Showing 21001 words to 24000 words out of 56747 words
Chapter 8 - SAKACINA KO HALIN MAZA Book Complete .pdf
ce kan shi ya ɗau zafi,shi dai ya san koma mene ne ba zai karya alƙawarin da
ya yi mata ba.
Bayan sun fito ya kalli matar A.k da take tattara gurin da yara suka ci abinci ya na dariya."To ni
madan zan wuce."Dariya ita ma ta yi "Wato an gama gulmar mu ko ba komai nima ina nan
zuwa gidana musha namu."
A.m ya ƙara dariya yana cewa."Baku da dama ne shi yasa musamman mutuniyar ki.A.k ya ja
hannun shi ya na faɗin.Muje ka ji in ka biye mata sai ta ɓata maka lokaci da surutun ta suka
fice.
******
Juwairiya ta ƙara samun aiki a gidan wata mata mai suna Hajiya Binta,matar ta na da kirki
matuƙar gaske yaranta bakwai.Kusan dukkan aikin gidan Juwairiya take yi,saboda yawan
yaranta take wahala a gidan sai dai amma babu laifi suna ƙaruwa da ita.Matsalar ta ɗaya
mafaɗaciya ce sam ba ta da haƙuri kamar zawo take,duk yadda take taka tsan-tsan amma sai
ta rori abin da za ta yi mata faɗa.
Saboda ba ta saba da irin aikin ba sai yake ba ta wahala ƙwarai,in ta dawo aiki ba ta iya taɓuka
wani aikin watarana ma sai tasha maganin ciwon jiki.
Ganin irin wahalar da take sha Mama ta ba ta shawarar ta haƙura da aikin,amma ta nace sai ta
yi musamman da ta ga kuɗin aikin na ta da tsoka.
Yaran matar kwata-kwata basu da mutunci ga rashin kunya abu kaɗan za su hauta da zagi suna
ci mata mutunci,mahaifiyarsu kuma ba ta son ganin laifin ɗanta hakan ya sa ba ta kula su.
Abin da ya ƙara tsorata ta ganin sun girme mata ƙaramar cikin su ita ce take tunanin za su zo
tsara da juna.
Hatta wankin su ita take yi musu don tsabar rashin mutunci harda pant da breziya suke ba ta
wanki,amma ta yi haƙuri ta jure burinta ta samu abin da za su dinga ci.
Sai dai rashin mutuncin da suke mata da ta fahimci ba me ƙarewa bane ta yi tsalle ta fara nuna
musu sam ba za ta ɗauka ba.
Hakan ya saka suka ƙara saka mata ƙahon zuƙa,domin zuciyar su tsabar hassada ce suna
ƙyashin kyan da Allah ya yi mata musamman da suka ga sun ɓata jikinsu da mayukan bilicin.
Abin da Hajiya Binta ta tsira ya sa Juwairiya ta ji aikin ya fita a ranta,saboda kullum ta zo sai ta
tuhumeta da cewar ta yi mata sata.Hakan ya tinzira ta ta saka a ranta duk ranar da ta ƙara za ta
bar mata aikin ta.
Haka kuwa aka yi taƙi zuwa aikin bayan kwana biyu da barin aikin sai ga motar ƴan sanda da
Hajiya Binta akan Juwairiya ta sace mata sarƙar gwal ɗin ta.
Juwairiya ta shiga cikin tsananin tashin hankali ganin yadda ɗan sandan yake ƙoƙarin tasa ta
zuwa ofis ɗinsu,hankalinta ya tashi matuƙa ya dinga kuka tana rantsuwar ba ta ɗauka
ba.Tsananin tashin hankalin da Mama ta shiga ba'a magana duk da ta san halinta,amma sai ta
shiga ruɗu ta din ga tamabayarta da in ta san inda yake ta fito mata da shi,hakan ya saka
Juwairiya cikin tashin hankali ta dinga wani irin kuka gani take kamar Mama ba ta yadda da ita
ba.
Baba Sani ya sami abin da yake so don haka ya ƙara zuga Hajiya Binta kan ta tafi da ita ofishin
ɗan sanda,burinsa ya cika dama tintuni yake addu'ar Allah ya sa haka ya faru.
Mama na gani aka tafi da Juwairiya ta na wani irin kuka gani take kamar dukan ta zasu ta yi har
sai ta amsa laifin da ba ta aikata ba.Ganin an tafi da ita Mama ta nufi hanyar shiga cikin gida
ranta na wani irin suya,hango halin da Juwairiya take ciki da yadda take kuka ta na kiran sunan
ta,sai kawai gani akai ta yanke jiki ta faɗi ƙasa.
Hankalin Mariya ya tashi matuƙa wacce take zaune a ƙasa ta na kuka sosai,gani take kamar ita
ta saka ta a cikin wannan hali saboda hanyar aikin da ta yi mata.
Ita da mahaifiyar ta suka kama Mama suka shigar da ita gida,sai dai daga baya kan dole suka
kwasheta zuwa asibiti ganin numfashinta na ɗaukewa gashi ta na aman jini!
Baba Sani ya yi matuƙar jin daɗin faruwar lamarin duk da ba shi da shiri akan hakan sai dai ya
na ganin yanzu ne burinsa zai cika akanta,don ya tabbata basu da wanda zai yi belin ta hakan
zai ba shi damar ɗora mata sharaɗin zai yi belinta amma sai ta amince za ta yadda da
buƙatarsa,don haka ma yaƙi zuwa ogishin da nufin sai sun yi mata dukan kawo wuƙa ta
galabaita saboda ya san ta a kwai kafiya.
Juwairiya na zaune a cikin cell ɗin ta ƙudundune kanta a cikin jikinta tun da suka kawota take
kuka,tunanin halin da Mama take ciki yake damunta wani irin sauro da yake damunta da ihu da
cizo,yasa take ta zubar jawaye ga yunwa dake ƙwaƙularta."Rabbi inni lima anzalta ilayya min
khairin faƙir."Abin da bakinta yake faɗi kenan cikin tsananin tashin hankali.
Tun da Hajiya Binta ta kawota ba ta ƙara zuwa ba sai washegari da safe lokacin ta matuƙar
galabaita,bayan sun tuhumeta amma taƙi amsa laifinta dukan tsiya suka yi mata sannan aka
maida ta.
Da rana sai ga Baba Sani ya shigo ofishin ya na zare ido,gurinta yazo ya na kallonta." Kin ga
abin da kika jawo ma kanki kosaboda shegen taurin ranki.'Yace ya na kallonta duk da ita ba shi
take kallo ba saboda taƙi ta kalleshi wani irin tsanar sa take ji matuƙa.
" Har yanzu kina da dama zan iya fitar dake amma sai kin amince za ki yadda da
buƙatata."Yace da ita ya na kashe murya.
Wani irin kallo ta watsa mishi " Allah ya yi min tsari da mugun nufin ka,da na amince gara na
tabbata a gurin nan ko ya zamo shine ajalina."
"Ok haka kika ce ko?To ai shikenan kuɗina ya huta tunna kin zaɓi rayuwar zuwa gidan mutane
kina sata."Yace tare da watsa mata harara ya fice daga ofishin,kuka ta saka tare da cigaba da
addu'ar ta ta na roƙon Allah ya kawo mata mafita.
Kwanan ta uku a gurin ranar da Hajiya binta ta shigo ta buƙaci a saki Juwairiya taga
sarƙarta,duk da cewa ƙazafi aka yi mata amma ko haƙuri basu bata ba.Ita dai da gudu ta dawo
gida tasan yaran Hajiya Binta suka ƙulla mata wannan ƙullalliyar amma Allah ya fisu kuma
addu'a takobin mumini.
Ƙarin tashin hankali da ta zo Mama ba ta a gida Ibrahim ne yake sanar da ita ciwon Mama,wani
kukan ta saka ta fita zuwa gidan su Mariya domin Mariya bata gaya mata Mama ba lafiya ba.
Yadda ta ga Mama hankalinta ya tashi ƙwarai rungume Mama ta yi ta na kuka sosai.Mama ce ta
buɗe ido jin muryar Juwairiya hankalinta ya ɗan kwanta ganin ta fito,don ba ta san halin da take
ciki ba shi ya sa jikinta yake rikicewa.
Likita ne ya shigo ya miƙa ma Mariya takadda yace."Gashi ki siyo wannan maganin ya kamata
ku din ga kwantar mata da hankali, domin ta na da hawan jini ga ciwon zuciya, matuƙar ana
ɓata mata rai to watarana zuciyar za ta buga!"
Wani ƙarin tashin hankali Juwairiya ta shiga jin Mama na da waɗannan ciwuka rungumeta ta yi
tana kuka."Mama kema mutuwa za kiyi?Don Allah karki mutu ki barni!Rayuwata za ta shiga
cikin garari.Allah na gode maka ka bani ikon cin jarrabawa,amma karka ɗauke min mahaifiyata
ka barni da azzalimi."
Mariya ta kama ta ta rungume ta na buga bayanta hawaye ya na kwaranya a fuskarta tsananin
tausayi ya cika mata zuciya ganin halin da take ciki."Kin ga ni Mama za ta barni ko!Wai me ya
sa rayuwata tazo a baƙin jadawali ne?Nake kurɓar ruwan bakin ciki mafi zafi da ƙuna a
zuciya."Tace cikin kuka." A'a Juwairiya karki faɗi haka!Kada ki kasa cinye jarrabawarki kin san
Allah ya na jarraba mutum dai-dai imaninsa.Kar zuciya ta sa ki yi saɓo.Ina ji a jikina zaki ji daɗi
a rayuwarki.Allah zai ba Mama lafiya."Ta gaya mata ta na shafa bayanta.
Daƙyar Juwairiya ta daina kuka sai ajiyar zuciya hannun Mama ta kama ta riƙe ta na
kallonta.Duk wani hidima na asibitin su Mariya da mahaifinta suka yi har kuka ta yi ta na gode
musu domin Allah ne zai biya su.
Bayan Mama ta samu sauƙi aka sallame su akan Mama za ta din ga zuwa ganin likita ta na
karɓar magani,hankalin Juwairiya ya tashi ta na tunanin ina za ta din ga samun kuɗin da Mama
za ta din ga zuwa ganin likita.
Kan dole ta ƙara saka Mariya ta nema mata wani aikin don sana'ar da suke yi sun cinye
tsugune kawai suke,da fari Mama taƙi yadda ta ƙara yin wani aikin amma daga ƙarshe dole ta
haƙura ganin yunwa na so ta yi musu tabo.
Kwasam ta haɗu da wani matashin saurayi mai suna Mas'ud Allah ya jarabci Juwairiya da son
shi yaro ɗan gata da sanyin rai ga kyautatawa.Shigowarsa rayuwarsu ya sa sun samu canji
sosai,duk da ya ga ita yar talaka ce amma be saka yaƙi sonta ba don da Allah yake
sonta.Mas'ud ya na temaka musu sosai ya na aiki a Jami'ar Ahamdu Bello a library kuma ɗan
samaru ne iyayen sa sun rasu sun bar mishi dukiya sosai,sannan ɗan kasuwa ne.
Juwairiya ba ta taɓa jin ta na son mutum ba sai akan sa, gabaki ɗaya ta ji ta na son ta aure shi
sai dai tasan hakan ba me yiyuwa bane,don babu yadda za'ai Baba Sani ya barta ta aure shi sai
dai akan yadda take jin sonsa, za ta iya fito na fito a tsakanin su ko gidan me unguwa za ta iya
kai shi.
Haba tunna ya ga ya na zuwa gurinta ya saka tashin hankali yayin da shi ma Mas'ud ya
kafe,ganin shi ma ɗan zamani ne sai yace bai tashi uren Juwairiya ba don bashi da kuɗi,nan
take yace mishi kar ya damu ya amince zai yi mata komai.
Ranar da Mas'ud ya kira Juwairiya ya gaya mata Baba Sani ya amince da auren su har ya ba
shi izini ya turo magabatansa,kawai jin sa Juwairiya ta yi amma ba ta yadda da abin da yace
mata ba.Ganin haka sai ya ƙyaleta kawai in ta ga zahiri ta yadda.
Da misalin huɗu da kwata ɗan Baba Sani ya yi sallama ya shigo ya yi kiran Juwairiya taje
shashin Baba Sani ya na kiranta a ɗakin matarsa.
Gabanta ya faɗi amma sai ta saka hijabinta ta nufi ɗakin ganin a kwai baƙi ya sa ta ji a ranta a
kwai abin da ke faruwa sai ta tsaya daga kofa ta na sallama."Yauwa Juwairiya shigo."
Baba Sani ya faɗa da murya sanyaya a hankali ta yaye labulen ta shigo tare da tsaya daga
nesa ta na kallon mutane jikinta ya bata dangin Mas'ud ne.
Miƙo mata alkur'ani ya yi tare da canza fuska kalar tausayi yace." Dangin yaron nan Mas'ud
suka zo neman auren ki,amma ni bazan cuce su ba sun yi min tambayar kina da tarbiya nace
gara suji a bakin ki, don nasan ke ƴar mace ce sannan kin yi yawon aiki gidajen masu kuɗi,duk
mazan gidan sun sanki a matsayin ƴa mace ga abin kunya na satar da kika yi,har aka kulle
amma ga kur'ani ki rantse musu hakan be faru ba "
Taɓ ji ta yi ƙasa ta gaza ɗaukarta ta ji wani irin hajijiya ya kamata." Inna lillahi wa inna ilaihir
raju'un."
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi na goma sha
ɗaya.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.
Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni
mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata
(SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da
irin taimakon da kike bani.
*FOLLOW, READ, COMMENT, SHARE*
*SAKACINA KO HALIN MAZA*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*SHAFI NA GOMA SHA ƊAYA*
Ganin taƙi karɓar kur'anin hawaye ya na zuba ƙuncinta ya yi murmushin mugunta,ya juyo ya na
kallonsu sannan ya ƙara saka kuka har da hawaye share-share yace." Kun ga abin da na gaya
muku ya zama gaskiya? A matsayina na ƙanin mahaifinta babu yadda ban yi da ita ba akan ta
zama macen ƙwarai, amma taƙi jin maganata!"
Juwairiya da take cikin wani yanayi na tashin hankali mara misaltuwa,ta rintse idanunta ta na jin
wani irin ƙaton abu ya taso daga ƙirjinta ya tokare mata kirji ya kuma ƙi wucewa.
Tana son ta ji saukar hawaye akan ƙuncinta ko ya rage mata raɗaɗin da zuciyarta take
ciki.Kunnuwanta ba za ta iya jure jin kalamai da yake yi ba,ya na aibanta ta ita da mahaifiyarta.
Ta muzanta iya muzanta da ƙyar ta yi nasarar jan jikinta ta fita zuwa shashin su,ta bar shi da
bayin Allah da suka yi zuru suna kallon shi,yanayin su bai nuna sun yadda da maganar da yake
musu ko akasin haka.
Da gudu ta faɗa ɗakin tare da ƙanƙamre Mama ta na wani irin kuka." Mama duniya ta min zafi!
Ina jin wani irin baƙin ciki a cikin zuciyata,wallahi nafi buƙatar mutuwa fiye da rayuwata! Wai me
na yi wa Baba Sani ya tsane ni haka!Gara ya kashe ni da ɗacin da yake saka ma rayuwata."
Mama ta rungumeta ta na shafa bayan ta don gani take kamar hauka ta yi." Lafiyar ki ɗaya
kuwa?Ki yi shiru ki yi min bayanin yadda zan fahimta."
Kusan minti goma ta na kuka ganin ta kasa magana sai ajiyar zuciya take,a ranta ta na jin baƙin
cikin rabuwa da masoyinta,don ta san yadda ya aibata ta babu yadda za'ai su yadda ɗan su ya
aureta.
Da ƙyar Mama ta samu ta daina kukan sannan ta yi mata bayani.Ran Mama ya ɓace sosai ba
ta san sanda ta ji jawaye ya na zuba a ƙuncin ta ba." Na gaji da halin da yake min! Zuciyata ta
fara gajiya amma ba komai Allah ya fi shi da ikon Allah sai ya yi nadama,akan halin da yake
miki."
Sosai Juwairiya take kuka koda Mas'ud iyayensa suka koma gida suka sanar mishi a abin da ya
faru,hankalinsa ya tashi matuƙa duk ƙoƙarinsa na ya fahimtar da su,amma sun ƙi ƙarshe wan
mahaifinsa ya gyara zama yace." Ko da a ce yarinyar ba halinta bane,to ƙanin mahaifinta ba ya
son ya baka ita ka kyale musu yarinya ga ƴan'uwan ka nan sai ka zaɓa a cikin su."
Ransa ya ɓace matuƙa da ma ya ba shi izinin ya turo dangin sa saboda ya faɗa musu haka.
Motarsa ya ɗauka sallama ya yi bai ko tsaya Mama ta amsa ba ya faɗa gidan,a yadda ta gan
shi ta san ba shi cikin hayyacin sa.
Da sauri Juwairiya ta ruga da gudu don ta saka hijabi ganin ya shigo." Mama ya Baba Sani zai
yi haka? Juwairiya ya aiba ta a gaban iyayena. Wai me kuka yi mi shi ya tsane ku?"Ya faɗa
yayin da idanunsa suka kawo ruwa.
Cikin jimamin lamarin Mama ta share hawaye ta kalli Mas'ud da ya haɗa kansa da gwiya
hawaye na zuba a fuskarsa,sai ya ba ta matuƙar tausayi ta san yadda yake son Juawairiya duk
da iyayensa suna da shi amma a haka yake son ta.
Ka yi haƙuri ka san matar mutum kabarin sa Allah be nufi Juwairiya matar ka bace,ka bi zaɓin
iyayen ka ni na san duk korar mata masoya da yake in har lokacin ta ya yi bai isa ya hana ba."
" Gaskiya Mama ba zan iya jure rashin Juwairiya ba zan je na sami Baba Sani duk abin da za'a
yi sai dai ayi haka kawai ya din ga cusgunawa rayuwarku.Ya katse ta da faɗin hakan ransa a
ɓace tare da miƙewa.
" Zo Mas'ud don Allah karka je a yadda ranka yake a ɓace za'ayi ɓatatta,ka san halin shi ba shi
da haƙuri ni ce na haifi Juwairiya ina me baka haƙuri ka haƙura da ita,shi kaɗai ne wanda take
gani a matsayin na ta in har aka ɓata mishi wa za ta riƙe?Ka yi haƙuri Allah be nufa za ka aure
ta ba."
Kawai sai gani ta yi ya saka kuka ya na kallon Juwairiya da ita ma take kuka na tausayin halin
da suke ciki." Juwairiya zuciyata za ta shiga cikin wani hali na rashin ki.Ki yi min addu'a Allah ya
ba ni mace me irin halin ki,ni na san ke wace ce ko idanunki mutum ya kalla ya san kina da
tarbiya da natsuwa.Ina sonki zan haƙura da auren ki saboda umurnin Mama."
Fita ya yi har da gudun sa ya na sharen hawaye Juwairiya ta miƙe da gudu ta shige ɗaki tare da
saka kuka.Sam ita ba ta ga dalilin da Mama za ta hana shi ba,ba ta san me Baba Sani yake
nufi da ita ba shi ya sa take girmama shi,abin da ya sa taƙi ga ya mata ta