Showing 12001 words to 15000 words out of 33266 words

Chapter 5 - YAN UBANCI COMPLET BOOK By Maman Afrah.doc

da wuri ba sai labarin abin da Umma Kanden ta yi jiya dan haka ya dau aniyar yin auren da gaggawa in yaso sai ta mutu da bak'inciki dan dama kowa ya san irin rashin mutuncinta da har Malam d'in ma bata bari ba. Daman da y'arta ce Ayuba yake so da wallahi ba zai tab'a Amincewa da auren ba, bare ma ya san Ayuba bazai tab'a cewa yana son y'ar gidan Kande ba domin mutum ne shi da ya san abin da yake. Bayan an tattauna tsakanin Malam Hamzan da Malam Buba sun tsayar da ranar aure wata d'aya dan dama anyi waya da baban Dr Ayuba ya amince da zabin d'an nasa dana mahaifinsa. fitowar su Malam daga d'akin Malam bayan sun tattauna zancen auren ne Kande da ke tsakar gida ta shiga zage -zage da kwashe musu albarka babu wanda ya tanka ta hakan ne ya sa ta k'ara kuluwa tana banbamin masifa.


Bayan sati biyu soyayya mai cike da tsafta, k'auna mai tarin yawa ga uwa uba kulawa, Dr Ayuba yake ba baiwa Hindatu dan a sati biyun wannan zuwansa maigatari uku ga waya Hindatu har kunyar yaya Nana take ji, sabo da yawan kira da yake mata ba dare ba rana ko yaushe baya gajiya da jin daddad'ar muryarta. Gashi ya sake mata manyan wayoyi masu tsadar gaske, Idan zai zo kwa kaya da kayan makulashe kamar sa yi magana, haka zai jibgo su kamar ba gobe. Shirye -Shirye ake ta b'angaren biyu dan yanzu biki saura sati daya a inda Malam Buba ya siyar da wata k'atuwar gonarsa miliyan biyu har da rabi domin yin hidimar bikin Hindatun. Su Umma Kande kwa anbi bokan anbi Malaman amma har yau bata sauya zani ba dan so suke ita da Ikilima a fasa auren in da yadda za, a yi ma ta kashe aurenta Dr Ayuban ya aureta amma abin ya ci tura. Dan tun da aka bata labarin wanda Hindatu za ta aura ta daina barci dan bak'incikin da Y'AN UBANCI da ke damunta, ga ciki amma kuma tak'i kwantar da hankalinta tana neman kashe kanta da damuwa. Shima Aliyu yana sane da duk abin da suke shiryawa amma ya yi kamar ma bai sani ba, dan dama shi mutumin kirkine zuwansa kukayasku na farko aka bashi labarin Umma Kande da Ikilima shi yasa ya yarda ya aureta dan ya gasa musu aya a hannu, aikwa ana kan gasawa.


An yi biki lafiya lau an kai amarya gidanta a garin Kano, a unguwar shagari quarters a inda Dr Ayuba ya sayi wani tanfatsetsan gida wanda duk wanda ya gani ya san an kashe nairori. Motocin da suka d'auki amarya kansu abin kallo ne dan a kukayasku akayi bikin gaba d'aya sai da aka kai amarya ne washe gari aka shirya kwarya -kwaryar dinner, yadda Umma Kande ta yi ta fad'a da mutane yasa Malam Buba ya hanata rakiyar amarya, ita kuma Ikilima ya ce kar ta je sabo da cikinta ya tsufa, amma haka suka murde kunne suka bi y'an kai amarya dan ita Kande cewa ta yi sai Malam ya bata gadonta tunda rabon gado yake ya siyar da gona akan bikin kwantan yarsa to kwa ko ya mutu Hindatu bata da gado ta ci kashinta.


Ana shiga garin Kano Umma Kande da Ikilima suka fara share hawaye ganin irin birnin da aka kawo Hindatun, ai da aka bud'e get duk yawan Motocin nan sai da suka shige harabar gidan, mamaki bak'inciki hassada dana sani su suka tirnuke su Umma Kanden, dana sanin k'wacen Aliyu da Ikilima ta yiwa Hindatun gashi yanzu Allah ya bata wanda baza, ma a had'a shi da Aliyun ba. Ganin gidan da aka kai Hindatun Umma Kande kamar ta yi hauka. Yanayin zafi ne haka duk y'ay'ansu aka basu part guda ga abinci da naman kaji ga lemuka masu sanyi ga a. c amma duk sanyin a. c nan bai sa Umma Kande da Ikilima sun rintsa ba sabo da bak'inciki.Haka washe gari aka je aka yi dinner mai k'ayatarwa, ganin amaryar tana sanyae da kayan alfarmar sai murmushi angon ke saka ta a wurin kuwa kamar dai naira ta yi kukan dole irin yadda ake zubar da kud'ad'e. Sai dai mu ce Allah bada zama lafiya da zuri, a dayyiba. Washe gari aka dauko y'an kukayasku aka maidosu garrinsu kowa da envelope mai d'auke da 5k inji angon Hindatu mutane sai albarka suke sanyawa amma banda uwar amarya Kande da Ikilima da suke ji kamar su hadiyi zuciya ga bak'incikin yaudarar da bokaye da Malaman tsubbunsu suka musu na cewa sai a wurin daurin aure za, a fasa auren amma gashi aure ya dauru har amaryar ta tare =??



Tunda akayi auren Hindatu ta canja ta zama kamar balarabiya, ga kulawa, kai ko ganin gida Dr bai barinta ta je, sai da Ikilima ta haihu sannan ya barta ta je suna, a inda ta kai atamfofi da lesina cikin akwati kayan baby ma akwati guda kai hatta IMRAN ma sai da ta masa nashi akwatin amma ba ko godiya. Ranar suna yarinya ta ci suna ABIDA akayi taro aka gama sannan suka wuce maigatari ita da yaya Nana tayi kwana biyu, daga nan ta wuce kukayasku ta yi kwana biyu sannan ta direbanta ya je ya maidota.




*BAYAN SHEKARA D'AYA*


Lokacin har Dr Ayuba sun yanke shawara da shi da iyayensa akan ya je k'asar chaina ya musu aiki na wasu shekaru in ya so daga baya sai ya dawo k'asar tashi ya cigaba da aiki. Ya amince da wannan batu yanzu sai shirin komawa suke abin su. Umma Kande da jin Hindatu za su koma k'asar waje ta kasa zaune ta kasa tsaye tana shige da fita akan ta hana tafiyar amma hakan bai iyu ba dan ko kad'an bata ji ana zancen fasawa ba, dan haka sai ta je gidan Ikilima suka shirya wata k'ullalliya akan Ikilima ta bata IMRAN kyauta dan a tafi dashi k'asar waje ta haka ne kad'ai zasu cimma burinsu akan Hindatun. Sannan kuma riba biyu tunda ga jininsu shima zai je k'asar waje. Sosai Ikilima ta yi murna da wannan shawara ta mahaifiyarta, dan ta san Hindatu ba za ta tab'a cutar mata da d'a ba,kuma ta san Aliyu ma ba zai hana ba tunda bashi da buri sama da IMRAN ya samu ingantaccen ilimi idan kwa ya ji zai yi karatu a k'asar waje to tabbas ba zai hana ba. A inda matsalar take shine tana wajen Malam shine zai hana ya kawo hujjar da bata da wani tushe,haka dai suka gama shawarar aka bar komai a hannun umma Kande dan tace ta san yadda za ta shawo kan al,amarin.Bayan ta koma gida ta je jikinta sanyi k'alaw sannan kuma tana yawan yin tagumi sosai alamomin damuwa suka bayyana, tun Ummi Ishalle bata kawo aka ba har dai ta fara tunanin tambayar Umma Kanden ko lafiya dan gaba d'aya ita ma yanzu ta fara tunanin ko dai Ikilima ce bata da lafiya domin ba k'aramin abu bane zai sanya Umma Kanden cikin damuwa, yanke hukunci ta yi akan ta tambayeta abin da ke faruwa idan bata fad'a mata ba shikenan.

"Ummar Ikilima dan Allah me yake damunki, ki ke yin tagumi ko Ikilima ce ba lafiya " cewar Ummi Ishalle.

Shiru umma Kanden ta yi kamar bata ji ba, har Ummi Ishalle ta fitar da rai cewa za ta yi magana sai kuma ta ce

"wallahi Ikilima lafiyarta k'alaw kawai dai yau ta zomin da wata magana ne wacce ta shallake tunanina, sannan kuma na k'ara gane cewa Ikilima yarinya ce mai hangen nesa da kuma k'aunar y'ar uwarta " ta k'arasa fad'a cikin sanyin murya.

"Ikon Allah to tunda dai har hangen nesa ta yi, kya saka kan ki cikin damuwa ,ai abin ki yaba mata ne ki kuma yi alfahri da ita domin yaro yana son a k'arfafa masa gwiwa a duk lokacin da ya yi abin yabawa"

"Hakane maganarki dutse sai dai wani hanzari ba gudu b???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a abin da ta fad'a ne nake shakkun fad'arsa dan gudun kar abin kir ki ya zama na tsiya "

mamaki ne ya turnuk'e Ummi Ishalle ganin wai yau itace Kande ke yiwa zance a nutse haka, kuma ma tunda Allah ya had'a su zama bata tab'a yi mata zancen da ya shafeta ba, kai yo da ita hirar arzik'i ake da ita? ba dan zato zunubi ba da ta ce akwai wata k'ullalliya, amma kuma anaso ka kyautata zato akan mutum. Ajiyar zuciya Ummi Ishalle ta sauke kafin ta ce

."Ai a rayuwa abin kirki baya tab'a zama na tsiya, duk abin da yake mai kyau to da kyansa yake dawwama, sannan kuma abin da yake marar kyau shima da rashin kyau yake dawwama"

"Tabbas maganarki haka take yaya Ishalle, amma nasan Malam ba zai karbi abincin a hannu na amma idan a hannunki ne zai amince da batun "


"Tabd'i yau ita Ummar Ikilima ce kira da yaya, lallai abincin babba ne sai yanzu ta gane abin da take so ta mata wato wata magana take so ta kai mata wajen Malam, tace a ranta a fili kuma ta ce ki fad'i =?
? menene insha Allah zan sanar da Malam kuma da yardar Allah zai amince ya karbI maganar da hannu biyu "


"To yaya dama ba wani abu bane Ikilima tunda har yanzu Hindatu Allah bai bata rabon haihuwa ba kuma gashi har ana shirin burinsu k'asar zuwa k'asar waje, kuma bata da kowa acan sannan mijin zai ke tafiya wajen aiki bata da mai tayata hira, shine tace ta karb'i IMRAN ta tafi dashi ta bata shirt halak malak, to shine nake ganin kar Malam yace nazari iyu ba amma in kece zai fi amincewa "

Shiru Ummi Ishalle ta yi gabanta na fad'uwa da k'arfi jin abin da Ummar Ikilima ta zo dashi, tsoronta d'aya kar azo a samu matsala dan ta san tabbas akwai wata manufa da suke da ita in ba haka ba ba ga Nana nan ma
bata haihuwa ba amma basu bata rikon d'an ba sai Hindatu ko dan ita mijinta talaka ne tabbas ko dan kud'i za su bata da kuma son d'an ya je k'asar waje to lallai akwai wata manufa ta daban"ta ke zancen zuci.


"Yaya kin yi shiru ko kina ganin abin ba mai yiwuwa bane,amma dai na ga kaifin basirar yarinyar nan ki tuna duk irin wahalar da uwa ke yi wajen d'aukan ciki da haihuwa amma ta iya cewa ta d'au d''a sukutum ta baiwa y'ar uwarta in ba a yaba mata ba ai ba, a ga laifinta ba"

"Haba Ummar Ikilima ba shiru na yi ba kuma wa yace miki ba,a yaba kaifin tunaninta ba, kawai dai ina tunanin ta yadda zan tunkari Malam ne, nima baki ga yadda Ikilima ta birgeni ba sai dai fatan Allah k'ara soyayyar y'an uwanta a tsakaninsu"

"Yawwa yaya na gode Allah k'ara had'a kan mu"

"Amin zan tuntub'i Malam d'in in ya dawo "

"Toh shikenan bari in shiga daga ciki "cewar Umma Kande murmushin samun nasara na neman kufce mata.

"Toh "Ummi Ishalle ta ce tana komawa d'aki ta zauna ta rafka uban tagumi duk abun duniya ya isheta, ta san kawai addu, a ce kawai za ta dage da ita akan Allah kawar da duk mugun nufinsu shi kuma yaron in akwai rabon zuwansa k'asar waje to Allah tabbatar da alkairi.


Bayan dawowar Malam gida Ummi Ishalle ta tunkari Malam d'in da maganar cikin hikima da tausa lafazi,sannan kuma ko da ta fad'a masa bata sanar da shi ba cewa Ummar Ikilima ce ta fad'a mata ba. Dan zai yi tunanin wani abu dan haka sai ta ce masa Hindatu ce ta sanar mata kuma daman kafin ta zo wajensa sai da suka yi waya da Hindatun ta sanar mata komai sosai ita Hindatu ta yi murna da batun ta ji dad'i sosai kuma ta san Dr ma zai yi murna dan akwaishi da son yara. Hakan ne ya baiwa Ummi Ishalle k'arfin gwiwar sanar da Malam d'in. Cikin iko da hikimar Ubangiji Malam d'in ya amince da maganar, bayan ya kira Dr Ayuba sun yi magana ya nuna amincewarsa dan dama Hindatun ta sanar dashi. Haka Ummi Ishalle ta sanar da Ummar Ikilima sosai ta yi murna itama ta kira Ikilima a waya ta fad'a mata dan yanzu kowa da wayarsa kuma ba aikin kowa bane sai na Hindatu.

Lokacin da Ikilima ta tunkari Aliyu da maganar sai da ya k'are mata kallon tsaf yana son gano manufarta akan haka amma bai fahimci komai ba, amma dai ya san da wata a k'asa abin da ya sa ya amince kwa dan ya yaba da natsuwa da hankalin Hindatun ya kuma san Hindatu ba za ta tab'a cutar da IMRAN ba.


An shirya IMRAN tsaf a inda Ikilima da Aliyu suka kaishi Kanon a mota, da Aliyun ya ga tana wani rawar kai wai ita mai motar miji sai da ya biya tasha ya yi lodin Kano ya cika baya da but ita kuma da IMRAN da ABIDA suka zauna a gaba sai wani cika take tana batsewa wai ba wanda zai gane motar mijinta ce>?#?.Sun je lafiya ya sauke mutane a tasha su kuma ya wuce da su gidan Hindatun, sun samu tarb'a mai kyau a inda masu aiki suka cika musu gabansu da kayan marmari da abubuwan motsa baki IMRAN kwa sai murna yake ganin hadaddan gidan da aka ce anan za, a barshi dama kuma ya san anty Hindatu tana kai masa kayan dad'i da kayan sawa yana k'aunarta duk da Mamansa Ikilima ta ce kar ta k'ara ji yana ce mata anty amma shi bai daina ba sabo d'a malaminsu na islamiya yace duk wanda ya fisu kar suke fad'ar sunansa. Haka suka baro IMRAN a can ko kuka bai yi ba yana d'aga musu hannu haka suka tafi Hindatu kan foziya kamar ta ari baki shima kuma Dr haka, dan ko da ya sanar da iyayensa ma sunyi murna da musu fatan Allah basu Ikon rik'o.



Sun samu tashi zuwa k'asar chaina a inda suka samu rakiyar y'an uwa da abokan arzik'i zuwa airport, sun sauka lafiya inda suka sauka a wani katafaran gida wanda bashi da nisa da asibitin da Dr Ayuba zai yi musu aiki. Rayuwa ce suke mai cike da farincikin da kulawa da kuma girmama juna tsarkakekkiyar k'auna mai tarin bege da kuma shauk'i su ma, auratan ke baiwa juna duk da Dr Ayuba yana fita wurin aiki amma hakan bai hana shi baiwa iyalansa kulawa ba da sauke nauyin hak'k'in kulawar su da ke kansa. Dan hatta IMRAN ya d'aukeshi kamar d'an da ya haifa ya sanya shi a makaranta mai tsada gashi babu abin da ya nema ya rasa.




"Haba yaya Ikilima ki masa a hankali mana shi fa bawai wurinki ne ba ya son zuwa ba a, a gidan baba Malam ne bai so na tafi na barshi "Hindatu ta fad'a ganin Ikilima tana yiwa yaron tsawa kamar za ta kai masa duka.

"To uwar iyayi na ga dai d'ana ne ko zaki hana na masa fad'a "Ta fad'a tana wani mata kallo mai nuna tsantsar tsana da bak'inciki.

"ki yi hak'uri "Hindatu ta ce cikin sanyin muryarta.

Banza ta yi da ita ta mik'a hannu ta rik'o hannun IMRAN da ta ke gani kamar wani d'an shugaban k'asa, ga wani kamshi da yake tashi daga jikinsa mai dadin shak'a. Cikin gidan ta shiga rik'e da IMRAN wanda ke waiwayen Hindatu,ita kuma Hindatun ta tsaya ta cewa direban ya jirata a mota bayan ya shigar da kayayyakin har da kayan IMRAN. Itama baya ta mara musu ta shiga gidan d'auke da sallama ,IMRAN ne ya amsa mata ta samu wuri akan tabarmar da aka dora kayan da suka zo da su ta zauna. Gaishe da Ikilima ta yi ta amsa mata ba yabo ba fallasa,daga wannan bata k'ara mata magana ba itama Hindatun bakinta ta kama take danna wayarta, ita kuma Ikilima sai tambayoyi take jerowa IMRAN akan k'asar waje wani ya bata amsa wani kuma ya yi shiru dan dama ba mai hayaniya bane sosai. Ana haka sai ga Aliyu ya shigo d'auke da pure water leda guda mai sanyi sai kuma d'aya hannun rike da bark'ar leda mai d'auke da lemukan roba guda hudu .

"Assalamu Alaikum " yace yana nuna tsantsar farincikin ganin IMRAN da Hindatu.

"Wa alaikumus salam "Hindatu tace tana murmushi kamar yadda shima ya ke murmushin dan ita Ikilima hankalinta yanzu yana kan kayan da aka kawo.

"Oyoyo abba" IMRAN ya tafi da murna ya rungume mahaifinsa.
Bayan gaishe -gaishe da aka gabatar tsakanin Aliyu da Hindatu da IMRAN shi kuma aka shiga hirar yaushe gamo sosai Hindatu da IMRAN suka saki jiki da Aliyun da ya gabatar musu da ruwan sanyi da lemon ma Hindatun ce kawai ta sha ruwan amma bata sha lemon ba. Kuma koda Aliyu ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login