Showing 3001 words to 6000 words out of 33733 words

Chapter 2 - BAYAN GANGAMI Part1 Complete by Ummu Heebah.pdf

27 Apr 2025

2106

na ƙi lallaɓa sha wuya ba da hannun da na ke riƙe
da shi ba, sannan ta shin hankalin shine yadda wannan murguje jen ƙaton ya ke nufo mu.
Amma cikin iko na Ubangiji sai na ji wata murya daga bayan mu tana faɗin
"Ansar ga Zaid nan ya tashi ba madara."
Wanda a ka ƙira da Ansar kuwa ba kowa bane fa ce wannan wanda ya tunƙaro mu, sai naga
ya tsaya yana cewa. "Ashe shine ke ta tsula kuka? Na zaci wani yaron muka samu." Yana fadar
haka yana juyawa .

Aikuwa muna ganin ya juya muka dauki hanya ba tare da mun sake juyawa ba, duk da irin
yadda zuciyata ta ke harbawa bai sa na kasa sauri ba har muka isa bakin wani katafaren wuri
wanda ya ƙawatu da ado amma shi ma duka na tanti ne. Wasu zaratan maza ta ko ina a
lamunsu masu gadi ne tunda kowa da makamin sa.
Haka muka dinga kutsa wa muna wuce su saboda bisa dukkan a lamu sun san da zuwan mu,
dan ba wanda ya ce damu cikan ku. Tafiya mai tsayi mukayi cikin tantin kafin muka iske kofar
shiga wurin OGA gaba ɗaya.
Shigar mu ke da wuya na hangi wata kujera irin ta juyawar nan, wanda ya ke zaune kuma ya
juya baya, ga wasu zaratan maza daga gefen sa suna tsatstsaye da manyan bindigu masu
shegen tsayi kowanne fuska a haɗe.
Cike da taraddadi na tsyaa ganin Kausar ta saki hannuna ta juya waje, cikin zuciyata na ce
"Yau na ga ta kaina ya zata barni a wannan wurin da ba mace sai maza, ga manyan makamai ."
Ina tsaka da jawabi da zuciya na ji wata murya cike da izzah da kauri kamar ta saraki ta ce,
"Kubra! Ina Miki Barka da zuwa , Biyayya a kan komai waji bi ne, sannan kuma kada kiyi wasa

da rayuwar ki, ina nufin duk sanda kikayi yunkurin guduwa tabbas! Zan sa a kashe ki da kaina."

Wani irin ruwa ne ya cinye ne dajin
maganar sa ta karshe saboda firgicin kisan da na ji ya ambatamin, domin Ni kuma a tawa
zuciyar bana jin zan bar ahalina na rayu a wannan wurin . Jin ruwan bai sake jiƙe min sawayena
ba yasa na sunkuya, ashe fitsarin wahala ne tare da jinin haihuwa! Tashin hankalin shine ganin
a babbar fadar OGA gaba ɗaya hakan ta faru. Ganin irin kallon da ɗayan na tsayen ya ƙure ni da shi yasa tuni na durkushe a gun na ce,
"Dan Allah kuyi hakuri ba da gangan na yi ba. Kuma na ji duka batun na sa sai dai......." Wata
uwar tsawar da aka kirɓamin ce ta sanya Ni haɗiye maganata....

" Ke Kubra anan ba'a neman wata alfarma sai abin da aka ce da kai kawai dan haka ki kama
bakin ki."

Kasa cewa na yi komai amma kuma tuni wani irin ciwon cikin bayan haihuwar nan da yake
kama mutum ya murɗe Ni har na fita cikin hayyacina wani abun mamaki shine ina dawo wa
hayyaci na na ganin bakin tantin kausar tana tare da ni sai dai kuma babu shawuya!
Cike da damuwa na ce "Ina yarona dan girman Allah."
Jujjuya kai naga kausar ta yi kuma ga wasu hawaye da suke son zuba daga idanun ta tana
kuma toshe bakin ta saboda kar wani ya ji me zatace nie oho ban sani ba.
Na yunƙura na sake cewa, "kashe shi suka yi ko kuma ƙarɓeshi sukayi?"
Ita dai bata ce komai ba ta kama hannu na da niyyar ta jani mutafi amma ƙyam na jaɓe a wurin
. Ganin haka ya sa wani dake gefe ya saki wani harbe wanda ban san sanda na gusa daga
wurin ba .
Amma duk da haka tafiya kaɗan mukayi ina tuna shawuya baya hannuna na zauna na fashe
da wani uban kuka mai cin zuciya harda birgima. Nan fa kallo yadawo kan mu......


Jejen fillo kuwa bayan abu ya lafa ne suka dawo da yarima ya gama galabaita ta sauke shi
daga bayanta amma me, tana sauke shi ta gane a she ma gawace a bayan ta! Tashin hankali
wanda bashi da rana ai tuni fullo ta yi waje ta fara kurma ihu tana faɗin " jama'a ku she she ni
yaron a mana ya mutu! Uwar shi ta bani shi na rike kar ya mutu ! Wayyo jama'a ku she she ni,
na ce yaron ya mutu ku she she ni."

Jin kwarmaton ta ne ya sanya mutane da suke zaune gefe gefe domin jira zuwa anjima su shiga
gari suga ya abin ya ke, sai suka taru a gidan, kowa yana shafa yarima abu ɗaya yake cewa ya
mutu! Fullo kuwa banda ihu ba abinda take zabgawa. Hakuri aka shiga bata aka fara tunanin
yadda za'ayi masa sallah mata suka zauna mazan suka fita waje. Fullo ta sake komawa gurin yarima ta zauna ta rungume shi tana kuka ta ce "Yaro bance wa
innarka zan bar ka ka mutuba ya zakamin haka do Allah. Haba yaro yau na shiga ukku!
Kamar a mafarki kawai yarima ya yi wata wawuyar ajjiyar zuciya wacce ta sanya fullo razana a
guje ta miƙe tana faɗin "Aradu ya tashi bai mutuba daman yaro ba zai mutuba yatona min asiri
."

Cike da alhini mazan suka taru kansa suna masa addu'o'in da kuma zuba mushi ruwa a fuskar
sa kadan kaɗan.

Cikin gari kuwa ba kowa sai wanda suka shigo daukar kayan su domin tafiya hijira dan haka
duk wanda ka gansa dauke ya ke da akwatin tafiyarsa ko buhun kayan sa.
Chan sai ga zulfa'u yarinya ƙarama tana ihun kuka ta na cewa "Mama mama ina mamana ya
yarima kajo ka ƙaini mama" Jin batun na ta ne ya sanya wani dattijo ya kalle ta ya matse
kwallar da ke fita daga idanun sa haƙika dole ya dauki yarinyar nan, sai dai idan ya dauke ta
mai zai bata shida bashi ko biyar a jikin sa? Kuma idan ya barta ya yi rashin hankali saboda
yarinyar bata wuce irin shekara huɗu ba ɗinnan da
dai me wayoce, yanzu haka Allah yasan halin da iyayen ta suke ciki wajen ne manta . Hannu ya
miƙa da zummar daukar ta kuma sai ya tsaya chak!! Kome ya gani ko ya tuna.........


PG 4

Ganin wasu samari sun tun karo shi ne yasa bai dauki zulfa'u ba, saboda yadda suke kallon ta
suna murmushi kamar da sanayya a tare da su.
Da sallama a bakin su suka ƙaraso wurin tare da faɗin, "Baba wannan yarinyar ina ka same
ta ? Kai ma sha Allah wallahi mun jima muna neman ta tun faruwar abin ga Chan baban ta shi
ma ya bazama tun safe ."
Kallon su ya yi ya ce, "To bayin Allah wannan dai nima yanzu na ganta kuma ina shirin na
dauke ta na ga tana kallon ku kuma kuna kallon ta shine ya sa na dakata da ɗaukar tata.

Amma na tausaya mata saboda yarinya irin wannan a wannan lokaci ai hatsari ne a ce bata
tare da iyayen ta."
"Haka ne baba wallahi an sha wuya matuka ainun kasan da yake abin da ya faru lokaci guda
ne shine fa kowa ya tarwatse. Amma bari na ƙira Nasir ɗin yazo ya ganta ko hankalin sa zai
kwanta." Ya faɗa yana kara wayar sa a kunnensa .

Jim kadan naji ya na sanar da nasir ɗin cikin farin ciki. Aikuwa bai ɓata lokaci ba ya zo wurin,
saboda ba nisa tsakanin inda suke da inda ya ke shiɗin.

Ita kuwa zulfa'u ganin su faruk ya san ya ta farin ciki domin faruk ƙani ne a wurin nasir dan
haka tuni faruk ya rungume ta bisa ƙirginsa.

Koda nasir ya zo hannun ya mika ya karɓe ta ya rungumeta a ƙirginsa ya fashe da kuka ya ce,
" Babyn mommy, yau na sa me ki jiya na samu haidar, amma kuma na rasa mommy da
yarima...." Ya ƙarashe maganar yana sake fashewa da wani kukan kamar mace.

Baba tsoho ya du be shi ya ce " yaro hakuri zakayi wannan lokacin da muka tsinci kan mu a
cikin sa kowa ya jijjiga! Amma abin da ya fi sauki shine mubarwa Allah komai mu miƙa lamurran

mu zuwa gare shi ."

Majinar kuka Nasir ya zuƙe ya goge hawayen ya ce "Haka ne na gode baba."

Da haka suka yi sallama suka wuce gida .

Kowa ya na zaune jungum-jungum kamar gidan ma koki . Ya Fido itace uwa a wurin Kubra sai
ƙannen ta mata guda uku wato Maryam da Hadiza da basma. Sai kawu Bala shine uba a gare
su wanda ya samo sunan ne daga yaran ƙanin sa da yake gida guda suke zaune.
Gefen ya Fido salame ce matar ƙanin kawu Bala sai goggo saratu surukar Kubra wato uwar
Nasir da su faruk.
Lokacin da su Nasir suka shigo kowa sai da ya mike duk tunani su zasu ga har da Kubra zasu
shigo, amma ganin su su kaɗai shine abin da ya sake kashe musu jiki, ya yin da Maryam da
basma suka zauna daɓas a wurin don su ko kula da zulfa'u ma basu yi ba sun zaci ba'a samo
kowa ba . Jin ana cewa sannu zulfa'u Allah sarki yarin ya ba wayo sanann suka gane ashe an same ta .
Jin ana ambatar sunan zulfa'u ya sanya haidar fitowa daga ɗaƙin kaka saboda tun da a ka sa
me shi ya ga babu su bai fitoba a ɗakin yana ta faman kuka.
Da gudun sa ya rungume ta ya fara kuka, "Babyn mommy mun rasa su mommy da yarima shike
nan sun kashe mana su yanzu ba mu da mommy mukam .
Jin kalaman sa tuni Maryam da basma suka fashe da kuka domin kamar dama jira suke idanun
su fal hawaye.

Saboda kaf cikin su ba mai kirkin aunty Kubra tana da hakuri duk da cewa tana da tsiwa amma
bata barin su cikin damuwa, komai na su idan tana da halin yi tana musu, hatta ya Fido Kubra
ce ke mata dinki lokaci bayan lokaci ita da baba.

Baba ya dube su ya ce , "Kuyi shiru in sha Allahu zata bayyana nan bada jimawa ba...." Ya faɗa
yana sunkuyar da kansa domin shi kansa ƙarfin halin rashin ɗiyar ta sa yake, musamman idan
ya tuna yadda take dauke da juna biyu haihuwa ko yau ko gobe.
Maryam ta ce, "Baba taya zamu iya dena kuka bayan ba musan halin da y'ar uwar mu ta ke
ciki ba? Ga ciki jikin ta, yanzu baba idan aunty Kubra na hannun mugaye me suke mata a
wannan lokacin ........tana kaiwa nan Nasir ya mike ya fice domin idan yana jin irin wannan
batun zuciyar sa zata iya bugawa.
Haka suka yi ta kokawa har suka hakura suka koma zaman kurame.


Dajin su OGA gaba ɗaya

Kuka sosai Kubra ke yi na rashin shawuya amma ba shi ba zancen sa har kusan dare. Iya
tashin hankali ta shiga ba kaɗan ba! Saboda ji take kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu .

Kusan shida na yamma wani mai fuska a rufe ya shigo tantin na su yana rike da shawuya ya
mika mata shi bai ce ƙalaba ya juya.
Cike da farin ciki ta ke kallon sa amma kuma ta kasa bude shi saboda firgita! Saboda ji ta ke
kamar gawa ya kawo mata.
Tunawa da yarima tuni ta yaye mayafin da yake rufe ta ga yana bacci abinsa cikin kwanciyar
hankali.
Ajiyar zuciya ta sauke, Amma kuma yau gaba ɗaya hankali ta ya karkata zuwa ga a halin ta! Ji
take yau dole ta je gida ko ta wane hali dan haka ta ƙudirci niyyar yau cikin dare dole ta san
abinyi wajen tserewa duk da bata san ko ina ba.......


Cikin dare kowa ya kwanta masu tsaro sun baje bindigu ta ko ina saboda su basa bacci haka
aikin su yake sai dai da safe ga kuma yadda macizai ke kai kawo a wannan dajin .

Amma duk da haka bai hana Kubra ta goyi shawuya ba ta su ɗaɗe ta fito a tantin cikin bakar
abaya, saboda kausar ta tafi gurin mijinta ita ma. Cikin sanɗa take tafiya abin da tana duba
gaba da bayan ta . Har tayi nisa da tantin saboda yadda take bin lunguna, sai dai kash jin
saukar wani abu a wuyanta tuni ta daskare a wurin ta kasa koda motsin kirki ..........



PG 5



Jin wani abu mai sanyi ya naɗemin wuya shi ne yasani suman tsaye don tuni zuciyata ta hau
dakan luguden uku uku. Sanyi da santsin abin shine ya tabbatar min da cewa maciji ne! Cike da
tashin hankali na ƙame wuri guda dan lumfashi ma da ƙyar na ke sauƙewa.
Jin yana tunƙarar hayewa kaina ta baya na fasa wani gigitaccen ihun da ya amsa kuwwa a
wannan dajin, har na mance mai ya fito dani.
Kafin kace Kwabo tuni wasu zaratan maza masu ɗauke da manya bindigu suka kewayeni tare
da haske min fuska. Hannu ɗayan ya sa ya kama macijin dake jikina ya jefar tare da tarwatsa
shi da albarushi.
Ƙarar albarushi ce ta sanya shawuya fasa ihu shi ma, jin haka ɗaya daga cikin su ya ce, "Wato
guduwa zakiyi ko? Ashe baki da hankali! Ance Miki ɗan gida ma yana iya fita a wannan ƙauyen
ba tare da an masa Rakiya ba bare ba ƙo?" Cike da fargaba na ke sauraran maganar sa mai
kama da tsawar aradu a kunnena.
Tsawar da ya sake jefamin ce ta sanya Ni tilas na yi magana .

" Ba gudu zanyi ba kawai na rasa yadda zanyi da yarona ba shi da lafiya yana min kuka shine
na fito nai man taimako. " Na tsara masa wannan ƙaryar da bansan sanda ta shiryuba cikin

ƙirjina.
"Wuce munafuka ko me ne ne ma dai zamu haɗu watarana idan gudun kike niyya ma,kuma
kinsan dokar gidan nan duk wanda muka kama da niyyar gudu kisa ne. Kema kawai na Miki
uzuri ne saboda baƙuwace ba don taausayi ba!"
Kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki haka na dawo tantin da na bari na zauna ina rafsar kukan
bakin ciki.
Sai yaushe zan kufce ne a wannan wurin? Ya Allah na ina yarima ina zan ganshi, duk runtsi
jikina yana bani ƙila zulfa'u suhadu da Nasir ko a mace ko a raye. Ya Ubangiji na yarima fa? Ta
faɗa tana sake fashewa da kuka.
Ya Ubangiji yarima yana cikin wani hali na gudun ceton rai na barshi, Allah kasa yarimana bai
mutu ba ya rabbi idan yarima yana raye Allah ka sa da shi da ahalina su samu rangwame na
rashi na.
Da ire-iren irin wannan tunani bacci yayi nasarar saceta durƙushe da goyon shawuya.




*Dajin Fulani*


Yarima zaune yana ta muzurai da idanuwa, Fulani zaune gefen sa tana bashi fura amma yaƙi
karbar furar.
Ta ce "Yaro do Allah ka sha fura kaji. Kuma ka faɗa min suna mamarka sai na kaika gida na san
yanzu tana chan tana neman ka." Jin ta ambaci gida tuni ya buɗe baki ya kurɓi furar yana
ruwan hawaye ya ce. " Sunan ta Kubra muna ce mata mommy ."
"Yawwa yarona kaifa ya shunan ka to do Allah ." Fulani ta faɗa saboda bazata iya tuna sunan
da ta ji mamarsa ta na faɗa masa ba.

"Yarima." Ya furta a taƙai ce.
"Yawwa yarima yarona yanzu anjima zan shirya idan munje shikin gari sai ka hiɗi mani sunan
anguwar ku na kaika."
Kai kawai ya girgiza ya sake gyara zaman sa idan ya tuna mommy sai ya fashe da kuka saboda
ya san ta mutu tunda ya ganta da jini kuma ga jirgi da yan bindiga sun kusa gunta suka gudu

Fullo bata hana shi ba saboda tasan dole ya yi kuka duk da cewa yana yaro amma sarai ta san
bazai mance komai ba.

Misalin biyu na rana ta fita ita da yarima suka fita bakin titi ta tare musu abin hawa suka shiga
gari .
Garin da har yanzu ko kwatan kwatan jama'ar da suke ciki basu bayyana ba.saboda gaba-daya
sunyi hijira duk kan wanda ya ke zaune yana zaune ne dan bashi da wurin zuwa ko kuma dan
ya rasa wani na shi yana cigiya.
Tunda suka shiga yarima yake hawaye kuma wani lokaci ya yi murmushin fullo ta dube shi ta

ce " Ina ne unguwar ku?"

"Jar ƙasa kofar samu naka." Ya bata amsa cikin tsananin son yaga ya gansa cikin gidan.

Basu yi wata tafiya mai nisa ba saboda basu da nisa da in da suka sauka.
Suna zuwa ƙofar gidan su ba kowa dan haka yarima ya kwace hannun sa daga wurin fullo ya
afka cikin gida yana faɗin daddy na dawo ina mommy?" Amma shiru dan haka sai yarima ya
tsaya ƙyam! Yana mamakin jin shurun ina jama'ar gidansu? Sabon kuka ya fara yi ya juyo
sukaci karo da fullo ta ce Ko ba nan ba ne gidan?" "Nan ne basa nan dai ina ga duka sun mutu ne ya faɗa yana fashewa da kuka."
Suna tsaye fullo ta rasa abinyi sai wani bawan Allah ya zo wucewa dan unguwar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login