Showing 27001 words to 30000 words out of 33733 words

Chapter 10 - BAYAN GANGAMI Part1 Complete by Ummu Heebah.pdf

27 Apr 2025

2274

masa nasir ya kamata gobe na koma kafin mu tare sabon gida ya aika min da wata
harara, amma duk da haka sai na ce da shi "Yaron nan har yau ba shi da suna balle yanka
yaushe za'ayi masa?"
Cike da izza ya dube ni ba ko kunya ya ce, "Kubra! Wallahi ba dan na san kina da ciki ba kika
fita Allah da wannan yaron ba wa bane ni sam......"
Ya faɗa yana yarfe hannu.

Cike da bugawar zuciya na kalle shi har wasu hawaye masu zafi na ce, "Nasir! Kasan mai ka
ke faɗa min kuwa ...........a fusace ya juyo cikin masifa.............







PG 25


Cike da mamakin maganar ta sa ta tsaya min cikin zuciyata! "Haba Nasir wai me ya ke damun
ka ne? Me ya sa kake min haka ne? Nasir ko ka daina sona ne ban sani ba?"

Na ƙarashe maganar cikin sautin kuka.
Kallona ya yi ya zauna gefen wani itace, "Kubra lafiya kalau nifa amma wallahi gaskiya zan
sanar miki tunda kika ce kinyi aure kan aure na wallahi ina da shakku a zuciyata! Saboda taya
zan yi farin ciki da matar da ta haɗa jiki da wani bayan ta na da aurena? Haba kubra kimin
adalci mana idan na ce miki har yanzu kina zuciyata zaki yadda."
Wani irin tashin hankali ne ya riski zuciyata na kalle shi na sake kallon sa cike da mamaki!
"Nasir yau ni ce ka ke gudu? Nasir ka mance irin tarin ƙaunar da na ke maka ne?"

Ban bari ya ji wani bayanin na ba na juya cike da ta fasar zuciya na shige ɗakin su basma,har
wasu taurari na ke gani suna hana min ganina sosai.
Gadon na faɗa na kwanta ina wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Shi kuwa gidan sa ya wuce cike da damuwa domin har ransa ya ke jin ba ɗaɗi akan abinda
ya min, amma kuma idan ya tuna kalaman sadauki abokin sa, sai yaji kawai ko ma mai zai faru
ya faru.

Ganin halin da nake ciki ba mai ɓullewa ba ne yasa na fara sanar da mahallici na halin da na
ke ciki, saboda shine gatana a duniya da lahira.

Haka baba ya maida ni gidan Nasir ba tare da jin ta bakina ba.
Bai ce komai ba ganina a cikin gidan sa tare da yaran sa, dan haka nima na cigaba da zaman
shirya kayan ƙaura zuwa dtr ɗin haidar ne ya ke taya ni haɗa kayan ya yinda yarima ya ke ta
yiwa shawuya wasa sai ga basma ta shigo.
Da farin ciki na tar ɓe ta ta zauna ta da fa ka faɗata.
"Aunty za'a koma binni."
"Basma kamar ban taɓa zaman gashuwa ba?" Na faɗa ina riƙe haɓa .

Dariya sosai basma ta yi. "Aunty yanzu dan Allah taya zaki haɗa gaashuwa da dtr kuma?

Taya state da local government zasu yi ɗaya?"

"Basma ke nan ni a wurina duk ɗaya ne fa tunda dai rayuwar gayu ce kuma nima na iya
ɗaukar gayun ba shike nan ba."

"A'a aunty duk dahaka sai kin kula sosai kar su gane ke y'ar ƙauye ce su raina min ke, kin
san su da jiji da kai fa mutanen dtr."
"Haba ke kuwa ai kowa kika gan shi wuri to tilas ya san yadda zai zauna da ma'abota wurin
domin gujewa raini, karki damu."

"Yawwa aunty na haka na ke son ji ."


Sai wajen dare muka gama haɗa kayan duka muka loda su gefe cikin gidan, kwansilik basma ta
yi mana wanda yarima ya taya ta cura mana yaji jajjage ya sha manja sosai yaji komaibya sha
maggi, har da salat ta yanka mana a ciki .

Bajewa mukayi muna haɗiɗiyar sa basma ta kunna waƙar salim smart na Allah ya jiƙaina idan
har ba ke wa'aɗin rayuwata ya zo karshe. Rerawa ta ke tana cin dan sulut din kamar ita tayi
wakar kallon ta na tsaya yi har sai da ta fara min dariya. Ta ce " Aunty wai dan Allah ki daina
kallona."
"Bazan daina ba basma, Wato irin kin fara soyayya ɗin nan ko? Shine kike nuna min."
Na faɗa cikin zolaya.


Kunya ce ta kama ta sai ta rufe idanu kasan cewar ta mai kunya sosai.

Bayan sati guda da komawa ta ne muka haɗa komai mu da su mama fedo da baba Bala da
basma mukayi ban kwana da jama'ar garin mu ba tare da sun san garin da zamu koma ba.
Saboda tsaro.

Mun sauƙa lafiya gida kuma ya yi masa Allah a anguwar sabon fegi ya ke kusa da ladabi suya.

Gidan su mama gida ne mai dauke da ɗakuna uku da falo a tsakiya wanda ya ke kunshe
da toilet a kowanne ɗakin sai karamin kitchen da kuma wani bayi a waje da kuma tankin ruwa
babba.

Haka gidan da na ke ya ke shima sai dai shi har da wajen ajjiye mota da kuma wurin dinning
table.

Farin ciki gaba ɗaya ya bayyana a fuskokin mu amma banda Nasir .

Kwanan mu uku ya koma kananma ya ce zai je ya dawo.
Amma shurun sa har wajen sati biyu kuma layin sa baya shiga.


Kwatsam basma ta na zaune a kayi sallah ma da ita tana fita sai ga Captain jamil, dan haka na
ce ta yi masa iso kawai falona .

Bata ɓata lokaci ba ta sauke shi kuwa, yarima ya je wurin sa suka gaisa saboda dukkan sanda
ya zo sai ya nemi shi, ya ce yana matukar kaunar sa.

Amma bazan mance kalaman da na ji jamli ya na faɗawa basma ba wanda har suka sanya ni
kasa tsayawa ya tafi na ji gaskiya lamari.

Har sai da na fito wurin da suke zaune..........


PG 26

Fitowa nayi ina riƙe da baki tsabar mamakin abinda na ji jamil ya na faɗa, ban yi ƙasa aguiwa
ba na doshi wurin su , amma kuma sai na ji bai kamata ba kawai sai na waske na yi hanyar da
zata sada ni da kitchen.

Koda na shiga kitchen ɗin mu kasa taɓuka komai na yi tsabar farin cikin da ya mamaye min
zuciyata, Allah dai ya sa kunne na dai dai ya ji min ba zolayata ya ke ba.
Aikin dole na kama yi ganin bai dace na sake koma wa ta gaban su ba.

Kusan awa guda ina zaune cikin kitchen ɗin tukunna na ji fitar su a falon dan haka da sauri na
dawo falo na zauna ina tsumayin jiran basma.
Bata jimaba ta dawo cike da farin ciki a kan fuskar ta.
Kasa jure nawa farin cikin na yi na mike na same ta tare da riƙe hannun ta na ce, "Basma,
sanar da ni dalilin da yasa kike farin cikin nan."
Murmushi ta yi, "Aunty sai kin bani tukuici tukunna."
Murmushi na yi na kalle ta "Karki damu zan baki."

"To aunty shike nan, na san ma kinji ai amma dai bari na sanar Miki. Gwamna ya. Ce da ke da
baba da mama fedo bana azumin sai a Saudiyya."
Ta faɗa tana rungume ni.
Sa ke rungumeta na yi muka yi ihun murna har sai da su haidar suka fito a ɗakin su suna
kallon mu.
Suma da muka sanar musu murna suka hau, yarima kuwa har da rawa wai zan kawo masa
bindigar roba da mashin.
Haka dai muka yi ta farin ciki nida yaran daga ƙarshe muka ta fi gidan su mama muka yada
zango.

Mama da muka sanar mata harda hawayen farin ciki. Baba ma ya yi farin ciki sosai
Sai dare muka koma gidan nida basma ita ce muke kwana tunda Nasir bai dawo ba.

Zama na yi bakin gadona na dauki wayata na fara gwada layin Nasir na waya amma shiru
baya shiga, na gwada ya kai so biyar amma amsar ɗaya ce.
Haka kurum na ji zuciyata ta yi min zafi, na so ace wannan farin cikin da Nasir zamuyi shi.
Amma ya maida kansa ge fe, kuma hakan ya yi mugun tsayamin a zuciyata.
Saboda tsawon zamana da shi bamu taɓa samun saɓanin da zai kai ya yimin yaji ba, amma
yanzu ya yi min a lokacin da na fi bukatar sa a gefe na.
Haƙiƙa ina kaunar Nasir domin zamana da shi ma ya fi ƙarfin a ƙirashi da soyayya sai dai
ƙaunayya.
Amma ga shi yau ya juya min baya, baya ko tausayin halin da na ke ciki. Ina amfanin kishi
akan abinda baka da tabbas.
Na ƙarashe maganar tare da goge hawayen da ya ɓurtso da ga Idanuna.
Ban san ya zanyi da shi ba ya daina guje min da zanyi, shi kuma ya gaza fahimta ta. Ya Allah
ka shiga lamarin wannan zaman na mu.

Amin na ji basma ta faɗa tare da da fa ka faɗa ta.
Dago idanuwa na yi na dube ta .
Ban ce komai ba na sake sunkuyar da kaina ƙasa .
Wuri ta samu ta zauna ta ce, "Aunty wai yanzu har fushi Nasir ya ke Miki? Duk irin halin da kika
shiga bai gani ba? Ko da kuwa a ce auren da a ka Miki wani abu ya faru ai ya kamata Nasir ya
yi haƙuri."
Shiru na yi na wani lokaci Sannan na ce.
"Basma haka ƙaddarata ta zo ni kuma da ga wannan gangamin sai Wannan.
Amma bana son su mama su sani kinji ."
"In sha Allah aunty ba wanda zai ji, kuma Allah zai kawo Miki mafita da wuri."
"Allah yasa haka my lovely sister na."


Bamu jima ba gwamna ya turo a ka je da mu muka bada passport a kayi dukkan shirin da ya
kamata saboda ba zamu jima ba zamu ta fi.
Kananma muka je mukayi sallama da 'yan uwa da abokan arziƙi sannan muka wuce gashuwa
nan ma mukayi sallama da 'yan uwa.
Sai da ya zama saura kwana uku tafiya Sannan Nasir ya dawo dtr.
ba yabo ba fallasa, saboda yana kula yaran sa ba kamar baya ba da su ma ya yi watsi da su.
Amma ta fanni na ba abinda ya sauya hatta shimfiɗa idan muka hau Chan ƙuryewar gado ya
ke wuce wa ya kwanta. Ban taɓa yi masa magana ba saboda ina jira na ga gudun ruwan sa.


Ashe kuwa ruwan na sa yana mugun gudu ne da tozarci da yaudara har ma da rashin sanin
daraja ta.

Wannan ruwan na shi ya yi guda da zuciyata fiye da yadda nake zato.

Kuma shine abu na farko da Nasir ya min na ji ma tsane shi a duniya tsana mai yawa.......


PG 27


Sai da lokacin tafiya ya rage saura awa biyar, sannan ya ce dani yana son muyi magana.
Cike da farin ciki na sa me shi ina fatan maganar da zamuyi ta kasan ce alkairi murabu cikin
kewar juna.

Amma kalaman da yazo min da shi ya tarwatsa dukkan tunani na.
"Kubra, ina son ki ajjiye hankalin ki da kyau ki saurari abinda zan faɗa miki ciki lumana."
Ajjiyar zuciya na sauƙe cike da damuwa saboda yadda na ga fuskar sa na san tabbas akwai
damuwa.
"Ina saura ranka mijina."
Na faɗa cike da fargaba da neman sulhu.

Sa ke tamke fuska ya yi ya ce, "Magana ce akan tafiyar ku a matsayi na na mijin ki sai dai ki
zaɓa, tafiya umara ko kuma zaman auren ki! Wanne kika ga ya fi miki, ya rage na ki."
Kamar sauƙar aradu naji sautin maganar ta sa har cikin kwakwalwata.
"Nasir me na maka haka? Wanne laifi na ke da shi a wurin ka?
Shin Nasir ashe lokacin Zaizo ka tsaneni irin haka? Yanzu tafiya Makkan ne ka ke min ɓakar
maganar a kan ta?"
Duka na jero masa tambayoyin .
Shi kuwa ko a jikin sa bai wani damu ba ya sake kishin giɗewa a jikin gado, wani takaici ya
kama zuciyata kamar na shaƙo sa na kama duka! Dan haka cikin ƙaraji na tashi ina huci na ce,
" Kayi dukkan abinda ka ga yada ce! Tunda dai haka ka ce!"
Fuuu na fice na bar masa ɗakin.
Bai ce dani uffan ba har na bar dakin, falo na je na zauna na fara rero sabon kuka kamar
wata amaryar da ake son rabata da iyayen ta.

Ana haka su mama fedo suka zo ita da su Maryam saboda na musu alƙwarin da safe Zanje
ban je ba kuma shawuya baya jin daɗi shine suke tunani ko jikin ne .
Ganin halin dana ke ciki sai sukayi turus! Suka tsaya, waskewa nayi na fara ƙokarin goge
fuskata kamar ba komai na ce dasu su ƙaraso mana, shigowa sukayi suka zauna duka jikin su
ya yi sanyi. Mama ce ta ce, "Kubra, me ya faru? Lafiya kike kuka?"
Shiru na yi bance komai ba saboda bani da abin faɗa, chan kuma sai dabara ta faɗo min,
"Mama wallahi idan na tuna wahalar da na sha da yadda rayuwa ta bani wahala nida yaron nan
sai dai na ji hawaye yana zuba daga idanuna."
Na shimfiɗa musu wannan ƙaryar kawai don bana son su san halin da muke ciki. "

"Haba kubra me sa zaki sa ka kanki cikin damuwa bayan kuma kin samu 'yancin rayuwa. Don
Allah ki dena, saboda zaki iya kamuwa da cuta idan har zakina bibiyar Abun arai."
Kalaman mama ke nan da suka faɗa cikin masarrafin jina.
"In sha Allahu mama zan ki ya ye hakan."
Na bata amsa cikin sanyin murya.
Gefe guda kuwa su basma Maryam Hadiza ne duka suka zauna kusa dani duk sunyi kalar
tausayi.
"Yawwa kubra Allah ya muku albarka dukan ku."
Da Amin muka amsa mata.
Sannan ta ce dani idan Nasir yana nan tana son suyi magana da shi.
Dan haka kai tsaye na je na sanar da shi ba tare da na tsaya na saurari abinda zance ba.
Bai jima ba ya fito yana murmushin munafurci yana gaida mama kamar ba shi ba, dukan su
suka gaida shi cikin sakin fuska illah basma da tasan halin da ake ciki.
Har da yiwa mama fatan zuwa ayi a sa'a kamar ba shi ne ya gama min tijara a ɗakin ba.

Mama ta dube shi. "Nasir Yakamata a yi wa yaron nan suna kafin mu tafi.Sunkuyar da kai ya
yi ya ce, "In sha Allahu mama zuwa gobe zan saka masa."
"Yawwa Nasir, Allah ya maka albarka."
Da amin ya amsa ya miƙe ya fita .
Hakan kuwa akayi ana gobe ta fita ya ce da mama sunan yaro Ahmad ya yi masa sunan rana
ba takwara ba ne . Na yi farin ciki sosai duk da cewa bai kawo abin yanka ba, abinda yasa bai
dame ni ba kuwa shine, sunna ce mai ƙarfi, ba waji bane sai anyi. Kamar yadda wasu suke
ɗaukar cewa dole ne har ma idan ba ayi ba ana dauka kamar an aikata sa ɓo. Haɗe dukkan kayan mu mukayi domin asubar fari zamu tafi Kano Chan zamu hau jirgin
yamma.
Nasir na samu yana kwance yana latsa wayarsa yana ta famar sakin murmushi ga dukkan a
lamu chat ya ke yi abin sa.

"Ina son magana da kai ."
Sai dai na furta ta sau uku sannan ya ce "Ina jinki."

"Nasir na zaɓi ta fiya Saudiyya idan har yanzu kana kan bakar ka, domin ba zan taba cewa
su mama bazan tafi ba saboda ka hanani.
Amma idan zaka iya sanar musu da kan ka sai na haƙura."

"Allah Ya tsare hanya ."
Shine ka ɗai abin da ya furta min ya juya ya kwanta abinsa."

Ba yabo ba fallasa na ɗan ji sauƙin damuwar da ta ke cikin zuciyata.
Cike da farin ciki jirgin mu ya ɗaga zuwa Saudiyya.
Ibada muke cikin farin ciki da kwanciyar hankali kullum sai munyi waya da su basma da
Maryam da Hadiza, a wurin su na bar yaran nawa dukan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login