Showing 27001 words to 30000 words out of 33266 words

Chapter 10 - YAN UBANCI COMPLET BOOK By Maman Afrah.doc

tattare da shi bin bayansa nake ba tare da ya sani ba, har dai ya je dede kan wasu sabbin kabarbura, haska fitilar wayarsa ya yi a jikin allon da ake rubuta sunan mutum da ranar da ya mutu, sai da ya tabbatar wannan ne kabarin da ya ke nema kafin cikin hanzari da zafin nama ya shiga tone kabarin har sai da ya bud'e kabarin tsaf sannan ya fito da gawar da ke nad'e a cikin likkafani, ajiyeta ya yi a gefe ya maida komai na kabarin ya rufe ba zaka tab'a cewa an tona ba. Kinkimar gawar ya yi cikin sauri ya fito dan bayaso me gadin makabartar ya ganshi, sai da yayu tafiya mai dan nisa kafin ya zi im da ya yi parkin d'in motarsa yana zuwa ya sanya gawar a bayan motarsa ya shiga ya bar wurin a 360.hanya ya d'auka sosai wacce za ta kaishi bayan gari sai da ya yi nisa sosai sannan ya samu wuri ya faka motar, cikin hanzari ya fito ya bud'e bayan motar gawar nan ya bud'e ya dakko wata doguwar riga sabuwa a ledarta ya sanya mata ya jefar da likafanin ya gyara mata kwanciya ya shiga motar sai da ya je wata gona da ke d'aya daga cikin ginakin da ke mak'otaka da wudil sannan ya faka motar ya fito da gawar ya ajiyeta a wurin sannan ya tsugunna akan gawar ya fara magana kamar haka.


"Na san kina jina dan haka nakeso in miki bayanin abin da ya faru dalla -dalla, na tab'a haduwa da ke a garin Gumel wata rana, na yi sata an kamani yara da manya na ta kallona hakan ya sa na ji ciwo sosai a raina, y'an sandan sun sanya min ankwa kenan sai gaki a mota kun zo wucewa haka kika sanya direba ya tsaya ki ka fito kika tambayi meke faruwa, anan aka baki labarin abun da ke faruwa, haka kika shiga mota ki ka bi motar yan sandan nan har police station ki ka yi belin d'ina sannan kika taho dani kika mun nasiha akan in bar yin sata in koma karatu na ce miki karatu baya cikin tsarina haka kika d'auki kud'ad'e masu yawa kika bani in je in yi sana, a, wannan abun da kika min ya dad'ad'a min rai amma kuma banyi sana, ar ba, na kashe kud'ad'en to a lokacin da wanda suka bamu aikin nan suka nuna min hotonki ina ganinki na ganeki sai dai babu yadda zanyi insa su fasa k'udurinsu dan ko ban karb'i aikin ba nasan za su samu wasu su basu aikin dan haka na karb'i aikin akan zan kubutar da ke, bayan an kamoki ni na bada shawarar a miki allurar poison haka suka amince ba tare da sun nemi dalili ba. Dan ko da aka tashi sai na ce ni zan miki allurar dan haka sai na canja allurar daga ta poison zuwa wacce za ta sa ki suma na wasu a wanni to shine yanzu na je na tonoki dan haka yanzu idan kin gama dawowa hayyacinki sai ki tafi inda zaki kar ki tab'a komawa gida matsawar kinaso ki rayu da ranki dan wanda suka bamu aikin nan basu da imani za su iya kasheki ko da yaushe ko su sa a kasheki dan haka yanzu sai ki je wani wuri ki cigaba da rayuwarki nagode"Yana gama fad'in haka ya shiga motarsa ya bar wurin a guje.


Sai da hasken rana ya fito ya haske fuskarta wannan ne dalilin da ya farfado da ita a hankali -a hankali take bud'e idonta wani haske ta gani gaw wanda ya sa ta yi saurin maida idon ta rufe, jim kad'an ta sake bud'ewa kad'an haka ta dinga yi da kad'an -kad'an har dai ta bud'e idon gaba d'aya. Wurin ta ke bi da kallo har dai ta fahimci a dokar jeji ta ke haka ta tashi ta zauna a hankali ta ke bin jikinta da kallo nan take abin da ya faru da ita ya shiga dawo mata, tun daga lokacin da aka tafi da ita da direba har zuwa lokacin da wannan matashin ke mata bayani, amma bata san ya akayi ba da aka binneta a matsayin gawa dan bata san me ya gudana ba ta dai ji an fitar da ita daga wani wuri mai mugun matsi da aka sanyata ,kenan wannan wurin kabari ne, lallai Allah ka rabamu da duhu da kuma azabar kabari ta ce, sai kuma maganganun da matashin ya mata tabbas ta ji maganganunshi, dan lokacin allurar ta saketa hayyyacinta ne kawai bata dawo ba,nan take kuma ta tuno da cewar ta ji matashin nan ya ce mijinta ya mutu, itama dan ya ceceta ne da yanzu kasheta za ayi, nan ta fara kuka mai tsuma zuciya na rashin mijinta mai sonta da kaunarta, sai kuma ta shiga tunanin halin da IMRAN da kuma FADILA za su shiga su ma tana tsoron kar a cutar da su to shin wanene wannan me sanya a kashesu a kawo masa takardun kadarori? ya ma akayi ya san da zancen takardun har haka ta faru? lallai akwai lauje cikin nad'i, shin shi ya kauro zaman duniyar ne da ya ke sakawa a karb'o masa abin duniya, haka dai ta yi ta sak'e -sak'e kafin daga bisani ta tashi daker ta tako a hankali har ta zo bakin titi tsallakawar da za ta yi sai kawai ji ta yi mota ta yi sama da ita.

"Subhanallah Innalillahi wa inna ilaihir raji, un "Malam inusa da Malam Inuwa suka fad'a a tare ganin sun bige mace wacce ba su ga tahowarta ba sai kawai ganinta sukayi ta hauro tsakiyar titi kafin Malam Inuwa ya taka birki har mai afkuwa ta afku. Haka suka kama ta suka sanya a mota suka nufi gari da ita domin kaita asibiti dan dama ana fitowa daga masallacin asuba suka tafi gonar Malam Habu domin yin gewaya shine haka ta faru a hanyar su ta dawowa. Emergency aka shiga da ita nan take likitoci suka dukufa akanta har dai suka samu nasarar ceto ranta.An sanya mata drip inda kuma aka gane babu jin ciwo a jikin nata, anan ne su malam suka kira gida suka sanar da iyalansu abin da ya faru, sai wajen azahar matan nasu suka zo da kulolin abinci suka duba jikin Hindatu dan lokacin har drip din ya k'are tana zaune amma bata magana sai dai idan an mata sannu ta gyada kai. Dan gaba d'aya abin duniya ya dameta, wajen karfe biyu na rana aka sallameta suka dawo gida sai dai Hindatu gidan Malam Inuwa aka kaita tare da matar Malam Inuwa a cewar Malam Inuwa tunda kwanaki ne za ta yi idan warware sai ta kwatanta gidan su a kaita. Haka Malam Habu ma suka shiga gidansu a lokacin Yaya Nana tana tankade garin tuwon dare, sannu da zuwa ta musu da ban gajiya suka amsa fuska sake dan suna jin dad'in zama da ita sosai dan yanzu sun d'auketa a matsayin y'ar su tunda gashi har shekara goma sha biyu amma babu labarin y'an uwanta har sun gaji da cigiya sun hak'ura tfn su Allah ya bata miji ta yi aure.Nan ta ke tambayar iya Talle mai jikin, ta ce idan ta yi sallar la, asar ta je ta dubota a gidan babanta inuwa, da to ta amsa mata a ladabce, hakan ya sa iya Talle ta ji kamar y'ar da ta haifa.



A b'angaren su Ikilima ma kwa tun kan a sanar da su mutuwar su Hindatu Okasha ya sanar da su amma ko a jikinsu to da me ma zai damesu tunda su suka bada aikin suka kuma ce idan ma kisa ya kama ayi dan haka da ya fad'a musu ma mutuwar cewa sukayi Allah jik'an rai dan su duniyar ce kawai a gabansu, tunda dai takardu sun zo hannu basu da wata damuwa. Dan Okasha ma bai sanar da su abinda ya yiwa Hindatu ba, dan ya fahimci basu da imani bare tsoron Allah, shi yasa ya kyalesu dan haka da suka baro kano ma Gumel suka zo suka damka musu takardun, sai kuma Ikilima ta ce su koma da dare can gidan Dr ABIDA za ta musu jagora su dakko kud'ad'e a ciki za su sallamesu to komawar da sukayi ne bayan sun d'akko kud'in ba tare da an kamasu ba, dan babu kowa a b'angaren Dr hakane ma ya basu damar cin karansu ba babbaka dan lokacin kowa hankalinsa a tashe ya ke. Kud'ad'en da suka d'akko kimamnin miliyan biyar ne dan haka su Okasha ko kwandala basu baiwa su Ikilima ko kwandala ba dan cewa sukayi ma ba za su karb'a ba, dak'er suka karb'a to bayan sun raba kud'in ne Okasha ya zame jikinsa ba tare da kowa ya sani ba ya je ya tono mummy Hindatu.



Misalin k'arfe biyar na yamma Yaya Nana ta gama komai dan yau bata da zuwa islamiya malamin dake d'aukan class d'insu baya jin dad'i dan haka yau hutu suke. Bayan ta kimtsa sosai ta yiwa iya Talle sallama domin zuwa gidan Malam Inuwa ta dubo bakuwar da aka kad'e. Da sallama ta shiga gidan ta tsugunna har k'asa ta gaishe da matar Malam Inuwa sannan ta tambayeta me jiki ta amsa mata, d'akin da aka ajiye bakuwar ta nuna mata akan ta shiga ta mata sannu duk da ta san ba amsawa za ta yi ba, sai dai ta ghad'a kai.


"Assalamu Alaikum "Yaya Nana ta shiga dakin bakinta d'auke da sallama.







"Yaya Nana " Hindatu ta ce tana mik'ewa tsaye daga zaunen da take idonta na zubar da hawaye.

"Hin...da.. Cewar Yaya Nana tana dafe kanta da ya matuk'ar sara mata ba tare da ta k'arasa sunan Hindatun ba.

Tahowa Hindatu ta yi cikin hanzari da zafin nama, kafin ta karasa har Yaya Nana ta tafi luuu za ta fad'i, da azama Hindatu ta sanya hannu ta tare ta, ta fad'a jikin Hindatu idanunta duk sun wani firfito sun kad'a sunyi jawur sai jan numfashi ta ke da d'ai d'aya.

"Wayyo Yaya Nana kar ki mutu ki barni, wayyo Allah " Hindatu ta ce ganin halin da Yaya Nana ta ke ciki.

Ganin kirjin Yaya Nana yana sama da kasa alamar numfashinta ya zo kirji, gashi kuma suna neman fad'uwa k'asa sabo da jikin Yaya Nana da ya saki sai Hindatu ta ji ta mata nauyi a hannunta, kwantar da ita ta yi a tsakiyar d'akin, ta hau jijjigata.

Yaya Nana ki tashi " Hindatu tace da k'arfin gaske, matar Malam Inuwa da fitowarta kenan daga kicin dan tun da Amina (yaya Nana ) ta shiga d'akin ta tashi ta shiga kicin duba tukunyarta, jiyo muryar Hindatu,ai da sauri ta yi cikin d'akin dan ganewa idonta abin da ke faruwa. Ganin matar da aka kad'e tana kuka tana jijjiga amina yasa gabanta ya yi mummunan fad'uwa dan tunanin da ya fara zuwar mata shine kar dai matar ce ta mata wani abun, dan yanzu rayuwar nan mutum bashi da tabbas kana iya taimakon mutum shi kuma ya zo ya cutar da kai.

"Menene ya sameta" matar Malam d'in ta ce itama tana hanzarin tsugunnawa gaban amina da ke kwance k'asa kamar ma ba numfashi.

"Ki taimaka min kar na rasa y'ar uwata"Hindatu ta ce tana sake fashewa da kuka.

Kallon mamaki matar Malam d'in ta mata jin ta kira Amina da y'ar uwarta, amma kuma halin da aminar ke ciki ya hanata tambayar hakan, da sauri ta fito daga d'akin ta dauk'i hijabinta akan igiyar shanya tasa ta nufi waje cikin sauri,tana fita Malam Inuwa da Malam Habu dake zaune kan benci suna magana ganinta a gigice tana d'ago musu hannu suka tashi cikin azama suka nufi inda take, kafin su k'arasa ta juya cikin gidan su ma mara mata baya sukayi hankula tashe dan gaba d'aya tunaninsu wani abun ne ya samu matar nan da suka kad'e dazu. Aikwa tunaninsu ya basu dai dai ganin ta nufi d'akin da aka ajiye bakuwar, suma cikin suka shiga amma abin mamaki sai suka samu sab'anin tunaninsu, dan kuwa sun ga matar da aka kad'e tana kuka tana kiran amina da wani suna wai Yaya Nana, aminar kuma na kwance, tunaninsu gaba d'aya ya tsaya jin tana danganta amitu da y'ar uwarta. Tunanin suka ajiye gefe suka rufu akan Amina nan suka gano halin da Aminar ke ciki, ruwa Malam Inuwa ya sa matar shi ta kawo a kwano nan ya Shiva karanta addu, a a ciki a take suka dukufa wurin yiwa aminar rukiya basu barta 0ba har sai da suka fitar mata da sauran sammun da ke jikinta wanda ya sakata manta komai. Ana gama mata barci ya yi nasarar d'auke ta.


Bayan ta farfado daga barcin ne aka zauna a tsakar gida inda aka shimfida tabarmi dan har Iya Talle ma ta zo bayan Malam Habu ya fito daga sallar magrib ya shiga gidan yake fad'a mata, shine ta biyoshi suka taho tare.



Kowa ya yi shiru matan suna kan tabarma d'aya mazan ma suna kan tabarma d'aya. Yayin da kowa ya kasa kunne yana sauraron abin da za, a tattauna, yayin da Yaya Nana da mummy Hindatu ke zaune kusa da juna kamar zasu komawa juna ciki.

"Alhamdulillah, Allah me kowa me komai da ya hadamu a wannan waje, wato yau Allah ya Hadamu da wata daga cikin dangi ko in ce y'an uwan Nana da muke kiranta da Amina yau gashi mun ga wanda aka santa sanayya ma ta y'an uwantaka, tsawon shekaru goma sha biyu babu wani wanda ya santa bare kuma wanda ya san wanda ya san wani daga cikin danginta. Sannan kuma mun sameta da rashin lafiya irin na hauka, wanda tsananin addu, a da neman magani Allah ya bata lafiya ya warkar da ita daga halin haukan da ta tsinci kanta wanda ba komai bane San adjutant hakan ba sai sammu akayi wanda bama da sunanta akayi sammun ba kawai dai Allah ya kaddara matane. To sai dai sammun na da wani lakani na ko da mutum ya warke daga halin hauka to babu wani abun da zai sake tunawa daga abin da ya shafesa har sai ya ga wani daga danginsa, to hakan ya nuna mana cewa wannan bakuwar dangin Nana da muka sakawa suna Amina a rashin sanin sunanta" Malam Habu ya kare maganar da jan numfashi.


"Tabbas wannan haka ne hak'ik'a Allah shi ke yin yadda ya so, gashi yau Allah ya kawo y'ar uwarta har gida cikin hikima da buwaya ta Ubangiji "Malam Inuwa ma yace yana gyara zama.


Shiru ne ya d'an biyo baya kafin Iya Talle ta ce



"Ina godiya ga Allah da ya kawowa amina ta y'ar uwarta har gida duk da na saba da ita bama son rabuwa da ita amma hakan ba zai sa mu ji ba dad'i ba, Allah sadata da sauran y'an ubanci lafiya "


"Hakika nagode da irin rik'on da kuka min tun daga lokacin dana tsinci kai na a halin rashin hankali har zuwa samun lafiyata da dawainiya da kuka sha yi dani kawo yau da Allah ya dawo dani cikin hayyyaci na gaba d'aya "Yaya Nana ta fad'i hakan tana jinjina godiyarta ga Allah.


"To nima dai godiyar zan yiwa Ubangiji Allah ka k'ara tsare bayinka daga sharri mutum da aljan"CewarMatar Malam Inuwa.

To ke bakuwar mu baki ce komai ba, duk da har yanzu kina zubar da hawaye, amma ya ci ace kin hak'ura hakan nan tunda gashi Allah ya hadaki y'ar uwarki amma kuma har yanzu baki ce komai ba, kina cikin damuwa, ya kamata ki mana bayanin barowarki gida har Allah ya kaddara haduwarmu muka bigeki a mota"malam Inuwa yace yana maida hankalinsa kan mummy Hindatu.

A nan mummy Hindatu ta d'akko labarin abin da ya faru tun daga fitar Dr Ayuba ya tafi d'akko takardu har kawo tonota a kabari da tasowarta daga inda Okasha ya ajiyeta suka kadeta.

Salati gaba d'aya mutanen wurin suka d'auka jin wani rashin imani da aka aikatawa su mummy Hindatu, duk da ba, a san ko su waye ba.

Jin wannan batu yasa su Malam Habu da Malam Inuwa suka yanke shawarar mummy Hindatu da Yaya Nana su zauna anan hannunsu sai komai ya lafa tunda kowa ya manta da batun Nana bare kuma Hindatun da aka san ta mutu an binneta, haka kuwa suka amince suka zauna a hannunsu sai dai damuwar da ba a rasa ba.




*DR AYUBA*


Wani dattijo ne ya je gonarsa da sassafe bayan ya gama d'an abin da zai yi sai ya karasa bakin ruwa domin wanke jikinsa dan bai so ya shiga cikin gari da k'ura a jikinsa, bayan ya gama wanke jikinsa tas kamar an ce waiga gefen hagun dinka aikuwa ya hangi mutum kwance a bakin ruwa, da sauri ya yi wurin da ya hango mutum kwance, yana zuwa ya ga mutum ne namiji kwance kamar ma baya numfashi. Jijjigashi ya shiga yi ganin alamun daga cikin ruwan yake sai kuma goshinsa kamar dai kujewa, da kuma yankan gilas, wannan ya tabbatarwa da dattijon nan cewa watakila hatsari ya yi ya fad'a ruwa ko kuma wasu mararsa imanin ne suka kaaheshi suka jefashi ruwa shine ruwan ya taho dashi nan. Danna masa kirji ya shiga yi tare da cikin sa aikuwa ruwa kamar jira suke suka fara kwaranyowa kamar anbude famfo, haka ya dinga yiwa bawam Allah n nan har ya cire rai daga cewa ya mutu sai kawai ya fara tari, tari yake sosai na ruwan da ya shak'a, mutumin nan da ake kira da suna liman, ya shiga yiwa Allah godiya ganin mutimin da ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login