Showing 30001 words to 33000 words out of 33733 words

Chapter 11 - BAYAN GANGAMI Part1 Complete by Ummu Heebah.pdf

27 Apr 2025

2273

su.

Kwanci ta shi asarar mai rai bamu yi aune ba har watan Ramadan ya zo karshe amma da
yake anan zamuyi sallah, wayar da mukayi yau na ji Muryar basma cike da damuwa amma
kuma na yi nayi ta sanar min komai amma sam ta ce ba komai.
Dan haka hankali na ya yi matukar tashi da zaƙuwar zuwa gida. Shigar yamma mukayi wa
dtr dan haka har wani sauri nake na kai ga gida.
Muna shiga na ga wata mata hakimce kan kujerar falona, Nasir ya na gefen ta suna shan
dariya saboda kallon da suke yi a waya ya ɗauke masa hankali.
"Nasir! " Na furta cikin ɗaga murya sosai.
Firgigit! suka juya suka kalle ni.
Idanun sa kawai na kallah na ga tsan-tsar rashin gaskiya a idanun sa.........


PG 28

Sororo ta yi matar ta wani yatsina fuska tana faɗin, "Baby wai yau daman zata dawo ne baka
sanar min ba?"
Kallon ta ya yi ya kasa cewa komai ya sake kallona ya fara yaƙen dole yana faɗin, "Har kun
iso ne?"
Ban kula shi ba na wuce ɗakina kai tsaye ina jin kamar na shaƙo shi na yi ta duka har sai na
ga baya motsin kirki na bar shi, amma kuma wata zuciyar tana ta bani hakuri.
Biyo ni ya yi ɗakin ya zauna bakin gado ya ce, "Kubra bayan kin tafi abubuwa da dama sun
faru kuma wal........" Hannun da na ɗaga masa ne ya sa shi yin shirun dole, "Bana son jin komai
Nasir daga gare ka! Kawai abinda na sani shine tunda dai gida nawa ba naka ba ko? To ko
matar ka ce ko ma ƙaruwar ka ce ka fita min da ita ayu ba sai gobe ba!" Ina hana fadar haka na wuce toilet ɗin da ya ke cikin ɗakin na rufe na fara kuka mai cin zuciya.
Shi kuwa daga nan wucewa ya yi wurin matar ya bata hakuri yadda take ta masa masifa ya
samu ya bata hakuri ta wuce ɗakin dake gefen nawa wanda a baya shine matsayin turaka.
Gidan mu ya shiga ya yi wa su mama sannu da zuwa gefe guda kuma su Hadiza suna masa
kallon banza game da cin amanar da yayi min.
Sai wajen magrib yara suka dawo a makaranta suka mana oyoyo suna ta farin ciki, kayan
tsaraba na cire na basu kowa na shi da su jallabiya da su huluna sallayoyi da sauran su.
Kusan tara na dare ya samu baba bala ya ce da shi ya na neman ya fiyar sa ya yi masa laifi
amma kuma ba laifi.
Baba Bala ya ce ba komai ya sanar masa, dan haka ya zuƙa masa ƙaryar wai daman ya ce
baya son tafiyar saboda bazai iya jurewa ba na ce da shi ya yi aure to shine bayan na tafi ya
haɗu wata bazawara suka daura aure harma ta tare.
Baba Bala ya ce ba kamai ai tunda ita ce ta zaɓi hakan, kuma ma sunnar Annabi ce ai Allah
ya yi muku albarka.
Ko da baba ya je wa da mama da zancen ta yi matukar mamaki, don ta san halina ba na wani
abu ban sanar da ita ba.
Amma kuma ta ce ba damuwa ai tunda ita ce tace ayi hakan.
Ina shiga gidan da safe na samu mama fuskar ta ba walwala, na dube ta "Mama mai ya faru

na ganki haka?"
"Ba komai kubra." Ta ce dani
Sai kuma ta ce.
"Kubra banyi tsammani zaki yanke hukuncin wani abu baki sanar min ba, amma tunda har ya
riga da ya faru shike nan. Sai dai ki sanin ki guji zama gida da kishiya gida guda idan ba dole
ba, saboda anfi samun matsalar zaman.
Ki na da damar cewa Nasir ya yi aure amma da baki bashi damar haɗa ki ba, ba wai ina
zugaki bane ."
Sakwato na yi kamar wata gunki.
"Mama ban gane me kike nufi ba , taya zan bawa Nasir damar aure har da zaman gidana."
Na sanar mata haka.
Murmusawa ta yi ta ce "Koma mene ne ai abinda ya riga ya faru ya faru tunda Nasir ɗin da
kansa ya ce kince sai kin tafi sai dai ya kawo wata gidan. Kinga kuwa ai ga watan Allah ya baku
zaman lafiya. "

Mama ta faɗa tana gyara ɗaurin kallabin ta.

"Haba mama wallahi bani ce nace masa ba wallahi karya ce yamin kawai! Kuma wallahi bai
isa ba! Nidai bamuyi haka da shi ba.
Kuma wallahi yau zata bar min gida."
Na faɗa ina miƙewa tsaye.

Mama ce ta ce na dawo na zauna. Bayan na zauna ne ta ne mi sanin gaskiyar lamari kuma
ban ɓoye mata komai ba yadda muka yi da shi ranar da su ka ganni ina kuka a gobe tafiya.
Mama ta jinjina lamarin sosai da sosai ta kuma yi min nasiha da nayi haƙuri na bi komai a
hankali.
Zuciyata na ji ta yi min sauƙi na tashi na tafi gidan .
Ina shiga na ci karo da ita tana ta wanin hura hanci ta tura ɗan kwali gaban goshi kamar zai
faɗi.
Ta tsare min hanya da gangan dan haka sai na kauce ban kulata ba, amma ta mangaje ni.
Kallon ta nayi murmushi ɗauke a kan fuska ta na ce, "Bani wuri na wuce karmashashiya,
saboda ke baki kai na haɗa jiki da ke ba shi wancan ɗan tauren da ya ajjiye ki shine sa'a na."
Zaburo min ta yi saboda daman jira take dan haka hannu na sa ha hankaɗe ta gefe na wuce
ciki abina.

Ko minti goma ba ayi ba Nasir ya shigo yana huci kamar zai dake ni.
" Duk abinda zakiyi kar ki kuma dukan baby! Idan maganar gida ne kuma ta zo ke nan na fa sa
chan jawar!" Ya faɗa yana nuna min yatsa. Shawuya da yake gefe kuwa sai miƙa hannu ya ke
kamar zai kama shi yana ta ɓangala dariya.

Cike da masifa Nima na zabura na ce, " To munafiki ! Wallahi baka isa ba sai ka bar gidan nan
ɗin kuwa. Ko ba duka ba ! To yanzu na fara. Butulu kawai irin ka. Na faɗa ina mai zama abakin
gado ina rusa Kuka.

Fice wa ya yi yana guna guni.
Dan haka na bi shi cikin ɓacin rai har bakin ɗakin Babyn inji shi na ce "Ke baby kike ko ma
Babyn roba ce azo a fice min daga gida wallahi ba gidan sa ba ne idan ma bai sanar Miki ba to
maza azo a fice min daga gida!"
Na faɗa cikin ɗaga murya jin haka yasa duka suka fito zuwa falon.
Ta zuwa zata min wani iyaye na dauke ta da mari na mai da ita gefe shi ma da yayo kaina na
hankaɗe shi na yi ya faɗa kan kujerar da ke bayan sa.
Saboda kamar wata zaki na ke jin kaina a lokacin.
Ganin na burkita su da masifa ina shiga ina jefo mata kayan ta zuwa falo yasa ya fice ban san
mai ya shirya ba sai da na ga baba Bala har gida ya shigo ransa a matukar ɓa ce...


PG 29

Sai da hantar cikina ta kaɗa ganin irin kallon da baba ya ke je fo min da shi, ita kuma makirar
tana ganin sun shigo ta zuɓe ta kama ihun ƙarya tana cewa wayyo cikin ta.
Baba Bala kai tsaye inda na ke ya nufo ni kuma na sunkuyar da kaina ban yi tsammani ba na ji
an wanke min fuska da marin da rabon da na sha shi irin sa har na mance,.
Cike da mamaki na ɗago idanun da suka rine min zanyi magana amma baba ya hanani sam! Ta
hanyar ɗaga min hannu. Dan haka dole na haƙura da maganar naa durƙusa a wurin ina
sauraran abin da zai ce.
"Ke da kanki ki ka umarci mijin ki da ya ne mamaki abokiyar zama kuma a gidan ki, dan haka
wallahi baki isa ba zama yanzu ta fara a cikin gidan nan! Kar ma na sake jin wannan batun na
faɗa miki.
Daga haka ya juya ya fice a gidan, ita kuma ta mike ta min gwalo ta shige cikin ɗakin ya rage
daga ni sai Nasir.
Duban sa na yi cikin kuka na ce,
"Kai kuwa mai na maka ka maida zaman auren mu haka? Mai na tare wa rayuwar ka? Wai
wanne laifi na maka wanda har ya kai ka saka min da wannan butul cin?
Kasan irin gwagwarmayar da na sha domin kare mutuncin ka? Ka san faɗi ta shin da na sha
kuwa? Nasir mai yasa ka zama butulu mai bakar zuciya? Ka mance irin soyayyar da take
tsakanin mu? Haba Nasir ka tausayawa rayuwar mu mana ko dan yaran ka."
Na ƙarashe maganar cikin kuka.
Bai ce dani uffan ba ya bini da kallo yana mai shigewa ɗakin matar sa.
Bayan na gaji da tsayuwar nima na shige nawa ɗakin ban sake fitowa ba har sai da yarana
suka dawo gidan tukunna.
A falo muka yada zango muna karatu nida su amma ba ko kunya Nasir ya leƙo kai ya ce mu
rage murya muna damun su.
Bance ƙala ba ban kuma kalle shi ba.
Haidar ne ya ɓata rai ya ce, "Mommy wai kawai dan daddy ya yi aure sai yana mana haka har
da ke kuma."
Harara na banka masa dole ta sa ya sunkuyar da kansa ,
Na ce "Haidar baban ka ko me zayyi fa baban ka ne dan haka bana son na ji wani ƙorafi ya fito

daga bakin ka indai har akan baban ku zakayi shi."
To ya ce badan ya so ba na ce dasu mu tashi mu shiga cikin ɗakina kawai muƙarasa karatun,
haka kuma mukayi a chan muka gama har lokacin sallah ya yi.
Haka muke ta fama da rayuwar mu ni da yarana a cikin gidan nice da gida sune da isa ita
kuma mandiyar ta sa ta samu ɗaurin gindi sai yadda ta ga dama ta ke yi a gidan.
Rayuwa mai tafiya ce kamar wasa har an sanya lokacin bikin basma da Captain Jamil,
Haka su Maryam ma sun fidda mijin aure Ita da Hadiza saboda duka za ayi bikin a ta re.
To dan haka duka hankali na yana kan hidimar bikin ne a matsayina na babbar yayar su,
Basma kuwa cewa ta ke ita wallahi aure ya fita kanta saboda yadda Nasir ya juyamin baya duk
da irin soyayyar ta ke tsaka nina da shi .
Zaunar da ita na yi har ma da su hadiza ɗin na ce musu, "Shi fa aure da kuke ganin sa daman
ya ga ji ƙalubale a cikin sa kuma kowanne bawa da ƙaddarar sa a rayuwa, dan haka kuyi ta
addu'a Allah yasa mazajen da zaku aura su zama haske a cikin rayuwar ku.
Kuma daman dole shi aure wani zama ne na a sa ɓa kuma a gyara ba wai zai kasance irin
soyayyar layi ba ne.
A'a ya danganta da kalar mijin da kika aura din. dyan haka kuyi hakuri da mazajen ku a ko
wanne hali shi yasa zaku ji motsi kaɗan ance sai hakuri fa wance, to zaman auren ke nan
daman .

Kuma in sha Allahu ina muku fatan alheri a rayuwar ku baki ɗaya." Duka rungume ni sukayi
suna kuka wai su wallahi ba su son rabuwa dani.

Dariya na yi musu saboda sun fara da wuri na shige toilet ɗi na na barsu a wurin zaune.
A ɓangaren Nasir kuwa ba abinda ya sauya daga gare shi a halin sa da matarsa .
Amma kuma duk da haka ban rasa komai ba saboda dukkan wani abu da ya samu na taimako
jama'ar hijira to gwamna baya mance wa dani har ma da shi kan sa, ba kama layi ba shan
wahala namu har gida yake zuwa mana, kuma hakan ya na samuwa ne daga gwamna saboda
yana duba wahalar da na sha . Shi yasa a rayuwa ba zan mance da gwamna *mai mala buni* ba saboda ya min alheri masu
mugun yawa a rayuwata .
Da irin taimakon da na ke samu wajen sa na samu na fita kunyar auren ƙanne na.

Biki ya kusa na shirya komai na gyaran jiki domin kuwa wurin shahararriyar mai gayran
jikinnan na kai su dukan su wato UMMU HEEBBAT ta gyara min su da kyau ciki da waje kama
da kan turaren da amarya ya kamata ta turara a cikin jikin ta da kuma jikin ta waje da abinda
zata sha ba mai cutarwa ba masu inganci ba wanda kuma ya fi karfin su ba,saboda wani lokaci
ana bawa amare maganin uwargida garin gyara, to ta ina zaku hada maganin da wacce ta saba
da wacce yanzu zata fara zai zama guda? Shi yasa da zarar ankai amare zasu fara rawar ƙafa
jira suke kawai azo wurin.
Tunda an gama haukata su, to ita Ummu HEEBBAT tana kiyaye hakan .
Dan haka sun sha gyara sun fito sai ta shin ƙamshi suke ga wani yalƙi da suke kamar sabin
babys, kuma duka wannan aikin Ummu HEEBBAT ne.
Haka har Allah ya kawo mu ranar bikin dangi kowa ya hallara har da jama'ar gashuwa da

kananma duka sun hallara a dtr an sha biki cikin farin ciki kuma dukkan su suma ba a gari
bane. basma gashuwa aka kaita saboda jamil ɗin a chan ya ke aiki.
Mun sha kukan rabuwa da basma saboda mun fi kowa shakuwa da ni da ita.
Har ɗakin ta na mata raki a garin gashuwa, kuma na samu jamil na bashi amanar ta da kaina
saboda kaunar da na ke mata ta daban ce.
Da kyar muka rabu ranar da zamu dawo dtr ɗin an sha fama tukunna.
Amma tijarar da na tarar Nasir ya shuka min a gidan sai da na ji dama ban zo ba.
Kuma na saka a raina daman saboda baba Bala ne nake daga masa kafa amma tunda ya bi
mutanen kananma duba gonar sa dan haka na ce yau za'ayi dukkan masifar da za'ayi agidan
koda kuwa karshen zamana da shi ya zo..........






PG 30

Last book 1

Kallon kallo muka tsaya yi nida Nasir na ce, "Me zan gani haka? Nasir nida gidana har ana
min waje da kayan ɗakina."
Na ƙarashe maganar ina nuna kaina.
Amaryar sa ce ta zabura ta ce, "Eh haka na ke so wannan ɗakin zan koma idan kuma da
gaske gidan kine kamar yadda kike tun ƙaho sai ki hana mugani. " Ta faɗa har tana wani kaɗa
jiki da hura hanci.
Nasir ɗin na kallah, "To ka sanar mata gaskiya a kan gidan idan ma ka ce mata naka ne
kuma yau dole wannan ta bar gidan tunda ba gidan tsoho be ne ! Nasir na gaji da rainin
hankalin da kake min a cikin gidan nan dan haka wallahi yau ko da zai zama silar rabuwar mu
da kai sai ta bar gidan nan yanzu ba sai an jima ba."
Na faɗa ina sauke lumfar-fashi saboda ban saba da masifa ba sai da ta riske ni .
Kallona ya yi ya watsar ya je wurin amaryar sa ya ce da ita, "Baby kiyi haƙuri bata da hankali
kinsan duk wanda yayi zaman daji kansa sai ahankali, gida kuma karki kula ta da wannan
shirmen nata da ta ke yi gida dai kin shigo ke nan sai mutuwa."
Sakwato na yi ina al'ajabin kalmar shi ta zaman daji ban san sanda zuciya ta zare ni ba na
dauƙi wani takalmin sa sawu ciki na kwada masa a bayan sa ita ma na buga mata a kai na ce,
"Hauka ka ce ba? Yanzu zaka ga ainahin Hauka ! Fuzgo ta nayi tana ƙokarin kai min duka na
buga ta da bango ta fasa ihu! Ganin jini ya ɗan ɓullo a goshin ta sanadin gorjewa tuni ya yi
kaina ya lafta min mari tare da faɗin na sake ki kubra! "
Chak! Na tsaya da komai na ji kalmar har cikin jikina duk kan gaɓoɓin jikina sai da suka amsa
kalmar.
Wani tashin hankali ne ya ziyar ci zuciyata saboda ban taɓa jin wannan kalmar a zaman mu

ba sai yau.
Cike da damuwa na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login