Showing 30001 words to 33000 words out of 33266 words

Chapter 11 - YAN UBANCI COMPLET BOOK By Maman Afrah.doc

Advertisement

tsinta a bakin ruwa bai mutu ba, sai dai har yanzu bai dawo hayyacinsa ba, sai dai yana numfashi a wahale, haka ya waiwaya gabas da arewa bai ga kowa ba da zai taimaka masa su dauk'i mutumin domin ya kaishi gidansa har Allah ya bashi lpia. Yana nan yana saka a ransa dan bai so ya tafi ya barshi a wurin gashi kuma ba zai iya daukan sa ba, zuwa can ya hangi wata amalaken shanu ta tunkaro wurinsa, a haka ya bari har mai amalanken ya k'araso zai wuce inda malam liman d'in yake d'aga masa hannu ya yi kafin daga bisani ya hangoshi haka ya masa bayani dan d'an cikin k'auyen ne, da farko k'i ya yi su taimaka masa amma kuma daga bisani sai ya yarda suka daukeshi suka sakashi a amalanken suka kama hanyar cikin gari, mai amalenken na kora shanu liman kuma da Dr Ayuba a baya. Suna zuwa aka shiga dashi gidan Malam Liman matar liman din ta shimfida musu tabarma aka kwantar dashi, shi kuma mai amalenken ya musu sallama ya tafi Malam liman ya masa godiya kafin kuma ya kira wani mai kemis na kauyen ya zo ya basu magana sannan aka sanya masa garwashi a wani d'aki aka shigar dashi domin ya ji dumin wuta saboda sanyin ruwa ya ratsashi.



Bayan kwana biyu Dr ya warware kuma ya baiwa su liman labarin komai a inda suka dinga kwantar masa da hankali, haka suka shawarceshi akan ya zauna ya kwan biyu anan dan ya fita daga cikin mutanen da y'an ta, addar nan za su kashe dan yanzu sun dauka ya mutu ne amma idan ya dad'e lokacin sun manta da shi sai ya koma cikin iyalansa, duk da ya basu labarin cewar zasu iya zuwa wurin matarsa shi kuma baya so su cutar da ita, haka dai suka bashi baki har suka samu ya hakura dan yana ganin girmansu sosai.





Tun kafin ayi bakwai su Ikilima da kande da ABIDA suka je suka sanya aka rufe bakin duk wanda zai nemi takardun kadarorin Dr suka kuma sa aka rufewa IMRAN baki akan kar ya nemi a bar masa FADILA a hannunsa sun fi so a tafi da ita kukayasku ta tashi cikin tsananin tsangwama da damuwa ta tashi babu kulawa babu gata dan basu baro wurin boka ba sai da suka sa aka fitar da yarinyar daga ran malam Buba da Ummi Ishalle da kuma iyaye da kakannin Dr.( wannan rashin imani da yawa yake)



Haka ummi Ishalle ta tafi da FADILA garin kukayasku lokacin da akayi arba,, in d'in mummy Hindatu,, dan ita anan aka barta har akayi arba, in kafin ta tafi da FADILA.Tun da FADILA ta koma kukayasku ta shiga damuwa ga rashin iyaye ga kyara da tsangwama daga Umma Kanden dan ABIDA takanas take tahowa kukayasku ta yi sati biyu dan kawai ta hana rayuwar FADILA sakat, amma Ummi Ishalle bata cewa komai yo an rufe musu baki daga ita har Malam d'in, kai hatta gashi da FADILA ke dashi sai da ABIDA ta sanya almakashi ta aske tas kuma wannan umarnin daga ikilima yake, haka rayuwar FADILA ta kasance dan abinci ma bata samun na kirki haka ta zauna kullum tana kuka tana tuna rayuwarta ta baya tana kuma tuna iyayenta da yadda suka nuna mata soyayya da kulawa haka ta hak'ura ta zauna sai dai bata wasa da sallah ko da wasa. Alkalamina bazai iya fasalta muku irin ukubar da rayuwar FADILA ta fuskanta ba a hannun mutanen nan marassa imani wato Umma Kanden, Mama Ikilima da kuma ABIDA.


Shema, u ta haihu a inda ta haifi d'iyarta mace, aka sanya mata suna SAFNA, bak'in ciki gun su Ikilima ba a magana, SAFWAN yana son yarinyar sosai inda babu scul to za ka sameshi rik'e da ita Ikilima da ABIDA har sun gaji sun k'yaleshi.





BAYAN SHEKARA UKU


YAya Nana da mummy Hindatu na gani suna ta shiri, saboda za su je wani kauye garin su malam Habu inda yayansa ke zaune da iyalimshi dan gobe yake so su tafi kukayaskudomin dai kowacce k'ura ce ke tashi yanzu ta lafa dan haka ma yake so su je su gaishe da yayan nashi duk da dai ba wani saninsa sukayi ba sai dai idan ya zo nan suna ganinshi, yanzu shima malam Habu yana da mota golf ya siya dan amfanin yau da kullum. Sun tafi iya Talle a gaba a inda su Yaya Nana suke a baya. Haka suka isa kauyen lafiya lau bayan an gaisa sun sha fura, anan Yaya liman ke baiwa dan iwansa labarin wani bawan Allah da ke zaune a a hannunsa tsawon shekaru uku dan dama basun had'u sun zauna haka ba a kwana kusa ba amma shi Yaya liman d'in ya san da zaman su Yaya Nana a hannun malam Habu. Anan liman ya kira Dr akan ya fito daga d'akin su gaisa dan tun da suka zo bai fito ba dann in ba masallaci ba baya zuwa ko ina koyaushe yana d'aki yana karatu ko nafilfili akan Allah ya tsare masa iyalensa aduk imda suke. Yana fitowa idanunsu suka sarke da na juna shi da matarsa abin alfahrinsa nan aka jimanta abinda ya faru itama ta bashi gaba d'aya labarin abin da ya faru da ita, sosai ya kuka jin wai har binneta an yi kuma ya shiga damuwa jin itama bata gida sai tausayin y'ar sa tilo ya kamashi wato FADILA, shin a wane hali ta ke tsawon wadannan shekaru uku? gaba d'aya ya ji hankalinsa ya yi gida har ma yana ganin kamar ba zai iya juewa ba zuwa goben kamar yadda su Malam Habu da Malam liman suka yanke shawarar a had'u gaba d'aya goben a tafi kukayasku har Dr. Haka aka yanke shawarar cewa su Dr za su tafi in yaso suma su Yaya Nana su tafi daga can wudil d'in in yaso sai su had'u acan.

*RANA BATA K'ARYA*



Washe gari Misalin k'arfe goma na safe motoci biyu golf, d'aya na d'auke da Yaya Nana, Mummy Hindatu sai Malam Habu da ke jan su, d'aya kuma tana d'auke da Iya Talle, matar Malam Inuwa, sai Malam Inuwan a gaba a inda wani abokinsu da ke hayar mota yake ja sabo da shatar motar sukayi. Sun iso kukayasku sun fara fitowa kenan sai ga motar su Malam liman ma ta tsaya, Malam liman d'in ne a bayan motar shi da matarsa sai Dr da direban da ya kawosu. Duk sun tsaya ana shawarar yadda za, ayi dan ba, aso mutane su tsorata in suka ga mummy Hindatu dan kowa ya san ta mutu sannan kuma itama Yaya Nana sun dad'e ba su ganta ba. Ana haka sai ga Malam Buba ya fito ranshi a bace sanandin shari, ar da aka kirawoshi akan ya zo ya yi a cikin gida wai Ikilima ce ta watsawa FADILA wani ruwa a cikin wata gora nan take wasu manyan kuraje suka baibaye mata jikin, shine dan ummi Ishalle ta yi magana Ikilima take mata fitsarar data saba, dama jiya suka dawo daga inda suka karb'o maganin shine suka biyo ta gidan dan su aiwatar da aikin su ga yadda maganin zai yi, yanzu ma Malam d'in fitowa ya yi zai sha iska dan gaba d'aya ya rasa me ke masa dad'i ganin sun kasa rik'e marainiyar Allah. Yana fitowa idanunsu suka sarke da na mummy Hindatu sai kuma ya ga Dr, bai gama mamaki ba ya ga Yaya Nana. Tsayawa ya yi a inda yake yana addu, a tare da jero sunayen Allah dan shi ya d'auka ma ko tunanin su da ya yi yanzu akan k'in rike musu y'a shine ya sa zuciyarsa ke masa gizo, amma rufe ido da ya yi ya bud'e ya ga kuma suna nan sai kawai ya fara tunanin ko dai ya samu tabin hankali ko kuma dai ya kusa mutuwa tunda ance in kana ganin matattu to kai ma ka kusa mutuwa, dan ya san dai da dr kad'ai ya gani bazai kawo komai a kai ba, dan dama bai ga gawarsa ba amma da hannunsa ya saka Hindatu a kabari, ita kuma Nana ya dad'e bai san ma inda take ba tsawon shekara uku ya tunota amma sai mijinta ma yake zuwa nemanta sai daga baya suka gane ashe ta dad'e bata tare dasu.Sai kawai suka dage da addu, a akan Allah bayyyanata dan sun fahimci aikin asiri ne.



"Kar kayi tunanin komai amsar komai tana wurinmu kawai ka bamu dama dan duk cikinsu babu wanda ya mutu har Hindatu, ka bamu dama mu maka bayani "Cewar Malam liman da ya fahimci halin da Malam buba ya shiga.




"Bismillanku"Malam Buba ya ce yana juyawa suka mara masa baya, a zauren gidan ya musu masauki dan dama manyan tabarmine a zaure a shimfide, da yake zauren na da girma sosai hanyar wucewa ce kawai babu tabarma, bayan kowa ya zazzauna Malam liman ya ce a sanarwa kowa na gidan ya zo domin ayi magana a gaban kowa, haka Malam ya shiga gidan ya sanar da su cewa suna da baki kowa yazo zaure, haka Malam buba ya yiwa kakan Dr waya cewa yazo shi da iyalansa akwai muhimmin abu a gidansa, daman iyayen na Dr sun zo biki garin haka suka taho dan ganin abin da ke faruwa. Ummi Ishalle ce a gaba ta shigo bakinta d'auke da sallama, ta samu wuri ta zauna ta gaishe da su bata gane Nana da Hindatu ba da yake suna daga can k'arshen zauren kuma da d'an duhu, sai ga ABIDA da umma kande sai Ikilima da itace shigowar K'arshe ta tsaya can tana yiwa FADILA masifa wai karta k'ara taba musu komai na gidan sbd gaba d'aya kurajen babu masakar tsinke, sai durar ruwa suke abin tausayi. Sun zazzauna cikinsu babu wanda ya gaishe da bak'in bare ya musu sannu da zuwa suma ba su gane si Nana ba dan duhun zauren shikwa dr dama kai ya Sunkuyar ba wanda ma ya kawo aka,, Ikilima da ABIDA aka nunawa can gefen inda su Nana suke zaune sbd iyalan gidan su Dr da suka shigo aka basu waje kowa ya zauna aka gaggaisa kowa ya kasa kunne yana sauraron banda malam buba dake jiran jin bayani dan shi ya ga kowa. Ikilima ce da shegen tsegumi ta kurawa matan nan biyu da suka zauna kusa da su aikwa idanunta ya sauka akan mummy Hindatu cikin azama ta matsa sai kuma ta fara karkarwa da sumbatu


"wayyo dan Allah fatalwa karki kasheni, ki min rai wlh bazan sake abinda nayi ba, dan Allah karki ke tsoratani wlh dama Umma Kanden ke sakani komai na biye-biyen bokaye akan neman duniya itace kuma ke nuna min in tsaneki tun tasowarmu itake cewa inke nuna miki y'an ubancin ke ba me k'aunata bace wlh bayin kaina bane duk zugarta ce, kuma wlh ko takardun kadarorin mijinki dana sa aka karbo suna nan a gida a ajje babu abin da na musu in ma so kike in maida sai in mayar da kaina nidai kiyi hak'uri kar in ke ganin fatalwarki, wlh ko yau ma ruwan sammun dana watsawa yarki umma kande ta sakani akan tunda baki raye kowane y'an ubancin ya koma kan yarki ita tasa akayi asiri aka d'auke hankalin Malam dana IMRAN dana Ummi Ishalle dan kawai yarinyarta taso babu gata" haka nan Ikilima ke ta faman zayyano abubuwan da sukayi ta yi a rayuwa har wanda suka saka IMRAN yaki ke duk wani tsubbu da makirci da sukayi sai da ikilima ta fad'a, tanayi tana rarrabewa a jikin bango kamar kadangaruwa, hakan da ta yi shi ya ankarar da kowa cewa Hindatu na wurin, kai hatta yaya Nana da kowa mutuwar tsaye sukayi jin sune silar b'atan yaya Nana, kowa ya ga Dr amma umma kande sai zare ido take har da sakin fitsari ganin mummy Hindatu wai ita dole ta ga fatalwa, anan itama ta ringa zayyano nata har asirin micijin da aka sanyawa ummi Ishalle sai data fad'a. Dak'er suka yarda sukayi shiru dan ABIDA ma sai fad'in wasu take gashi sun kasa tashi dan duk a tsure suke suna ganin idan sun gudu ma zasu ganta a duk in da suka je. Nan dai akayi shiru Malam liman ya zayyana komai da komai, banda kabbara babu abinda kake ji, sai kuma jikin su umma kande da ABIDA da Ikilima ya yi sanyi jin ba fatalwa bace gashi kuma sun tonawa kansu asiri, haka dai akayi shiru, sai Yaya Nana ta ce tana da magana bayan an bata dama sai ta ce.


"Dama batun y'ar gidan Hindatu nakeso in yi na ji ana cewa y'ar ta aka watsawa, ruwa, sannan kuma Hindatun ta fad'a min cewa haihuwarta d'aya, ko zaman da mukayi a wudil idan na tambayeta ina d'ana sai ta ce yana lpia to shine nakeso in sani wace y'a ce ake magana "

haka aka bayyanawa yaya Nana komai anan ta ce tana da magana.

*DARA TACI GIDA*

*SHARRI DAN AIKENE*


*IN ZA KA GINA. RAMIN* *MUGUNT*

" A sani na Hindatu d'a namiji ta haifa, ita kuma Ikilima y'a mace ta haifa kuma ni da na kawo yaran ban bamcewa su ABIDA cewa ga jinsin da kowacce ta haifa ba, amma ai ita me karbar haihuwar ta san cewa ga abinda kowacce ta haifa mesa bata banbance ba"yaya nana ta fad'a tana kallon Hindatu, kowa ya saki baki da mamaki kalaman da suke fitowa daga bakin yaya Nana, wani uban ihu Ikilima ta kurma nan ta hau zage zage akan cewa karya yaya nana take, aka dinga tafka musu anan Dr ya tambayeta ko ta san sunan matar data karb'i haihuwar fad'a masa ta yi dan bata manta ba, wayar Malam buba ya karb'a ya kira IMRAN ya sanar dashi ya je ya sanar da shugaban asibitin shi ya aikoshi a tafi da metron d'in ,sosai IMRAN ya shiga farinciki jin muryar dr yana ji dama a jikinsa dr bai mutu ba ,haka ya d'akok matar nan ya biya gida ya dakko iyalinsa suka tasamma kukayasku matar tana ta fargaba, amma ta wani sashen tana murna dan tunaninta ko haihuwa za ta karb'a shisa shugaban asibiti ya bada sunanta na ce hmmmm.



a can ma kukayasku Malam buba kiran Aliyu ya yi mijin Ikilima akan ya dakko duk iyalinsa su taho kukayasku, haka kwa akayi sai gashi ya zo shi da shema, u, SAFWAN sai kuma SAFNA wacce ke da shekaru uku kyakkyawar yarinya son kowa k'in wanda ya rasa. Suna zuwa mummy Hindatu da Dr na kallon SAFWAN suka gano tsananin kamar da yake yi da Dr komai nashi har tafiyar irin na Dr ne, wanda a da basu ga hakan ba, bayan zuwan su Aliyun da kamar awa d'aya sai ga su IMRAN sun k'araso, Aliyu ya ji miyagun aiyukan da matarsa Ikilima da y'ar sa ABIDA, ta aikata ya kuma yi ce Allah shiryesu dan ba zai musu baki ba,dan laifin duo na umma kande ne ita d'ora Ikilima akan mummunar akidarta, itama ta yiwa ABIDA tarbiyar da aka bata kenan,shima da lefinsa da ya zab'i Ikilima a matsayin matarsa yana da kyau mu zab'i abokan zama nagari dan su dora mana yara akan tarbiya da turba tagari.

An tambayi matar ta tabbatar da cewa haka zancen yake kawai ta banbantawa su Ikilima y'ay'an ne jin an ce mijin Hindatu yana da arzik'i kuma wannan ce haihuwarta ta farko hakan ya sa ta ji kyashi da Hassada shi yasa ta ce mace Hindatun ta haifa dan kar su samu gado idan Dr ya mutu, su samu kaso mai yawa kinga idan macece ba za su samu wani gado mai yawa ba kamar na d'a namiji, anan matar ta nemi yafiyar Dr da Hindatu suka yafe mata, nan take Aliyu ya dankara Ikilima saki har uku, sannan ya mik'awa su Hindatu SAFWAN ya kumskuma sa aka kira masa FADILA tana fitowa kowa sai da ya zubar da hawaye dan tausayinta, Ikilima kwa sai rusa kuka take ganin yadda ta maida y'arta ta cikinta da hannunta, ga muguwar azabar da suka sha dandana mata duk a rashin sani.haka Malam liman yasa hannu a aljihu ya fito da wani kullin magani aka bashi ruwa ya zuba ya yi addu, a ya watsa wa FADILA ruwan sai gashi kurajen sun bata bat, yace yayi ne dan fa FADILA da Aliyu ba dan Ikilima ba dan da a jikinta kurajen suke sai dai ta dandana kudarta tunda babu imanj a zuciyarta. Haka Aliyu ya tafi da FADILA da shema, u, SAFNA kwa dak'er ta yarda sai SAFWAN take yiwa kuka haka suka tafi shima ranshi babu dad'i dan da su ya saba.Malam buba ya kira mijin yaya Nana a waya ya sanar dashi komai shima beyi kasa a gwaiwa ba ya zo ya tafi da matarsa, Malam buba ma ya saki umma kande saki uku kuka da magiya amma yaki ya saurareta haka yace su fice masa daga gida ita da Ikilima, haka Aliyu na zuwa gida ya dakko takardun kadarorin Dr gaba d'aya a d'akin Ikilima ya kawowa Dr sosai sukayi mamaki da yadda abun ya kasance gashj dai Ikilima ta sa an sanya sunan SAFWAN a jikin takardun ba tare da ta san dama ba danta bane, gashi shi kuma Dr burinsa ya cika na son mallakawa dansa takardun kadarori gashi ba sai an sha wahalar canjawa ba Allah kenan.




*BAYAN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login