Showing 1 words to 3000 words out of 56747 words

Chapter 1 - SAKACINA KO HALIN MAZA Book Complete .pdf

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K

SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*



*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*


*SHAFI NA ƊAYA*

REPOSTING
Sanin cewar a kwai banbanci a cikin duniyar da Allah subuhanahu wata ala ya halitta masu
ɗauke da halittu mabanbanta jinsi,bayan ya halicci duniyar mutane, da kuma waɗanda ba'a ji
ko gani gare su sai dai duk wanda ya yi imani,ya na da yaƙinin samuwarsu a cikin duniyar da
muke cikinta,da sauran halittu na dabbobi.Allah gwani wanda ba shi da abokin tarayya a cikin
gwanintar halintunsa,ya halicci mutane ya kuma nuna babu wani banbanci a tsaƙanin su,sai
wanda ya fi wani tsoron kiyaye abin da ya sharaɗa game da bautarsa,tabbas wannan haka ya
ke a gurin Allah,amma kuma yayin da jinsi na bil'adama suka ɗauki sabanin haka,sun ɗora
mizanin hankalin su suna auna banbanci na jinsi ta hanyar duba ga mulki,kuɗi ko kyawu na
halitta.Su na kallon waɗanda suka mallaki waɗannan ababen na more rayuwa ga mafi
ƙololuwar more rayuwa,wanda duniya ta yi maraba da zuwan sa kuma su ke kurɓan ruwan mafi
ƙololuwar ɗaɗi a cikin ta.
Haka ta kasance ga wannan matashi mai cike da kyawu da kuɗi da kuma baiwar ilmi da Allah
ya azurta shi dashi,ya na ji da kansa da kuma kalar rayuwar da ya tsinci kansa a cikin ta,bai san
a kwai wani ƙunci ko wani ƙalubale da Allah ya ke jarabtar bayin sa,waɗanda suka yi imani
domin ya gwada ƙarfin imanin su da shi. Tabbas duniya ta na gara masa ƙwallo yadda ya ke so,domin ya fito daga cikin farin jadawali na
tsarin rayuwarsa don ya yi gam da katar da bai fito daga cikin baƙin jadawali ba!Waɗanda da
duniya ta ke musu kamun kazar kuku, su shiga halin ƙaƙa na iya tare da tunanin makomar
rayuwar su. Sanye ya ke cikin shadda ruwan bula gizina,sai ɗaukar ido da sheƙi take ga wani daddaɗan
ƙamshi da ke tashi a jikin sa wanda ya ke sanyaya zuciyar duk wanda ya shaƙi ƙamshin.
Tuƙi ya ke cikin gwanance wa da kuma yanga,dan yadda yake jan motar ya ke kamar mai jin
bacci ya na lumshe idanunsa masu kama da mai jin bacci.Gefen sa amininsa wato Ak ya ke
zaune a kujerar mai zaman banza da wayarsa riƙe a hannunsa ya na dannawa.Jefi-jefi su na
taɓa hira duk da hirar ta su,ba ta wuce na 'yan daƙiƙa yayin da shuru yafi yawa a tsakanin

su,kasancewar ta kowannen su ya na ji da kansa, dan sun haɗu ta ko ina ga kyau kuɗi da kuma
wayewa da tsantsar ilmi.

Wani irin ƙara motar ta yi ya ja birki ya tsaya cikin tashin hankali ganin wani tsoho ya shige
masa gaba har ya buge shi da motar.Ya tsaya ya na kallon gurin da takaici,ganin yadda tsohon
ya ke son ɓata mishi lokaci.
Da sauri ya kuma buɗe murfin ƙoofar zai fita ya na faɗin"Wannan wawan mutumin zai ɓata min
lokaci,an gaya mishi bani da aikin yi ne?" Ya fice ba tare da ya kula Ak da yake mishi magana
ba,da sauri Ak shima ya fito sanin halin shi sai dai kafin ya ƙara sa Am ya wanka ma wannan
tsohon mari har guda biyu. "Ba ka da hankali ne da wannan banzan ƙarfen na ka zaka ɓata min lokaci?Shashasha kawai!"
'Dan tsohon ya yi taga-taga ya faɗi har ya na fasa baki,da sauri Ak ya kama hannunsa ya mike
sai kawai ya fashe da kuka,don shi kaɗai yasan halin da yake ciki.
"Haba A.m ya zaka mari wanda ya haifeka rashin mutincin na ka ya kai haka?Dubi halin da
yake ciki amma baka tausaya mishi ba."
Harara ya watsa mishi kamar ba zai ce komai ba,har ya fara taku zuwa motar shi sai kuma ya
buɗe baki ya ce,
"Kai baka ganin abin da ya yi min?Jiya na fara hawa motar nan amma ya ƙuje min mota.Nasan
kaf zuriyarsa babu wanda zai iya siyan ko da tayar motar ce."A.k ya yi shuru ya na kallonsa
cikin takaicin halin sa,na rashin daraja talaka da nuna tsantsar tsana da hantara,amma shi a
ganin sa ya kama ta ya dinga kawaici saboda yasan waye Ak kuma waye asalinsa. "Da izinin Allah sai ka sami dai-dai da kai ya faɗa ya na jin tsoro kasancewarta yasan waye shi
ɗa ne ga Alhaji Muhammad Turaki,waye bai san wannan family masu ji da kuɗi da ilmi da
wayewa.Cikin sa'a sai A.m bai ji abin da ya faɗi ba don ya juya ya nufi motarsa ya na tsaki.
A.k ya zaro kuɗi masu yawa ya miƙa mishi ya na ce wa." Gashi Baba ka yi haƙuri don Allah ka
je asibiti a duba ka." Ya faɗa ganin duk ya ƙuje a hannunsa.Da sauri ya karɓe ya na
godiya,ganin kuɗ'in da ya ba shi dan shi gaba ta kai shi ,dama ya fito zai je ya saida kekensa
gashi kuma ya sami wannan kuɗi. 'Dan tsohon ya dinga saka mishi albarka ya na hawaye kamar zai yi mishi sujjada, juyawa ya yi
ya nufin motar da A.m yake ƙoƙarin tayar wa,sai kuma ya tsaya ya na kallon titin da alamun
abin hawa yake nema a ransa ya na jin kawai ya haƙura da abokantakansu don ya sama ma
zuciyar sa salama,da irin cin kashin da A.m yake yi wa talaka a gaban sa. A.m ya kashe motar ya fito ya na mishi maganar ya shigo,amma ko kallon inda yake bai yi ba
sai ma juyar da kansa da ya yi,ya na kallon titi fuskar sa kamar an aiko mishi da mala'ikan
mutuwa.
"Well." Ya ce tare da ɗaga kafaɗunsa ya juya ya na faɗin"Shike nan tun da baza ka taho muje
ba ni na tafi,sai mun haɗu a ofis ka taho min da fayal ɗin da mukai maganar dakai,sannan ka
shirya gobe ne tafiyar mu". Ya ta da motar ya bar gurin A.k na kallon motarsa har ta ɓace wa
ganinsa,ya ja numfashi mai zafi ya fesar ya riƙe habbar shi ya na jiran ɗan acaba,sai kuma ya
fasa hawa mashin ya fara taku ahankali ya na jiran adaidaita.Tafiya kaɗan ya yi ransa a jagule
ya na jin zafin yadda yake nuna tsanar talaka karara baya kawaici a gabansa,yasan cewar
bazai taɓa iya canza aminin nasa ba don tsanar talaka a jinisa yake kasancewar duk family
d'insu basa son talaka ya rabe su,shi kansa don Allah ya bashi tarin baiwar ilmin kasancewar

Allah ya yi mishi baiwa da samin na'ura mai ƙwaƙwalwa,kuma saida suka mai da shi wani don
yanzu ya na jin kansa a cikin jerin masu hannu da shuni.
Murmushi ya so ya suɓuce mishi sai kuma ya dake,ya kauda kansa tamkar bai ga motar A.m da
ta yi ribas ta dawo ba,da ma yasan dole ya dawo kamar yadda suka saba duk sanda suka yi
faɗa a tsakaninsu, wanda ba ya wuce sati don A.m bashi da haƙuri ko kaɗan gidan su da gurin
aiki duk sun san haka,shi kuma A.k ba ya ɗaukar raini mafi yawancin lokuta mutane su na
mamakin yadda abokantakarsu ta yi ƙarko a haka don kullum cikin faɗa suke kamar wasu yara
Daddy shi ne ɗan sasanci,sam baya gajiya kasancewar ya na ji da shi saboda irin ci gaba da ya
ke kawo mishi a cikin kampanin sa,ya sani cewar in har babu A.k to kampaninsa bazai ci ga ba.
A.k ya kauda kansa bai tanka mishi ba sai wayar sa da ya ciro da nufin ya kira direban sa ya zo
ya ɗauke shi,don ya fasa shiga cikin a daidaita."Ganin ya taho kamar zai buge shi da motar
amma bai kula ba,sai ɗauke kansa da ya na kallon gefe don cike yake dashi.
A.m ya leƙo ta tagar motar sa ya ce ya na murmushi mugunta,don daga ganin yadda ya yi ya
san ya gaji matuƙa."Don Allah ka zo mu tafi kasan dole na dawo,Daddy ya kira ni ya na son
ganin mu". Banza ya yi da shi ya ci gaba da tafiya,ganin haka ya fito tare da kashe motar sai
kawai ya kama shi da kokuwa zai tura shi cikin motar,kamar dai yadda suka saba duk lokacin
da suka yi fad'a.
Bai wani ja ba ya shige cikin motar ransa a haɗe,dariya sosai A.m yake mishi don ya na
matuƙar son aminin nasa saboda riƙo da gaskiya, kuma bashi da shishshigi a lamuran sa.
Tun da suka shiga cikin motar babu wanda ya yi ko tari a cikin su,da ma ɗabi'ar su ce shirin
basu cika magana ba kasancewar kowa naji da kansa.
Wayar A.k ta yi ƙara alamun ana kira amma sai A.m ya kai hannunsa ya kashe wayar baki
ɗaya,don yasan mai kiran taɓe bakinsa ya yi ya ci gaba da tuƙi cikin kwanciyar hankali.A k ya ja
fasali tare da buɗe baki da nufin ya yi magana,amma da ya kula rigima yake ji sai kawai ya
kauda kanshi bai ce ƙala ba don har yanzu ransa a ɓace yake da abin da A.m ya yi ma
mutumim da ya haife shi.
Ko da suka ƙaraso tangamemem get ɗin gidan mai gadi ya buɗe musu get,A.m ya yi parking bai
kula da gaisuwar da maigadin yake mishi ba ya shige cikin gidan,yayin da A.k yabi bayan sa
kasancewar ba'a yi mishi shamaki da cikin gidan ba.

*******
Juwairiya zaune a gefen ƙanin ta Ibrahim ta zuba mishi idanu, ya yin da hawaye suke gasar
turarreniya a fuskarta,ji ta ke kamar ta yi hauka tsabar damuwa ta na jin wani irin baƙin cikin
halin da suka tsinci kansu. Zura hannunta ta yi a cikin kofin ruwa ta shafi fuskar Ibrahim da
yake kwance rai kwakwai mutu kwakwai,sai kuma ta kama shi ganin yadda ya zaburat amkar
zai shiɗe.
Mama da ke tsaye a bakin ƙofa fuskarta ɗauke da tsananin damuwa da ƙunci ta janye tagumin
da ta yi tare da ajiyan zuciya mai ƙarfi."Anty Juwairiya mutuwa zan yi ga shi Baba ya ƙi
dawowa."
Ya faɗa da wata irin murya da yake ƙoƙarin haɗa kalmomin da su."Baza ka mutu ba Ibrahim
ciwo ba ya kisa."Mama ta ce cikin tausayin sa.
Juwairiya kuwa ta kasa magana sai kuka ganin gudan jinin na ta ƙanin ta tilo na cikin wani
mawuyacin hali, ji take da ma ace ciwon a jikinta yake.Sun jima suna tsaye a kansa da

numfashin sa yake baraxanar ɗauke wa,hankalin su a tashe sai shafa masa ruwa suke yi suna
kuka gunun ban tausayi.
Juwairiya ce ta miƙe ta na faɗin"Mama bai kama ta mu zuba mishi ido mu na kallon sa a cikin
wannan halin ba,tunna Baba bai dawo ba zan fita na samo abin da za'a kaishi asibiti.Ta ce cikin
kuka Mama ta kasa ce mata komai duk da ta na tunanin in da za ta samo kuɗin,amma har ta na
shirin fita ba ce komai ba."Juwairiya na shiga uku!Ya sume."Ta ji muryar Mama cikin ƙaraji
dai-dai lokacin da ta fice da ga gidan.




*Follow,read,comment,share.*





*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*



*SHAFI NA BIYU*


Da sauri Juwairiya ta dawo ta rungumshi da hannunta ɗaya,ɗayan kuma ta na shafa mishi
ruwa, ajiyan zuciya ta sauke mai ƙarfi ganin ya buɗe ido,don hankalin su ya tashi maƙura gani
suke kamar mutuwa zai yi ganin yadda idanunsa suka ƙaƙƙafe.
Juwariya ta miƙe ta na faɗin."Tun da ya farfaɗo bari na je na naimo mishi magani."Miƙewa ta yi
ba ta jira amsar da Mama zata ba ta ba ta fice da ga cikin gidan ta na sharar hawaye.
A hankali ta ƙarasa shiga cikin shagon na sa ganin yadda ya haɗe rai tun da ya hangeta ta na

tahowa,tamkar an aiko masa da mala'ikan mutuwa ya haɗe ransa babu wani walwala.Jikin ta ya
yi sanyi sai ta tsaya a bakin ƙofar ta kasa mishi magana kuma ta ƙi ta tafi duk da kallon kora da
hali yake mata.
"Lafiya ki ka yi min tsaye kofar shago kamar na saki ki?Ya faɗa ransa a ɓace"Don Allah ka
taimake ni Bala kasan mai ya kawo ni a karo na biyu,wallahi suna cikin wani hali na rantse
maka wannan karon zan naimi kuɗin ka na baka."Ta faɗa da muryar kuka fuskarta bayyane da
damuwar halin da take ciki. "Ni ina ruwana na gaji da baki bashi kuma ba kawo min kike ba,sannan na nuna miki hanyar da
zaki bi mafi ɓulluwa kin nuna a'a wai ke ustaziya,to sai kije can amma ko maganin biyar ba zan
baki ba."Tamkar zai kai mata duka yake magana ganin haka sai kawai ta juya,dan ta saka a
ranta yau bazai bata ba. "A'a Juwairiya tafiya zaki yi."Ya faɗa da sanyin murya ganin ta kama hanyar fita,sai kuma ya
ƙara matso da fuskarsa gurin ta yace."Kin cika kafiya ki yadda ki amince ko sau ɗaya ne,Allah
zan baki duk abinda kike so.Kin san ina son ki Juwairiya na san babu yadda za'ai na same
ki,wannna dalilin ya sa nake so ki amince min kar soyayyata ta faɗi a banza." Ƙarashe fita ta yi da ga shagon dan abin da yake so bazai samu ba.Mahaifiyarta kullum ta na
mata nasihar ta tsare kanta da ga aikata zunubi mai girma wanda Allah yake fushi da wanda ya
aikata,kuma ya yi hani ga bayinsa muminai na ƙwarai.
Gidan ƙawarta Mariya ta wuce ta same ta zaune akan tabarma a cikin falo ta na gugan kayan ta
da dutsen guga na gawayi,sallama kawai ta yi ta zauna a kan tabarma ji take kamar zatai
hauka."Juwairiya lafiya kike mai ya faru?"Mariya ta jera mata tambayoyin da ta kasa ba ta
amsa ba,sai ta janye hannunta da Mariya ta kama tare da share hawayen da ya gangaro mata. Mariya ta ƙarashe share mata sauran hawayen ji take ita ma kamar ta saka kuka,ta ɗago
idanunta da suka kaɗa suka yi ja ganin ƙawar ta ta na kuka tace."Ki yi min magana
Juwariya!Kin san ba na jure ganin ki a cikin wannan hali,abin da ya sa naƙi dawowa kin san
halin Baba Sani na rasa yadda akai ya takurawa rayuwar ki baya son kowa ya raɓe ki,dan
haushin koron da yake yi nake ji irin kullen da yake miki ko fa yaran sa baya yi mawa,lamarin sa
akwai ayar tambaya ,dan ina tunanin akwai lauje cikin naɗi!"Ta ja fasali ta na kallon Juwairiya da
kukan ta ya tsananta,tuna yadda ya tsane ta yake azabtar da rayuwarta.Mariya ta ci gaba da
magana cikin ɓacin rai ta na cewa.
"Ina jin takaicin halin da kike ciki amma ki sani bawa bai isa ya canza ma wani rayuwar sa
ba,kin ga da Baba Sani baya miki kulle sai na sama miki aikatau ni bashi nake yi ba hankalina
kwance.
Juwairiya ta sauke ajiyar zuciya duk da baƙin cikin da take ji na ƙin barta ta yi aikatau,wanda
mahaifinta ma ya amince amma ƙememe ya hana ta da ta na yi ƙila da basu shiga cikin uƙubar
rayuwa ba,gashi tun da ta gama sakandiri ya hana ta karatu amma yaran sa duk sun yi.
Duk da lamarin na ci mata tuwo a ƙwarya amma ba ta ce ƙala ba,sai dai zuciyar ta cinkushe
take da damuwa tare da tunani iri-iri.
Mikewa Mariya ta yi ta shiga kicin ta zuba tuwo da miyar kuɓewa ta kawo mata ta na
faɗin."Gashi tun ɗazu na so na kawo muku amma ina tunanin wannan Baban naki,kuma Auwal
tun da ya tafi islamiya bai dawo ba balle na bashi ya kawo miki."Ta miƙa mata tare da kwance
ƙullin zaninta ta ciro naira ɗari biyu ta miƙa mata. Tsabar murna sai kawai ta rungumeta tare da fashewa da kukan murna,Mariya na taimakon ta

ƙwarai ta na fatan Allah ya bata ta taimaka mata.
Rako ta ta yi ta siya magani sannan ta kaita dai-dai kwanar lungun gidansu.Da sauri Mariya ta
saki hannunta ta na faɗin."Na shiga uku wallahi gashi nan duk da ƙin kaiki gida da na yi amma
ya na nan ya na sa ido ya san ki fita,ke Juwairiya wannan ko mijin ki ne sai haka."Ta ruga da
gudu har ta na tuntuɓe bayan ta gama maganar don Allah ya saka mata tsoron shi,bashi da
mutunci in dai akan Juwairiya ne.
Juwairiya da jikinta ya fara rawa ji ta yi kamar ƙasa baza ta iya ɗaukar halintar ta ba,ta tsorata
iya tsorata zabura ta yi kamar zata ruga sai kuma ta fasa ta na karanta wallahu galibun ala
amrih ganin ya tunkaro ta.
Ya ƙaraso ya na mata wani irin kallo da shi kaɗai yasan ma'anarsa."Ina kika je?"Ya tambayeta
da murya kakkausa tare da saka ƙafafunsa ya take mata 'yan yatsun kafar,ta rintse ido ta na jin
wani iri madarar azaba ya na taso wa daga kan 'yan yatsun na ta ya na zagaye ilahirin
jikinta,taso ta matsa domin akoda yaushe ya tsaya kusa da ita ta na ƙalubantar yadda yake
matsowa daf da jikinta.Amma hakan ya ci tura ganin yadda ya take kafarta ya hana motsinta.
"Bana hana ki yawon maula da uwarki ta koya miki,bayan Yayana bai rage ku da komai ba."Ya
faɗa ya na ƙara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login