa.

A na shi ɓangaren kuwa yana gama wayar ya saki wani ƙayataccen murmushi har sai dai na ge
fen sa ya ɗan taɓa shi ya ce "Ya de Captain Jamil, ko ka faɗa soyayya ne?"

"Hummm! Kamal wallahi ba zan ce komai ba a yanzu amma dai kam na san ina daf da faɗawa
cikin soyayya. Sai dai da yake ban saba da yinta ba ko kuma in ce ban taɓa ba har wani tsoro
na ke ji ni kadai idan na tuna ta."


Dariya sosai wanda a ka ƙira da kamal ya tuntsure da ita ya da fa ƙa fadar Captain Jamil ya ce.
"To kuma me ne ne abin tsoro? Kai dai akwai wani sauna wato idan ba a filin da ga ba baka da
wani kuzari."

"Eh daman na miji ai yaƙi a ka san shi da shi.


Da haka dai kamal ya yi ta tsokanar sa har wani lokaci.


Ganin ba wani sarki sai Allah yasa ta gyara zaman ta amma kuma sai ta tuna cewa ta gwada
buya mana ko Allah zai sa ta tsira idan da rabon rayuwar ta zatayi tsayi.

Da wannan tunanin tashige wani lungu wanda ba lalle a san da mutun ba a ciki.
Dan haka da Alhaji ya dawo ya sha mamakin rashin ganin ta awurin. Amma ko kaɗan baiyyi
tsammanin zata buya ba ko ta gudu tunda dai ya san gidan nan daga shi sai a halin sa suka
san kan gidan.


Amma wani abun mamaki duk yadda ya ne mi ya ganta ya rasata, har ya fara haɗe gumi yana
ƙiran ke baiwar Allah wallahi kiyiwa kanki ƙiyamar laili ki fito tun kafin na kamaki!
Amma shiru. Iya ta shin hankali ya shiga a wannan lokaci dan haka ya ƙira yarima ya ke sanar

masa ko dai yazo ya tafi da ita ne. Amma yarima ya ce sam bai dawo ba ya dai sake dubawa
tunda dai bawan da ya ke iya shiga gidan sai shi sai Hajiya su suka san password ɗin gidan .


Abin mamaki dai Alhaji ya rasa kubra kuma ya gaza tafiya gida daman shirin sa shine idan ya
biya bukatar sa da ita sai ya wuce gida da sa fe ya kaita wurin oga! Amma kuma ga shi ta
kwafsa masa. Saboda haka ba yadda za'ayi yabar gidan har sai ya ganta koda zuwa gobe ne
tunda dai ya san ta na gidan .
Wayoyin sa ya kulle duka saboda kar wani ya kira shi ma data gidan sa.

Hajiya kuwa iya tashin hankali ta shiga na rashin dawowarsa gida ga wayoyin sa duka ba sa
shiga.
Ta damu yarima da yaje ya duba ko yana dayan gidan amma sam ya ce ba wani abu sun yi
waya ya ce aiki ne ya masa yawa. Dan haka dole ta koma part ɗin ta.

Shi kuwa ya faɗa mata haka ne dan ta barshi tunda dai ya san inda daddy ya ke amma dai bai
dauka zayyi amfani da ita ba ne iya abin da ya sani zai kaita wajen oga ne a maimakon Hajiya
da suka so a abasu wanda tsautsayi ya jefa daddyn su ciki kuma yana addu'a ya rabu da su
lafiya kafin su cutar masa da mommyn sa.

Gari na waye wa Hajiya bata yiwa yarima magana ba ta fice kai tsaye gidan Alhaji ɗayan ta na
zuwa ta sanya hannu ta bude ta shiga.


Shi kuwa yana cikin falon abin duniya ya masa yawa dai yau yayi da na sanin rashin sanya cct
Camera a wannan ɓangaren. Kuma ya yi haka ne saboda ko da wani abu zai faru irin haka
wataran kar Hajiya ta je ta kallah kuma dai gashi yau da yana nan da ya masa rana .

Jin sautin shigowar mutun ne ya sanya shi ɗagowa cikin firgita sai kuwa ya yi arba da Hajiya,
tuni ya miƙe ya fara in ina yana mata sambatu na karya. "Wallahi ina cikin damuwa ne ban son
koma wa gida ki shiga ta shin hankali."

"Haba Alhaji ko wacce irin damuwa ce ai gwanda ka dawo gida ka kwana kusa dani....."

Jin sautin Hajiya ya sanya kubra ta miƙe da ga buyar da ta yi dan dole ta fita dan idan Hajiya ta
ganta tabbas zata samu fita daga wannan gidan. Tunda daman ta galabaita ga kuma yunwa ga
shawuya suman sa biyu kafin waye War gari bata san mai ya dame shi ba ga shi ko kuka bayyi
ba bata san me ne ne matsalar sa ba. Dan haka fitar ita ce mafita kawai

Alhaji yana yiwa Hajiya daɗin baki kawai sai ji ya yi kubra tana faɗin .

"Hajiya ki taimake ni wallahi zai kashe Ni ......!" Cike da ɗimuwa hajiya ta juya ta dube ta cikin
tsantsar mamaki ta ce "Kubra! Wa ya kawo ki nan "

Bata samu damar magana ba saboda Alhaji ne ya yi zaraf ya ce .

"Gwanda da kika bayyana kanki matsiya ciya! Ai yanzu kin gani tsintacciyar mage........ Halin ki
na taimakawa al'umma ya ja ana neman raba ki da mijin ki, ya faɗa yana goge ido tsabar iya
munafurci..


Ta shin hankali ne ya ziyarci zuciyar Hajiya gaba-daya ta ka sa gane inda ya dosa .... Ita kuwa
kubra ka sa koda motsin kirki ta yi.........



PG 19
Ganin irin sharrin da Alhaji ya ke neman yi mata ne ya sanya ta dur ƙushewa a wurin da take.

Hajiya ta kalle ta ta sake maida kallon ta a wurin Alhaji ta ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login