Showing 54001 words to 56747 words out of 56747 words

Chapter 19 - SAKACINA KO HALIN MAZA Book Complete .pdf

Advertisement

saboda tashin hankalin da ta ga ya shiga,abincin da ta girka
masa ya yi jifa da kwanonin da suke jere a dinning ɗin,ya zaro wayar sa ya kira ta sai dai har ta
gama ringing ba ta ɗauka ba.

Jifa ya yi da wayar ta faɗi a kan tayas ta fashe ya dunƙule hannun sa guri ɗaya ya furta." Zainab
ki na son sa min hawan jini sai dai wannan karan ba zan ɗauki wannan iskancin ba,ina mijin ki
ki tsallake ki tafi wata ƙasa hakan ba zai yiwu ba.

Idanun Juwairiya suka kawo ruwa sai hawaye ganin ita kuma haka Allah ya ƙaddara rayuwar ta
su dun ga sauke fushin su akan ta.

" Ke!"

Ya daka mata tsawar da ya firgita ta sannan ya ci gaba da magana da ce wa." Wallahi yanzu
jikin ki zai gaya miki dukan ki na yi zaki saka min kuka bayan na gaya miki na tsani kuka a
rayuwata,maza fice ki ba ni guri sannan ki ƙara min wani abincin.

Hakan ya ƙara saka ta sakin wani kukan tuna yadda ta sha wahalar girkin ya zubar kuma yake
buƙatar ta ƙara yi masa.
Da sauri ta wuce kicin ta bar shi a falon ya kai gwauro ya kai mari da ga ƙarshe wayar sa ya
ɗauka da nufin ya kira A.k,sai dai kuma ya ga aika-aikar da ya yi tsaki ya yi da nufi ɗaki don ya
ɗauko wata.

Bai jima ba ya fito bayan ya yi wanka ya canza kaya ko kallon abincin da ta girka bai yi ba ya
fice daga gidan.

A haka suke ta zama na rashin daɗi duk da A.m na buƙatar ya kawo ƙarshen zamanta a gidan
amma ya kasa,haka dai yau ya daure da nufin zai yaƙi zuciyar sa don ta bar mishi gidan sa
saboda ba ya son ganin ta a ciki.

Da misalin biyar da rabi ya dawo gida Juwairiya na falo ta na kallo da ƙaton hijabin ta,ya na
hango ta ya tsaki wawan tsaƙi saboda shi haushin hijaban da take sawa yake yi bayan ta san
ko shi wanene a gurin ta.

" Wawiya ƙazamiya a haka yadda kike ɓoye jikin ki ko uban me take ɓoyewa shi bai ga abin
sha'awa a jikin ta ba."

Ganin sa ya sa ta miƙe da sauri za ta shige cikin ɗakin ta.


"Ke."
Tsayawa ta yi ba tare da ta kalle shi ba don ta san wani wulaƙancin zai yi mata.
Hararar ta ya yi ya zauna akan kujera tare da ɗaukar remote ya canza tasha,sannan ya kalle ta
ya ce " Gidan uban wa za ki saboda dodo ya dawo ko?Wai haka kika ga matan aure suna
rayuwa a gidan mazajen su kullum cikin hijabi ke sam baki da wayewa ne?"

Juwairiya ta yi sororo ta na kallon shi jin wani sabon salon da ya fito da shi,amma ba ta ce masa
komai ba sai kallon shi da take tamkar baƙo a gare ta.

" Maza ki je ki kawo min abinci."

Ya ce ganin ta kafe shi da ido ba ta san shi ma ransa a ɓace yake maganar ba saboda tsanar ta
da yake ji kuma wai ta na matsayin matar sa.

Juwairiya ta so ta bi umurni n shi ta cire hijabin sai dai ina sam ba za ta iya ba,don tsananin
kunyar shi take da ke,don haka ta ƙi cire hijabin ta ɗauko abincin ta na ije mishi ta ruga zuwa
ɗaki.
Bayan ya ci abinci ya na zaune a falon har aka kira magariba ya yi sallah bai dawo ba sai da
aka kira isha'i,sannan ya dawo gida ya rufe gidan duk da ran sa a ɓace yake akan Zainab kuma
ya rantse in ta dawo sai ta ga abin da zai yi mata,amma sai ya daure ya ɗauki wayar sa ya
shiga ɗakin.
" Ki biyo ni ɗakina kin san ba zan iya kwana a ɗakin ƙasƙantu ƴan aiki ba."

Ya fice kallon sa kawai ta yi amma ba ta ce mishi komai ba har ya fita ta gyara kwanciyar ta tare
da karanto addu'ar bacci ta janyo bargo ta kwanta.
" Wataƙila maganar Baba Sani ta yi tasiri a zuciyar sa ya yadda ba ni da kamun kai ne har yake
tunanin na bi shi ɗakin sa a she zai bushe da jira na.

Washegari da safe bai ci ko abincin karyawar da ta yi masa ba ya fice daga gidan, don ko da ta
gaishe shi harara ya banka mata.
Sai abin ya ba ta dariya kawai ta ruga da sauri ta laɓe a ƙofar falon ta na kallon sa har ya fice
saboda wankan da ya yi ya tafi da imanin ta.

Sakin labulen ta yi ta zauna a falo tare da ɗaukar filo ta rungume a ƙirjinta ta na jin wani irin
nishaɗi, don ko kaɗan ba ta yi tunanin rayuwa tare da shi ba ko da kuwa a matsayin matar sa
kuma ƴar aikin matar sa.
Bai shigo gidan ba sai da daddare tare da A.k suka shigo suna ta hira abin su.
A.k na ta baza ido ya gan ta bai gan ta ba musamman da ya ga Zainab ba ta nan,kallon A.m ya
yi da yake ta aika ma cikin sa abinci saboda tun zuwan Juwairiya gidan hankalin sa ya kwanta

na rashin samun abinci.

" Kai wai ina maryar ka ne ?Tun na yanzu madam ba ta nan na san ƙila an samu baby?"

Ya faɗa ya na kallon shi ya na dariya tare da kai mishi duka a kafaɗan sa.Taɓe baki ya yi ya
ce.Ina zan sani kai kyale ni da wani amarci Juwairiya muguwar bagidajiya ce kullum cikin hijabi
ka san kuma ba haka Zainab take min ba."

Ya ɗan kalli A.k da ya daina cin abincin ya na sauraron sa ya ce."Jiya da na kira ta ɗakina ƙin
zuwa ta yi ban san tunanin ta a kai na ba."

" To kai in ban da abin ka A.m ai kai za ka bi ta kuma kuma mace take Hausa dole ta ji kunya."
A k ya ce da shi ya na kallon sa.A.m ya ƙara taɓe bakin sa ya ce." Ok ka manta abin da ƙanin
mahaifinta ya ce a kan ta ni ban ga abin kunya ba."
"A haba A.m ka san halin sa kar ka yadda da maganar sa kuma koma mene ne kai ka amince
za ka aure ta sai ka ba da azama mu sami baby.".
Dariya suka yi duka daga bisani A.k ya matsa mishi ya kira ta su gaisa ya na zaune ya ƙwala
mata kira ba ta jima ba sai ga shi ta fito,kamar dama laɓe take musu ta na jin maganar da suke
yi.

A.m tashi ya yi ya nufi ɗakin sa zai ɗauko tsaƙon da A.k ya biyo shi ya karɓa ba tare da ya kalle
ta ba.

Da ladabi ta gaishe shi ya amsa ya na ta tsokanar ta dai murmushi take masa.
" Na so mu haɗu kafin ayi auren ki da shi sai dai kuma Allah bai nufa ba ko Juwairiya?"

Ya faɗa tare da mai da maganar ta tsigar tambaya.Ɗaga masa kan ta ta yi ta na kallon shi " Ok
ba komai da ma na so na ɗan miki wata magana ne Juwairiya don Allah duk yadda zuciyar ki za
tai ki karki yadda ki saka son A.m a ran ki kawai ki sama ran ki zaki ci arziki ki tafi ne.Ki ɗauke ni
a matsayin Yayan ki duk lokacin da wata matsala ta haɗa ku ki sanar da ni."
Ya yi maza ya ƙarashe maganar jin takun A.m daga matakalar bene.Kallon sa ta yi sai kuma ta
ji ya burge ta sosai yadda bai ɗauki rayuwar sa da zafi ba.
Ɗaga masa kanta ta yi alamun ta ji amma kuma a cikin zuciyarta sai ta ce.
" Ka makaro A.k da ce wa ka yi na yaƙi zuciyata da take son sa ƙila da na karɓi shawarar
,amma na riga na daɗe da shiga cikin kogin son sa."

Sai da A.m ya yi masa rakiya sannan ya dawo ya tsaya ya na kallon Juwairiya da ta kasa tashi
ta na ta tunani a ranta." Me hawayen banza maza ki tashi ki gyara min ɗakina saboda yau
haushina da kike ji sai kika huce akan ɗakin,sam gyaran bai yi kuma ki ƙara wanke bayi."
Ya faɗa tare da zama a falon kamar ya na son ta gama sai ya shigo.
Wucewa cikin ɗakin ta yi ba tare da ta ce masa komai ba amma ya faɗi son ransa ne kawai
duba ga yadda take ba da dukkan lokacin ta in ta je ɗakin sa gyara.

A.m ya na ganin ta shige ya bi ta tare da tura ƙofar a hankali ganin ya shigo ta tsaya dama tun
da ta shigo ta rasa mai za ta gyara saboda ɗakin ya na tsaftace da kyan sa.

" Ki zo mu kwanta a gadon da baki taɓa hawa ba amma albarkacin aurena zai saka ki din ga
moresa in matar so ba ta nan."

Hawaye suka wanke mata fuska ba ta ce mishi komai ba kuma ba ta motsa ba bare ya saka ran
za ta hawo,asalima gaban ta ne ya faɗi ras!

Hannunta ya jawo ya na faɗin." Na lura kuka shi ne farin cikin ki to ki sani ba zan taɓa buɗe
bakina rarrashe ki ba,ko na ɗauki hannuna na share miki hawaye da su.

Yanayin da suka shiga a ranar yanayi ne mara fasaltuwa da bayyanuwa a gare su musamman
Juwairiya da ta sha kuka har ta gode ma Allah,domin kwana ta yi ta na kuka ko kaɗan ba ta bar
shi ya rintsa ba,wanda in ta tuna dalilin kukan na ta biyu ne sai ta ƙara sakin wani kuka.

A.m da bacci ya fara ɗaukar sa a hankali bayan wata sabuwar duniya da ya shiga kuma ya
kasa fahimtar wace duniya yake ciki,kukan da take yi ya na ɗaga masa hankali ya yi maganar
duniya taƙi yin shiru,har ya gaji ya ƙyaleta ya rintse idanun sa da ƙarfi ya na son bacci ya ɗauke
sa. Ganin taƙi dai na kukan ya janye bargon da ya ƙudundune kan sa da shi ya kunna fitilar ɗakin."

Ke wai ke."

Sai kuma ya yi shiru daga ninyar faɗar da yake ya yi mata ya ɗan sausauta murya ganin dare
ne ya ce." Ko fa wace mace da kika gan ta a gidan mijinta da haka ta fara.Kuma idan bakya
son haka ba sai ki gaya min ki gode ma Allah auren kwangila muka yi so ba daɗe wa za ki yi da
ni ba."
Hakan sai ya saka Juwairiya ta ƙara fashewa da kuka ganin ta ba ma mutumim da ya tsane ta
rayuwarta,ga shi bai san mahimmancin ta ba bayan wahalar da ta sha yake gaya mata
waɗannan kalamai.

Bakinta ta murguɗa a ranta ta ce." Mugu kawai azzalimi."sai kuma ta ci gaba da kukanta wanda
A.m ya lura harda shagwaɓa don shi ya gama fahimtar ta shegen shagwaɓa ne da ita shi ya sa
da an yi magana sai kuka.

Wani irin walƙiya a ka saki lokaci guda aka fara tsawa nan ne A.m ya fahimci garin hadari ne ya
taso,da sauri ya sauka don ya duba ko windina a kulle ne kawai sai ya tsinci kan shi da jin daɗin
ya na yin garin har ya buɗe labule ya na shaƙar iskar gurin.

Iskar ya ƙara ma Juwairiya zazzaɓin da ta ji ya saukar mata ganin haka sai ya rufe windon ya

na addu'ar Allah ya sa ta yi shiru kenan,jin ta sassauta sautin kukan da take yi sai ya koma ya
zauna.

Wayar sa ta fara ruri da sauri ya ɗauka don gabansa ya faɗi ya na tunanin waye da daddare zai
kira shi,ganin numbar masoyiyar sa ya sa shi miƙewa da sauri take ɓacin rai ya bayyana a
fuskar sa.

A wannan lokacin da yake duba wayar sa aka tsuge da ruwa sosai kamar da bakin ƙwarya.
Zubbur ya miƙe ganin numbar Zainab ce ya yi kamar ba zai ɗauka ba,saboda tun da ya gaya
mata zai dawo ta de na ɗaukar wayar sa ashe mara mutuncin tafiya ta yi tabar ƙasar.Sai kuma
ya kanga wayara a kunnin cikin tsanani ɓacin rai a ransa ya na tunanin Allah kawai zai raba ta
da shi.
" Hello zauji don Allah gani a airport ka zo ka ɗauke ni kuma na samu ƴar matsala da kayana
har mutumim ya na min barazana.Ga kuma ruwa da ake yi kazo ka ji zauji."

Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi ya kalli Juwairiya da take cikin wani hali don shi kan sa ya
san ya wuce gona da iri,kuma ba tare da sanin haka ba ya kuma kalli kansa da har yanzu ya
kasa tantance duniyar da yake ci.


Tunani ya fara yi ko Zainab ta hauka ce ne da za ta dawo da tsakar dare sai ya ɗauki wayarsa
da nufin ya duba lokaci, ai wallahi ba zai fita yanzu ba sai dai koma mene ne ya faru
musamman da ta ɓata masa rai ta yi tafiya ba tare da izinin sa ba.

Tsananin mamaki ya kama sa da agogon wayar sa ya nuna mishi ƙarfe biyar da mintuna,ya na
cikin kokwanton ko wayar sa ce saitin ta ya goce sai ya ji ladani ya kwaɗa kiran sallah.

Da sauri ya yaye labulen ɗakin don ya ƙara tabbatar ma kansa take kuwa ya ga har hasken
alfijir ya keto gari ya fara wayewa..
Sai hankalin shi ya ƙara tashi musamamn da Zainab ta turo masa tsaƙon ba sai ya zo ba,don
sun
Anan na gama reposting na "SAKACINA KO HALIN MAZA". Duk wacce take son complete ɗin
sa an kammala littafin za ta iya siya a kan naira 600 ta wannan asusun bankin 08144072423
Jamila Lawal opay. Littafin an riga an kammala shi reposting na yi. Littafin "RANAR WANKA, BA
A ƁOYEN CIBI" Ya zama complete za a same shi a 600 ga mai buƙata sau ya tura ƙudinsa ya
sha karatu lafiya. Akwai kuma "KURA DA FATAR AKUYA 600

daidaita da mutumim yanzu haka ma suna hanyar gida,saboda mijin Anti Fati ya turo direba ya
ɗauke su kuma duka za suzo gidan.

Anan na gama reposting na SAKACINA KO HALIN MAZA. Duk wacce take son complete ɗin sa
an kammala littafin za ta iya siya a kan naira 600 ta wannan asusun bankin 08144072423

Jamila Lawal opay. Littafin an riga an kammala shi reposting na yi.


TO FA JUWAIRIYA GASKIYA NA TAUSAYA MIKI DA RANAR KI TA KASANCE A HAKA KOMAI
DAI MENENE ALLAH YA BAKI HAƘURI DA JURIYA.KUCI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN
SAKACINA KO HALIN MAZA

NAƘI YIN TYPING DA YAWA SABODA GASKIYA FANS BA KWA RUWAN COMMENT SAI DAI
KU YI TA BIYO NI TA PC KUNA FAƊIN ALLAH YA ƘARA FASAHA INA GODIYA AMMA NI NA
FI SON NA GA RUWAN COMMENT YA NA TASHI DON GAKA IN KUNA SON NAADIN GA
TYPING DA TSAWO KU DIN GA COMMENT.






TAKU

JAMILA LAWAL ZANGO


ƊUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ƊIN KU YA NA SAKA NI NISHAƊI.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login