Showing 15001 words to 18000 words out of 33266 words

Chapter 6 - YAN UBANCI COMPLET BOOK By Maman Afrah.doc

buk'aci Ikilima ta kawo mata abinci cewa ta yi bata gama ba dan mugun hali dan kar aci nama,ita kwa daman sauri ta ke ta je ta ga iyayenta haka ta musu sallama Aliyu yana ta mata godiyar kaya kamar ya ari baki ita kuma tana ta cewa ba komai, sun fito bakin kofa ita da Aliyu da IMRAN suna Lallab'ashi akan ya yi hak'uri, aikuwa sai ga wata yarinya a guje kamar an biyota tana zuwa ba sallama ba natsuwa dan har buge Hindatu ta yi garin zuwa kusa da IMRAN, tana wani tattabashi tana washe hak'wara.

"Haba ABIDA wai yaushe zaki nutsu me yasa kullum bakya tafiya ta natsuwa sai gudu kamar wata barewa? kina gani kika bige auntynki amma ko ki bata hak'uri "Aliyu ya mata magana ganin ko a jikinta data bige babba

"Lah yau dai Allah ya nuna min kai IMRAN daman ban Sanka ba sai a waya lokacin da ka tafi mama ta ce ina k'arama "ABIDA da ko ta kula da maganar Abbanta sai ma hankalinta da ta maida kan IMRAN. Haushi da takaicin irin tarbiyar da Ikilima ke baiwa yarinyar ya tsayawa Aliyu a rai ba ta jin magana ko kad'an ga rawar kan masifa sai abin da Ikilima ta ce take yi.

"Haba kai kwa ai bata lura ba, kasan yarinta "Hindatu ta ce tana murmushi

Shi dai Aliyu bai k'ara magana ba.

"Wai ba da ke Abba ke magana ba amma ki kai shiru "IMRAN ya fad'a fuskar nan babu annuri, ganin ta bige mummyn shi kuma Abbansu ya mata magana ta yi biris.

Zunburo baki ta yi irin na sangartattun yara maras sa jin magana ta juya ta shige gida Hindatu na kiranta amma ko juyowa bata yi ba ta shige abin ta. Sallama Hindatu ta musu IMRAN na ta d'aga mata hannu itama haka har sai da ya daina hangen motar sannan ya hak'ura.


satin ta guda a kukayasku ta tafi maigatari can ma kwana biyu ta yiwa yaya Nana ta dawo kukayasku duk da zaman ba wani dad'i ya ke mata ba sabo da Umma Kande duk da bata fiya zaman gidan ba, ficewa ta ke wataran kuma ta ce ta tafi Gumel haka take zaune dan dama halin Umma Kande abu ne da aka saba sai dai ganin iyayenta da ta ke yi kad'ai ya sa bata damu da hakan ba. Su Umma Kande kwa sun kasa zaune da tsaye ne kawai dan ganin sun samo maganin da zai cika musu burinsu na janyowa Hindatu bak'in jini a wurin Dr koma su rabata da auren baki d'aya dan yanzu suna gani wannan ce damar da suka samu tunda ga IMRAN duk abin da suka bashi zai musu dan idan ya tafi su basu da yadda za su je k'asar Chaina. To fa inda gizon ke sak'ar shine sun kasa shawo kan IMRAN dan gaba d'aya ya tubure musu sai ma nuna musu yake abin da suke so su yi ba mai kyau bane, gashi yanzu kwana biyu ya rage su koma k'asar chaina amma kuma har yau bai yarda da musu aikin ba.Umma Kande Gumel d'in ta ke zuwa su sakashi gaba suyi ta lallashi amma a banza tun suna lallashi har suka dawo masa fad'a kamar sa cinyeshi d'anye, har barazanar hana shi komawa suka yi amma ko a jikinsa sosai suke dana sani akan turashi k'asar waje dan dama sabo da cikar burinsu amma gashi yazo da gardama da ace ABIDA ce da babu abin da zai gagareta ta musu domin tun yanzun wannan da take da ta takwas gagararriya ce ta bugawa a jarida.Ranar da Hindatu za ta biyo ta d'aukeshi su tafi Kano ana gobe jirginsu zai tashi a ranar ne ya yanke shawarar karb'ar magungunan da su ke so ayi amfani da su dan bayaso su yi rabuwar rashin dad'i da mahaifiyarsa duk da abin kirki ta ke so ya yi mata ba amma zai karb'a dan hannunka baya tab'a rub'ewa ka yanke ka jefar, kuma duk lalacewar mahaifiyarka sunanta mahaifiya duk da babu biyayya a yin sab'on Allah ko kuma cutar da wani bawa dan wannan sab'on Allah ne dan kwa wurin boka da Malaman tsubbunsu suka karbo magungunan.

Umma Kande ta yi sammakon zuwa Gumel dan su jaddada bashi maganin dan jiya har wurin wani malami ta je aka yi aiki akan IMRAN dan ya amince da buk'atarsu, aikwa tana zuwa ya yarda ya amince haka suka mishi bayanin magungunan dalla --dalla da wanda zai barbad'a mata a abinci da wanda zai zuba mata a ruwan shayi kar har da wanda zai saka mata a ruwan wanka. Haka suka danka masa cike da farinciki suna sanya mishi albarka. Sallama Umma Kande ta musu ta nufi kukayasku lokacin da ta zo har Hindatu ta gama shiryawa, direban ya zo d'aukanta Umma Kande har fadan wasa take mata wai za ta tafi bata mata sallama ba, sosai Umma Kanden ta ke fara, a wacce bata tab'a yi ba tunda Hindatun ta zo garin abin har mamaki ya basu kai ita Ummi Ishalle ma sai ta ke zaton ko murnar tafiyar Hindatun ta ke yi. Haka dai ta shiga mota ana mata fatan sauka lafiya rakiya k'ofar gida har da Umma Kande.Sun iso Gumel suka je daukan IMRAN ya shirya suna zuwa aka d'an gaggaisa dan sosai Hindatu ta ga canji a wurin Ikilima tana ta dariya da musu fatan sauka lafiya, bata san sharrin da suka k'ulla mata ba, shi kwa IMRAN duk jikinsa ya yi mugun sanyi idan ya kalli mummyn tasa sai ya tab'a ledar magungunan da take cikin aljihunsa, gaba d'aya ya ji tausayinta ya kamashi gashi dai ita babu komai a ranta sai alkahiri amma su suna binta da sharri duniya kenan.




Direba ya bud'e bayan motar ita kuma ABIDA sai zayyano kayan da take yi Hindatu ta siyo mata ta ke, ita kwa Ikilima sai dariya ta ke sabo da tsabar son samu ganin ABIDA na ta fad'in abin da ta gaggaya mata ta ce a siyo .Hindatu sai cewa ta ke za ta aiko mata idan ta je. Aliyu sai hararar Ikilima ya ke dan ya san aikinta ne, sai tab'e baki ta ke ganin sun raja, a da hira IMRAN ya waiwaya hagu da dama ya ga ba mutane sannan hankalin iyayensa ba akansa ya ke ba, hannu yasa a aljihunsa hannunsa har karkarwa yake ya d'akko magungunan juyawa ya yi ya nufi wajen k'aton kwalbatin da ke d'aya gefen gidan na su yana zuwa ya jefa bak'ar ledar da ke d'auke da magungunan da su Umma Kande suka kashe mak'udan kud'ad'e ji ka ke tinjim saurin juyawa ya yi a tsorace dan kar karan fad'awar magungunan ya maido da hankalinsu, amma sai ya ga ba su kawo a ka ba ajiyar zuciya ya sauke yana yiwa Allah godiya sannan ya ce

"Ai in Allah ya yarda matsawar ina raye babu wanda zai cutar da ke mummy na" Yana gama fad'ar haka ya juya ya tafi wurinsu ba tare da dukkansu sun lura da ba ya wajen ba. Yana zuwa suka shige motar suka tafi ana ta d'aga musu hannu.



*BAYAN SHEKARA GOMA*


A lokacin har Hindatu sun dawo Nigeria dan Dr Ayuba ya gama musu iya shekarun da ya d'auka, yanzu ya dawo Nigeria da zama dan yanzu asibitocin da ya gina a garin kano sun kai bakwai sosai yanzu arzik'insa ya hab'aka dan ba k'aramin kud'i ake biyanshi a China ba. Yanzu haka ya d'auki ma,aikata da su ke aiki a asibitocinsa shima kuma a d'aya daga cikin asibitocin nasa ya ke aiki. IMRAN ma shi kala-kala kula masa da d'aya daga cikin asibitocin nasa, tunda Shima b'angaren health d'in ya karanta. Kuma har yau a gidan Hindatun ya ke da zama idan daily har ya ke Gumel say dai ya je ya gauche da su ya musu kwana biyu ya koma. Duk da ba sosa Ikilima ke sakar masa fuska ba sabo da tasha sakashi aiki amma kuma sai ya dinga mata gardama ko d'akin ya yi ta mata nasiha yanzu haka ta maida burinta kwacakam kankara ABIDA domin ta dalilinta ne kad'ai za ta cika burinta akan Hindatun, domin halin ABIDA da IMRAN akwai matuk'ar banbanci kamar dai ba ciki d'aya suke ba ko kuma dan ba ruwan tarbiya d'aya aka shayar da su ba. Yanzu IMRAN na da shekaru 24 a duniya a inda ABIDA ke da shekaru 17 amma gaba d'aya yadda idon ABIDA ya ke a bud'e sai ka d'auka y'ar shekara talatin ce. Ga abokai y'an duniya maza da mata kai ciki kwa har da y'an shaye -shaye da y'an daba, wasu ta san su ne a makaranta irin gagararrun nan da suka k'i karatu suka fand'are suka fi k'arfin iyayensu, sai su fad'a harkar dabanci da shaye shaye, to dalilin makaranta ta san su tunda itama ba ta kirki ba ce shi yasa ba za ta yi abokai na kir ki ba.wasun su kuma a yawon garinta ta san su. To a yanzu maganar da ake, Ikilima tana da ciki tsoho haka ma Hindatu tana da ciki tsoho cikin da Dr Ayuba ya ci buri akan shi, cikin da Dr Ayuba ya yi alkawarin mallakawa duk abin da ya mallaka matsawar ya zo duniya.Kulawa soyayya sosai yanzu ya ke nunawa Hindatu ga uwa uba d'anta IMRAN da shima ya d'auki so da k'auna ya dorawa cikin tun kan ya bayyana a duniya.

Yanzu saura sati biyu edd d'in Hindatu ya cika Inda ,kuma yau saura kwana shida Dr Ayuba zai yi bikin bud'e wani asibitinsa da zai yi, mai suna ""Fisabilillahi "" asibiti ne da zai bud'e shi domin talakawa mararsa k'arfi irin wadanda basu da kud'in da za su biya idan wata lalura ta same su ko kud'in magani ko kuma na aiki, to shine ya ginashi a inda ya d'auki mataki, aikata da za ake yin komai kyauta sabo da ba ya son ya ji ana cewa wani ya mutu ta dalilin rashin kud'in aikin da za,a masa, ko rashin kud'in siyan magani. Duk da mutuwa k'arar kwana ce to amma komai yana da sanadi dan haka ya d'auki nauyin yin wannan asibitin kuma ba kowa ne ya bashi shawarar ba sai IMRAN tare da shi suka yanke shawarar. An gayyaci y'an uwa da abokan arzik'i zuwa wurin taron bud'e asibitin, taron ya had'a da manyan mutane da za su halarci wajen. Tun da Ikilima da umma kande suka ji za,ayi taron suka dage da neman maganin da zai zama cikar burinsu, duk da tsohon cikin Ikilima haka suka tafi wani luluk'in daji a Niger ita da Umma Kanden sun masa bayanin suna so a yiwa wata mata kurciya a inda suke so ta tafi a nemeta a rasa sannan a had'a mata da hauka dan kar ta zauna a cikin hayyacinta.





ABIDA jin k'aran Bud's k'ofar d'akin da yaya Nana ke ciki ya sa ta yi saurin juyawa ta kama hanyar zuwa falo kamar dama ba a tsaye ta ke ba, dan kar ta ganta a tsaye ta yi tunanin wani abu da ban,dan za ta yi tunanin me ya sa ta tsaya bata shiga falon ba, gashi Kuma gaba d'aya alamun rashin gaskiya ya bayyana a tare da ABIDA sabo da ba ta yi tunanin fitowar yaya Nana ba a lokacin. Da ya ke d'akin da yaya Nana ta ke kusa ya ke da na Hindatun tana fitowa sai kawai ta nufi d'akin Hindatu dan ta fito su tafi, tana zuwa ta bi ta kan maganin da Ikilima ta barbad'a ta shige falon, a inda suka kusan yin karo da Hindatu da ke k'ok'arin fitowa dan dama lokacin da Ikilima ta lek'ota zobe ta manta akan mirror shine ta koma sai kuma da ta ji kiran da ABIDA ta mata shine ta taho, murmushi su ka yiwa juna ita da yaya Nana kafin su juyo suka fito tare. A lokacin da ABIDA ta koma babban falon gidan wanda acan ne Ikilima ta ke zaune, ganin ABIDA ya sa ta tashi ta nufo ta wanda sanadin hakan ne ta hango abin da ya mugun razana ta, da yake hanya ce street kana hango har can k'ofar d'akin Hindatu da yake ita ABIDA ta baiwa hanyar d'akin Hindatu baya sai bata ga abin da mahaifiyarta ta gani ba.nufo ABIDA da Ikilima ta yi sai idanunta suka sauka akan yaya Nana da ta shiga d'akin Hindatu, ganin haka ya sa ta k'wala wani uban k'ara wanda ya isa kunnuwan su Hindatu suka nufo gurin hankali tashe.


"Subhanallah menene "Hindatu ta tambaya tana kama Ikilima ganin ta dafe saitin mararta, da ya wani murd'a mata take ta fara jin d'an cikinta ya hautsina da k'arfin ,sanadin ganin yaya Nana ta taka maganin da ya zama makaminta na b'atar da Hindatu shine ya tayar mata da nak'uda.

"Ikilima ko haihuwar ce ta zo "itama yaya Nana ta tambaya a rud'e ganin Ikilimar ta tsugunna sai cije leb'e ta ke, duk da bata tab'a haihuwa ba ita yaya Nana ta san tabbas akwai ciwo a nak'uda.

Haka suka kamata suka shiga da ita wani d'aki, da kulawa nan falon, dan ta kasa magana kwata -kwata, itama kuma ABIDA duk ta tsorata dan itama ba ta san me Ikilima ta gani ba amma dai tunda ga Hindatu ta taka magani burinsu zai cika sai ta ji komai da sauk'i.

"Amma yaya Nana ko direba zai, a kira a tafi asibiti kin ga halin da take ciki kawai a hak'ura da zuwa wurin taron, mu kaita asibitin gwabnati kar mu je d'aya daga cikin asibitocin Dr dan za,a iya fad'a masa gani a asibiti kuma kin ga yana da baki kar mu katse masa. Idan ma ya kirani zan ce na fasa zuwa wurin taron gwara idan ta haihu kowa ya ji haihuwar" Hindatu tace kamar ta yi kuka ganin yadda Ikilima ke ta had'a zufa sai murkususu ta ke.

"Eh hakan ya fi kira direban kawai mu je asibitin"Yaya Nana ta ce cikin hanzari.
Kiran direban ta yi cewar ya fito da mota ga su nan zuwa, tana kashe wayar Ikilima ta k'wala wani wawan ihun da ya sa Hindatu ta tsorata ai ita ma take mararta ta murd'a say kuma bayanta ya rik'e salati ta d'auka suka k'arasa da Yaya Nana itama nak'udar ce gadan -gadan. Haka Yaya Nana ta kira y'an aiki mata guda biyu suka taimaka mata aka kama su Hindatun aka kai su mota, Yaya Nana ta tafi da d'aya daga cikin masu aikin mata ce za ta kai sa,ar Ummi Ishalle dan kar su tafi su kad'ai tun da ABIDA yarinya ce kuma itama Yaya Nanar ba sanin kankara gadon abin ta yi ba.Haka suka yi mota biyu suka nufi asibiti bayan Yaya Nana ta d'akko wasu kaya daga cikin kayan haihuwar Hindatun da zannuwa da duk wasu abu da za, a buk'ata har da fallaye biyu na atamfa masu iri d'aya kuma a rabe suke. Bayan zuwansu asibitin gaba d'ayan su aka shiga da su d'akin haihuwa, sai Nurse d'in suka hana kowa shiga bayan sun haihu sai aka ce mutum d'aya ta zo sai Yaya Nana ta tafi, sun shigo dakin a inda Yaya Nana ta bada fallen atamfa guda biyu iri d'aya, aka dauki jariri aka bata ta taho da murna ta baiwa ABIDA ta koma ta karb'o jaririyar ta baiwa tsohuwa da sukayi zo da ita, ta musu bayanin da nurse d'in ta mata akan sun sha wahala sosai dan haka an musu allurar barci dan su samu hutu. Ruwa ta ce za ta biyo tana jin kishi, a hanyarta ta dawowa daga siyan ruwan ne ta ji kanta ya mugun sara mata, ya kuma sara mata a karo na biyu, ledar ruwan ta jefar kafin a karo na uku ta ji kamar an buga mata guduma, nan take ta ji ana juyata kafin me wannan sai ta nemi tunani da hankalinta ta rasa dan kuwa d'ankwalinta da mayafi ta cire ta yi jifa da su sai kawai ta fara tik'ar rawa, ta sille takalmanta ta ruga bakin get d'in asibitin a guje. Mutane sai kaucewa suke suna cewa
Ga mahaukaciya nan"



Yaya Nana fitowa ta yi daga cikin asibitin tana ta soshe -soshen kai, wata bola ta hau daga tsallaken asibitin ta je ta ke tsince -tsince haka dai ta yi ta tafiya daga bola zuwa bola kai Allah ka rabamu da mak'iya hauka ba dad'i.

A can cikin asibiti tsakanin y'ar aikin Hindatun da ABIDA babu wanda ya bi ta kan dawowar Yaya Hindatu dama bokan ya ce idan Hindatu ta taka maganin babu wanda zai k'ara tambayarta kowa zai manta da ita ba wanda zai k'ara ko da tunata. Y'ar aikin mai suna hanne ita ke tambayar ABIDA

"ABIDA wanne ne d'an Hajiya a ciki"

"Haba Hanne in dai ba tsufan bane ya kama ki baki ga ni namijin bane a hannu na hakan na nufin shine na mama macen kuma ita ce ta aunty Hindatu.

"To amma dai bari sai mun tambayi malamar mai karb'ar haihuwar mu tabbatar "Hanne ta ce tana kallon ABIDA .

"Tunda baki yarda ba shikkenan " cewar ABIDA tana mata wani kallon raini. Ana haka sai ga nurse d'in ta fito rataye da jaka dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login