Showing 15001 words to 18000 words out of 33733 words
Chapter 6 - BAYAN GANGAMI Part1 Complete by Ummu Heebah.pdf
amsa min. Abinda ya sanya na ji kwarin guiwa shine
yadda ta amsa min ɗin ba wata nuna kyama ko kuma rashin son jama'a. Dan haka na fara koro
mata ƙudirin da ke zuciyata na son wurin fakewa kafin gobe saboda ina cikin tashin hankali
kuma ban san ina ne nan ba, amma dai na san sunan garin mu kuma idan na samu mota har
gida zan iya gane wa.
Shiru ta yi wanda har sai da na fara tunanin ko ba zata taimaka min ba ne sai chan kuma tace,
"To na ji dukkan bayanin da ki ka min, sai dai yanzu duniya ta lalace ba gaskiya. Amma duk da
haka ba zan barki cikin wannan halin ba zan taimake ki, abin da na ke so da ke shine ki sanar
min da abin da kike so. Na farko na taimaka miki saboda ke mace ce kuma bana son na ga
mace cikin tashin hankali a duk inda ta ke.
Idan kuma kin zo da niyyar wani munafurci ne ko yaudara to Allah ya na ganin ki kuma ya mai
da miki kanki .
"Wallahi Hajiya ba zaki sa me ni da ko ɗaya daga ciki ba in sha Allahu.
"To Allah yasa ina saura ranki."
Ta faɗa tana gyara mayafin da yake ka faɗar ta.
Dago da kaina na yi na dubi shawuya cike da tausayawa na sake mai da kallo na gun Hajiya na
ce, "Wannan nake son a fara taimaka da riga saboda tunda yazo duniya bai taɓa sanya ko da
wando ba ne. Sai kuma idan da abinci ataima kamin da shi saboda wallahi na kai tsawon mako
guda ban ci komai ba.
Sai abinda ya samu cikin kariyar Ubangiji na rayu nida wannan yaron da na raɗa nasa suna
shawuya.
Jin kalamai na tuni na ga tausayi ya wanzu a
fuskar ta, ta kuma jin jina min ta ce, " Muje da ga ciki."
Ta faɗa tana mai juyawa na bi bayan ta cike da farin ciki yau ɗaya zan samu nutsuwa a rayuwa
ta na ci abinci na zauna wuri ɗaya ba tare da wata fargaba ba, tunda dai na ga a lamun
tausayina a wurin ta.
Ciki muka shiga ta kaini wani ɗaki kamar dai dakin sauƙar baƙi wuri ta nuna min na zauna ta fita
jim kadan ta dawo da abinci shikafa da miya harda nama ga wani haɗin shayi mai kauri ta ajjiye
min.
Ta sake fi cewa ta dawo hannun ta dauke da kayan sawa na wa da kuma na shawuya masu
kyawun gaske.
Farin ciki fal zuciyata kamar zanyi ihun murna na durƙuhe a wurin ina hawaye ina godiya .
"Ba komai baiwar Allah ki ci abinci ."
Ta faɗa ta na fita a ɗakin .
Ai kuwa ban yi ƙasa a guiwa ba na fara aikawa cikina abinci sai da na ji na yi hani an tukunna
na ture gefe guda na dauki kofin shayin da na ɗaga sai da na shanye na sauke, wata zufa ta ke
sai na yi hamdala ga Allah .
Mai makon na sanyawa shawuya kaya sai na mance da wannan batun kawai na hau kallon sa
ina masa waƙa abinka da uwa da ɗa.
Shikuwa ƙuru ya yi yana kallona domin ko dariya bai fara ba, idan yana yi ma ban sani ba tunda
ban taɓa samun nutsuwa ba sai yau.
Har wajen minti talatin tukunna Hajiya ta shigo ta dube Ni ta ce, "Ga bayi nan cikin ɗakin kiyi
wanka kiyi ma yaron ki shi ma sai ku sanya kaya ."
Da to na amsa mata ta fita na ta shi na shiga cikin bayin na ga komai yadda yake na san kan
abin tunda dai ni ma y'ar zamani ce kuma wayayya ƙaddara ce ta mai dani haka! Ruwan zafi na
haɗa na sanya shawuya na masa wanka tas bawan Allah yana ta kallo na shidai na ajjiye shi
gefe guda nima na fesa wanka harda su gasa jiki. Na sake dauraye shi fes muka fito zuwa
ɗakin kayan na sanya shi ma na saka masa na shi.
Ba laifi mun ɗan farfaɗo sosai sai dai uwar rama a gareni kam ba magana, saboda kallo ɗaya
zaka min ka ɗauke kai !
Tuni na ji wani irin bacci mai nauyi ya kamani dan haka sai na kwanta kamar wani gida na samu
ba wata fargaba, aikuwa bacci ya ce salamu alaikum.Na jima ina bacci tukunna na farka na ga
Hajiya zaune kusa da ni ta yi min murmushin.
Na ce "Dan Allah kiyi haƙuri wallahi ban san baccin yazo min ba."
"Kai haba dai ai shi bacci baya sallama karki damu. Yanzu kina a jahar Nijar ne kuma cikin garin
zinder. "
Idanu na zaro ta re da furta, "zinder!!"
"Tabbas kuwa."
Ta bani amsa.
"Hajiya ji na yi abun ya yi nisa nifa y'ar jahar Yobe ce kuma a ƙaramar hukumar kanamma.
"Chab! Gaskiya kina ne sa. Amma me ya kawo ki nan? Kuma me yasa kika faɗa cikin wannan
halin?
Shiru na yi kamar ba zan ce komai ba, saboda ban son na tuna koda tsinke ne a cikin labarin a
binda ya faru da ni amma ya zama dole na sanar mata halin da na ke ciki.
Dan haka na tsunduma ƙogin mummunan labari na farko har zuwa yanzu.
Banyi mamaki ba ganin fuskarta sharkaf da hawaye, saboda na san labari na ya chan chanci a
yi masa kuka.
Saboda na fuskanci ƙalubalen da ni kaina ban taɓa tunani ba.
Ta tausaya min matuka sosai yadda kukasan y'ar uwar ta ta jini.
Cewa ta yi da ni, " Ki kwantar da hankalin ki in sha Allahu idan mijina ya shigo gida anjima
zamuyi magana, kuma zaki koma gida da yardar Ubangiji."
Na yi farin ciki mara misaltuwa sosai da sosai dan banyi tsammani samun haka daga gare ta
ba.
Amma kuma babu abinda ya fi ɗaure min kai kamar yadda na ji wayar da Alhaji mijin Hajiya ya
ke yi da dare bayan ya shigo gida........
PG 15
Wani irin yawu na haɗiye da na ji batun nasa saboda na san ko shakka ya ganni ko ya ji labari
na to tabbas nida shawuya gudun mu ya zama na banza! Tunda abinda ya ke nema ne ya
samu har gida.
Kamar na gudu idan na tuna da irin wayar da yake yi saboda kalaman sa babu Allah a ciki
Tunda na ji yana cewa ina zai samu mace mai ɗayen jego ya haiƙe mata kuma sanan ya bada
jinta tunda ba zai iya bayar da matar sa ba!
Ban san me suka ce masa ba dai na ji ya sake ce mu su zai duba lamarin.
Kuma na san tabbas yau Hajiya zata sanar da shi zuwana. Abin da zai ji kawa shine kaya ya
tsinke a gindin kaba!
Ni kadai na ke ta batun da ba ni da mafita. Shin ko sulalewa zanyi na gudu ne a cikin daren
yau? To idan na gudu kuma me Hajiya zata fassara Ni?
Idan kuma na zauna har garin Allah ya waye to tabbas na san Alhaji zai so ya ganni!
Da wannan tunani dai na ke zaune har na fara jin ya kamata na sanar da mahallici na domin
shine komai na wa a duniya ta da kuma lahira ta.
Alwala na yi na hau darduma na fara karatun Alkur'ani cikin ƙasa da murya tunda dai ina da
sauka a kaina dan haka na yi ta karatu har zuwa wani lokaci da bacci ya fara cin ƙarfina,
addu'o'in ne man tsari na yi na sanya sakata a ɗakin domin ji na ke cikin dare ma Alhaji zai iya
zuwa ya same Ni dan haka sai da na sa sakata na kwanta.
Basma ce ta ke ta faman tafiya bakin titi hannun ta dauke da manyan ledoji na kayan ɗanyen da
ta siyo a kasuwa hannun ta ɗaya kuma rike da hannun yarima har sun zo zasu gifta wata mota
ta jam'ian tsaro ta ji yarima ya kwace hannun sa daga na ta motar ya nufa da gudun sa ya sha
gabansu wanda tilas direban motar ya ja wani wawan burki! Ganin abinda yarima ya aikata tuni
ta shiga damuwa saboda da sun buge shi ya zatayi ? Kuma ta san halin sojojin nan da masifa
shin yanzu wanne hukunci zasu ɗauka a kanta tunda zasu ganshi ƙarami ne ƙila suce ita ce ta
sanya shi .
Tuni wani soja ya duro daga saman motar ta su ya tun kare shi, kafin ya yi magana yarima ya
fara magana kamar haka,. "Yawwa zo ka kashe ni tunda ko ina kuna nan kuna yawo amma kun
ƙi karɓo min mommy daga hannu y'an ta'addan da suka sace ta! Ka kashe ni don Allah na huta
da wannan damuwar! Kashe ni ko zan dai na tuna halin da mommy ta ke ciki. Bana son rayuwa!
Na ce bana son rayuwa!!
Ya faɗa cikin amo mai sauti! Wanda dukkan wanda ya ke kusa sai ya juya.
Ga baki ɗayan su sojojin sai da suka tsaya suna kallon yarima, ni kuwa ƙamewa na yi da
tunanin irin hukuncin da yaron zai jamin.
Amma cikin iko na Ubangiji sai na ga ɗaya daga cikin sojojin ya zo kusa da shi ya durƙusa ya
rungume shi ya na hawaye.
Cike da mamaki na saki ledar kayan hannun na suka zube ƙasa saboda ban taɓa ganin soja
yana kuka ba. Kuma ance suna da taurin zuciya ba sa kuka da wuri.
Amma kuma sai ga akasin haka a wurin wannan sojan.
Ya ce "Yarona ka yi hakuri mommy zata dawo gida ka ji, ka tuna min yadda na rabu da uwata
amma ban samu ko ganin gawarta ba. Haƙika uwa uwa ce, idan har wannan yaron zai damu da
uwar sa to tabbas uwa ba abin ya da wa ba ce. Haƙika na tausayawa wannan yaron saboda
yana cikin maraicin uwa, kuma wallahi da da yadda zanyi a yau sai na je na dawo da mahaifiyar
sa. Amma sai dai kash! Nima umarni na ke bi.
Ya faɗa yana ƙarewa sauran sojojin kallo .
Wani daga cikin sojojin ya ce ina wacce kuke tare? Ko kai kaɗai ne?
Wata irin faɗuwar gaba ta riske ni saboda na san dole sai sun min tsawa kuma ban kaunar ko
da kallon soja ne a rayuwata bare magana da shi.
Dan haka yarima yana nuna ni na fara mazari ina ƙifta idanuna.
Kalaman sojan ne suka daki masarrafin da ke kai min sauti, wani yana yi na ji gaba ɗaya ya
riski zuciyata saboda ba haka ka tsammachi muryar ba.
Dan na zaci zan ji ta kamar sauƙar aradu ne.. amma kuma sai na ji ta cike da sanyi da nishaɗi
wanda har sai da na lumshe idanuna na bude.
Ganin ban ce komai ba wani daga sama ya rattaɓa min tsawar da sai da na take ledar kayan
miyan.
Da in ina na fara magana, "Don Allah kuyi hakuri yana cikin damuwa ne wallahi bani na sanya
shi ba. Kuyi hakuri."
Murmushin na ƙasan ya yi ya ce "Ka ma shi ku tafi ki sanar min da gidan ku an jima zan so
wurin baban sa idan yana nan."
Sanar masa na yi cike da fargabar abinda zayyi na kama hannun yarima na su ri kayan miyan
na yi gaba ba ko wai wa ye.Sauri na ɗinga yi har muka dawo gida.
Koda mama ya Fido ta ganni cikin wannan halin ta san akwai abin da ya faru, dan haka duka
suka tsare ni da tambaya.
Banyi ƙasa a guiwa ba na sanar musu komai da ya faru.
Kowa ya yi mamaki a kan abinda yarima ya aikata.
Dan haka Hadiza ta kama hannun su ta ce "Karka sa ke wasa da rayuwar ka da sun buge ka
fa? Bana son irin haka.
Shi kuwa faruk kasa cewa uffan ya yi har sai da aka ce wani soja yana magana a bakin ƙofa
tukuna ya yunƙura ya fita saboda baba baya nan dole shine zai wakilci gidan .
Koda gari ya waye kubra ta kasa samun sukuni, jin an taɓa kofar ba ƙaramin tashin hankali ta
shiga ba da ƙyar ta samu ta buɗe.
Ganin Hajiya dauke da manyan fulasai na abin ƙaryawa ya sa dole na ƙirkiri murmushin dole
tare da russunawa na gaida ta .
Amsawa ta yi cikin sakin fuska ta kuma sanar min da na ci abinci zata zo muyi magana anjima
idan na gama.
Ko da ta fita sam na kasa sanya abinci a bakina saboda sai na ji kamar an sanya min wani abu
acik. Amma idan na tuna da halin kirki irin na Hajiya sai na ji kawai bazata sanya min komai ba,
kuma ƙila bata san ma mijin na ta yana aikata wani mummunan aiki ba.
Da haka na ƙudiri niyyar cin abincin.
A falon Hajiya kuwa Alhaji ne zaune yana waya cikin raɗa yana cewa, "Ranka ya daɗe in sha
Allah komai ya zo karshe.......
PG 16
Shigowar Hajiya ya sanya shi ƙatse wayar yana faɗin "Hajiya bari na je na dawo wani lamari ya
ta so min da wuri."
"To Alhaji kuma na ce maka muna da baƙuwa mai neman taimako amma da ka tsaya ka ganta
ai."
"Kash! Hajiya ina ce a gidan zan kwana? Maganar nan abarta idan na dawo ma yi ta."
"Shike nan yadda ka ce, Allah ya dawo da kai lafiya."
Da Amin ya amsa ya na saɓa binjima a ka faɗar sa ya fice.
Cike da damuwa ta zauna a falon saboda ta so ace ya ji batun ta sun taimaki wannan baiwar
Allah da ta ke neman taimako.
A ɓangare Kubra kuwa abinci ta ci ta ƙoshi saboda ta miƙiwa Allah lamurran ta duka!
Shigowar Hajiya ne ya sanya ta ta yi zuru tana jiran taji mai zai faru.
Hajiya kuwa zama ta yi gefen ta ta ce, "Kubra, ina me baki haƙuri saboda Alhaji ya fita cikin
gaggawa bai tsaya ya ji batun ki ba, na so ace ya tsaya na sallame ki yau kin ko ma ga ahalin
ki.
Sai dai kash! Ya fita tun bai ji ba kuma ba zai dawo ba sai dare.
Dan haka don Allah kiyi hakuri zuwa gobe sai ki ta fi."
Tunda ta fa ra batun ta na sauƙe wata kyakkyawar ajiyar zuciya saboda na ji akasin abinda na
ke tunanin ji.
Ganin ni ta ke saurare sai na yunƙura na buɗe baki na ce "Hajiya na gode sosai da taimakon da
kike min ko na ce ki ke kan yi. Amma idan ba damuwa zan iya ta fiya ba tare da Alhaji ya dawo
ba, tunda wallahi iya taimakawa a rayuwa kin taimaka min. Tunda na shiga wannan halin ba
wanda ya taimake ni kamar ki."
"Haka ne, ina son ki haɗu da Alhaji ne saboda ki samu ta go mashi mai yawa. Amma idan kina
son tafiya gida sai na kaiki na sanya ki a mota ki tafi.
"Yadda kika ce Hajiya ni mai biyayya ce."
"Na fuskanci kina son zuwa gida kuma daman dole ki so hakan duba da irin yadda kika sha
gwagwarmaya.
An jima yarona yarima zai zo sai ya kai mu ta sha."
Jin ta ambaci sunan yarima sai da zuciyata ta doka! Ya Allah na ko yarima ya rayu? Ko ina fullo
ta yi da shi? Tuni na ji kamar na yi tsun tsuwa na je gida.
Ganin ban ba ta amsa ba ne ya sa ta ce, "Bari na shiga na shirya kafin ya zo."
Kai na gyada mata a lamun to sai ta wuce cikin part ɗin su na koma cikin sabon tunani.
Koda haidar ya fita ya samu soja tsaye gaisawa sukayi da shi ya ne mi da ya ga na da mahaifin
su.
Sai ya sanar masa baya gida amma idan ya dawo zai raka shi wurin sa kawai ya basu layin sa .
Kafin sojan ya yi yunkurin bayar da layin sai ga baba Bala da Nasir ɗin sun dawo .
Ganin soja a wurin sai da zuciyar Nasir ta buga yana fatan ace labari kubra aka zo masa da shi.
Bayan sun bashi wuri ya zauna ya ke sanar musu da dalin zuwan na shi. Yana son ya ji ya abin
ya ke daga bakin manya.
Labarin suka ba shi tun daga farko har ƙarshe da kuma abinda fullo ta sanar musu game da
Kubra ɗin.
Koda ya ji komai ya yi matukar girgiza sosai Dan haka ya miƙe tsaye yana mai mai ta kalmar
innalillahi wa'inna ilaihirrajiun.
Tuni suka shiga halin ɗimuwa suna son sanin me ya ke faruwa.
Kallon su ya yi ya ce baba haƙiƙa mun tafka babban kuskure wallahi . Saboda duk lokacin da
muka gaza haɗuwa dasu to muna shirya musu kwanta bauna ne daga baya.
Ina mai ɓakin cikin sanar muku da ce wa bayan fitar su ba jima wa cikin daji jirgi ya sanya musu
wuta duka sun ƙo ne. Kuma bana raba ɗayan biyu matar nan sun dauke ta, dan da basu dauke
ta ba da tabbas ta bayyana yanzu.
Nasir jin kalaman sojan ya yi kamar wutar garwashi wanda bai san sanda ya chakumi wuyan sa
ba amma kuma ko kalma ɗaya bai furta ba ya