Showing 27001 words to 30000 words out of 56747 words

Chapter 10 - SAKACINA KO HALIN MAZA Book Complete .pdf

burge ni."

Ba tare da wani shakku ba A m yace."Bayan kyau a kwai hankali da natsuwa .Rayuwarta a kwai
tarin tausayi ka aureta kawai ta haifa maka yara.

Da sauri A.m ya buɗe idonsa ya ɗora akansa wani irin ɓacin rai da takaici ta ya ya zai haɗa shi
da ita ƴar talaka me talla ita yake nufin ta haifa mi shi yara!Ina imposible wasa yake yi.

Ya buɗe baki zai yi magana sai kuma ya figi motar tamkar zai zubar da su,A.k dai bai ce komai
ba koma kashe su zai yi, ya yi amma iyakan shawarar da zai iya ba shi kenan kuma in dai bai
ɗauka ba to ba zai ƙara kula shi akan damuwar sa.

Ƙofar gidansa ya ije shi ba tare da yace komai ba bayan ya fito daga motar ya leƙa ta tagar
motar yace.Allah ya bamu alkhairi ka yi tunani shawarar da aka yanke ina sauraranka."
Ba tare da ya tanka mishi ba ya ja motar a guje dariya ya saki tare da girgiza kan shi ya shige
gidan sa.
A.m da ya koma gida sai yaji wani tashin hankali game da maganar da ya yi mishi,amma ya
kasa amincewa wanka ya yi ya kwanta don baya so ya yi tunani akan maganar,sai dai bayan
baccin ya kwashe shi sai ya yi mafarkin ga Juwairiya ta na kuka ta miƙo mishi yara guda biyu
shi kuma ya na cikin ƙaton rami ya fito da ninyar ya ƙarɓa sai ta ɓace ta na wani irin ihu,ihun da
ya fargar da shi ya miƙe a zabur! Ya na salati don har yanzu bai daina jin sautin kukan a cikin
kunninsa ba.

" Ita za ta haifa min yara amafarkin da na gani kenan amma a kwai matsala.Tabbas matsala
babba don ko ni auren ta zan yi cikin sirri ba tare da sanin kowa ba wato auren wucin gadi,na

ƴanta mata rayuwa na ba ta jin daɗi amma mu yi aure na tsawon shekara ɗaya tazo a matsayin
me aikin gidana bayan ta samu ciki, na ɗauke ta na kai ta wani gurin in ta haihu na biyata na
karbi yarona na kawoma matata masoyiya Zainab."

Tofa masu karatu kun ji A.m abin da yake so.
*Hakan zai yiwu?
*Ta ya ya A.k zai karɓi lamarin shin zai bashi goyan baya kuwa?
*Wani irin aure yake son yi?
*Shin ya zai yi da Baba Sani da ba shi da buri sai dai rayuwar Juwairiya ta wulaƙanta,zai
amince mutum me daraja da matsayi ya aureta?
*In ma ya amince taya za'ai Juwairiya ta yi rayuwa a gidansa a ɓoye a matsayin matarsa amma
kuma azahiri ƴar aiki?
*Ta ya ya za ayi auren sirri ba tare da sanin Mama ba?
Ku dai biyo ni a shafi na gaba"SAKACINA KO HALIN MAZA"
NAGA RUWAN COMMENT IN ANA SO NA CI GABA.TAKU JAMILA LAWAL
ZANGO❤❤




Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/G0J8rS0cxTtCCC38iwA3B9
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_


*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*SHAFI NA GOMA SHA BIYU*



Juwairiya ta na ɓacewa ganin sa ta tsaya ta tsuguna tare da sakin wani gigitaccen kuka sosai
wanda ba ta san dalilin yin hakan ba,sai bayan tasha kuka sosai zuciyarta ta fara jera mata tarin

tambayoyi."

Me ya sa nake kuka ga mutumim da na san ba zan taɓa samun shi a cikin rayuwata,na sa ni
cewar dariya ba so ba ne.! Maganar da ya yi min ba ya nufin zai iya sona a cikin ransa,sannan
na tabbata ya yi aure har ma da iyali saboda kamalar shi ta nuna na cikakken mutum me iyali."

Ta tallabe fuskarta da hannunta wani sashi na gefen zuciyarta,ya na ƙara jaddada mata da
cewar ko da ya nuna ya na sonta Baba Sani ba zai taɓa ba shi auren ta ba,mutane wanda ba
su kai shi matsayi ba sun nemi auren ta amma ya hana bare shi da ga ganinsa kasan ya jiƙu da
nera,da duk wani ababen more rayuwa.
Sai ta share hawayenta tare da ɗaukar tiren jiri na jiri ya na iban ta ta na ji kamar ta haɗiye
zuciya ta mutu in ta tuna wannan tsohon ze mallaki jikinta.

Gizo-gizon hoton sa da murmushin da ya yi mata lokacin da ya tabbayi sunan ta idanuwanta
suke hasko mata,ta rintse idanunta da ƙarfi ta na son su daƙile mata ganin ta ga mutumim da
take jin kamar ya saka ta a aljihun sa su yi ta yawo.

Bayan ta dawo gida ta na zaune jingine da bangon ɗakin su idanunta a sama ta na aikin tunanin
da ta ɗaura ɗamara da shi tun lokacin da idanunta suka yi tozali da shi.

Mama dake tsaye ta na karantar yanayin ta tun da ta kawo mata kuɗi tace wani mutum ya
siye,ta zauna a gurin ta na kallon sama sai hakan ya tabbatar mata da a kwai lauje cikin naɗi.

" Juwairiya lafiyar ki kuwa."Mama ta kalleta lokacin da ta dafa kafaɗarta,amma ba ta ji ta ba har
sai da ta maimaita sau biyar ba ta ji ba sai ta juyo da fuskarta.

Ga mamakin ta sai ta ga ta juyo tare da saka hannunta ta rungumeta ta fashe da kuka,hankalin
Mama ya ƙara tashi dama tun safe take jin wani irin zafi-zafi a ƙirjin tare da sauke wani irin
ajiyar zuciya mai kama da zai tafi da rayuwarta.
Yaƙe me kama da murmushi ta yi tace." Akan maganar auren ki ko Juwairiya ya za mu yi da
ƙaddarar ubangiji,komai kika ga ya faru Allah ne ya ƙaddara."

Ta sauke irin wannan ajiyar zuciyar da ke barazanar ɗauke numfashin ta sai kuma hawaye suka
fara turereniya a kan ƙuncinta.
Ta buɗe baki da nufin ta yi magana amma ta kasa sai ta rufe bakin tare da sakin kuka wanda ya
fi na Juwairiya sauti.

Hankalin Juawairiya ya tashi matuƙa!Tun da lamarin ke faruwa Mama ita take kwantar mata da
hankali amma yau haƙurin ta ya gaza.

" Don Allah ki de na kuka wallahi na haƙura ba zan ƙara nuna damuwata ba,in dai akan auren
nan ne kin san yanayin ciwon ki.

Ta faɗa ta na share hawayen ta don ta na tsoron kar ciwon Mama ya tashi,ga shi aure za ta yi
babu wanda zai kula da ita sai Ibrahim wanda ba cikakkiyar lafiya gare shi ba,don har ɗingishi
yake yi kafar sa ɗaya ba lafiya.

Mama ta miƙe ba tare da tace komai ba ta fice daga ɗakin ta na jin matuƙar tausayin ta
kasancewar ba ta sami bango abin jingina ba.Tanimu ba mutumim aure ba ne ita kuma mace ta
na zama zinariya ce in har ta samu miji na gari,ta fauwala ma Allah lamuran sa saboda Allah na
iya can za lamuran sa iya addu'ar da take yi wa Juwairiya rayuwar ta ba za ta taɓe ba.
Buta ta ɗauka ta shiga bayi ta tsarkake kanta ta fara kai kukan ta ga Allah Sarki gwani gagara
misali!

Ganin haka Juwairiya ta miƙe tare da sakin kuka ta toshe bakin ta bayi ta shige ta saki bakinta
ta na kuka mai tsuma zuciyar me sauraro." Me ya sa ka shigo rayuwata a lokacin da nake jin
duniya ba ta da muradina a cikin ta gyambo biyu kake so na yi ta jinya a cikin rayuwata! Na
rashin ka da auren mutumim da na tsana a rayuwata!"Kuka sosai ta yi sannan ta fito ta yi alwala
tabi sahun Mama.

Wunin ranar ta yi shi ne a suku-suku tamkar wacce ba ta da lakka a jikinta,ta kasa cire shi a
ranta.Da daddare ta na kwance sai mutsu-mutsu take ta na jin Mama na ajiyar zuciya ƙut!Ƙut!
Wanda hankalinta ya tashi kwarai ba ta rintsa ba sai kusan asuba ta ji ɓarawo bacci ya kwashe
ta.
Da asuba bayan ta yi sallah ta na karatun alkur'ani ta yi mamakin da Mama ba ta tashi ta yi
sallah ba,sai ta miƙe dai-dai lokacin da Ibrahim ya shigo ya dawo daga masallacin dake kusa da
su.

" Mama ki tashi ki yi sallah." Amma shiru ba ta amsa mata ba da sauri ta ƙara jijjigata sai dai ta
ga Mama idanunta sun ƙanƙance jikinta ya saki da ƙyar take janyo numfashin dake barazanar
kuɓucewa gangar jikin ta.

" A'a Mama don Allah karki mutu ki bar mu kin ji Mama!"Kuka take sosai ta na girgiza Mama
da ta ƙasa buɗe idanun ta saboda nauyin da sukai mata,a jikin ta ta na jin wani irin zafi me
kama da rushi ya na zagaye ilahirin jikinta don har huci yake ya na fitar da tiriri me zafin gaske!

Jin ihun Juwairiya ya sa matar Baba Sani ta shigo wanda hankalinta ya tashi matuƙa ta na
tausayin su sosai,sai dai ta san halin tijararren mijinta zai iya shuka mata rashin mutunci koma
ya sake ta bare yanzu da yake mata rashin mutunci zai ƙara aure.

Kuɗi ta miƙa ma Juwairiya ta saka yaron ta ya nemo me keke napep aka saka Mama a ciki
zuwa asibiti.

*********
Bayan A.m ya fita gidan iyayen shi ya nufa don ya ɗan kwana biyu be leƙa su ba,ya na shiga ya
ga ana ta murnar matar ƙaninsa ta haifi ƴan biyu gidan ya cika sai murna ake,saboda daga
asibiti nan aka wuto da ita.

Jikinsa ya yi sanyi ya irga yaransa yanzu huɗu kenan sai kawai ya ji zuciyar sa na bugawa,bai
ƙara shiga cikin tashin hankali ba sai da aka ɗora masa yaran masu kama da larabawa a kan
cinyarsa.

Gidan gabaki ɗaya sun ruɗe suna ta ɗaukar yaran waya kamar zasu ƙarar da jikin su saboda
ɗaukar hoton,har sai da ya tsawatar da su bari sannan suka dena suna ta kallon yaran.

Hawaye yaji suna bin ƙuncinsa ya kasa ɗaukar yaran ya na kallon su gunun sha'awa kamar ya
kwace yace ƙwansa ne shine ya haife su.

Ganin ya na hawaye sai dukannin su jikin su ya yi sanyi suka koma suna rarrashin sa,amma ya
kasa tsaida hawayen da ke kwaranya kamar an buɗe famfo.
" Zainab an ya kin yi wa rayuta adalci kuwa?"
Ya tamabayi kansa dai-dai lokacin da mahaifiyar sa ta dafa kafaɗun sa ta na rarrashin sa.Bayan
ya sawa yaran albarka ya fice daga gidan kai tsaye kampanin su ya wuce tare da jiran A k su
haɗu da shi farfajiyar kamfanin.

A.k ya sanar mishi ya na kampanin in ya iso ya kira shi kawai,amma sai A.m ya nuna ya fito
kawai ya jira shi saboda yanayin da yake ba zai iya ƙara kiran waya ba.

Ya na isowa ya same shi tsaye da waya a hannun sa da alama waya yake sai kuma ganin shi
ya sa ya kashe wayar,tare da maida ta cikin gabar rigar sa ya ƙarasa gurin da A.m ya yi parking
ɗin motar sa.

Ina ga muje farfajiyar da Daddy yake hutawa abin zai fi ko a bisa mu yi magana don nima ina da
maganar da nake son mu tautauna akai."A.k yace da shi bayan ya nufi hanyar gurin ba tare da
ya ji amsar da ya ba shi ba.

Ganin haka sai shi ma ya bi bayan sa ba tare da yace komai ba.Bayan sun zauna shirun na su
na ƴan mintoci ya biyo baya wanda sai da nabi dindigi na gano dalilin shirun na su a duk lokacin
da suka haɗu kafin su fara maganar da ta kawo su,wanda suna yi ne don su sami natsuwa tare
da nazarin maganar da zasu tautauna a tsakanin su.
A.k ya buɗe baki da nufin zai fara magana amma sai A.m ya hana shi ta hanyar taran
numfashin sa tare da gyara zama yace."Abokina ka fara bani dama na yi magana domin na
samo mafita a kan damuwata,na yi tunani sosai kan maganar da muka yi da kai na

Juwairaah.Tabbas yarinyar ta kwanta min a rai kuma na yaba da hankalin ta amma saboda
alƙawarin da na yi wa Zainab,kuma ita kaɗai nake son takasance matata zan auri Juwairaah mu
yi auren
kwangila da ita shekara ɗaya,kamar yadda ka bani labarin ƙanin mahaifinta ni kuma zan siya
shi da ruwan kuɗi ya fasa auren da zai yi mata da wannan tsohon."

Ya numfasa ya na kallon sa ko zai fahimci yadda ya karɓi zancen,amma sa ya ga ya na mishi
kallo kamar irin amma ka zare ko!

Bai damu ba ya ƙaɗa kansa yaci gaba da cewa."Tunna ka gaya min ta yawon aikatau sai mu
ɗauketa akan za ta koya wa matata girki da kula na tsawon shekara guda,kaga a wannan
lakacin in ta samu ciki zan ɗauke ta daga gidan na kai ta wani guri,na san yadda zan tsara
Zainab ta amince ta karɓi ɗan burina na ga ɗana kafin na mutu.
"Amma baka da hankali ko na ɗauka alkhairi ya sa ka kira ni nan,ashe ka je ka bugu ne ka zo
ka ɓata min lokaci."A.k yace tare da miƙewa yayin kamar zai fice daga gurin bayan ya miƙe sai
ya dawo ya ƙara zama ya na kallon sa yace." Aikin banza kawai na ɗauka auren ta za ka yi na
ɓata lokaci na gurin sanin tarihin rayuwarta! Abin takaici sai ga shi kazo ka na min maganar
banza. Shin baka da zuciya ne a ƙirjinka har ka kasa tausayawa rayuwarta na halin ƙuncin
rayuwar da take ciki? Ko ƙyamar talaka da kake yi ne ya sa kake son ka cutar da zuciyar ta.

Ya ƙara miƙewa don ji yake kamar ze rufe shi da duka ya na jin zai iya gaya mishi duk maganar
da ta zo bakinsa,saboda tun jiya da ya ji halin da take ciki Allah ya saka mata tsananin
tausayinta a ranta.

A.m hannun sa ya kama shi ma sai hawaye ya na faɗin." A tsakanina da ita waye yafi kusanci
da kai ina cikin wani hali bani da nufin na cutar da Juwairaah wallahi tsananin son ganin ɗana
ya sa nake jin zan iya komai.In har ka amince ka bani goyan baya mukai auren sirri da ita na yi
maka alƙawari rayuwar Juwairaah sai ya canza daga talauci zuwa mafi ƙololuwar jin daɗi na
rayuwa.Kuma ko banza aurena zai zamo katanga a tsakanin da tsohon mutumim nan,ƙanin
mahaifinta da yake takurawa rayuwarta duk haɗuwana da ita zai saka ya dena saka mata
ƙahon zuƙa."


" Rufe min baki nace! Shashasha!Kawai ka san yadda zuciyar mace take da rauni kan
soyayya.Kai fa namiji ne da ko wace mace za ta yi mafarkin samu,ka na tunanin in ka auri
Juwairiya za ta iya haƙuri da rashin ka ne,a kan maganar soyayya kuɗi ba ya tasiri mace za ta
iya baka rayuwarta kuma ta sadaukar da rayuwarta duka gabaki ɗaya in har ta na sonka,ba za
ta taɓa damuwa da halin rashi ko baƙin cikin da za ka saka taɓa."


Ya saukar da zazzafan huci ya ja numfashi sannan ya kalle shi da idanunsa da suka kaɗa suka
yi jajur." Ina tunanin yaudarar Zainab kake da kake faɗin ka na sonta don da ka san yadda

soyayya take tasiri da baka buƙaci auren Juwairiya na wucin gadi ba, don na tabbata kafin ku
rabu sai Juwairiya ta faɗa kogin son ka koda yankan namar jikinta kake yi ɗanye,bare kuma za
ka raba ta da abu mafi girma a rayuwarta kawai za ka rabu da gangar jikinta ne amma zuciyar
da da ruhinta duk za ka raba ta da shi.Ba ka san yadda uwa take zama akan yaron ta
ba,saboda ba ka haihu ba shi ya sa baka san soyayyar da Allah ya saka tsakanin ɗa da mahaifi
b..."

"Ya ishe ka! Rufe min baki nace banza mara mutunci! Har ni za ka yi ma gorin haihuwa na
rantse tunna ka yi min gori sai na aureta kuma na raba ta da yaran na kai ma matata,na yi
alƙawarin sai kaga ƙwaina a duniya."

Ya matso tare da taɓa ƙirjin shi da ɗan yatsa yace." Saboda nace zan aure ta ka wani tada
jijiyar wuya'duk na gane kauce-kaucen ka don ta na talaka ba ka son na aureta.To siyan ta zan
yi da kuɗina kai ma ka san in ka yi tunanin zan aure ta na yi rayuwar har abada ka yaudari kan
ka, me zan yi da ƴar talaka wanda basu da komai sai tsiya,kuma ka sani ko ban aure ta ba ina
da kuɗin da inna ce zan auri ƴan mata waɗanda suka fi ta kyawu da ɗaukaka zan iya auren
goma in ana yi."


"To kaje ka auri ƴan matan duniya duka in kana son ɗan ƙaruna amma ba zan haɗa hannu da
kai na saka rayuwar ta a cikin matsala."

Ya faɗa tare da ƙoƙarin barin gurin rigar sa ya jawo ya juyo da shi gaban sa ." Ko ka sa min
hannu ko ka ƙi sai na aure ta ita kaɗai ce na ji zan iya rayuwar aure da ita ba yan masoyiyata
Zainab,don haka in dai kuɗi na aiki ka ba ni sati biyu za ka gan ta a gidana kuma a matsayin me
aikin matata za ta shigo gidan."
Ran sa ya ƙara ɓaci da ya tuna ya sha zuwa gidan ya ga Zainab ta daki me aiki,hakan ya na
nufin in ranta ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login