Showing 12001 words to 15000 words out of 56747 words
Chapter 5 - SAKACINA KO HALIN MAZA Book Complete .pdf
ita ina wannan wayar ta na ƴar gidan Malam Shehu kuma me za ta ce ma Anty Naja."
Kamar ya san me take tunani sai ya kaɗa kansa yace."Karki damu na san me kike tunani zan yi
mata bayani.Kuma ba ni da nufin na cutar dake alkhairi ne zuciyata,don Allah ki karɓa kin san
babu kyau mai da hannun kyauta baya."Yace da ita ya na wani marairaice fuska sai kace
maraya.
"Gaskiya ka bar shi bana so ina gani a matsayina na ƴar aiki bai kama ta na riƙe irin wayar nan
ba,don daga ganin ta na san za ta yi tsada kuma in Anty Naja ta gani me zan ce mata?"Sai ta
tsinci kanta da furta hakan yayin da takai aya ta tsare shi da ido ta na tambayarsa.
Shi ma ya ɗan razana jin tambayar da ta yi mishi kansa ya ɗan sosa ya kafe ta da idanunsa
yace."Haba Juwairiya kina abu kamar ba mace ba,kice mata saurayin ki ya baki mana."
"Ka yi haƙuri don Allah ba na son kyakykyawar alaƙar mu da matarka ya ɓace,kai sheda ne
mace ce na ƙwarai kuma ta yi min halacci."Tace dashi da murya raunanniya yayin da hawaye
suka fara turereniya a fuskarta.
Ganin haka sai jikinsa ya yi sanyi ya ɗan yi shiru ya na nazarin maganar ta zuwa can ya ja
numfashi yace."Laifi ne don nace ina sonki ni fa bani da nufin na cutar dake,kawai ina son ki
zamo uwar ƴaƴana ne."Tsananin tsoron da ta nuna ta na me gwalo ido sai abin ya ba shi dariya.
Tafe take cikin sauri bayan ta tashi daga aikin zuciyarta tunanin sabon halin da mijin madan ɗin
ta ya fito dashi,yake damun ta har ta fara tunanin ko ta aje aikin ƙila in Anty Naja ta gane ba
lalle-lalle ne ta fahimce ta ba.Kallon tsadaddiyar wayar dake riƙe a hannunta da ya bata take
kallo wanda ya rantse ya maya in har ba ta ɗauka ba to zai ba wa Antynna ta da take tsoron
sani ta bata da kanta.
Abin mamaki dai-dai za ta shiga gida ta ji an dameta da hon,kamar ba za ta juya ba sai kuma ta
juya in da ta ga mijin Anty Naja a cikin mota ya na ɗaga mata hannu,wato biyo ta ya yi ba tare
da sanin ta ba ya ga gidan su.Tsabar takaici ba ta kula shi ba ta shige cikin gida.
Koda ta gaya ma Mama abin da ke faruwa hankalin Mama ya tashi ƙwarai ta yi shuru kawai ta
na jinjina abin a ranta,ta ɗauki tsawon lokaci ba tare da tace komai ba zuwa can ta nisa
tace."Ina ga ko haƙura da aikin nan tunna mun sami jari Juwairiya,ni nafi son kiyi aure shine
mutuncin ki.Kin san maza basu da ta ido zai iya furtawa hakan ya jawo miki matsala gara mu yi
rabuwar mutunci,in ban da shi ma ina ke ina kishi da Anty Naja mace me mutunci."
"Nima haka na gani Mama hankalina ya tashi ƙwarai."Tace da ita ta na juya wayar da ya ba
ta."Kinga gobe ki mayar mishi da wayar shi,kice ni na ce ki mayar masa na tabbata ya tsorata ki
ne amma ba zai yi gigin bata wayar ta baki ba,in dai ba ya na so ya kira ma kansa ruwa bane."
"To Mama in sha Allahu zan mayar masa,ni ma bana son na riƙe irin wayar nan don Allah kaɗai
ya san abin da Baba Sani zai faɗawa jama'a."
"Haka ne Allah ya fishi."Ta bata amsa tare da miƙewa don ɗauro alwalar kiran sallar magariba
da ke ta kwaɗawa masallacin kusa dasu.
Washegari da ta je gidan bayan fitar matarsa ya dawo kamar yadda ƴan kwanakin yake mata,ta
na ganin shi ta ƙara tamke fuska kamar ba ta ganshi ba ta ji gaba da aikin ta.
Ta yi tunanin zai yi mata magana amma sai ta ji shiru na tsawon lokaci,da sauri ta waigo sai ta
ga ita yake kallo kamar bai taɓa ganin ta ba.Miƙa masa wayar ta yi tace."Mahaifiyata tace na
dawo dashi,kuma don Allah ka yi min rai ka fita sabgata domin ba za ta amince aci amanar Anty
Naja ba." "Ni kuma sai na shiga wani hali ko?Wannan dalilin ya sa kika ƙi ɗaukar wayata jiya da
daddare sai ma kika kashe wayar.Dama masoyi ya na zama maƙiyi Juwairiya?"Ya ƙarashe
maganar da sigan tambaya,a yadda ya furta maganar sai ta ji ranta babu daɗi,ganin namiji mai
natsuwa ya na mata magiya akan ta so shi.
Wani irin abu ta ji a ranta in da ace matarsa ba ta shiga tsakani ba,babu yadda za'ai taƙi auren
shi sai dai ba za ta zama butulu ba.Ganin taƙi kallon sa bare ya saka ran za ta yi magana,sai
ma hawaye da ta soma ganin haka ya ɗauki wayar da ta ije mishi ya fice ya san ta na
sonshi,amma tsoro ne ya cika mata zuciya in ko haka ne zai je har gida ya nemi aurenta.
Kwana biyu haka suke wasar ƴar ɓuya ganin haka sai ya dena shiga sabgar ta ko dawowa gida
ya dai na,ya na shirye-shiryen zuwa gidan su ya nemi auren ta.
Ranar wata yammacin talata ta tashi daga aiki kasancewar an yi rana sosa,da yake lokaci ne na
damina garin ya fara haɗa hadari.Juwairiya sauri take ta isa gida saboda ta kauce ma baƙin
hadarin da yake tasowa ya na canza garin da yake duhu sosai.
Hon ta ji an danna mata ta waiga sai ta ga Daddyn Abnaj ne ya na mata murmushi yace."Maza
shigo na kaiki gida kar ruwa ya zane min masoyiyata."Ta yi kamar ba za ta shiga ba amma
ganin har an fara iskar hadari ya sa ta buɗe gidan baya ta shige,tare da haɗe girar sama da
ƙasa don karya tambayeta dalili
Hakan sai ya ba shi dariya sosai bai ce komai ba suka fara tafiya, sai ya sai ta madubin motarsa
dai-dai in da take zaune."Wato na zama direban ki ko."Ya jefa mata tambaya dai-dai lokacin da
ya fara tafiya.
"Ina wuni."Tace ba tare da ta amsa mishi tambayar ba.
"Ba zan amsa ba ina fushi."Yace ya na kallonta ta gilashin motar.
Ba tace mishi komai ganin hakan ya sa ya fara magana da murya mai taushi."Matsalar ƴan
mata kenan da kun ga namiji ya na ƙaunarku,shikenan kun samu zaren ja amma babu komai
nima lokacina ya na nan zuwa,don na fara hango sona a cikin ƙwayar idanunki."
Ta ɗan saki ranta saboda ta fara sabawa da shi ya wan janta da ɗawainiya da yake musu ta ja
numfashi ta sauke ta fara magana da cewa."Ku kuma maza ba amana ka san kusancin dake
tsaƙanina da matar ka,amma ka bijiro da wannan lamari haba kai ma ka auna ka gani bai dace
ba."
"Kija min aya da ya hana hakan ko hadisi."Ya faɗa a raunane kuma a taƙaice.Babu amma
Bahaushe ya na girmama al'adarsa hakan ya saɓa ma al'adar Bahaushe."Sitiyarin motar ya
buga da ƙarfi yace "Kin ji ko in da karatun naki ya tafi ina miki zan can addini kina yi min wata
magana can,kawai na gane bakya sona ki ce na haƙura kina da wani hakan zai sa na bawa
zuciyata haƙuri duk da na san za ta shiga wani hali."
Yanayin da ya yi maganar sai ya bata tausayi amma ta san abin da yake so ba mai yiwuwa ba
ne.Murfin motar ta ɓalle za ta fita ganin sun ƙaraso gida ya yi parking,sunan ta ya ƙira da wata
irin murya.Ta waigo ba tare da tace ƙala ba,sai ƙasa da kanta da ta yi wato alamun ta na
sauraren sa. "Ki yi tunani zuwa ƙarshen sati nan nake so na turo magabata na,ina ganin za ki dakata da
akin nan kafin kizo a matsayin ƙanwa kin ga sai ki ɗora daga in da kika tsaya ki na samun lada
rututu!
Ɓalle motar ta yi ta fice dai-dai lokacin da ya miƙa mata ƴan rafar ɗari biyar kusan kimanin dubu
ishirin ba tare da ta karɓa ba ta fice,musamman da ta ga Baba Sani tsaye a ƙofar gida shi da
wani mutum ya zura mata ido.
Ganin jikinta ya soma rawa ya kalli in da take kallo,sai hakan ya yi mishi daɗi domin faɗuwa
tazo dai-dai da zama,ya buɗe murfin motar ya fito ya nufi su Baba Sani dake kallon Juwairiya
kamar ya shaƙe ta.
Da sauri ta matsa za ta bi ta bayansa ta shige cikin gidan da ya bake ƙofar,amma sai ya daka
mata tsawa tare da jan hijabinta."Ina zaki ƴar iska maza dawo,iskancin naki ya kai har a kawo ki
gida a mota.Kawai sai ya saka salati da ƙarfin sa ya ci gaba da cewa."Inna lillahi gara da ka
mutu Yaya Ahmed in da ka na raye Juwairiya ita za ta ƙashe ka.Karuwa kika zama fa ke ko
kunya duniya ba za ki jiba tunna baki ji na Allah ba."
"Ashsha!Subuhanallahi haba Malam ya za ka dinga jifan ta da waɗannan muggan
kalamai?Iya sani na Juwairiya yarinyar kirki ne ta ɗaɗe ta na tare damu ta na mana aiki.Yanzu
haka mun daidaita ne nake son ka bani auren ta,ma'ana na yaba da hankalinta ina sonta."
Wayyo Allah faɗin haka da ya yi wato ya na son Juwairiya ji Baba Sani ya yi kamar ya watsa
mishi fetur ya kyasta ashana domin baƙin cikin sa biyu ne a kan maganar.Na farko ta ya ya za
'ai mutum me hannu da shuni yace ya na sonta,sannan kuma baƙin kishinta ya taso ya lulluɓe
mishi zuciyarsa kawai sai ya ƙara kuka ya na faɗin ma abokin da suke hira cewar."Kaji ko wai
na ba shi aurenta bayan ya gama iskanci da ita ni nasan ya na naɗe tabarmar kunya ne.Amma
ta ya ya zai auri mazinaciya!Ba Juwairiya dake tsaye ta na kuka ba har ta Daddyn Abnaj sai da
yaji wani irin abu ya soke shi ya rintse idanunsa ya na jin kamar ya shaƙo wuyar Baba
Sani,take ya fahimci wani abu wato na zaman ƙunci da suke yi iya zaman su da ita bata taɓa
basu labari ba,duk da ya san cewa ba lai-lai bane ta gaya musu kasancewar ta na da zurfin ciki.
Ya kalli Juwairiya da ta ƙara sautin kukan ta ganin mutane sun fara taruwa Baba Sani yaci gaba
da magana da ƙarfi ya na nanatawa,sai ta ruga da gudu dai-dai lokacin da Baba Sani ya kai
mata bugu a bayanta.
Ba ta san ya suka ƙare ba ya dai shigo gida ya na ta faɗa tare da ja mata jifa'i kala-kala,
Juwairiya ta so ta tanka saboda abin da ya yi mata a gaban mutumim da yake girmama lamarin
ta,amma Mama ta hana duk san da ya gaya mata baƙa ta buɗe baki za ta yi magana Mama za
ta hana ta,har ya gaji da rashin mutuncinsa ya fice.
A ranar Juwairiya ta ci kuka sosai ta ji ta ƙara mugun tsanar shi a ranta.
Washegari ganin taƙi shiryawa taje aiki Mama ta shigo ɗakin ta tsaya ta na kallonta
tace."Juwairiya ba zaki je aiki bane naga rana ta yi."
"Na haƙura da aikin Mama gara na zauna a gida dama kin san mun yanke shawarar na daina
zuwa,sai ga abin da Baba Sani ya yi min a gaban shi Allah kunya nake ji matuƙa.Karuwa ya kira
ni."Sai kawai ta saka kuka ta na jin zafin kalmar da ya danganta ta da ita."
Mama a ranta har tafi Juwairiya damuwa amma sai ta ɗan gyara murya tace."Ki yi haƙuri komai
lokaci ne watarana sai ya yi dana sani,amma da kin daure kije kila ma ya shafa miki lafiya don
na tabbata ba zai ƙara miki maganar soyayya ba,ganin yadda ya tozar taki."
"To Mama shikenan a haka rayuwata za ta ƙare duk wanda ya fito neman aurena sai Baba
Sani ya ɓata lamarin gaskiya na gaji."Tace cikin hawaye yayin da ta tuna katoɓarar da ta yi na
faɗin hakan,kamar ta nuna ta na son auren kenan sai ta zari hijabinta da sauri ta fice zuwa aiki.
Ko da ta isa bata sami Anty Naja ba duk da ta san dama abu ne me wuya ta same ta,abin
mamaki ta yi sallama ta shiga fuskarta babu walwala,sai ta same shi zaune akan one siter ya
zuba tagumi ya na kallon hanya,ganin ta ya saka shi sakin ajiyar zuciya mai ƙarfin gaske.
"Shigo mana Juwairiya hankalina ya tashi matuƙa na yi zaton wannan mara kirkin Baban nan
naki ya hanaki zuwa "Yace da ita ganin ta dogare a bakin ƙofa,ta ɗan tsaya ta na kallon shi sai
kuma ta ƙara haɗe fuska haushin sa take ji don shi ya yi shishshigi a lamarinta,har ya saka Bab
Sani ya yi mata wannan tozarcin.
"Gaskiya ban ji daɗin abin da ya faru ba!Haba sai kace ba ƙanin mahaifinki ba.Lamarinsa ya
tsoratani baƙin cikina yadda yaƙi yadda da maganata akan ina sonki da aure.Kawai ki gaya min
dangin ku naje can na nemi aurenki."
Yace da ita ya na kare mata kallo don ya fahimci a wani hali take,takaici ya kamata jin abin da
ya faɗa sai ta miƙe hanyar kicin ba tare da tace mishi komai ba.
Gabanta ya sha tare da riƙe mata hijabi yace."Na fa fara ƙosawa da halin ko in kula da kike min
haba waike dutse ne a ƙirjin ki ba zuciya ba!Ki ji tausayina ko don halin da kike ciki ki zaɓe ni a
matsayin mijin ki hatta mahaifiyarki ba za ta zauna a wannan gida ba.
Takai hannu da nufin ta ƙwace hijabinta sai ya riƙe hannun cikin kalar tausayi ya na jin kamar ya
yi mata kuka,ganin sam ba ta da rangwame akan soyayya.Baki ta buɗe da nufin ta yi magana
sai suka ji sallamar Anty Naja ta shigo da sauri da alamun gajiya tare da ita.
Da sauri ya saki hannunta ya matsa gefe ya na zare ido,ita ma cikin tashin hankali ta tsaya ta
kasa haɗa ido da ita ta na jiran tashi n hankalin da za ta fuskanta.
Amma sai dukansu ta basu mamaki ta faɗa kan kujera ta na lumshe ido "Wash Allah! Na gaji
matuƙa Juwairiya bani ruwa don Allah."Tace cikin sakin fuska ba tare da ta fahimci komai ba."
Da sauri Juwairiya ta shige kicin ta na mamakin sokanci irin nata haba ta ya ya za'ai tace bata
fahimci komai ba.Bayan ta kawo mata ruwan ta haɗo har da abin motsa baki,ta shige kicin ta ci
gaba da aiyukan ta can sai ga shi ya shigo yace."Ina jiranki in kin gama zaki tafi ina hanyar da
nake tsayawa sai mu ƙarashe tautaunawar.
Ganin ba zai saduda ba Mama tace ta haƙura da aikin in ta bata kuɗin aikin ta na wata haka
kuwa aka yi,bayan ta yi mata albashi ta ƙara mata harda zannuwa masu kyau biyu nata sai
ɗaya Mama ta ɗinka,kasancewar suna da biki a family ɗin su kuma tare da Juwairiya za su tafi
garin Kano.
Hankalin Anty Naja ya tashi matuƙa ganin ba ta zo aiki ba,ta shiga ruɗani ta din ga tunanin ko ta
yi mata wani abu amma bata gano ba.Shi ma hankalinsa ya tashi sosai duk da yaso sai sun
gama daidaitawa a tsakanin su sai tabar aikin,amma ta yi sauri gashi ya na son yaje gidan ya
na tsoron tijararren ƙanin mahaifinta
Sai ya azalzala ma Anty Naja ta shirya ya kaita har ya na mata barazana da ya na nan akan
bakan sa in dai ba Juwairiya ba sai dai ta bar aikin,ai kuwa ba shiri ta shirya suka taho ya ijeta a
kofar gidan ta shiga ciki ya zauna da yaransa ya na jiran ta fito,burin sa ya ga Juwairiya.
Juwairiya na tsakar ta na girki Mama ta na zaune ta na jan carbi ta yi sallama ta shigo,da sauri
Juwairiya ta saka hannu ta rufe fuskarta ta na dariya.
Anty Naja ta harareta ta na kallon Mama tace."Da ma Mama haka Juwairiya take bata da kirki?
Kawai ta guje mu ba tare da mun yi mata wani abu ba,hankalina ya tashi ƙwarai Mama gaskiya
ba ta kyauta ba."
Ta ƙarashe maganar ta na kallon Juwairiya sannan ta ɗora da cewa "Ko mun yi miki wani abu
ne?Ai gaya mana ya kamata ki yi ba ki ɗauke kafafunki ba.Ni da yara da Daddyn su Abnaj duk
hankalin mu ya tashi."
Mama ita ba tace komai ba tace komai ba sai dariyar yaƙe take mata,bayan sun shiga ɗaki
suka yi gaisuwa a tsakanin su sanann shiru ya biyo baya.Sannan Anty Naja ta katse shirun
tace."Me ya faru Mama kwana biyu bata zo aiki ba na yi tunanin ko wani ba lafiya,amma da
nazo naga kowa lafiya.Ko na yi laifi ne Mama."
Matuƙar kunya sai ya lulluɓe Mam ta ji kamar ta nitse ta rasa yadda za ta fara mata bayani,har
Juwairiya ta yi sallama ta shigo,ganin Mama ta kasa mata bayani ta kalli Juwairiya tace."To ko
auren ne ya zo,in kuma wannan ne Mama ai ni ce me haɗo kayan ɗaki ko?"Ta ƙarashe
maganar ta na me tsigar tambaya. I ta dai Juwairiya ba tace komai ba ta na ta wasa da yatsunta,Mama ta daure tace."Ba shi bane
ban san dai yadda zaki ɗauki zancen bane shi yasa na kasa sanar miki,amma ranar wanka ba'a
ɓoyan ciji."
Gaban Anty Naja ya faɗi daram!Sai ta ji zuciyar ta ta raya mata lai-lai a kwai abin da suke ɓoye
mata,duk da bata san ko menene ba amma taji ta firgita Allah ya sa ba wani lamari me girma ya
faru ba.
Ganin ta yi shiru ba tace komai ba jikinta ya yi sanyi Mama dai ta daure tace."Dama mijinki ya
bijiro da wata magana ya na son auren