Showing 1 words to 3000 words out of 33266 words

Chapter 1 - YAN UBANCI COMPLET BOOK By Maman Afrah.doc

??ࡱ?>?? ?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?F?WordDocument????1?0Table????????? Data
???????????????????? P???KSKS?1??x???????rr????4?r r r r r r r r t $???*rr r r ????r ?r ??r r ?  ?'AN UBANCI

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

Godiya da ya yabo sun tabbata ga Allah madaukaki, tsira da aminci su tabbata ga Annabin rahma (S. A. W).
page 1

Malam Buba mai almajirai malami ne da yake koyar da almajirai a k'auyen kukayasku dake Maigatari L.G a Jihar Jigawa, Malami ne da ya yi suna ya shahara sosai a cikin ?auyen na Kukayasku da ma wasu k'auyukan da ke mak'otaka da kukayasku, kai har ma da rugage da ke kusa da nesa kai har ma daga kauyukan Niger irinsu garin isa,Dogo dogo, Shakunu da dai sauransu. Duk da cewa su ma k'auyukan na da mayan malamai amma shahara da kuma tsayuwa tsayin daka na malam Buba ya sa su ke kai masa yara almajirci. Malam Buba yana da matan aure guda biyu uwar gidansa itace Ishalle sai kuma amarya mai suna Alawiyya, y'arsa d'aya a duniya mai suna Nana y'ar gidan Ishalle ce dan ita amaryar Allah bai ba ta haihuwa ba. Suna zaune lafiya da iyalansa kuma yana kula da su kamar yadda ya kamata. A kwana a tashi sai matarsa amaryar ta nemi ya sawwak'e mata sabo da tana so ta je wani wurin ta yi aure ko Allah zai bata rabon haihuwar, haka Malam Buba ya saki Alawiyya ba dan ransa ya so ba sai dan kar ya shiga hak'k'inta domin idan bai amince ba kamar ya tauyeta ne tun da tana ganin kamar rashin haihuwar daga gareshi ne , dan tun da ya haifi y'a d'aya , shiru ka ke ji. Yanzu yarinyar zata kai shekara takwas. Duk da ya nu na mata duk a in da ta ke sai Allah ya nufe ta da samun haihuwar tukunna zata haihu amma haka ta matsa ya sawwak'e mata ta je ta yi wani auren. Bayan shekara d'aya Malam ya sake auro wata matar mai suna Kande, bazaware ce aurenta uku amma bata tab'a haihuwa ba.Kande wata masifaffiyar mata ce wacce tsabar fad'anta ya sa mazan ke sakinta, Malam Buba bai yi wani bincike ba akan ta sabo da ta nuna masa ita mace ce mai ladabi da sanin ya kamata, wanda a zahiri kuma ba haka bane kawai buge ne.

Bayan Kanden ta tare da farko zama kamar abin arzik'i, sai daga baya ta fito da halinta na asali daman an ce mai hali baya canjawa.Rashin mutunci kala-kala Kande ta tsiro da shi wanda hakan ya matuk'ar sanya Ishalle a damuwa domin kullum ba su da zama lafiya kai hatta da Malam da almajiransa basu tsira ba daga rashin mutuncin Kande. Haka zaman ya cigaba da kasancewa babu dad'i babu dad'ad'awa, sam Malam Buba ya gaji da fitinun Kande gashi ba yadda son ya sake ta gudun kada mutane su d'aukeshi mutum mai auri saki. A kwana a tashi haka rayuwa ta kasance gaba d'aya gidan ta zamewa Ishalle kamar wani kurkuku gashi ko Nana bata son zama a gidan sai dai ta je mak'otansi, har abin ya kai Ishalle ta daina zama a tsakar gida sai dai a d'aki in ba wani Abu za ta yi ta bata ko k'aunar fitowa tsakar gidan da sunan ta zauna tasha iska. Malam ma sabo da masifar Kande sai da zaman gidan ya zame masa kamar kufai.

Bayan shekara d'aya matan na Malam dukansu Allah ya azurta su da samun ciki, Malam ya yi murna sosai dama samun wannan k'aruwa duk da hali irin masu Kande amma hakan bai sa ya ji ba dad'i a ransa ba damuwa samun cikin Kanden sai addu, a da yake Allah sauke su lafiya. Kande kam ta yi matuk'ar bak'inciki ciki da Ishalle ta samu ciki domin so take ta samu ita kad'ai dan ta yi ta haihuwa sabo da gadon dan Malam Buba akwai gonaki da shanaye d'a sauran Dabobi wannan dalilin ne ya sa mazan Kande ta amince da aurensa ba wai dan kasancewarsa Malam ba ita wannan ba damuwarta bace. Tun da cikin na su ya tsufa Kande ta dinga bin malamai da bokaye tana so ta salwantar da abin da ke cikin Ishalle, dama tun yana k'arami take ta son a zubawa Ishalle amma hakan ya gagara.cikin yawon Malaman nata ne ta had'u d'a wani boka wanda ya yi mata wani asiri ta biyashi mak'udan kudad'e dan ya gaya mata mai zai faru, haka ta dawo gida da farinciki.A haka har ita Kanden ta haifi d'iyarta mace duk da ta so haihuwa namijin domin gadonsa ya fi yawa, ranar suna aka sanyawa yarinya Ikilima. Bayan sati uku da haihuwarta itama Ishalle ta fara nak'uda, tun tana yi d'auke k'arfinta har dai ta galabaita, ita kuma kande tana d'akinta tana dariyar k'eta.Malam Buba kuma yana d'akinsa ya hau buzu yana ta addu, a Allah sauketa lafiya. Gozomar da zata karb'i haihuwar ce take ta mata sannu a haka har dai haihuwar ta zo gadan -gadan, amma me dai -dai fitowar kan d'a me gozoma zata gani wani k'atoton kan miciji ne ya kawo kai, Dan sauri Gozomar ta ja da baya tana salati ita kuma Ishalle wahala ta isheta bata ma san meke faruwa ba. Kafin me miciji yana fitowa zilululu tsayinsa ya kasa k'arewa ai da gudu Gozomar ta fito daga d'akin ta nufi turakar Malam Buba hankali a mugun tashe, haka ta kira Malam Buba ya fito da sauri ya nufi d'akin Ishalle hankali a tashe dan ya d'auka ma Ishallen ta mutu ne dan gozomar d'akin kawai ta ke nunawa ta kasa masa bayani tsabagen rud'ewar da ta yi. Malam Buba na shiga d'akin idanunsa ya sauka akan wani dank'areran bak'in maciji a gaban Ishalle da take a mugun tsorace ta takure a wuri d'aya sai ruwan hawaye ke zuba kamar famfo.

YAN UBANCI
NA


MAMAN AFARAH



K'arasowa Malam Buba ya yi tsakiyar d'akin bakinsa d'auke da addu, a, yana kallon micijin da yake kaiwa tsakiyar d'akin wani irin mugu mugun Sara na ban mamaki, so yake ya fita ya d'akko wani ruwan addu, a a d'akinsa domin zai yi amfani dashi amma kuma zuciyarsa ba ta so ya tafi ya bar Ishalle da macijin a d'akin Dan gudun kar ya sareta domin girman miciji ya wuce misali tabbas zai cutar da ita dan da ganin macijin kasan cewa ba na lafiya bane. Ganin micijin ya tunkaro inda ya ke yasa yake ja da baya domin hatta idon macijin jajawur ya ke kamar garwashin wuta,Malam Buba nan take ya shiga karanta addu, o, i dan tunda yake bai tab'a ganin maciji mai girma da suffa irin tarbiyar wannan babban, dan har wani irin gashi ne a jikinsa fari tass kamar furfura, Kande tana tsaye a jikin labule tana hango Malam ta windon d'akin Ishalle ya wani rabe a jikin bango bakin nan sai motsi ya ke alamar ana janyo addu, a sosai ta ke dariya marar sauti har da hawaye dan dama boka ya fad'a mata cewa miciji Ishalle zata haifa domin ya dad'e da sanya aljannu sun narkar da jinjirin d'a ke cikin Ishallen sun ajiye k'aton maciji.

Malam Buba so ya ke ya d'akko ruwan addu, a a d'akinsa wanda zai yi amfani dashi shi wajen yiwa macijin addu, a amma kuma ba dama, nan take ya shiga k'walawa Kande kira domin ta d'akko ruwan a d'akinsa amma Kanden ta k'yaleshi ga macijin ya gama zuwa dab dance shi neman saransa ya ke, da ya gaji da kiran Kanden sai ya shiga kiran gozomar, gozoma tana wajen zaure a tsaye kamar ka ce kulle ta ce cass dan ma tana tausayin Ishalle sabo da macece mai hak'uri da dattako ga sanin ya kamata amma da wata ce zata haifi maciji da tuni ta tsufa a gidanta. Haka ta zo ta tsaya daga bakin kofa Malam Buba ya fad'a mata ta d'akko masa wata gora a rataye a jikin bango a d'akinsa haka ta d'akko ta zo tana d'ari - d'ari ta mik'a masa ta window.Malam karb'a ya yi ya fara k'ok'arin bud'ewa ,yana gama bud'ewa ya tsiyayo ruwan a hannunsa ya yi bismilla ya watsawa micijin nan take micijin ya yi wani irin k'ara mai ban tsoro, sake tsiyayo ruwan ya yi ya karanta ayatul kursiyyu ya k'ara watsawa micijin sai kawai Malam Buba ya ga idanun macijin sun koma koraye yana wani mirginawa a tsakar d'akin da Malam ya watsa masa a karo na uku sai kawai ya fara hayak'i ya ke zama kamar toka,a take tokar ta ke bin kofar d'aki har sai da ya zamana babu ko d'igon sauranta. Gozoma da ke wajen zaure a tsaye tana ganin ikon Allah bare Kande da take jin kamar ta je ta shak'e Malam Buba domin so ta yi micijin ya kashe Ishalle da Malam d'in in ya so sai ta ci gadon ita kad'ai dan ita bata MA zancen Nana dan har mantawa take da ita Dan bata fiya zaman gidan ba kullum tana mak'ota

YAN UBANCI
NA

MAMAN AFRAH


Malam Buba ya yi matuk'ar tashi tsaye da addu, a sabo da abin da ya gani ya matuk'ar gigitashi, ganin abin da Ishalle ta haifa ya san sihiri ne sai dai duk da an ce zato zunubi ko da ya zama gaskiya amma tabbas babu wacce ya ke zargi sai Kande dan ita ce za ta iya aikata hakan. Tun daga wannan ranar Ishalle ta k'ara tsorata da lamarin Kande dan ita yanzu kwata-kwata bata son abin da zai had'ata da Kande ko yayane duk da irin zaman da suke amma a haka Kande ta maida Ishalle y'ar raino, ko yaushe za kai samu Ikilima a wurin Ishallen ko kuma in Nana tana nan ta rik'eta wani lokacin ma Nanar ake gayawa su fita mak'ota dan Lokacin Nana tana dariyar shekara goma.


BAYAN WATA TARA


Lokacin cikin Ishalle ya tsufa dan bata wani dad'e da haihuwar micijin wannan ba ta samu rabo,haka wannan lokacin ma Kande ta dinga bin malamai da bokaye akan a zubar da cikin tun yana k'arami amma ina k'arfin addu, a da Malam Buba da Ishalle suke yi ya hana afkuwar ayyukan da Malaman ke yi. Dan Kande har wurin bokan da aikinsa ya ci wancan karan ta je amma ya koreta yace ba zai yi na sabo da wancan da ya mata ta bari an k'ona musu aljani dan haka bai ma saurareta ba. A haka cikin ya isa haihuwa ai kuwa. Ishalle ta santalo d'iyarta zuk'ek'iya mai mugun kyau gata fara tass d'a ita, bak'inciki kamar ya kashe Kande amma haka ta daure dan akwai k'udurin d'a take da shi a gaba.

An yi suna yarinya ta ci suna Hindatu, a lokacin Ikilima tana dariyar wata goma a duniya. Haka rayuwa ta ci gaba d'aya kasancewa a gidan Malam Buba, dan sai ya zamana Ishalle ke d'awainiya d'a duka yaran daga Hindatu har Ikilima dan dai yanzu abin da d'an sauk'i sabo da Kande bata fiya zaman a gidan ba idan ta ajiye Ikilima ta shiga gari yawo sai a mance ma da ita,Malam Buba har ya gaji da al, amuranta, amma ita kuma Ishalle ta ji dad'in hakan dan har ga Allah sun fi sakewa ita da yaranta, dan ko kad'an bata damu ba damuwa bar mata Ikilima dan take yi dan itama yarinyar tafi sakewa da Ishalle kuma tafi samun kulawa.


BAYAN SHEKARA UKU

A lokacin Ikilima tana da shekara hud'u Hindatu kuma na da shekara uku amma idan ka gansu zaka d'auka sa, anni ne, dan kan su d'aya sai dai Ikilima bak'a ce yayin da Hindatu take fara tass kyakkyawa ajin farko duk kayan da aka sanya mata sai sun mata mugun kyau, amma Ikilima sai k'aton goshi gata bak'a ba zaka tab'a had'a Ikilima da Hindatu ba wannan dalilin ne ya sa Kande ta k'ara hasala ta k'ara tsanar Ishalle da d'iyarta Hindatu dan yanzu da Nana dan sun yiwa d'iyarta rata ta ko ina.Yanzu ko d'akin Ishalle Kande bata barin Ikilima ta je dan ta koya mata komai duk da yarinya ce amma kuma tana rik'e duk abin da uwar ta fad'a mata dama gata fitsararriya zagi kwa tun da bakinta ya bud'ewa ya haddace shi kala-kala kamar karatun fatiha, dan idan Ikilima ta lailayo zagi za ka yi zaton wata k'atuwa ce ta yi, gashi kullum Kanden burinta ta cusawa y'arta tsanar y'an uwanta tana nuna mata ba d'aya suke ba, tana nuna mata ba uwa d'aya suke ba kowa uwarta da ban shi Malam Buba dama yanzu ya zama bashi da iko da gidan dan Kande ta gama barbad'a masa magani ya cigaba a abinci. Ko makarantar allo da ake koyawa yara karatu a k'ofar gida Ikilima bata zuwa kuma ba laifin kowa bane Kande ce ta hanata zuwa sai dai ta zaunarta a d'aki tana koya mata yadda zata je cin zalin Hindatu dan ita babu ruwanta ko fad'a irin na yara bata it's ba Kuma ma ba tarbiya Ishalle bace nunawa yaro yana ci zalin d'an uwansa dan ko Nana da take da shekara goma sha uku Ishalle bata nuna mata ba ta ci zalin Ikilima ko kuma ta yiwa Kanden rashin kunya ko k'iwiya, kullum tana nuna mata d'aya suke da Ikilima da Hindatu duk y'an uwana ne basu da wani banbanci.


Bayan shekara hud'u aka yi bikin Nana da wani saurayinta d'an cikin garin Megatari, mai suna Surajo, bikin da Kande ta shiga ta fita dan kar ayi amma kuma Allah ya nufe sai an yi haka aka yi na dan ta so ba. Tsabar bak'inciki har rama ta yi dan ita yanzu barin k'aramin Y'AN UBANCI take taya y'arta ba bare ma yadda ta tsani Hindatu kamar mutuwarta kullum in dai zata kalli Hindatu ta kalli Ikilima sai ta ga kamar Ikilima ta shafa gawayi sosai take ganin banbanci na kyau a tsakaninsu sai dai ta yi alk'awari sai Ikilima ta riga Hindatu yin aure kai in da hali ma Hindatu ta dawwama ba tare da ta yi aure ba..




Kande bata da wani abin da ta sanya a gaba sai Hindatu ,ta kafawa yarinyar karan tsana na babu gaira babu dalili sai ta shiga d'aki ta zauna ta ringa turo Ikilima tana dukan Hindatu idan ta daketa ta ji ta d'auki kuka sai ta koma d'aki da gudu wurin uwarta hallaw daga an d'an jima Kanden za ta sake turo ta dan ta sake dukan Hindatu amma tsabar hak'uri da kauda kai irin na Ishalle bata ko d'aga kai ta kalli Ikilima bare har ta sanya Hindatu ta rama ko kuma ita ta ramawa Hindatu. A haka kullum suke tun abin baya damun Ishalle har dai abin ya zo yana damunta yau da gobe sai Allah kuma tsakanin uwa da d'a sai Allah sannan kuma ita zuciya bata da k'ashi.Wani lokacin haka za ta hana Hindatu fitowa ko k'ofar d'akinta sabo da Ikilima kar ta daketa amma sai Kande ta aikata har cikin d'akin Ishalle ta doki Hindatu kuma bafa a hankali take dukanta ba da k'arfi dan idan Kanden za ta aikata sai ta nannaga mata kan cewa tayi dage k'arfinta idan zata daketa. Kai wata rana har cizon Hindatu Ikilima ke yi dan duk jikin Hindatu tabon cizo ne dan idan ka tsaya ka k'arewa yarinyar kallo idan tana dukan Hindatu za kaga tsantsar tsana a fuskarta domin gaba d'aya Kande ta koyawa yarinyar Y'AN UBANCI yarinyar ta gama gane cewar Hindatu ba y'ar d'akinsu ba ce, ba uwarsu d'aya ba kawai gaba d'aya Kande ta yi amfani da jahilci da Kuma son zuciya wajen koyawa y'arta mummunar d'abi, a. Wanda a b'angaren Ishalle ba haka abin yake ba kullum bata da buri da ya wuce nunawa Hindatu ta so y'ar uwarta Ikilima sabo da dukansu abu d'aya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login