Showing 6001 words to 9000 words out of 33733 words
Chapter 3 - BAYAN GANGAMI Part1 Complete by Ummu Heebah.pdf
ya gansu ya
ce da su ai duka mutanen gidan suna gidan kakan su ƙanin mai gidan ne ya bude yanzu amma
ban san inda ya tafi ba.
Koda yarima ya ji haka kawai bai tsaya cewa komai ba ya kama hannun fullo tiryan tiryaan sai
gidan kakan su.
Yana zuwa ya shiga da gudun sa ya yin da fullo ta ke biye da shi domin wannan karon bata tsya
baya ba.
Ganin sa da sukayi ya sanya duka suka mike daga zaman makoki da suke
Wasu na kukan farin ciki wasu na murna da dariya chan ya Fido ta ce "yarima ina ka baromin
mommyn ka?"
Jin wannan tambayar tuni ya yarima ya sake fashewa da kuka sabo, ganin haka Hadiza ƙanwar
Kubra ma ta rungume shi cikin kuka ta ce "Sanar da mu ka ji yarona kaji."
Da hannu ya nuna fullo wanda sai sannan suka ganta . Wurin zama aka bata daga bisa aka
nemi ƙarin bayani daga gare ta .
Itama kukan ta fara kafin ta fara basu labarin haɗuwar su da Kubra da rabuwar su tana kai
ƙarshen labarin Maryam da Hadiza suka sume. Nasir kuwa sake maimata kalmar ƙarshen ya ke
" Haihuwa a dajin kuma ga yan bindiga?"
Ganin yana neman zauce wa yasa malam ya zaunar da shi, gida duka ya dauki kukan mutuwar
kubra domin su sun bata mutuwa ne kawai.
Hakan kuwa shine yayi dai dai da zuwan dogarai uku suka ce da kubra ta
zo a daura mata aure ..........,.
Pg6
Cike da firgici na sunkuyar da kaina yayin da zuciyata ta ke min luguɗen dakan ɗaka, saboda ji
nake kamar zata tsaga ƙirjina ta fito ga wani azababben zazzaɓi da ya riski dukkan gabobina
lokacin guda!
" Aure kuma!" Kalmar da na furta cikin zuciyata, wanda yayi daidai da uwar tsawar da ɗaya
daga cikin su ya sa ke je fa min.
Ciki da damuwa na yunƙura na miƙe na goya shawuya muka dauki hanyar fadar OGA gaba
ɗaya.
Zuwan mu ke nan na hangi maza shida gefen kujerar sa dukan su durƙushe a gefen sa. Yana
nan yadda na barshi ranar ma kamar baya tashi saboda yauma bai juyo ba,wuri na samu na
durkushe kamar yadda na ga sunyi.
Kamar saukar wahayi haka muke jin sautin Muryar sa cikin sanyi ya ce. "Na so a daura auren
kina kusa amma kuma rashin isowar ku da wuri tuni har an gama komai. Dan hakan ku bata
kudin sadakin ta da kuma goron ta ku nuna mata mijinta akai ta gidan ta . Allah ya basu zaman
lafiya." Tunda ya fara maganar na ke jin wani irin zugi yana saƙƙowa daga cikin zuciyata har zuwa cikin
cikina da ya kewani irin murɗawa. Ganin abin da na ke ganin sa kamar wasa yana son zama
gaskiya ko na ce ya zama ma shine ya ke sake je fani cikin ruɗani!
Jin takun mutum kusa dani ya sani saurin ɗagowa daga sunkuyar da kan da na yi ƙasa. Sai ya
ce dani "Ga wannan kudin sadakin ki ne kamar yadda OGA ya faɗa ga kuma goran ki. Sannan
wanchen mai ɓakin kayan shine miji a gareki dan haka ta shi muje a ra ka ki gidan ki." Tunda
ya fara bance komai ba kuma ban kalli wanda ya nuna min din a matsayin mijin ba saboda bana
bukatar hakan, hannu na sa na dauki kuɗin da goran na miƙe domin bin umarnin su.
Ganin na miƙe ne yasa duka suka miƙe suka sanya ni gaba saboda sumin rakiya. Haka muka
ɗunguma tafiya mai nisa da fadar OGA gaba ɗaya chan wani tanti suka kaini wanda ya fi na wa
girma da kuma kayan aiki cikin sa na bukatar mace. Murmushin ya ƙe na yi wanda ya fi kuka
ciwo na ce cikin zuciyata "Harda wasu kayan aiki wato ga yar iska mara sanin addini." Ganin na tsaya ina tunani ya sanya ɗaya daga cikin su ya ce ki shiga ciki anjima ango zai zo da
kayan amarchi.
Ban furta ko kanzil ba na shiga ciki na zauna ina faman sauki lumfar-fashi.
A chan kuwa gida da ƙayar a ka shawo kan su Maryam suka farfaɗo daga sumar da sukayi .
Shi kuwa Nasir wani irin kuka yake mai tsuma zuciya idan ya tuna da Kubrar sa da irin zaman
da sukayi na amana yadda ta ke mai biyayya a gare shi. Amma ace irin wannan rabuwar
zasuyi? Ai gwanda ace shine ya mutu ya barta da ya fi masa sauki. Ko kuma ace mutuwa ta yi
sukayi mata sallah suka binne to da zaifi samun sukunin da rashin sanin tabbas.
Wannan abin shine abinda ya fi ƙo na masa zuciya. Ganin halin da ya ke ciki ne ya sanya MLM
ya zo wurin sa ya dafa kafaɗar sa ya ce . "Nasir rayuwa fa daman cike ta ke da ƙalubale mai
tarin yawa, saboda ba dukkan yadda kaso kayi rayuwa ka ke samun yi ba.
Komai kuma da kake ganin yana faruwa ba wai dan an tsane mu ba ne , A'a sai dan a jarraba
imanin mu. Dan haka ina son ka dauki wannan jarabawar da ta riske mu, a wannan lokacin na
san dole zaka ji zafi amma idan ka tuna cewa komai Allah ne ya ke tsara shi to tabbas zaka
samun nutsuwa a zuciyar ka. Kuma ka yawaita ambaton Allah a koda yaushe hakan zai sanya
ka samun nutsuwar zuciya.
Da wadannan kalaman Nasir ya samu ya ji wani irin ƙarfi ya riski zuciyar sa tuni kuma a wannan
lokacin ya fara ambaton sunan Allah kamar yadda MLM ya ce da shi.
Mama fedo ce zaune da yaran na ta a barandar da ke gaban ɗakinta.
Hakuri ta ke sake basu ya yinda idanunta suke zubda hawaye saboda tabbas ta yi babban rashi
a cikin yaranta idan har ya tabbata Kubra ta bar duniya.
Mafi girman tashin hankali kuwa shine ace tana raye amma basu san inda zasu same ta ba.
Shin ta ina zasu fara ya kuma zasuyi da yaranta domin kullum sai sun tambayi ina mahaifiyar
su, illah yarima da yasan inda ya barta . Shi baya magana sai da adukkan lokacin da ya tuna ba
shida wani aiki sai na kuka.
Misalin shabiyu rana zulfa'u ce zaune a cinyar Basma ƙanwa ga Kubr. Ta ce "Aunty Basma idan
mommy ta dawo zan koma wurin ta saboda na jima ban ganta ba kuma ina son ta haihu na yi
gaɗa." Jin kalaman zulfa'u sune suka sanya zubar hawayen basma a ɓoye. Saboda ɗazu mama
ta yi musu nasiha cewa su daina kuka sai addu'a, kuma sun yi mata alkawarin haka . Ta ce "zulfa'u yarinyata mommy zata dawo nan ba da jimawa ba, kuma zaki koma hannunta
har sai kince inzo in dauke ki. Gaɗa kuma kamar kinyi in sha Allahu saboda mommy zata baki
abun yin idan ta dawo ɗin." Ta karashe maganar cikin ƙarfin zuciya, saboda yadda idan ta kalli
yarinyar ta ke sake bata tausayi.
Kowa ya watse a garin a wannan lokaci sai wanda sukayi saura irin su family Kubra da suke
zaman tsammanin ko zasuji labarin ta.
Amma jin wannan labarin shine ya sanya malam yanke shawara da su bar garin na wani
lokaci. Tunda har yau sojojin sun hana su zaman nutsuwa dan tunda abin ya faru suke musu
ihu bayan hari! Dan motsi kadan Zasuyi ta harba roket masu girma suna musu fargar jaji tunda
abin ya riga da yafaru to abar jama'a su zauna lafiya mana! Kuma hakan da suke yi ne ya sa
duk wani mai son zama yake barin garin.
Ko da yaje musu da wannan batun basu ƙi amincewa ba domin gwanda su bar garin su huta da
tashin hankali suji da damuwar inda zasu ga Kubra a mace ko ra ye.
Nasir dai kawai ya amince ne amma har cikin zuciyar sa kuwa baya son ya bar garin ba tare da
ya ga kubra ba.
Amma haka suka hada kayan su domin tafiya maihaifar kakannin su
Domin su huta zuwa wani lokaci.
Kubra zaune ta tafka uban ta gumi ta ji mutum ya shigo ba ko sallama da wasu ledoji a hannun
sa ya ajjiye su gefen ta ya ce " Ki dauki Wannan sune kayan amarchin da ake bayarwa a
wannan dajin kuma ki sanya a ranki nine shugaban ki idan kina son zaman lafiya ."
Jin batunsa na yi dole ma na bashi amsa tunda daga ni sai shi kuma banga wannan
zarbaɗediyar abar ba wato bindiga, daman ita na ke tsoro dan haka na ajjiye shawuya gefe na
mike cike da ƙarfin hali ina muzurai wai dole Ni gani jaruma na ce " Ko taya zanyi biyayya a
cikin wannan auren?"
Kallo na ya yi cike da mamaki ya furta " Ban fahimta ba."
Sake gyara tsayuwa nayi "Ina nufin aure kan auren da a ka min, taya ina da miji kuma yana
raye bai mutuba zan zauna da wani a matsayin miji ?"
Dariya ya bushe da ita ya ce, "Kubra!! Wannan doka ce kuma dole ki bi kuma kowa haka ake
masa daga lokacin da kika shigo dajin nan idan kina da aure to auren ya watse saboda ke a
matsayin sabuwa kike a wurin."
Wani malolon taƙaici ya riski allon ƙirjina har ya fara min zugi na ce " To kuwa gaskiya bazan iya
zaman nan ba saboda Ni ban taɓa jin wannan lamarin ba sai yau. Kuma bazan taɓa hada jiki da
wani ba har sai auren da ke tsanani mu ya inganta." Cike da harzuƙa ya dube ni ya daga hannu
ya shimfiɗa mini wani mari Mai zafi wanda sai da na ga wasu taurari suna ya wo.
Ba shiri na durƙushe a wurin ina mai zubar da hawayen damuwa .
Kallon ta ya yi ya ce zan baki lokacin ki yi nazari kafin na zo na karbi hakkin aurena, na Miki
haka ne kawai dan na ga kina jego .
Kuma agidan nan ba ki da damar guduwa saboda ko da kin gudu to akwai inda idan harkinje ba
hanya sai koguna, kuma mutanen mu ne suke tsallake kowa da umarnin mu! Dan haka zaɓi ya
rage na ki. Ko kiyi biyayya mu yi zaman aure ko kuma ki gwada guduwa ki shiga hatsari
kamawa, kuma aka she ki........ Yana gama fadar hakan ya kwance ya juya mata baya a kan
ƙaramar katifar da yake.
Wani irin yanayi ta ji wani abu na son bugeta ta Sume saboda tashin hankalin da ta ke ciki.
"Allah ya rabbi ka kawo min sauki cikin wannan uƙubar da nake ciki.....
PG 7
Ganin ko ya kula harma ya fara baccin sa hakan ya sanya na tashi daga zaman da na ke na
dauki buta na yi alwala duk da cewa ina cikin halin jego. Amma hakan bazai hanani zaman yin
addu'a ba, dan haka wuri na samu na zauna na fara kai kukana wurin mahaliccina saboda shi
ka ɗai ne zai fidda ni ga wannan ukuɓar dana ke ciki.
Tsawon lokaci na dauka ina zubar hawaye gaban Allah ina sanar masa damuwata sai na ga
shawuya ya farka na shafa addu'o'in na dauke shi. Nono na fara bashi yana sha ina kallon sa
hawayen idanuna suna zuba kan fuskar sa. Da yanzu muna gida da yana cikin net killace cikin
kayan sanyi ga yan'uwa sun kewaye mu. Zanci kaza na sha shayi mai kauri na gyara jikina da
ruwan zafi! Amma tunda na zo sau ɗaya naga idanun ruwan zafi, abinci kuwa iya ka abincin
gado ne wato wake da shinkafa sai su taliya suma kuma duka masu yaji ne.
Gari na wayewa ya kawo min kayan abinci masu yawa a cikin harda kayan miya dakuma kifi
bushashe. Banyi wasa da rayuwata ba na ajjiye komai a gefe tunda na sanar da mahallici na
nasan zai tseratar da ni.
Dan haka na zage na daura ruwan zafi na na juye cikin wata kula na daura girki na na dafa
taliya da miyar ja wadda ta ji kifi, bayan na sauke na sake daura wani ruwan .
Ruwan kular na juye rabi na yiwa shawuya wanka tas farine tas da shi ga idanuwa ma sha
Allah kamar na Nasir dan yana matukar kama da shi.
Sauran ruwa na ɗiba na shiga dan zagayen da na gani na shiga gayar jikina ba karamin wahala
na ci ba saboda gaba daya na yi tsami kasancewar ba kulawa tun farko na sha a zaba kawai
daurewa na ke da na fito na samu ruwan ya tafasa shi ma sai na juye cikin kular na sake daura
wani na janye wutar saboda ina samu ina kama ruwa da shi wannan na kular kuma shi ne zan
dunga sha.
Ina so na samu ƙarfi jiki na warware sosai ta yadda zan iya jurewa dukkan wata wahala da zan
fuskanta a wajen guduwa dan na ci alwashin tse re wa. A binci na zauna na ci na ƙoshi na sha
ruwan ɗumi nan danan kuma ruwan nonon ya fara malalowa domin daman ni daga na haihuwa
ba wani jinkiri nono yake zuwa. Dan haka na ki shingiɗe har barci ya yi awun gaba dani abinka
da mai jego ba za'a rasa gajiya ba.
Kusan kwana shida muka dauka haka har mun fara sabawa da zama wuri ɗaya domin na lura
yana da sanyin hali ga kuma ba shi da yawan zaman gida, ranar da muka zauna gida ɗaya
muka kusa yini muna dan taɓa hira sai ranar na gane ainahin kamar sa. Fari ne dogo mai tsayi
ga jiki gare shi dai dai gwargwado. Ba shi da muni amma kuma bashi da yawan fara'a ya ɗan
bani labarin sa saboda ya ce mun mata ɗaya ya taɓayi bai sake wata ba sai yanzu.
A raina na ce wannan ɗin ma baka samu mata ba. Daga gare ni dukkan yadda ya so ya ji wani
dan labari ban ba shi ba na kance masa na mance komai nawa. Satin mu guda ya fara fita dani
bayan gari da nufi na sake da shi domin na lura shi acikin y'an ta'addan ma yana da tausayin
mace mai jego .
Kowanne na miji yana fita da matarsa yawan shan iska har bakin ruwan da suke faɗa harma
wani lokaci wasu suna hayewa domin su samu sakewa da matansu. Kullum mukaje wurin ina
lura da dukkan wani motsi saboda na samu hanyar kufcewa. Amma abin ya fi ƙarfin tunani na
saboda mugun tsaron da yake a wannan dajin ! Haka na ke lallaɓa rayuwata ina ta ka tsan-tsan
da komai.
Abu na farko da ya fara daga min hankali shine yadda wannan mijin nawa da ban san sunan shi
ba ya fara neman hakkin auren sa a gare ni! Na shiga damuwa da firgici da na fahimci lamarin,
saboda a tunanina zan samu wata damar tserewa kafin ya amfana
dani.
Nasir ne zaune bakin gadon su da Kubra idan ya kalli kayan ta da yake ajjiye a kan gadon
wanda ta goge ta ce shine zata sa gobe suje gidan Hajiyar sa. Wani hawaye Mai zafi ya ke
zubarwa idan ya tuna yadda sukayi rayuwar su cikin farin ci da ƙaunar juna.
Baya mance ranar da ta ke ce masa idan ta haihu tana son su koma wata jahar daban da zama
domin ta gaji da rayuwa a wurin da ya ke da fargaba
Duban ta ya yi ya ce "Haba ƙurraty na, ai komai kika ga ya faru to rubutacce ne shi. Dan haka
ko ina zamuje idan har Allah ya tsara wani abu zai faru ba fata ba to tabbas sai ya faru."
Kallon sa ta yi cikin yanayi na sanyin jiki tace " Haka ne Habibi amma wallahi sam wannan garin
ya fita a zuciyata saboda wallahi bana son abinda zai tarwatsa min zuri'a ko ace na rasa ka !
Saboda ina matukar kaunar ka Habibina yadda baka tsammani.
Murmushin na yi dajin batun na ta na karshe na ce "Haba ƙurratul aini na, Ba sai kin fa ɗa ba na
fi kowa sanin haka kuma in sha Allahu ba abinda zai faru."
Sake gyara zaman sa ya yi bayan ya dawo daga duniyar tunanin matar sa ya dauki kayan ya
sanya cikin durowar kayan ta ya rufe ya yi maza ya fita a ɗakin domin komai zai iya faruwa da
shi idan har yana kallon dukkan abin da ya shafeta.
"Ƙurraty! Allah ya bayyana min ki in sha Allahu baki mutu ba."
Nasir ya faɗa yana share hawayen idanun sa.
Ganin kwana biyu ya matsa da zancen ne na buƙaci da ya zo muje wani ƙauye mana to domin
muma musha amarchin mu Chan tunda haka ne. Bai yi musuba ya amince min, kuma na sanar
da shi na fison ƙauyen da sai an tsallake ƙogi saboda na ga duniya Nima.
Ya ce dani ba damuwa gobe na shirya mutafi.
Hakan kuwa ta kasance tun safe na ke shirin fita saboda ni kadai na san me na shirya cikin
zuciyata
Kamar misalin ƙarfe goma na safe ya zo ya ce dani Bismillah,dan haka muka dauki hanya muna
tafiyar ƙafa har zuwa bakin ƙogin da yake da ta zarar ba nisa ba ce sosai a wurin su amma kam
zai kai kamar kilo mita guda da rabi.
Koda zuwan mu ya sanar da su inda zamuje ba su hanamu ba suka sanya mu cikin
kwale-kwale ya yin da wani farin cikin ya riski zuciyata don ji nake komai ya zo karshe.
Amma mai zai faru tuƙawa biyu akayi na