Showing 33001 words to 36000 words out of 56747 words
Chapter 12 - SAKACINA KO HALIN MAZA Book Complete .pdf
shahadar kiran wayarsa duk da ya san ba dole ba ne ya ɗauka saboda ya yi fushi
tunna mai tsanani da shi.
ilai kuwa wayar ba ta shiga wanda ya tabbatar mishi da ya yi blocking ɗin layin ne,ɗaga wayar
ya yi zai yi jifa da ita sai ya fasa ganin kira ya shigo a ransa ya na addu'ar Allah ya saka shi
ne,duk da ya san abu ne mai wuya ya kira shi
Ganin kiran Daddy sai hankalinsa ya tashi ya kai hannu zai kashe bai san sadda hannunsa
saboda ruɗewa ya danna masa amsa kira ba har kuma ya saka a amsa kuwa.
"Son lafiyar ka kuwa wai me ke faruwa ne?Rejecting ɗin wayana kake yi are you alright kuwa?
Ina A.k wayarsa ba ta shiga lafiya yake mai ya faru tsakanin ku mutane suna ta kirana suna
complaining tun shekaranjiya na ɗauka ko bai jin daɗi.Gashi gobe ne tafiyar ku chaina.
Daddy ya fara magana ya na jero mishi tambayoyi cikin tsananin damuwa wanda ya ƙara ta da
hankalinsa to mai zai cewa Daddy shi kam ya yi nadama sosai ya san ya na da saurin fushi
amma nan da nan yake sauka.
"A.k ya yi fushi sosai dama haka yake da ɗaukar abu gaskiya na shiga ruɗani kawai na haƙura
da auren bani da rabon haihuwa ne don ba zan iya karya alƙawarin da na yi ma Zainab ba,ba
zan iya rabuwa da ita ba don ina son ta na tabbata duk ranar da na kawo wata mace Zainab za
ta yi kisa in kuma ba ta yi ba za ta kashe kanta ko ta rabu da ni,ni kuma ina sonki bazan iya
rabuwa dake ba."
Sai kawai ya rintse idanunsa ya na jin wani gululun baƙin ciki ya tokare shi a maƙogaron sa ya
duka ƙasa don jin shi yake zai faɗi."Hello ka na ji na a kwai abin da kake ɓoyewa son ban yarda
yadda yake girmamani,zai daina zuwa aiki ba maza ka shirya muje gidan sa duk in da kake ka
dawo ina jiranka ga shi nazo ofis ɗin ka baka nan."
Muryar Daddy ya katse mishi tunanin sa ya firgita lokacin da ya faɗi haka dama ya san babu
wanda zai yi gigin gaya masa sun samu saɓani ne in ba so suke su rasa aikin suba.
" Um um Daddy ba ni kusa na fita a mashin zan karɓo tsako bari na dawo sai muje."
" Ok duk ma in da kake yanzu ka yi maza ka dawo."
Daddy ya ba shi umurni tare da katse wayar sa ya bi wayar da kallo ya san dai a kwai abin da
ya haɗa su,amma haka kawai A.k ba zai ƙi zuwa gurin aiki ba sanin sa mai ƙwazo da kiyaye
halalin sa.
Kamar an ce ɗaga labule sai ya hangi A.m ya zura da gudu ya na sanɗa ya fice daga kampanin
kamar wani ɓarawo,kamar yadda mutane suka tsaya suna mamakin haka tare da tunanin
lafiyarsa kuwa Daddy sai abin ya ba shi dariya ya kira Mudassir ya nuna mishi shi,dai-dai
lokacin da ya fice da gudu har ya na buge kai da get.
Dariya suka ƙara kwashewa da shi." Wai me ke damun son ne ya canza kwana biyu."Daddy
yace ya na kallon Mudassir shiru ya yi kawai don ba za'a ji mutuwar Sarki bakin shi ba.
Yafi kusan rabin awa in yakai hannu zai ƙwaƙwasa gidan sai ya janye ya kai ma iska naushi ya
na jin tsananin nadamar abin da ya yi masa.
" A'a yallaɓai kai ne a tsaye."
Megadin gidan da ya fito da ninyar ya siyo abu a shago ya gansa tsaye.Jikinsa ya hau rawa don
shi bai ji ya ƙwanƙwasa kofar ba ya san zai sha faɗa." Don Allah ka yi haƙuri wallahi ban ji ja ba
kuma ba bacci nake ba."
Ganin ya gigice sai ya buɗe baki a wahalce yace." Karka damu yanzu na zo."A taƙaice ya haɗa
kalmomin don baya son magana.
" To shigo zan ɗan siyo a bu a shago ne."
Yace ya na waigen in da yabar motarsa amma ganin bai gan ta ba ya wuce abin sa.
A hankali yake taku zuwa cikin gidan ya na isa kofar shiga falo ya ga an buɗe ƙoda tun kafin ya
ƙwanƙwasa,matar A.k ne ta na dariya." Hangoka na yi na Zey."Tace masa da masa.
" Uhumh kawai yace ya ƙara sa ciki ya zauna."Ina mijin ki na yi mishi laifi don Allah ki ba shi
haƙuri tun kafin ya fito duk da na san ba dole ba ne ya fito."Yace mata cikin damuwa.
" Oh wannan tsakanin ku ne ya dai kama ta ku din ga haƙuri kun girma fa shi ma tun da lamarin
ya faru yake ta huci na ba shi haƙuri amma yaƙi."
Tace sannan ta miƙe ta nufi ɗakinsa ba ta jima ba ta dawo fuskarta babu walwala na ƙin zuwa
da ya yi duk irin haɗa shi da Allah da ta yi kan ya gane kuran sa.Bayan fitar ta ne A.k ya rintse
idanun sa ya na jin ɗacin abin da ya faru tsakaninsu shi da Allah yake son shi ba wai don kuɗin
sa ba,amma haka A.m ya rufe idanunsa ya na gaya masa baƙaƙen maganganu kuma sab ba
zai goya mishi baya akan abin da yake so ba.
A.m ya canza fuska tun da ta gaya mishi bai ce da ita komai ba idanunsa a rintse ya miƙe
tamkar wanda ƙwai ya fashe mawa a ciki ya fice ba tare da yace komai ba,abin da ya sa ya zo
tsoro yake kar A.k ya gaya ma Daddy abin da ke faruwa kawai ya haƙura,amma tun da yaƙi
fitowa bari ya ɗauko Daddy koma me zai faru ya faru.
Da ya koma hankalin Daddy ya tashi ganin yadda ya ɗan faɗa tsakanin kwana biyu,dafa
kafaɗarsa ya yi." Ka na cikin damuwa lafiya wai me faruwa ne?Ina A.k ɗin?"
Ya jera masa tarin tambayoyi a tare ya shaƙi numfashi ya fesar sai kawai ya kwanta akan
kafaɗar Daddy cikin muryar kuka ya na hawaye yace." Daddy A.k ya yi fushi da ni mun ɗan
sami saɓani ne saboda wata ƴar matsala kuma na je gidan sa na ba shi haƙuri,ni na janye
wannan maganar amma yaƙi saurarata har ya ije aiki.Daddy shi ne ya ɓata min rai na kasa riƙe
kaina na faɗa mishi baƙaƙen maganganu, amma na yi nadama sai dai ya datse layina layika na
ba ya son magana da ni."
Sai ya sa kuka kawai hankalin Daddy ya ƙara tashi yau shagwabar ta tashi kenan.
Miƙewa ya yi." Oya tashi muje gidan na sa amma ba ka kyauta ba duk da tsaƙanin harshe da
haƙori ana saɓawa,nan gaba ka kiyayye ba'a ɓata ma wanda yake kusanci da kai sosai in ma
hakan ta faru ƙoƙari ake a riƙe fushi don dole zaku ne mi juna."
Daddy yace ya na shafa bayan sa." Gaskiya ne Daddy na ba shi haƙuri fa kuma na yi nadama.
A lokacin da suka isa gidan da matar shi ta shiga da nufin ta gaya masa,har ya ji muryar Daddy
a falo da sauri ya zo ya durkusa ya na faɗin." Da kan ka Daddy ai da ka sanar min ni zan zo."
" Ta ina zan sanar maka bayan ka kashe wayarka.Son ya yi laifi a yafe mishi don kawai kun
samu saɓani za ka dai na zuwa aiki, in ka ƙara hakan zan hukuntaka ta hanyar turaka ƙasar
waje ka yi wata biyu ba tare da ka dawo gurin iyalin ka ba,saboda ka ɓata min rai kuma na yi
fushi da kai."
Jin abin da ya faɗa da sauri maman Najwa ta miƙe tare da ficewa ko gaisuwar da ta tsaya ta yi
ma Daddy ba ta yi ba,don ya ba ta kunya duk da ta san in ya yi hakan ya cutar da rayuwar
masoya.
" Ka yi haƙuri Daddy na yi nadama hakan ba zai ƙara faruwa ba! Da ma A.m ɗin ne ya...."
" Daddy ya yi haƙuri kawai ya koma aikin sa ni nama haƙura akan maganar da muka yi na fasa
na janye."
Yace da sauri ya na kallon A.k don ya tsorata ya ɗauka gaya ma Daddy zai yi.Daddy ya kalle su
duka kamar a kwai abin da suke ɓoye mishi wanda shi ne ya kawo musabbabin faɗan.
" To wai me ya kawo rikicin?"
Ai kafin ya rufe bakinsa A.m yace."Daddy ba komai ai mun shirya ya wuce."
A.k dai bai ce komai ba Daddy ya kama hannunsa ya haɗa." Kar na ƙara jin kun yi faɗa ku yi
min alƙawari."
"Hakan ba zai ƙara faruwa ba Daddy komai ya wuce."Kamar sun haɗa baki don a tare suka
faɗa. " Ok ka shirya ka taho aiki dama ina son na ƙara maka girma."
A ranar dai ba wata magana na amininai da ya shiga tsakanin su,amma tare suka fita zuwa
aikin sai dai A.k ko zuwa su tafi cin abinci kamar yadda suka saba bai yi ba,don har yanzu ya na
jin haushin abin da ya yi mishi hakan ya sa yake yin azumi don ya rage mishi fushinsa tunna ko
Allah muna mishi laifi kuma ya yafe,amma shi mutum ne wanda ya san mahimmancin kansa.
Ƙin zuwa su je suci abinci hakan ya tabbatar ma A.m bai huce ba sai da ya daidaici ya gama
tarin aiyukansa da ya jibga ma kansa,ya shiga ya na zaune a kan kujerar ofishin ya rintse
idanun shi wataƙila bacci yake.
Shigar shi ya farkar da shi ya tashi ya zauna." Don Allah ka yi haƙuri haba na san ina da
fushi,amma ba ni da riƙo na lura kafi son Juwairiya da ni na haƙura da haihuwar don ni ba zan
aure ta ba don na rayu da ita har abada,amma tunna ba ka so mu manta da zancen.
Ga mamakinsa sai A.k ya bugi bayan sa ya na dariya yace." Haba na manta da wannan kuma
akan maganar Juwariya na yadda ka aure ta Allah zan ba ka gudummuwa in har Daddy zai
amince ya nema maka auren ta a sirri."
Ya ɗan kalle shi ko ya yi tunanin wasa yake masa amma bai ga alamun haka ba sai ya rungume
shi ya na faɗin." Na ji daɗin amincewar ka yamzu mu tafi gurin ƙanin mahaifin ta."
Tofa masu karatu kun dai jin yadda ta kaya game da waɗannan aminan juna,Baba Sani zai
yadda ya basu auren ta.Ku ci gaba da bibiyata na gode da yaba lintafina da kuke.
ƊUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ƊIN KU YA NA SAKA NI NISHAƊI.
MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha
huɗu.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.
Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni
mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata
(SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da
irin taimakon da kike bani.
COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*Page 14*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Sakamakon aiki da ya yi musu yawa sai hakan ya hana su zuwa kamar yadda suka shirya a
ranar,saboda ba su tashi daga gurin aiki ba sai bayan sun yi sallar magariba daga nan kowa ya
nufi gidan sa.
A.m ya ji daɗi sosai ranar kasa bacci ya yi gani yake kamar ya auri Juwairah ya gama
musamman da aminin sa ya amince,duk da a cikin zuciyar sa har yanzu ya na tunanin mai ya
saka A.k ya sauko har ya amince duk da dokin naƙi da ya hau daga farko.
A haka dai ya yi ta saƙe-saƙen shi amma ya rasa gano komai daga ƙarshe ya janyo bargon da
Zainab ta rufe jikinta da shi ta na bacci,ya rufa da shi tare da juyawa dai-dai fuskarta ya
rungumeta ya na shaƙar daddaɗar ƙamshi daga gareta,yayin da hankalin sa yake kwance
kamar ya yi baƙo ya mutu a ransa duk ya ƙosa gari ya waye su ji yadda za su kaya da ƙanin
mahaifin Juwairah.
A.k kuwa ko da ya koma gida hankalinsa a tashe gani yake kamar ya aikata zunubi me girma
akan amince masa da ya yi,amma da ya auna a mizanin hankali sai ya ga da ta auri wannan
tsohon rayuwar ta ta shiga garari gara A.m da ko ba komai za su samu ci gaba a rayuwa,duk
kuma abin da zai faru wannan kuma ya bar ma Allah lamuran sa shi yake da iko akan
komai,kawai abin da zai yi shi ne ya gaya ma Juwairiya kar ta yadda zuciyarta ta fara son A.m.
Ya daɗe sosai ya na shawara kafin ya furta ya amince da auren musamman da ya ji
mahaifiyarta ba da lafiya,a taƙaice dai tsotsan tsamiya suke yi a rayuwar su tare da alhini.
Washegari da safe A.m ya yi mishi dirar mikiya ko karyawa a gidan sa ya yi,wanda Maman
Najwa ta yi mamakin sammakon sa amma sai ta yi tunanin ko ya na son A.k ya manta komai.
Bayan sun gama karyawa suka nufi gidan su Juwairiya.
Baba Sani ya na ƙoƙarin fita gurin aiki da ƴar ƙaƙuran motarsa da yake riƙe da makullin ta a
hannun sa ya na karkaɗawa.
Ganin su a kofar gidan sai ya yi turus ya na tunanin mai ya kawo waɗannan larabawan kofar
gidan ko sun yi makuwa ne,saboda ya na da ɗagawa sai ya ɗauke kansa zai shige cikin motar
sa ba tare da ya kalli in da suke ba,duk da tunani ya cika ran shi ganin sun tunkaro sa.
"Assalamu alaika Malam barka gurin ka muka zo,don Allah ko zaka ba mu lokacin ka duk da ba
ka san da zuwanmu ba,amma in ka bamu ƴan mintuna zamu tafi musammam in ka yi ma abin
da ke tafe damu kyakykyawar fahimta."
Yace da shi da murya mai sanyi duk ƙoƙarin sa ya tabbatar masa da baƙin sa ne saboda fuskar
sa ta nuna kokwanton ko sun yi makuwa ne,duk da ya san ya na da ƴan mata amma ko kaɗan
bai yi tunanin za su zo neman ɗaya da ga cikin su.
Ya kalli A.m da ya ɗaure fuskar sa kuma bai ce komai ba ya lura wamda ya yi mishi magana ya
fi shi sakin fuska,sai ya mai da hankalinsa ga A.m yace a cike da shakku don shi har yanzu bai
yadda gurin sa suka zo ba.
" An ya gurina kuka zo ko kuma kun yi makuwa ne wataƙila tambaya ce da ku."
" Ka na shakkun mun zo gurin ka ne mu ba mutane ba ne? Ko aljanu ka gani." A.m ya ce mishi
ba tare da ya kalle shi ba hankalin sa na gurin wayar sa dake hannun sa ya na daddannawa.
Baba Sani nan take ya ji ran shi ya ɓace ya kalle sa a ran sa ya na faɗin." Ba ka sanni ba kenan
amma bari na ji da wanne kuka zo."
" Gashi kuma sauri nake zan tafi aiki sai fai ku dawo wani lokacin." Ya ce fuskar sa a ɗaure
ganin A.m ya zo da rainin wayo.Am ya buɗe baki zai yi magana sai A.k ya watsa mishi kallo
kuma aka ci sa'a ya yi shiru ya ci gaba da kallon wayar sa.
" Don Allah ka yi haƙuri ka bamu ƴan mintina kamar yadda na buƙata da farko ka saurari abin
da yake tafe da mu."
A.k ya ce cikin marairaicewar fuska ya kuma haɗa hannun sa biyu ya na roƙon sa.A.m kuwa
kofar gidan ya din ga bi da kallo ya na jin wani tsigar jikin shi na tashi,wai shi zai haɗa jini da ƴar
wannan wulaƙantaccen gidan mai kama da bola,duk da Baba Sani ya na ƙoƙarin gyarawa
amma abincin wani gubar wani.
" Ok to muje in har zaku taƙaita maganar da ta kawo ku a cikin lokacin da kuka iba."
" In sha Allahu."
A.k ya bashi amsa a lokacin da suka shiga cikin gidan zuwa ɗakin Baba Sani A.m ya na ta
wulƙita ido ko zai ga Juwairah don shi yanzu ma ya