Showing 33001 words to 33733 words out of 33733 words

Chapter 12 - BAYAN GANGAMI Part1 Complete by Ummu Heebah.pdf

27 Apr 2025

2105

ɗaure zuciyata na haɗiye kukan da yake shirin to na asirin zuciyata na
ce, "Na ji na gode sosai amma yanzu abarmin gida!"
Take ya fara wani borin kunya dan haka ba yadda zayyi da ni ya ce, "Baby zo mu tafi idan
manya sun shiga lamarin ta barmin gida!" Da wannan yaudara ya samu kanta suka haɗe
dukkan kayan su suka fita suka barshi a wurin.

Ɗakina na shiga na zauna bakin gado na fara rafsa kuka saboda wallahi har zuciyata ina
ƙaubar Nasir ban taɓa tsammani zai sake ni saboda wata ba, sai gashi yau ya ƙaryata zuciyata
da gurbataccen tunanina.
Har ma nayi dana sanin shiga harkar sa.


Sai wajen awa biyu suka zo da mai jega ya kwashe musu kayan su ya jefa min shaidar sakin
ya yi gaba abinsa.
Bayan na sha kuka da godewa Allah akan irin tawa ƙaddarar nazaci bayan gangamin da na
sha a dajin idan na dawo gida zan samu salama ashe da ma nayi zamana da sabon mijin da na
aura a dajin wataƙila tunanin yarana da iyaye ya sa na zama mai gajeren kwana na mutu na
huta! Sai dai kash! Bakin alƙalami ya bushe, aikin gama ya gama.
Koda na je wa da mama da batun ta min faɗa sosai amma kuma ita da kanta ta ga rashin kirkin
Nasir da abinda ya min,kuma ta ce dani idan har ya zalunce ni na zuba idanu tun a duniya zai
ga sakamakon sa.
Haka na ci gaba da zama da yarana har tsawon watannin uku kuma koda baba ya dawo bai
wani ɗauki zafi sosai a kaina ba.
Dan haka na dan samu sukunin rayuwa ya yin da shawuya ya ke da shekara uku a rayuwar
sa .
Ba laifi ya zama lukuti duk da cewa gaba ki ɗaya shayarwar sa na yi ne cikin tashin hankali.

Su yarima da haidar kuwa yanzu suna jss 2 ya yinda zulfa'u ta ke primary 4
Ba zato ba tsammani watarana muka tashi da wata mutuwa wacce ta yi sanadiyar shigar
dukkan dangin mu tashin hankali wanda idan kuka cire mama da baba to bawan da ya kaini
tashin hankali kai wani lokaci ma har gwanda su mama da baba tunda suna zaune saɓanin nida
hankali na ma ya gushe. Tunda dai da zarar na dago kai idan na tuna cewa babu basma a cikin duniyar da na ke sai na
sake sume wa,a Gaza gane wa yake dan dama dama tsakanin nida jamil, kamar akan mu aka
fara mutuwa.
Na shiga wani yanayin da har sai da aka fara sallama rayuwa ta tunkunna na dawo ɗan kaɗan

Na sha jinya na lalace amma bayan wani lokaci na samu nutsuwa har ma na fara fita aikin da
gwamna ya sama min wanda ya samu ne a lokacin da bani da lafiya, an yi shine amin bazata
amma kuma da aka zo aka tarar bana hayyaci na.
To da na dawo normal kuma sai na fara rayuwa kamar komai bai faru ba duk da dai cewa

akwai tabon a zuciyata.
Ji na nake kamar wata sabuwa yadda komai ya ke guda cikin rayuwarmu nida yarana lafiya.

Amma dawowar Nasir cikin rayuwa ta, da irin kashin shanun da ya shafamin a fuskar dukkan
wanda yazo aure na, shine tashin hankali da ya zama barazana ga rayuwa ta har ya kai ga
jama'ar da muke tare duka suna baya baya dani.

Ban gama sanin Nasir mugu bane sai da ya min wani mugun sharrin wanda duka duniya ta
ɗauka ya barni cikin halin ni 'yasu........

Alhamdulillah anan na kawo karshen book1


In sha Allahu zuwa wata na biyu a sabuwar shekara wato fabarairu zan zo muku da na biyun sa


Ku kasan ce dani ta ku Ummu HEEBBAT.


Ina muku fatan alheri fans a duk inda kuke na gode sosai da yadda kuke min addu'o'in alheri
saboda wannan littafin


Ƙarshe.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login