Showing 39001 words to 42000 words out of 56747 words

Chapter 14 - SAKACINA KO HALIN MAZA Book Complete .pdf

kawo shi gidammu wanda har Baba Sani ya yadda na zo gurin sa.Aurena yake son yi?".

Ta tambayi kanta sai ta yi saurin kawar da wannan bahagon tunanin ta ce " Kai ina wutsiyar
raƙumi ta yi nesa da ƙasa."


"Wai ni kurma kika zama bayan rabuwarmu?Ko kina mamakin ganina ne"

Ya ɗan tambaye da hasala a ranshi ganin yadda take basar da shi kuma ya tsani hakan.

" A'a ai ba'a mamaki da ikon Allah."

Iya abin da ta ce kenan ta ƙara naɗe bakinta ta yi shiru tanani fal a zuciyarta.


Ganin ta tafi wani tunanin daban sai ya ce " Haka ne ba'a mamaki da ikon Allah don haka kar ki
yi mamakin na zo nai man aurenki amma fa na kwangila auren shekara ɗaya nake son mu yi
dake kuma cikin sirri."


Juwairiya ta ɗago kanta da sauri ta kalle shi a wannan karan ba tare da ta ji nauyin sa ba."
Aurena zai yi amma na kwangila mai hakan yake nufi?Sannan kuma cikin sirri to suwa ye ba' a
son su san auren?"

Tambayar da ta yi ma kanta kenan a cikin zuciyarta wanda ba ta san maganar ciki ta fito fili
ba.Ya gyara gilashin idanun sa ya miƙe tare da juwa mata baya.

" Yes abin da kika ji hakan nake nufi kin san ke ba sa'ar aurena ba ne,na tabbata kina tunanin
me ya sa zan aure ki?Kamana ɗan gayu kuma ɗan masu da shi yayin da ke kina talaka kucaka
dake.Ki kalle ni mai aji kama na ban yi kama da wanda zai aure ki ba."

Ya numfasa ya juyo ya na kallonta ganin yadda ta saki baki hanci ido ma'ana ta yi galala ta na
jin tatsuniyar da yazo mata da shi.

" Matata Zainab wacce nake so fiye da komai rayuwata mace mai aji yarinya ƴar babban
gida,Allah bai nufe ta da haihuwa ba ni kuma bazan iya haɗa ta da wata ƴa ɓace ba don na yi
mata alƙawarin bazan yi mata kishiya ba,ga shi ina son na ga ƙwaina a duniya shi ya sa nake
son na aure ki a sirri ki haifa min ɗa ɗaya na ba ta amma a gidana zaki zauna amatsayin ƴar
aikin ta."

Wani irin hajijiya ta ji ya ibeta sai ga shi a gabansa ta zare ido jin a bin da ya faɗa,take ta ji wani
hajijiya zai yarda ita ƙasa ta rintse idanunta,hawaye suka fara turereniya a kan fuskarta da ta
shiga da tashin hankali.

" Allah na roƙe ka ka farkar da ni daga wannan mummunar mafarkin na farka ba tare da na gan
shi kamar yadda yake tsaye a gabana! Ya Allah ka ɗauke ganina da shi na har abada da
kunnuwana su ƙara ji min abin da yake faɗi ba,Ai gara na auri Alhaji Tanimu da na amince na
auri mutumin da nake jin,bayan shi babu wani ɗa namiji a duniya shi ne yake son na yi rayuwa
a gidan shi a matsayin ƴar aikin matarsa.


Wayyo Alla!gara na ga ranar mutuwata don zan fi samun maslaha a cikin ƙabarina da na
amince da buƙatarsa.




Tofa ga dai Baba Sani ya amince shin Juwairiya za ta amince ya auren zai kaya?Ku dai ci gaba
da bibiyar lintafin SAKACINA KO HALIN MAZA.





ƊUBBIN GAISUWA GARE KU SABODA COMMENT ƊIN KU YA NA SAKA NI NISHAƊI.

MAMAN SUDAIS

AISHATU MINNA
FATIMA ZARA JOS
SAHURA NURA RABIN RAINA
NABILA MAMAN SAFWAN
HAMDIYA UMMU ABDULHAKIM








Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Mu haɗu a shafi noma sha
huɗu.Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba 08144072423_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni
mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata
(SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da
irin taimakon da kike bani.



Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/LQfVU1ABdFI14btWRhUB1K



*SAKACINA KO HALIN MAZA?*



*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*

*SADAUKARWA GA:-*

*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

*Page 15*






BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

A karo na biyu ta ƙara gwalalo idanunta." Ina hakan ba zai taɓa yuwu ba!Gara na rayu a cikin
talauci na kuma mutu a cikin sa.Anya ya san me yake faɗi kuwa.
Sai kawai ta nufi hanyar fita ba tare da tace mishi komai ba.
Juwairaah!"

Ya kira sunan ta da sauri tare ƙofar ya kama hannunta wani irin hajijiya ya kama ta wani abu
mai kama da shokin,ya na zagaye jikinta yayin da yake fitowa daga gurin da ya riƙe ta ya na
ƙara wutar sonsa a cikin zuciyar ta.

" Don Allah ka cika ni ba zan iya abin da kake faɗi ba,hakan ya tabbatar min da ka tsane ni ba
ka son ganin farin cikina dama na san ni ba'a sa'ar auren ka ba ne, to amma kaje ka auri mata
masu aji irin matarka ta yadda za ka samu ƴara daga gidan kuɗi,ba irina wanda mahaifina ya
mutu bai bar min komai ba.

Ta faɗa tare da fisge hannunta da sauri ya sha gabanta ya toƙare kofar da take son ta fice,
jikinsa ya yi sanyi ganin kamar ba za ta yarda ba,amma kuma ya zama dole ya san yadda zai yi
ya shawo kanta,saboda amincewar ta ne kawai zai sa ka ta jure duk wani abu da za ta gani a
gidan.

" Nima na so haka na sami mace mai aji kama ta, amma kin san babu wata mace mai aji wanda
zan nema ta yadda da hakan.Kasancewa ta ɗa namiji da kowa ce mace za ta yi burin samu shi
ya sa naƙi nai mar me aji iri na, don na san ba za a kwashe dai-dai da ita ba,kuma kema fa so
nake na ceci rayuwarki daga ƙangin talaucin da kike ciki.
Ya ƙarashe maganar da murya na salon yaudarar shi ya na son ta amince.
Hawaye suka ƙara turereniya a fuskarta ta kalleshi da nufin ta saka wani mugun tsanar shi a
cikin ranta,amma sai ta ji wani madarar son sa ya na ƙara shiga cikin bargon jikinta a duk
sanda ta yi kuskuren haɗa ido da shi.

" Sai ni talaka ko?Ni da Allah bai saka min zuciya na so ba.Ko naƙasun talauci ya na yin tasiri a

zuciya duk lokacin da ta ke son wani?Shi ya sa za ka zo ka cuci rayuwata ta ɗa na kake son na
haifa na ba wata mace na har abada?Don Allah ka fita daga cikin rayuwata na roƙe ka na san
ba za ka samu matsala da ƙanin mahaifina ba,amma ni ba zan amince da mugun nufin ka a
kaina ba.A yau na yi burin dama ban taɓa sanin ka a cikin rayuwata ba."
" Ke ya ishe ki ƴar talaka kawai zaki zo ki na jera min wasu maganganu kamar wani ɗan
ki!Dama ban yi miki dole ba."

Ya faɗa tare da kaucewa ya ba ta hanya ganin hakan ya sa ta zura da gudu za ta fita,dai-dai
lokacin da Baba Sani ya yi gyaran murya."Ya kamata ka wuce abokin ka ya na jira,kawai ka
nemo waliyin ka a duk sanda kake son a ɗaura auren kar ka damu da ita ko amincewar ta"
Da ido ya kalleta ya na gasgata abin da yake faɗi." Kin ji da kunninki abin da kwaɗayayyen
ƙanin mahaifin ki yake cewa?Don haka ina tambayar ki ne don kar ayi ba tare da yaddar ki ba
kizo ki ɓata komai."

Ya zaro waya mai kyau da tsada ya ije mata." Ga shi zan wuce na gaji da wannan kukan nan
naki da kika tasa ni da shi.Fisabilillahi sai kace na zo gidan ta'aziya,duk abin da kika yanke zan
kira sai ko gaya min." Ya miƙa mata kuɗi masu yawa." Ga shi ki je ki yi ma marasa lafiya
siyayya.Ina ƙara gaya miki ɗa ɗaya kawai nake son ki siyar min bayan nan zaki iya auren namiji
wanda ya fini,domin zan ƴanta rayuwarki zan gina ma mahaifiyarki gida na ba su duk wani jin
daɗi na rayuwa.

Shekara ɗaya ne fa kawai za ki yi kina ma masoyiyata aiki in ma kin sami ciki, da wuri zan
ɗauke ki daga gidan kin ga kin huta kenan,sannan ki iya takun ki ba da sani ta zan yi komai ba."

Ya numfasa ya na kallon ta yadda ta yi zuru ta na kallon shi,yayin da zuciyarta ta ci gaba da
bugu cikin tashin hankali.
"kamar yadda na gaya miki haka za ki yi don haka ko kallona kar ki yi in dai ta na kusa da
ni.Kasancewarta ba mai zaman gida ba ne kinga haka zai bamu damar aurenmu ya tafi cikin
sirri."

Ya ce da ita sannan ya fice ya barta a tsaye tamkar gunki sai da ta ɗauki tsawon lokaci sannan
ta yi zaman ƴan bori a ƙasa tare da fashewa da kuka.
" Don Allah karfa ku yi min ƙarya ku dawo fa in ba haka ba wallahi sai na nemo ku duk in da
kuke don ba zan ga samu na ga rashi ba.

Motar su na ɓacewa ya ruga da gudu ya shige ɗakinsa alokacin Juwairiya har ta miƙe ta share
hawayenta za ta fice." Ƴar albarka Juwairiya zo mai ya baki."

Sai kuma ya hangi damin kuɗin da ko ta kan shi ba ta bi ba, ai da sauri ya dafe ya na washe
baki sannan ya miƙa mata dubu biyar ya ce." Gashi maza ki tafi Juwairiya ya gaya miki komai
ko?Ai Allah ya tarfa ma garin ki nono kin huta da auren wannan mutumin,dama ɗan iskan tun
da ya ga na ba shi auren ki ya dai na bani komai,duk da na yi baƙin ciki amma ko ba komai ai

na samu ta sanadin ki rayuwata za ta shiga cikin jerin masu da shi."

Juwairiya ba ta ce komai ba har ta kai ƙofa za ta fita, sai kuma ta dawo ta ce." Ni fa ba zan aure
shi ba haba Baba ka ji tausayina mana!Wallahi in..."

"Rufe min baki banza shashasha!Don ma kin samu zai aure ki wallahi da bai zuba uban kuɗin
nan ba, to ko megadin gidansa yake son ki yi masa ba zan bari ba,ai ke gaba ta kai ki ko banza
a shekara ɗaya zaki rayu cikin daula,ko banza za'a sha zaƙi da maiƙo a rabu da tuwo wanda
shima ba kullum ake samu ba."
Da sauri ta fice jin maganar da yake mata wanda duk cin fuska ce.

Juwairiya ta shiga cikin tsananin hankali tun lokacin da ta fito da ga ɗakin Baba Sani ta kife
kanta ta na wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai saurare.

Yayin da tausayin kanta ya rufe ta ganin mutumin da take matuƙar so ya zo neman ta akan
auren kwangila."Yanzu inna auresa shekara ɗaya za mu yi? Shima tsakanin mu tamkar mage
da ɓera tunna matarsa ta yi katanga a tsakanin."

Abin da take ta faɗi a ranta kenan sai kuma ta share hawayen da damuwa cike a zuciyarta,don
ta rasa yadda za ta kwatanta wannan auren da yake son su yi,amma a ranta ta ƙudira koma me
zai faru sai dai ya faru don ba za ta aure shi ba,ai gara ya barta a cikin tsananin talauci saboda
in talaucin bai kashe ta ba,tsananin son da take mishi da kishin matarsa zai kai ta lahira!
Ko da ta isa asibiti ba yan ta gama girki abin mamaki sai ta ga Baba Sani zaune a can,ya dage
sai zuba ruwan surutu yake yi tamkar wani aku.

Sai Juwairiya ta kasa shiga ta tsaya ta na kallon shi da mamaki ganin yadda yake ta magana
har da dariya ga uban leda da ya siyo musu abu.

Mama shiru ta yi ta na kallon shi da mamaki."Oh ikon Allah duniya juyi-juyi!" Abin da ta ce
kenan cikin tsananin mamakin sa.

"Ƙaraso mana Juwairiya kin ga har na riga ki ai daga gurin aiki sai na taho,ban san kina gida
ba."

A sanyaye ta shigo tare da ije abincin dai-dai lokacin da Baba Sani ya tashi tare da yi musu
sallama ya tafi.

Da sauri Juwairiya ta bi bayan sa ya na ƙoƙarin shiga motar sa ta riƙe murfin motar idanunta na
zubar hawaye " Ba zan aure shi ba gara ya barni a halin da muke ciki,amma ba zan yi aure ba
wanda mahaifiyata ma ba'a son ta sani!Tun wuri ka mai da masa da kuɗin sa ni zuciyata ba irin
naka ba ne!Na san mutuncina ai talauci ba hauka ba ne "

Kau ya gaura mata mari " Baki da hankali kina wasa da ni ke baki san halina,ni murucin kan
dutse ne! In har kika ce ba za ki yi wannan auren ba,kin ji na rantse miki Juwairiya zan iya
kashe ki har da mahaifiyar ki.Don haka in baki bi umurnina ba ki kuka da kanki."

Ya ja motar sa ya barta a nan tsaye cikin tashin hankali sai kawai ta rushe da kuka,sai da ta yi
mai isar ta sannan ta yi shuru ta wanke fuskarta ta shiga cikin ɗakin da Mama suke.

" Ikon Allah abin duniya ba ya ƙarewa kin ga abin mamaki ko.Ai addu'a takobin mumuni ne."
Juwairiya ta ce."Umh Mama."Sannan ta ɗauki filet ta zuba mata abinci.
"Juwairiya bayan fitar ki likita ya zo ya ce in dawo ki je ki same shi,sannan ya ba da takadda
kamar na magani ne."

Ta ce cikin damuwa da murya ƙasa-ƙasa kai da ga ji ka san ta na cikin jinya mai tsanani.
" To Mama bari na je na same shi."
Ta miƙa mata abincin sannan ta fita zuwa ofishin likitan.
"Ok zauna"

Ya ce da ita bayan ta ƙwanƙwasa ta shigo a hankali ta zauna cikin tsoro-tsoro don ba ta san
dalilin da likitan ya kira ta ba.

Ga sakamakon gwajin da muka yi ma mahaifiyar ki nan gaskiya ta na cikin matsala ya kama ta
a canza mata asibiti,saboda zuciyar ta ta kumbura dole a yi mata aiki.
Da sauri Juwairiya ta miƙe tare da zare idanun ta jin abin da likitan ya faɗa." Na shga uku Allah
ka kawo min ɗauki!Mama za'a yi wa aiki!"

Sai hawaye shar-shar a fuskarta ta koma ta zauna kamar yadda likitan ya umurce ta ganin ta
tada hankalinta.

" Ki yi haƙuri! Jarrabawa ce amma kar ki yadda ta ji lalurar da take da shi wannan dalilin ya sa
na so namiji ya zo na gaya mishi,amma sai ta nuna ke ɗin dai zan gaya ma wa."

Da sauri ta miƙe tare da ficewa daga ofishin har ta kai ƙofar ɗakin da Mama ke kwance, sai
kuma ta ja da baya ta tsaya kamar wata zararra!Tuna likita ya ce kar ta gaya ma Mama komawa
ta yi wani guri ta na son ta yi kukan amma ba hawaye sai tuƙuƙi da zuciyarta take yi mata.

Ta ɗauki tsawon lokaci sannan ta koma cikin ɗakin.Da daddare Juwairiya ta kasa bacci sai
juye-juye take,abin duniya ya haɗu ya yi mata yawa ji take kamar ta ɓace a cikin duniyar.

Kwana biyu kuma sai Ibrahim ya fara ciwon ƙafa wanda in ya na yi yake fita cikin hayyacin
sa,don har tsuma yake na tsawon lokaci bai farfaɗo ba.Abin duniya ya yi mata yawa ga tunanin
A.m da yake son ta baƙunci kabarin ta kafin mutuwarta,duk ta yi fari ta rame kamar wacce ba ta
da jini a jikinta sai ƙashi da ya zama ado a jikin ta.

Zaune take a gefen Mama ta zura mata ido ta na tausayin halin da suke ciki,don ko wannen su
da jinyar da yake yi.Hannu ta sa ta yarfe zufan dake goshin ta,wanda yake tsatstsafo mata duk
sanda ta tuna da A.m.
" Inna lillahi."
Ta ce tare da miƙewa ta tsaya bakin windo sai hawaye." Wai dama haka ciwon so yake?Allah
na roƙe ka ka cire min soyayyar son maso wani a cikin rayuwata,yayin da nake tsananin son sa
shi haɗuwar mu ya zama dama a gare shi ya faranta ma masoyiyar sa rai.

Likitan ne ya yi sallama ya shigo wanda ya saka Juwairiya ta juyo da hawayen dake zuba a
fuskarta,ya tausaya mata sosai amma sai ya miƙa mata takadda ya ce." Ga shi Juwairiya an
baku sallama duk da jikin mahaifiyar ki bai warke ba,amma baku da kuɗi kuma mai asibitin ya
na buƙatar kuɗi."
Juwairiya da ta ji ta daskare amma sai ta kai hannu ta ƙarɓa jikinta a sanyaye ba tare da tace
mishi komai ba,ita zuwa yanzu hawaye sun ƙare da ga fuskarta sai wani azaban raɗaɗin baƙin
ciki da take kurɓar ruwan sa mara daɗi a cikin zuciyarta wanda yafi na guba illah.

Sai ta fara haɗa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login