Showing 30001 words to 33000 words out of 56747 words

Chapter 11 - SAKACINA KO HALIN MAZA Book Complete .pdf

ɓace za ta dake ta kenan aiko in dai haka ne a kwai zalinci.

" Ai kin banza kawai sai dai in zaka ɗauki numfashina ma'ana ba ni a raye,amma ni da kai na
zan tona asirin ka kuma na ga uban da zai karɓar maka auren tunna ba ƴar tsana ba ce,sai da
waliyin ka za'a baka.Yace a fusace.

" Ok haka kace ko zan nuna maka true color ɗina dama duk abin da aka haɗa da jaki sai ya ci
kara,ka haɗa hulɗa da talaka matsiyaci da be da komai sai tsiya na yi dana sanin tarayyata da
kai don bi amfana min komai ba,duk halaccin dana yi maka ni da dangina muka ƴanta
rayuwarka shi ne zaka saka min da haka!"

To fa ran A.k ya ɓace matuƙa kawai sai hawaye ya kalli A.m da yake ta ga ya mishi maganganu
mara sa daɗi da baƙan ta rai,don shi in dai ran shi ya ɓace bai iya magana ba."

" A she haka kake dama na daɗe ina tunanin wannan ranar za ta zo,saboda a gaba na kasha
wulaƙanta talawa irin na na gode in sha Allahu daga yau ba ni bakai,ba zan ƙara hulɗa da kai
ba kuma na bar muku aikin ku ka sana ni ba jahili ba ne ko yau na yanke alaƙa da ku sai kun yi
jimamin rashina."Yace ya na me tabbatar da hakan a ran sa.

Kai ɗin me kai ɗin banza me kake da shi kaje a kwai waɗanda suka fika ilmi da zasu buƙaci
gurbin ka.".
Lamarin fa ya yi tsamari gabaki ɗayan su kowa ya hau dokin zuciya duk da zo mu saɓa zo mu
zauna,amma ba su taɓa samun saɓani irin na yau ba.

Ko da A.k ya nufi hanyar fita A.m jawo kwalar rigar sa ya yi tare da dawo da shi ya hau shi,da
dambe don gani yake ya ma rai na mishi wayo ya na karkashin sa,sai ya manta abokantakar su
ya dawo kan matsayi.

Aiko A.k a zuciye ya kai mishi mari ya kauce shi ma ya kai mishi suka rikice da dambe
kici-kici.Me ba ma fulawa ruwa ya zo ya gan su da gudu ya ruga ya yi kiran mutane,su raba don
ba zai yi gigin shiga tsakiyar su ba su bar shi da jinya yadda suke ji da karfi.

Da ƙyar mutane suka raba su sai huci suke tamkar wasu zakuna.Faruwar lamarin sai ya yi
matuƙar bawa mutane mamaki,tuna yadda suka shaƙu kamar wasu ƴan'uwa suna ta jimamin
lamarin me ya haɗu ko ma dai mene ne lamarin me girma ne,amma da suka tuna tsakanin
harshe da haƙori ana saɓawa sai suka ba su haƙuri tare da ɗauko musu ruwan sanyi,domin ya
sanyaya zuƙatan su saboda sheɗan da ya yi nasara haddasa fitina a tsakani aminnan ko nace
ƴan'uwa.


A.k da ran sa ya ɓace ko jiran wanda ya nufi zuwa cikin kampanin ya ɗauko musu ruwa bai yi
ba ya fice ya na jin a ran sa ya tafi na har abada.

Ko da a ka ɓalle murfin gorar ruwa aka zuba mishi ruwan wurgi ya yi da kofin tangaras ɗin ya
nufi motar sa,ya shige tare da figar ta kamar zai tashi sama.


Ko da ya iso kofar gidan ya shiga sakin hon ba ƙauƙautawa.Allah Sarki Audi direba dake cikin
bayi da cikin sa ya murɗa ya shiga kenan ya ji hon wanda ya tabbata matar gidan ne me
shegen yawon tsiya,amma da ya tuna ya ga ta fito ɗazu sai ya yi maza ya fito ba tare da ya
gama abin da yake ba sai dai hon ɗin da ake saki na rashin hankali.
Ya na wangale get ɗin sai yaga megidan sa ne yake ta zuba wannan hon,hankalin sa ya tashi
kwarai don a tunanin sa ba lafiya ba.

Ya na shiga ko parking bai yi ba ya fito ya ƙarasa gurin Audi direba dake mishi sannu ya na son

ya kulle get ɗin ya ruga bayi,don har lokacin cikin sa bai dai na murɗawa ba.

Mari ya zabga mishi." Kai wane irin banza ne matsiyaci kawai gidan ubanka ne da zan ɗauki
lokaci ina hon baka amsa min ba? Ko kuɗin da nake biyan ka da shi haƙo su nake!"


"Allah ya baka haƙuri ina bayi ne cikina ya lalace."


Bai saurare shi ba ya shige cikin gidan falo ya shiga gibbiyar ta na kwance a doguwar kujera me
cin mutum uku da remote a hannunta ta na kallo.


Ba tare da kallon in da take ba ya shige cikin ɗakinsa ruwa me sanyi ya dinga kwankwaɗa har
sai da ya cika cikin sa,amma bai ji zuciyar sa ta dai na tafarfasa ba don ji yake kamar za ta fito.


Ya yi cilli da robar ruwan dai-dai lokacin da ta shigo ta na mishi kallon ko ya taɓu ne? Tsaki ta yi
kawai ta fice ta san in ta tambaye shi zai iya gaya mata baƙa ita kuma sai ta rama,don haka ba
ta tanka mishi ba ta ɗauki wayar ta dake kan gado ta fice a ran ta ta na faɗin." To wa kuma ya
taɓo wannan kububuwan?Ba zan yi mishi magana ba ya ƙare a kaina bari na bari ya huce."Ta
koma ta yi kwanciyar ta ta na kallo.


Tofa masu karatu kun dai jin yadda ta kaya game da waɗannan aminan juna.Ku ci gaba da
bibiyata na gode da yaba lintafina da kuke.

ƊUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ƊIN KU YA NA SAKA NI NISHAƊI.

MAMAN SUDAIS
AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM

Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha
uku.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni
mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata
(SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da
irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.



*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 13*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

A.k ya na tuki ya na jin zuciyar sa na wani irin tafasa sai dukan sitiyarin yake ya na tsaki ji yake
kamar ya je ya shaƙe shi,ya na ji a ran sa ba zai ƙara hulɗa da shi ba don ya tabbata ba shi da
mutunci kuma yau zai mayar mishi da motar da ya siya musu a tare da suka je Dubai.


Da sauri ya taka burki ganin ya na son ya buge wani yaro dake sai da rake a tire,ya yi ƙoƙarin
janyo natsuwa don ya samu ya isa gida lafiya saboda da ƙyar yake gani.

Matarsa na zaune ita da yaranta suna assigment sai ganin sa ta yi ya shigo kamar an jeho
shi,bai amsa sannu da zuwa da suke mishi ba ya shige ɗakinsa wanda ya ɗaga hankalin ta ta
miƙe ba shiri ta bi bayan sa.


Ganin yadda ya haɗe kai da gwiwa ta ɗauka rasuwa a kai don haka jikinta a mace ta ƙarasa
gun sa tare da dafa shi.

" Lafiya Baban Najwa in ce ba wani abu mummuna ya faru ba?"


Ta faɗa cikin tsoro ganin yadda idanun sa suka canza sannan ta ƙara cewa." Ka yi haƙuri dama
haka duniya take ni dai fatana ba mutuwa akai ba,ko wani mummunan lamari ya faru! Don Allah
ka yi magana."
Bai amsa mata ko ɗaya ba ya ɗauki ruwa ya na sha.Ganin haka sai ta janyo jikinta bayan ta
ƙara A.c ɗakin ta janyo mishi kofa a ran ta ta na addu'ar Allah ya sa lafiya.


Kimanin rabin awa ya ɗauka a cikin ɗakin sannan ya yi wanka ya fito da duguwar farar jallabiya
a jikin sa,gefen ta ya samu guri ya zauna ya na kallon ta da ɗan murmushi a fuskarsa.

Sai hakan ya sanyaya zuciyarta da take ta bugawa ta na tunanin ko wani abu me girma ne ya
faru.

Ido ya zura mata bai ce mata komai ba hannunsa ta kama tare da ɗora kanta a kafaɗan sa."
Zuciyata ta ku san bugawa da na ga ka shigo a cikin wannan halin."

Shafa gashin kan ta ya yi yace a hankali da muryar da har yanzu a kwai ɗan ɓacin rai a cikin
ta." Mun yi faɗa ne da A.m kuma me zafi don har na bar mishi aikin sa,zan kuma mayar mishi
da duk wani abu da ya mallaka min."

Ya faɗa ya na furzar da wani irin huci mai zafin gaske.

Kallon sa take da irin ba za ku taɓa canzawa ba duk cewar ta san suna faɗa amma wannan

karan da alamar faɗan ya yi tsamari ganin yadda ransa ya ɓace.

" Me kuma ya ƙara haɗa ku?"

Miƙewa ya yi ya ɗauki wayar sa zai koma ɗaki jin tambayar da ta yi mishi wanda ya ɗaukar ma
kan sa wargaza shirin,amma kuma bai gaya mata ba sai yace." Wanann kuma sirri ne a
tsakaninmu."

Ya ƙarashe shigewa bayan ya riƙe hannun Farha dake ta nacin ya ɗauke ta tun da ya fito daga
ɗaki,ya bar ta a tsaye ta na jinjina wane irin rikicine ya faru a tsakanin su har ya yanke barin
aikin.

" Ko ma mene ne su suka sani haba! Suna girma suna cin ƙasa." Tace cike da takaicin halin su
sai kuma ta yanke shawarar ta kira Zainab ta tambaye ta sai da wayar ta yi ringin sau
ku,sannan ta ɗauka tare da sakin wawan ajiyar zuciya.

" Hello sahiba ki yi haƙuri ina falo na bar wayar a cikin na manta da ita,sai da Atine me aiki ta
kawo min.Ina yarana?"

Ajiyar zuciya ta yi tace " Ba komai wallahi suna lafiya dama na kira ki na tambaye ki ko A.m ya
na nan,na ga aminin na sa ya shigo kamar sun sami saɓani hankalina a tashe yake."


Tsaki ta yi ta taɓe baki." Humh ke kika kula shi ni nawa da ya shigo ko kallon sa ban yi ba,na
kyale shi don ba na son ya haɗa min zafi saboda ni ma a cike na ke da wata da ta yi min rashin
mutunci a tiktok."Ta ba ta amsa ta yamutsa fuska.


"Zainab!Wai ke ba zaki dai na yin rawa a tiktok ba! A da baki aure amma yanzu ke matar aure
ce hakan bai dace dake ba,kin ci sa'a shi A.m sam ba ya yin tiktok amma in Allah ya so ya
kama ki sai kiga wani ya tura mishi kuma ba zai ji daɗi ba."

" Umh ke ni kyale ni lokacina ne kin san iya yawan adadin mutanen da suke bibiyata,so kike na
yi asaran mutanen da suke zuzuta kyawuna?Ai in kika ga na dai na ƙila na mutu ne."


" To Allah ya shirye ki da masu hali irin naki a matsayin ki na matar aure ji je kina bayyana surar
ki ɗora waƙa ki nabi don kawai ki yi suna ko burge mutane,ba yan kin san haramun ne a addini
kuma bayan haka malamin ahalari yace.Wal mar'atu kulliha aurati ma adal wajha wal
kaffaini.Wato ita mace dukkannin ta al'aura ce sai dai fuska da tafukan hannaye. Gaskiya ya..."

" Wash Allah na! Wallahi Maman Najwa kin cika cika mutum wannan dalilin ya sa ban cika zuwa

gidan ki ba.Ke kullum sai kin yi ma mutum wa'azi,ke da uztazi kika aura sai kin addabi mutum
da wa'azi ina ga ko sallah mutum ya yi zaki ce ba dai-dai bane." Ta ɗan numfasa ko za ta ce
wani abu sai ta ɗora da cewa jin ta yi shiru ajiyar zuciya ta sauke.

"In kin kira ni ne ki yi min wa'azi ba ni da buƙata matar liman sai kije masallaci ko in da ake
buƙata.Ni ya maganar mu na fara yin sana'ar zuwa waje kin yi mishi bayani."Ta canza maganar
don ta gundire ta ita ba ta da wani aki sai na yin wa'azi ita kam ba za ta iya ba,ita dai da ta ga
za ta iya kashe rayuwar ta da kuruciyar ta sai ta yi Allah ya ba ta sa'a.

Dariya ta yi jin ta canza maganar tace." Na gaya miki tun ranar ni ba zai barni na fita zuwa wata
ƙasa saro kaya ba,gara mu dinga basu kuɗin ko mu yi oder kin san yanzu komai a sauƙaƙe
yake."

"Taɓ kin yi makaranta amma kamar baki waye ba ok da ma kina jira ya amince miki ne? Dama
ba sana'ar kike so ki fara ba,ai koni da kika ji nace zan yi ba zan gaya mishi ba,sai ya ji na fara
ke ranar da na ɗan sako mishi maganar Yayyina suna zuwa waje yin business,bai kalle ni ba
yace ai da yake mazan na su mahaukata ne basu san mahimancin iyali ba.Shiru na yi bance
komai ba ai sai dai ya ga na ɗaware inna dawo koma me zai faru ya faru Am ready for the
conseqeuncy."


A ranta ta na girmama irin halin Zainab wacce sab ba ta tsoron miji ga shi Allah ya yi mijinta da
son girma,sai dai bai samu macen da za ta ba shi wannan girma ba aiko za'a sha daru don shi
ma ba daga baya ba.

" To shike nan Allah ya sa ki gane ni dai ba zan baki kuɗina ba kar mijin ki ya ji na baki,ni ina
daraja aurena ke na lalata miki na ki gara na ba shi ya yi min oder hankalina kwance,sannan ki
je ki rarrashe shi ki ji abin da ya haɗa su ko ma bai gaya miki ba don Allah ki ba shi kula kina
sakaci da mijinki fa kar wata ta yi miki kwace."


Ta faɗa da tsigar tsokana duk da ta san Zainab yanzu za ta harzuƙo mata da shegen baƙin
kishinta amma ta kasa kula da shi.


" Kinga ni ko zamu fara Allah babu wata matsiyaciyar mace da za ta shigo min gida,na kuma
riga na gaya miki in ta yi wannan kuskuren to ta tabbata ni ce ajalin ta.Kuma hankalina kwance
yake ya yi min alƙawari,wace mace za ta aure shi baya haihuwa ko ni haƙuri nake."

Faɗin likita ba Allah bane Zainab in Allah ya so sai ya haihu domin ubangiji yudabbirul amri ne
ya na jujjuya lamaruran sa,don haka ban ji daɗin abin da kika faɗi haka kuma kinga ya na
iyakan ƙoƙarin sa.


Zainab sai ta ji wani iri a ranta ta na fatan hakan don yanzu yadda A.m yake son ya haihu har
yake zubar da hawaye ta na son ko ɗaya ne ta haifa mishi ita fa ba ta son tara yara.
" Ina fatan haka Allah ya amshi addu'armu sannan da kike cewa na je na rarrashe shi Allah ya
sauwaƙe haka kawai kema kin faɗa min don ki tsokane ni ne ko?A kan maganar fita waje ai
dama ban miki dole ba.Ni na gaji da wayar nan don takaici kike ƙara min zan shigo gidan ki
kawai mu tautauna ki gashe min da yara."

Ta maza ta datse wayar ta na baƙin cikin halin da ƙawarta ta ɗaukar ma kanta saboda ta yi aure
sai ta hana ci gaba a rayuwar ta?Tsaki ta yi ta ɗauki wayarta ta ta shige ɗaki zuwa can ta fito ta
ci ado kamar wacce za ta gasar kyau,ta ɗauki key ɗin motarta da wayarta ta fice ta na ba za
ƙamshi mai sanyaya zuciyar duk wanda ya yi katarin shaƙar shi.
A.m riƙe da waya a hannunsa a cikin haɗaɗɗen ofishin sa sai ya duba numbar A.k da nufin ya
kira sai kuma ya yi cilli da wayar a kan duguwar kujerar da ke cikin ofishin.


Ya yi haka yafi sau a ƙirga gabaki ɗaya abubuwa sun rikice mishi a kampanin wanda har Daddy
ya fara ƙorafi,ya sani A k wani jigo ne a cikin kampanin amma ransa ya ɓace ya je ya gaya
mishi maganganu mara sa daɗi ga shi tun ba'a je ko ina ba ya fara dana sani.


" An ya Juwairaah auren ki alkhairi ne?"Ya faɗa da tsigar tambayar kansa saboda ganin da ya yi
kan maganar auren ta kawai ya bata da aminin na sa wanda suka zama kamar ƴan'uwa.


Miƙewa ya yi ya tsaya a windon dake ofishinsa ya na kallon waje ganin Daddy ne da ƙaninsa
yake tuƙa shi,ya yi maza ya fice daga ofishin tare da shigewa cikin wani ofis wanda ya san ba
za su neme shi acan ba ya kulle kansa.


" Wayyo Allah na! Ya zan yi na san Daddy ya biyo ni ne ganin na ƙi ɗaukar wayarsa ga shi
kwana biyu A.k bai zo ba abubuwa duk sun caɓe.


Sai ya yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login