Showing 24001 words to 27000 words out of 56747 words

Chapter 9 - SAKACINA KO HALIN MAZA Book Complete .pdf

san duk ranar fa ta
gaya mata ƙudirin sa akan ta, ƙila zuciyarta za ta buga domin abin ya yi muni.

Tun daga wannan ranar ba ta ƙara gani Mas'ud ba ko wayar da ya siya mata Mama ƙwacewa ta
yi ta ije,don a yadda ta ga take-taken ta za ta iya kiran shi kuma shi ma haka.Tun ta na saka ran
ze dawo har ta cire sai dai ta wahala kafin ta cire son shi a ran ta,sannan da ga baya taci gaba
da al'amuranta.
Mariya ta sami miji za ta yi aure anan kusa da layin su za ta yi auren don haka su Juwairiya su
ne ƴan mata.Su Juwairiya an sha gayu da lalli an yi kyau sosa,ana ta hidimar biki don ba zama
an saci ɗan ɓarawo.
Zaune suke ana hirar ƴan mata Juwairiya ta kalli Mariya yadda ta sha kyau yace."Su amarsu kin
ganki kuwa,dama komai munin amarya ranar bikinta sai ta haska."

Fari ta yi musu ta na dariya tace." Ku zauna kuna rungume filo ni dai Allah ya hutashshe ni na
shige daga ciki,ku tsaya kuna ruwan ida kwayi kwantai."
Wani irin dundu Juwairiya ta duma mata ta nafaɗin." Ji min ƴar baƙin fata wato fatan da kike
mana kenan tunna kin shige daga ciki ko? To in sha Allah muna bayan ki."Sauran ƴan matan
suka taso mata ita dai Mariya dariya take musu,sannan tace." Ai ke Juwairiya Baba Sani ya
hana ki aure da tuni kin haihu ma.Amma ba komai Allah ya na tare dake lokacin ki ne kawai ba
yi ba."
Shiru ta yi sai hawaye yayin da mutanen ɗakin suke ta ba ta baki.
A haka suka sha bikin Mariya aka kaita ɗakin ganin Juwairiya za ta tafi ta kama ta tare da saka
kuka.Sai kuma ta ba Juwairiya tausayi ta rungumeta ta na share mata hawaye.

Mariya ta share hawaye tace." Maganar da mukai dake akan aikin nan kije Allah za kiji daɗi kin
ga ni na yi aiki da su."Juwairiya tace." Ke ni raba ni da aikin nan don na yisu amma ban ji da
daɗi ba."
" Allah ki gwada wannan kin ga yanayin halin da kuke ciki,ga shan maganin Mama dole kina
buƙatar kuɗi."
" To zan shawarci Mama duk abin da tace sai na je."Da wannan Juwairiya ta tafi gida cike
da kewar ƙawarta wacce ta temaka mata.

Koda ta yi ma Mama magana shiru ta yi zuwa can tace." An ya zan barki kiyi aikin nan nifa tsoro
nake yi kina ganin rashin mutuncin da Hajiya Binta ta yi miki,amma tuna kin ce Mariya tace ta
na da mutunci sai ki je Allah ya tsare ki."

Numfashi ta saki tace." To bari na gwada mu gani."

Juwairiya ta fara aikin cikin jin daɗi ga karatu da take samu ake yi wa yaran lesson da islamiya
matar ma ba ruwanta.

Watan ta biyu a gidan ranar ta kammal aikin ta za ta tafi matar tace." Don Allah Juwairiya ki

tsaya zamu je gidan biki ni da yarana,zuwa yamma zamu dawo sai ki tafi in kuma na yi dare zan
kaiki a mota."

Duk a ranta ba ta so ba amma sai ta amsa da." To." Ta koma ta zauna yayin da ita kuma ta
shirya da yaranta suka fita.

Tun da suka tafi har aka kira sallah ba ta dawo ba,ranta ya fara ɓaci don ba ta son ta yi dare kar
Baba Sani ya dawo ya kuma ƙara mata wani sharrin.

Jin ƙarar mota sai ta yi maza ta leƙa ta windo ta na tunanin ita ce,sai dai cikin takaici ta koma ta
zauna ganin mijinta ne ya dawo.
Ya shigo da sallama ya amsa ya na kallonta." Juwairiya har yanzu ba ki tafi ba?"Ya tambayeta
ya na kallonta." Eh tunna ka dawo bari na tafi "
" No ki kira ta nima ƙara fita zan yi."
Don takaici ko amsa mishi ba ta yi ba to me ya dawo da shi koma wa ta yi ta zauna.

Ya shiga cikin ɗakin sa mintina biyar ya fito sai kawai Juwairiya taga ya yi kanta gadan-gadan!
Da sauri ta miƙe tare da saka salati dai-dai lokacin da ya fisgota ya haɗa ta da jikin sa da ƙarfi.

Kasancewar shi namiji me jiki da ƙarfi ya yi nasarar kayar da ita ƙasa tare da yi mata
rumfa,yayin da dabbe ya kaure ko kaɗan ba ta yi tsammanin ya na da wannan halin ba.Kuka ta
saka ta na rokon shi,amma bai kula ta ba yaci gaba da ƙoƙarin ida nufin shi.

" Inna lillahi Faruk!Me zan gani dama amanata kuke ci?"Ta furta cikin ƙaraji! yayin da ta yo kan
juwairiya ta hau ta da bugu.

Juwairiya ta yi kuka ta yi ihu ji take kamar numfashinta zai fita domin kanta ta hau ga ta da
ƙiba,da ƙyar ya samu ya ɓamɓare Juwairiya ta samu ta gudu.

Da ƙyar ta samu ta isa gida ta na kuka a ranar ta rantse ba za ta ƙara yin aiki ba,ko da mutuwa
za su yi yadda ta shigo Mama ta tsorata.

Bayan ta yi mata bayani tana kuka Mama sai da ta zubar mata da hawaye ganin halin da take
ciki.A ƙalla sai da ta yi sati ta na jinyar jikinta don har sai da ta kwanta ciwo.

Haka rayuwa take tafiya musu yau baƙi gobe tsummma ga ciwon Mama ya yi tsanani.Wani abin
ƙarin tashin hankali Ibrahim da dama can ba lafiyayye bane,saboda sikila ne shi jikin sa da ya yi
sauki amma a cikin kwana biyun nan jikin ya tashi.

Ciwon shi sai yake son ya danne na Mama amma duk wanda ya ganta ya san ta na cikin
tsananin ciwo.Ga kuma Baba Sani da ya sanar da Juwairiya ya yi mata miji wato Alhaji Tanimu.

A ranar da Baba Sani ya gaya mata sumewa ƙau ta yi don ya tabbata Baba Sani ba ya

ƙaunarta,don ita da ya aura mata shi gara ta zauna ba aure ko ace mutuwa ta yi.

Waye a faɗin garin be san Alhaji Tanimu ba wanda ya mai da mace tamkar rigar sawan
shi.Mutum ne mara addini ga shi kamar wani hor.Kusan duk shekara yake sakin mace ya ƙara
aure bayan ya tabbatar sun sami ciki,don baya son haihuwa a tunanin ta shi kan shi be san iya
yawan yaran shi ba,duk da wasu ya na ba ma iyayensu mata kyauta wasu kuma ya kai su
almajiranci.

Sannan an sha kama shi ƴara ƙanana ya na musu ya lalata musu rayuwa irin mutumin da Baba
Sani yake son ya zama mijinta kenan.Ai Juwairiya ƙaramin hauka ta yi don gara yace ta shiga
duniya.

Shiko Alhaji Tanimu se ɗinkirama Baba Sani kuɗi yake yi hankalinsa kwance ganin zai mallaki
wannnan zuƙeƙiyar,shi ya sa be damu ba ko sanda ya zo zance taƙi fitowa tallar ta fa aka kawo
mishi har gida.

Rayuwa a wannan karan tafi yi wa su Juwairiya illah ga aba abinci sannan dukkanin su ba
lafiya,ga Baba Sani da yake ta shirye-shiryen bikin ta don har an kawo kayan sa rana watan
gobe biki.

Mama ta shiga tashin hankalin ciwonta ya ninku ga yunwa har takai sai su wuni ba su saka
komai a bakin su ba.
Juwairiya ta tsara ma kanta ta gudu amma in ta ga halin da su Mama suke ciki sai ta ji kamar ta
kashe kanta ta huta,ita kanta ba lafiya take da shi ba don ta na ganin har tafi su Mama jigatuwa
saboda zuciyarta da take ji kamar za ta fashe.

Ganin yunwa zai kashe su sannan duk kuɗin da Baba Sani yake karɓa bai ta ba ba su koda na
sabulu ba,ta je gurin Mariya ta ara mata naira dubu biyu ta fara jarin gyada.Da wannan suke
samun abinci.

*******
Zaune yake cikin damuwa sai kuma ya miƙe don a yau jin sa yake duk shawarar da amininsa ya
ba shi zai iya ɗauka saboda halin da yake ciki.Makullin motar shi ya ɗauka ya nufi gidan A.k.
Sai dai cikin rashin sa'a ba ya nan don haka bayan sun gaisa ya fice daga gidan ya samu wani
guri mara hayaniya ya tsaya,tare da ciro waya ya kira A.k.

Ba'a fi minti goma ba sai ga A.k akan mashin ya sauka ya buɗe gaban motar ya shiga ya na
share zufa."Am sorry aboki motar da ka siya min na kai ta service ba'a gama ba kan dole na
baro motar na hawo mashin.Are you under the weather?"Ya tambayi aminnin nasa ganin
yanayin sa.
Yace ya na kallonsa bai tanka ba illa ajiyar zuciya da ya yi ya kauda kansa gefe guda,ganin
yadda aminin na sa yake ya san yauma ba lafiya to ko dame yazo oho don ya san dai zancen.

Suka ɗan yi shiru ba tare sun ce uffan ba na tsawon lokaci sannan A.k ya katse shirun da
cewa." Lafiya na gan ka wani iri in ce ba mutuniyar bace ta haɗa maka zafi."

"Akan maganar da na nemi shawarar ka yau ma na ƙara bijiro maka da ita.I really need your
advise pleese help me out."A.k ya kalle shi yadda idanunsa suka kaɗa suk yi ja ga mamakin sa
sai ya ga hawaye ya na sauka da ga ƙuncinsa.
Ya kama hannunsa ya haɗa da nasa ya riƙe sosai ya na kallonsa ya ci ga ba da cewa."I know
my wife she is a woman of raging jealousy.Bazan iya haɗa ta da wata mace ba kuma ba yan
haka na yi mata alƙawari,amma ina jin zafin rashin yaro da ba ni da shi wanda hakan in ban
ɗauki mataki ba zai iya taɓa lafiya ta,domin a yanzu ya kai matsayin da ba na iya bacci.
Tun da ya fara magana A.m ya yi shiru ya na kallon sa a ransa tunani yake to ko amininasa ya
ci kai ne ko kuma rashin haihuwar ya taɓa tunanin sa, kamar yadda yace shi dai ya san ta aure
ake samun haihuwa ya ba, shi shawara yaƙi bi saboda wani alƙawari na shi na banza to amma
bari ya ji me yake tafe da shi.
Ganin ya yi shiru ya dafa kafaɗarsa ya na cewa."Try to be patient ka san zuriya kake buƙata
kuma dole a aure za ka same shi,ba zaka so ka sami ɗanka ta zina ba wanda na san ba halinka
bane,amma ni banga dalilin da zai sa kaƙi ƙara aure ba bai ita ta ɓata mahaifinta da kanta
ba?"Ya ɗan faɗa da zafi kuma da tsigar tambaya. " Haka ne." Ya ba shi amsa sannan ya ci gaba da cewa." Duk akai na ne ta samu wannan
matsalar gaskiya i can't make up my mind ko zan iya cin amanarta."

Ƙarin takaici maganganunsa suka ƙara ba shi gani yake ba shi da tsayuwa a gidan sa,amma shi
bai ga yadda matar shi zai ta da hankalin shi ba,don kawai zai ƙara aure kuma duk laifin tane.
Ya kaɗa kafaɗunsa yace."It is up to you ni dai na gama baka shawara."Yace amma sai kuma ya
ga hankalin aminin nasa ba shi a gurinsa wataƙila ma be san me yace ba.

A hankali ya bi gurin da yake kallo shima Juwairiya ce da tiren gyaɗa a kanta da ga ganinta ka
san ta na cikin wani hali, kusan ma ta na tafe ta na share hawaye saboda har Alhaji Tanimu ya
kawo kayan auren ta na jin gara ta haƙura ta aure shi,wataƙila shi Allah ya tsara ya zamo
mijinta ta san bawa ba ya wuce abin da Allah ya tsara mata,sai dai yanayin halin da Mama da
Ibrahim suke ciki ya sa ta zagaya wa da gyaɗar da yau ba ciniki ta haɗa da kuɗin da Mariya ta
ba ta ta kai su asibiti.

A.m da ya zuba mata ido ya na kallonta bai taɓa ganin mace me sanyi da wani irin shauki a tare
da ita ba sau,haka kawai ya ji ta kwanta mishi a rai ba wai son ya na son ta ba irin zai iya
magana da ita har ya ba ta lokaci su yi wasa da dariya,kuma ya nemi shawarar ta kuma zai iya
yin komai don ta yi farin ciki,zai iya cewa yau ne rana ta farko da ya ga wata mace bayan
Zainab har ya na jin zai iya mata magana.

Wato in ya fahimci zuciyar shi ƙawa yake son ya mai da ita ko ƙanwa." To amma duk tsanar
talaka da na yi sai ace na yi ƙawa da ƴar talaka kuma ƙasƙantacciya ƴar talla kai an ya da

wuya.".
Yace a zuciyar a cikin zuciyarsa ya na me ƙoƙarin kauda idanun sa daga gareta don jin hakan
bai dace ba ace duk matsayin shi.Sai-dai idanunsa sun kasa ɗauke kan su daga kallonta ya na
ƙara zaƙulo kyawunta.

Ta na tafe cike da damuwa har tazo ta gaban su za ta wuce." Me gyaɗa." Kalmar da bakinsa ya
furta ba tare da ya ba shi umurni ko tunanin hakan ba.

Juwairiya ta ji wani irin sansanyar murya mai kama da sarewa ta kira ta ta na son ta juya amma
sai ta daƙile kanta da juyawar,don ƙila in ta ga mamallakin wannan muryar ba ta san halin da za
ta shiga ba sai kawai ta ci gaba da tafiya yayin da aranta take addu'ar Allah ya sa karya ƙara
kiranta, don ta san in ya ƙara kiran ta ba za ta iya tursasa zuciyar ta da ƙin juyawa ba. A.m ransa ya matuƙar ɓaci ƙazama da ita ta na talaka zai kira ta taƙi waigowa ya so yaje ya yi
watsi da kayan tallar,ya ga uban wa take taƙama da shi taƙi amsa kiransa amma da ya yi
tunanin ko kurma ce sai ƙara kiran ta a karo na biyu.
Cak! ta tsaya amma ba ta wai go ba ta na addu'a a cikin ranta yayin da idanuwanta suka zaƙu
da suga wannan mamallakin muryar.A hankali ta tako ta iso gun motar su ta tsaya ta kasa
magana kuma ta kasa ɗaga ido ta kalle shi.
Kusan minti goma ta na tsaye ba tare da ya kalleta ba me ya gani oho ganin ita ma ba ta da
ninyar ta yi mishi magana kuma ba ta tafi ba A.k dai ya na zaune ya na kallon ikon Allah.

A.m ya buɗe motar da nufin ya yi mata wulaƙanci dai-dai lokacin da idanuwan su suka tsarƙe da
na juna.
Kyansa yanayin jikinsa idanuwansa da yadda yake kallonta suka ruɗa ta ta yi kamar za ta faɗi,
amma sai ta dafa jikin motar sa ta na kallon shi cikin wani irin shauki,lokaci guda ta ji abu me
kama da guduma ya sauka akanta! Yayin da wani irin shokin na soyaryarsa suka dinga ɗana
mata son shi a cikin ranta,har ta ji za ta iya mutuwa in ba ta same shi ba.
Idanun su da suka tsarƙe da juna sai ya tsinci kansa da kasa mata rashin mutuncin da ya yi
ninya a yatsine yace."Nawa-nawa gyaɗar."
Ta zuba mishi idanunta sai kuma ta janye ta lumshe su tare da kauda ganin ta gare shi ahankali
da sanyaryar murya tace.Hamsin gwagwani ɗaya."
Ya ɗan ƙura mata ido haka kawai kyawunta da muryarta yake ruɗan shi a kanta."Duka buhun
nake so nawa."Yace tare da barin kallonta lokacin da ta ɗora idanunta akan sa.
Zare ido ta yi " kwai yawa fa kusan na dubu uku da ɗari biyar ne.Tace mishi hakan sai ya burge
shi ya tsinci kansa da yin murmushi.
"Ok bari in ci Allah ya sa da daɗi."Da sauri ta saka hannunta da baya rabo da lalli ta miƙa
mishi ta na faɗin." A kwai daɗi kaci kaji."
Yabi hannunta da kallo ya karɓi gyaɗar ya ɓare tare da taunawa,lumshe idanunsa ya yi yace da
ita."Gaskiya a kwai daɗi zuba min a leda sauran kiyi sadaka da shi."
Da sauri ta zuba mishi sannan ta kalli gefen A k da ya yi mutuwar zaune saboda tun tarihin
rayuwarsa da A.m yau ce rana ta farko da ya siyi abu a gurin masu talla,sai ya yi lakato ya na
kallon A.m da ke cin gyaɗa har ya na faɗin ta ƙara mishi ya yi daɗi.

" Yayana kai fa ba ya cine."Ta kalle shi sai kuma ta mai da maganar da tsigar tambaya ta na
kallon A.m,kaɗa kafaɗunsa ya yi ya na kallon shi ya ma manta da shi yace."Ba ya ci."
Juwairiya tace " Ka tambaye shi ne?"Sai kuma ta kalli A.k tace."Wai haka Yayana?"
"Yes Am ok."Yace da ita ya na kallonta.
Zuba gyaɗar ta yi ta miƙa mishi ta na faɗin."Kaci a kwai daɗi."Ya ƙarɓa tare da faɗin."Thanks
sis."
A.m ya zaro kuɗi da yawa ya miƙa mata. Gashi sis ki cire kuɗin ki sauran ki ƙara jari."Zare kuɗin
ta ta yi tace."Siyan da ka yi na gode."
Hakan sa ya yi matuƙar birge shi ya na ta kallonta har ta yi nisa ya leƙo ta cikin murfin motar
yace." Manene sunan ki."
Ya ɗan ɗaga muryarsa yadda za ta ji don ta yi nisa,waigowa ta yi ta kalle shi tare da sakar masa
murmushi ta tabbata wannan kyakykywa gayen ya yi mata sata mafi girman abu a
rayuwarta,wanda ta san ba zai dawo mata da shi ba kawai za ta ci gaba da renon giɓin rashin
abin da ya ɗauke mata har iya tsawon rayuwarta! " Sunana Juwairiya Ahmad."Tace tare da ƙoƙarin ɓullewa a ranta ba ta son ta ƙara haɗuwa da
shi don ta san babban goro sai magogin ƙarfe.
A hankali ya kwantar da kan shi akan jikin kujerar da ya saukar da kansa ya na murmushi ya
furta.Juwairaaah! Da wata irin murya ya ja sunan ya yi mishi wasali sosai." Ta na da kyau haka
kawai sai na ji ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login