Showing 36001 words to 39000 words out of 56747 words
Chapter 13 - SAKACINA KO HALIN MAZA Book Complete .pdf
manta da kamannin ta.
"Maza ku gaya min mai yake tafe daku da farko ina fatan ba laifi na yi ba kuka zo kama ni."Ya
faɗa kamar kuma ya ji tsoro a fuskar sa.
Hakan ya sa A.k ya murmusa shi ko A.m ko kallon sa bai yi ba.A.k ya gyara zama ya kalli Baba
Sani ya ma rasa yadda zai fara ya na son ya ce A.m ya faɗi buƙatar da ta kawo su,amma ya
san dunƙula maganar zai yi ta yadda ma ba zai fahimce shi ba ya lalata abin,bayan dai in ina da
ya yi,ya kuma shiga ƙumbiya-ƙumbiya daga ƙarshe ya faɗi abin da ya kawo su don barin kashi
a ciki baya maganin yunwa.
Alokacin da Baba Sani ya ji maganar da A.k ya faɗa sai ya ji kamar bai fahimci maganar ba
kuma har ga Allah a cikin zuciyar sa ya gasgata hakan da bai ji ba.
" Ikon Allah bayin Allah don Allah ka ƙara maganar wallahi ban ji me ka ce ba yadda ka san
ciwon kurumta ya kamani,a lokacin da ka yi maganar sake faɗi kamar yadda ka faɗa kuma da
Hausa don Allah ba turanci ba.
A.k ya so ya yi dariya jin ya ce ya yi magana da Hausa ƙila in ya ƙara maganar da larabci zai ce
ya yi mishi,A.m ya mai da wayar sa a aljihun rigar sa shi bai ga dalilin da A.k zai tsaya ya na
ɗan waken zagaye ba,ya san a ran shi irin abin da suka zo mishi da shi bai isa ya hana auren
Juwairah ba
" Auren Juwairiya kuka zo nema!" Ya maimaita hakan ya fi sau ba adadi daga bisani ya miƙe
zubbur ya na faɗin." Haba dama na yi tunanin a lokacin da na ganku irin yaran manya ne da
suke shaye-shaye su yi ɓatan kai su dami mutane,kun ga tunanina ya zama gaskiya ga ku
kamar mutanen kirki ta waje amma ta ciki ba hali."
Ya numfasa sannan ya ci gaba da cewa ba tare da ya ba su ikon koda jan numfashi ba." Wallahi
na ɗauka wani abin ya kawo ku ko ba sa rana akan Juwairiya a bazan taɓa yadda ta auri wani
daga cikin ku ba,bare na ba da Juwairiya yanzu haka bikinta saura sati ɗaya don haka ku wuce
ki bani guri ƴan ƙwaya kawai."
A.m ya harzuƙo ya na faɗin." Wa kake ce ma ƴan ƙwaya kai ne mugun ɗan ƙwaya da ka kasa
gane mutanen kirki da na banza,ba giya muke sha ko kuma kamfanin ƙwayar muke haɗiya."
"A.m ya kamata ka saukar da fushin ka kasan me muka zo nema."
A.k ya ce mishi tare da kama shi ya zaunar ya na dafa kirjin sa.
" A'a ka barshi ya yi min rashin kunya ya biyo ni har gida zai gaya min magana,a ɗakina fa
kake.To bari kaji ko mutuwa za kai sai dai ka mutu, kai ko maka mutu ne aka fito da kai a
ƙabari,a ka ce na baka auren Juwairiya numfashin ka zai dawo wallahi sai dai a turbuɗaka a
cikin ƙasa ta rufe maka ido." " Wai tsaya kun ma san me kuka zo min da shi?Juwairiya da na tsana a rayuwata shi ne zaka
kazo ka na da kuɗi ka aura taɓ wallahi ina."
Da aka kai wannan gabar sai A.m bai ce komai ba ya rintse idanun shi kawai don aikin A.k
ne.Amma sai ya ji A k ya yi shiru ya na kallon Baba Sani da yake faɗin ƙiri-ƙiri ba ya son ƴar
wansa ta ƙaru,kai wannan wane irin mutum ne an ya a kwai zumunci a duniya saboda son
duniya ko ya ce son kai,mutane sun manta zumunci bayan Allah ya gaya mana zamu tsallaka
siraɗi mara zumunci ba zai sha ba.
A.m ya buɗe baki zai yi magana ganin A.k yaƙi magana dai-dai lokacin da Baba Sani ya
sausauta murya ko me tuna ya sa ya yi sanyi ya ce." To kai in ban da ku me za ku yi da mace
irin Juwairiya yarinyar da ta gama zagaye duniya ta na yawon aikatau kuma duk mazan gidan
sun san ta,sam ba ta da hali mahaifiyarta ta koya mata bin maza har sata take yi ka tambaya
har kulle ta a ka yi a prison."
Ya ƙara sausauta murya ya matsa kusa da A.k don ya fi A.m sauƙi ya fara magana kamar zai yi
mishi raɗa amma A.m ya na jin me yake faɗi." Ina da yara sun yi karatu na boko in kuma so
Juwairiya ba ta san komai ba har talla yi take yi,ai da ka aure ta gara na yi maka fatan ka mutu
ba aure.
" Juwairah nake so kuma zan aureta ko da ace duk mazan duniya sun san ta a matsayin ƴa
mace."A.m ya ce ransa a ɓace.
" To ba zan ba da ba kuma kamar maganar ta ita matar wani ne na rantse,a yau zan ɗaura mata
aure ba sai an jima ba don ina zargin ku za ku iya sace ta.To ni sai in ce kamar an yi maka baki
kamar ka mai zai saka ka auri Juwairiya uban ta har ya mutu faskare yake yi, a gurin faskaren
ya sara ma kansa ya mutu shi ne za ka ce ka na sonta.
" Nima ba son ta nake ba ban taɓa jin ina son wata ƴa mace bayan matata ba,kai ma in ka furta
ina sonta ka yaudari kan ka don duk faɗin unguwarku ban ga macen da zan ji ina son ta ba."
Kawai sai ya yi galala ya na kallon shi a ransa tunani yake to uban me zai yi da ita,koma dai
mene ne ba za ba shi ba in ma ya na son ya yaudare shi ne ya ba shi aurenta,yadda ya rantse
Juwariya ba ta ba jin daɗi a duniya tun da ta kange kwaɗinsa a kan ta gara ya ba ma wannan
tsohon ya wulaƙanta rayuwar ta.
" Ku faɗi ko me za ku ce ni ba yaro ba ne kuma ba zan baku auren ta ba yanzu ma zan ɗaura
mata aure don haka ku cire wanann tunanin."
A.k ya karkace ya zaro makullin mota ya ije masa a gaban sa sannan ya janyo cek da ga aljihun
sa ya ije na kimanin miliyan biyar.
Wayyo Allah zo ka ga ido sai ya zare ido can kuma ya fara mitsinan kansa ya gane ko mafarki
yake." Ka bar cutar da kanka ta hanyar mintsnin kanka ba mafarki ba ne a zahirin gaskiya
lamarin ke faruwa,in har ka bamu haɗin kai har gida zan canza maka rayuwar ka ta dawo
sabuwa in har zaka ba ni auren ta."
A.m ya ce da shi ya na kallon sa yadda ya ruɗe kamar zai zare." Ikon Allah don Allah in mafarki
nake ku dake ni sai na farka wai ni ne zaku ba wannan kuɗin don ku auri Juwairiya an ya ku ba
ƴan cin kai ba ne?"
Ya faɗa ya na ƙarewa A.m kallo tunanin sa shi ne babba a wurin cin kai saboda ya fi A.k jiki da
faɗi."Ko ma duniya muke ci ba ruwan ka in mun cinye ta tunna ba ƙaunarta kake ba."
A.k ya ba shi amsa amma kuma sai A.m ya kalle shi ya ce.
"Ka daina danganta mu da wannan mu mutane ƙwarai ne kawai fatanmu ka amince da
buƙatarmu."
Ga mamakin su sai suka ga ya tattara kuɗin ya saka a aljihun wandon sa har da makullin motar
ya fara zare ido. " Duk da cewar na tsane ki saboda wani ƙudiri na wa ba na fatar in da za ya
huta ta ji daɗin aure,amma ba zan bari wannan damar ta wuce ni ba Juwairiya sai dai wallahi
ina tsananin baƙin cikin faruwar lamarin da na ɗaya daga cikin ƴata kuka nema Allah bari na
kira ta sai dai Juwairiya ta nuna mata kyawun halitta amma ta na da hali."
Miƙewa ya yi sai A.k ya kamo hannunsa ya zaunar da shi." Ka barshi ba buƙata ita dai
Juwairiyar ya gani yake son ya aura na wucin gadi,shekara ɗaya tak za ta yi zai rabu da ita don
a cikin sirri za' a ɗaura auren."
Ya ɗan kalle su a fakaice ya tabbatar da gaske suke yi ko fim suke son shirya wa suka yaudare
shi haka." Tabbas haka maganar abokina yake ni zan aureta na shekara ɗaya matata ce ba ta
haihuwa,shi ne nake son ka aura min ita bayan ta haihu zan ɗauke ɗana na sake ta ita ma zan
biya ta kamar yadda da na yi maka."
Wani irin daɗi ya cika mishi rai ya kama hannun A k ya riƙe ya na faɗin." Kasan Allah ko auren
kwana ɗaya kake son yi da ita zan baka, kai duk abin da za ka yi da rayuwar ta ba nida matsala
in har za ka bani kuɗi sai dai da sharaɗin komai ya din ga biyo wa ta hannuna."
" Wannan kuma ba zai yiwu ba za mu baka duk jin daɗi na rayuwa,amma Juwairiya na cikin
wani hali a yanzu ina da labarin mahaifiyarta da ba lafiya kuma za 'ayi mata aikin zuciya kaƙi ka
taimaka,ga ƙaninta da yake da matsala tun mahaifinta na raye yake da burin a yi mishi aiki don
haka zamu fitar da shi da mahaifiyarta,ita ma mu saya mata gida,sannan ba su da cin yau bare
na gobe ka ga ya dole mu inganta rayuwarta wanda da shi zamu ci ƙarfin ta har ta amince da
auren."
Baba Sani take ya haɗe rai jin baza a ba shi na Juwairiya ba da ya rantse ba zai ba ta da yawa
ba,amma sai ya ɗan saki fuska ya na ce wa." Ni ma ki yi min uzuri ba ni da shi ne da na taimaka
mata,wannan aikin wahala kawai nake yi ai nima abin a taimaka min ne."
A.k tsaya wa ya yi ya na mamakin sa ya sani ce wa a kwai mutane masu son kuɗi amma
wannan ya wuce tunanin sa an ya na da imani kuwa.
Yauwa a matsayin ƴar aikin gidana za ta zo wanda za ka gaya ma mahaifiyarta za ta aiki na
tsawon shekara ɗaya ta koya wa matata girki,wanann dalilin ya sa na ingamta rayuwar ta
haka."Ba ka da matsala in ma a matsayi ƴar gadi za ta zo ai wallahi sai an yi auren,na san
yadda zan yi da su duka hatta mahaifiyar ta tunna ka ba ni kuɗi ba ka da matsala.
Yace ya na tare da zaro makullin motar ya kalla sai kuma ya maza ya mayar lokacin da A.m ya
miƙe a tunanin sa ƙwacewa zai yi don ya ga ba shi da kirkin ɗaya.
" Oh Juwairiya ban sani ba a she ke jarina ne mahaifin ki ya mutu ya bar min dukiya nima na yi
kuɗi!Ai wallahi ƴan mata biyu zan gallo a rana ɗaya wayyo Allah!Ashe dama zan yi kuɗi Wallahi
mutane za su ga rashin mutunci ehe."
" Yauwa ina motata kuma a ina gidan yake sannan kamar yadda ba ka son matar ka ta sani
haka iyayenka kenan ni ne waliyin ku duka ba matsala in ma ka na son a ɗaura yanzu ba
matsala."
Tsabar takaici ya sa A k yaƙi ce wa komai don ya fahimci jahili ne ku kuma son kuɗin ne ya rufe
mishi ido yake faɗin ya zama waliyin su duka,sai shi ma ya miƙe ba tare da ya ce mishi komai
ba A.m ne ya miƙa mishi takadda ya ce ga shi duk abin da kake son ka sani ya na ciki.
Zai fita A.k ya kalle shi ya ce " Ai ya kama ta a kira Juwairiya mu gaya mata ko in ce ka yi mata
bayani ka san waƙa a bakin me ita tafi daɗi."
A.k ya ce mishi cikin gatsali shi har ya fara jin kunyar ta tun kafin ta fito haka kawai daga
haɗuwa sau ɗaya sai su zo mata da wanann tatsuniyar.
" Baku da matsalar ga ya mata ita ɗin banza ai gaba ta kai ta."Ya ɗan matso ya na cewa." Dama
wannan ɗan iskar tsohon ba ya bani wasu kuɗin kirki yau zan mayar mishi da kayan tsiyar
shi,ana harkar kuɗi me za' ayi da tsiya ai ni mutuwar mahaifin ki gaba ta kai ni gobarar Titi a
Jos."
" Ga ra dai ka kira ta shi ya sanar mata."A.k ya ce shi dai A.m bai ce komai ba sai dai ya ji wani
iri lokacin da Baba Sani ya fita daga ɗakin ya na faɗin bari na dubo ta shegen yawo ne da ita ai
kai da zama za ka yi da ita sai ince baka dace mata ba."
Juwairiya ta na duƙune a murhun gawayi ta hira wutan yafi sau ba adadi amma da ta hura sai
ya mutu muɗis,kusan kuka take son ta yi don har ta fara hawaye ganin wutar ta taƙi kamawa ta
miƙe tsaye tare da zura mata ido,ji take kamar ta ɗora hannu aka ta yi ta ihu.
Ta takaici ta kalli ledar taliyar da take son ta dafa ma Mama ba ta jima da dawowa daga asibiti
ba take son ta ɗora musu abinci da ruwan zafi ta kai musu.
Kawai sai ta ki muryar Baba Sani ya na magana tare da ƙoƙarin shigowa duk da ba ta ji me
yake faɗi ba,amma ta tsorata matuƙa gani take kamar zai ce ta dafa taliyar ya ɗaura aurenta.
" Juwairiya ina kike ashe dama ke jarina ne?Oh ikon Allah dare ɗaya Allah kan yi bature."Oya
maza biyo ni kika abin mamaki aike kin samo mana can jin rayuwa Juwairiya yarinya ɗiyar
albarka."
Cikin rashin hayyaci ta tsaya ta na kallon shi sam taka sa fahimtar wai yau Baba Sani yake ce
mata ƴar albarka,sai ta fara shakkun ko ya zare ne jikinta ya fara rawa ta matsa nesa da shi,ta
na karanto duk addu'ar da ta fito bakinta.
" Ke ban san hauka maza wuce kina da baƙi a falona kuma wallahi in kai min hauka,zan iya
ajalin ki kin san bani da wasa akan kuɗi gara ma ki kiyaye!Maza wuce."
Da sauri ta ruga zuwa shashinsa jikinta na kyarma haka kawai jikinta ya ba ta Alhaji Taminu ne
ya zo,sai ta rintse idanunta ba ta son ganin shi a haka ta faɗa ɗakin tare da sallama wanda na
yi tsammanin a zuciya ta yi,don ko ita kanta ba na tunanin ta ji.
Tsayawa ta yi a ɗakin ta kasa buɗe idanunta sam ba ta son ganin fuskar sa mai kama da biri.
Wani ƙamshi wanda ta shaƙe shi a rayuwarta wanda ba za ta taɓa manta mamallakin ƙamshin,
ba har iya tsawon rayuwarta,tun daga ranar da ta shaƙe shi take jin ƙamshin a jikinta har zuwa
yau da ta haƙiƙance ma kanta lai-lai wannan mamallakin ƙamshin,mai sanyaya zuciya da kawo
nishaɗi ga duk wanda ya shaƙesa ya na kusa da ita,musamman da ta ji sautin da zuciyarta take
ta na bugawa da ƙarfi kamar za ta fito fat!Fat!!Har sai da ta dafe gurin.
A hankali ta sauke idanunta da suka kaɗa sukai jajur saboda wahalar hura wuta da tasha,duk
da taji an kira sunan ta wanda ta gane ba muryar sa ba ne saboda ko tari ya yi za ta gane
muryarsa,amma sai ta tsinci kanta da ɗora idanunta a kansa yayin da idanunnata sukai rau-rau
sun canza kala suna ba da wani tarwatsi a cikin su.
A.m da ya ji shigowar ta duk da ba ta yi sallama ba amma ya ji an buɗe kofa an shigo,sanann
kiran sunan ta da A.k ya yi sai ya kasa ɗaga idanunsa ya kalleta,duk da ya na son ya kalli
wacce yake so ta zamo ɗa ga abu ɗaya tal mafi soyuwa a gareshi don ko sun rabu aba' a sake
ma tuwo suna.
"Ya ilahi! Allah na roƙe ka ka farkar da ni daga mafarkinsa da nake,kuma wanann ya zama na
ƙarshe tunna na kusa zama matar wani."Ta faɗa aranta ta na ƙoƙarin mai da hawayen da suke
son bayyana ɓoyayyaen lamarin da ke cikin zuciyarta.
" Juwairiya ki zauna mana."
A.k ya ce ganin hankalinta ya tafi wani gurin ga mamakinsa sai ya ga ta nemi ƙasa ta zauna
tare da saukar da kanta ƙasa.
Gaishe su take son yi amma ji take kamar babu harshenta a cikin bakinta ta ƙara buɗe bakinta
amma ta kasa.
Ganin sun yi shiru duka sai ta ƙara ƙasa da kanta ta na kallon kafen ɗin dake ɗakin tamkar ta na
son ta gano ko an maguɗi gurin yin sa.
A.k ya miƙe ya kalli A.m da yake ta danna wayarsa amma a zahirin gaskiya bai san me yake
dannawa ba, tunanin sa ta ina zai fara kuma ta fahimce shi,shirun da ya yi ya na son ko A.k zai
yi mata bayani amma sai ya ga ya miƙe.
" Bari in jira ka a mota in kun gama tautaunawar ina mota."
Ya fice ya na girmama lamarin da suka zo da shi. " Juwairaah! Babu gaisuwa wataƙila kin
manta ni ko."Ya faɗa don rashin sanin ta in da zai fara.
Ta ɗago idanunta ta zuba mishi amma ba ta ce mishi komai ba,sai dai a ranta ta ce." Ta ya ya
za'ai na manta da kai bayan ka tafi da zuciya da ruhu gangar jikina kawai ka barmin,amma to
mai ya