Showing 18001 words to 21000 words out of 33266 words

Chapter 7 - YAN UBANCI COMPLET BOOK By Maman Afrah.doc

lokacin tashin aiki ya yi.

"Malama ina da tambaya,"Hanne ta tambayeta tana nufar inda take itama ABIDA tashi ta yi ta bi bayanta.

"Ina jin ki"cewar nurse d'in ta tsaya tana sauraren abin da Hanne za ta ce.

"Dama matan nan da muka kawo su biyu, da suka haihu aka ajiye su a d'akin hutu shine mu ke so a fad'a mana jinsin da kowacce ta haifa.

"OK bak'ar ce ta haifi namiji, farar kuma ta haifi mace" tana gama fad'in haka ta juya abinta ta tafi ba tare da ta ce komai ba, sannan ba tare da ta saurari wani abu daga garesu ba.

"To yanzu tunda kin ji da kunnenki ai sai ki yarda "ABIDA ta fad'a tana juyawa ta koma in da suke zaune.

"ki yi hak'uri ABIDA ba wai yarda bane ban yi ba kawai dai inaso a tabbatar tunda su duka baas cikin hayyacinsu lokacin da suka haihu" Cewar Hanne lokacin da ta k'araso wurin ABIDA.

"Ke ki ka sani "Ta ce tana tab'e baki.

Bayan kamar minti talatin, aka kira su ABIDA domin su zo wurin y'an uwansu, haka su ka shigo d'auke da yaran, ABIDA na shigowa ta nufi gadon da Ikilima ke kwance tana murmushi,Hindatu na ganin Hanne ta nufo gadon da ta ke d'auke da jariri ya sa ta fahimci cewa na hannun Hanne shine abin da ta haifa, wasu hawayen murna da jin dad'i ne suka fara gangarowa zuwa kumatunta, dan ta kasa tantance irin farincikin da take ciki. Hannunta har karkarwa yake da Hanne ta mik'a masa jaririyarta hannayenta ta zaga sama tana mai godewa Allah akan kyautar da ya mata, tana karb'ar y'ar ta mata addu, a sannan ta rungume ta tana jin wata iriyar k'auna da soyayyar da kowacce uwa ke yiwa y'arta. Itama Hanne sai murmushin take zabgawa ganin uwar d'akinta na cikin farinciki dan tana jin dadin zama da Hindatu domin Mutuniyar kirki ce ta d'auketa kamar uwa sabo da tana girmamata iya zaman da su ka yi bata tab'a b'ata mata ba kai ba ita kad'ai bama hatta sauran ma,aikatan babu wanda zai koka da Hindatun.

"Baba Hanne kin ga kyautar da Ubangiji ya min" ta ce tana dariyar murna.

"Na gani Hajiya hak'ik'a Allah shine abin godiya ,shine mai ji kuma mai gani ,shi ke bayarwa a lokacin da ya so kuma shine ke hanawa a lokacin da ya so dan haka godiya ta tabbata Allah madaukaki " Cewar Hanne.

"Wannan haka ya ke Baba Hanne Alhamdulillah "Hindatu ta ce cikin farinciki.

Tunawa da ta yi da y'ar uwarta Ikilima ya sa ta yi saurin juyawa inda gadonta ya ke domin lokacin da suka farka ma ta ganta kafin su ABIDA su shigo har ta ke mata sannu amma Ikilimar ta yi banza da ita ta k'aura kai gefe. Yanzu ma tana juyawa ta ga Ikilima da ABIDA sun zubo musu ido suna zance k'asa -k'asa.

"Aunty Ikilima bari Baba Hanne ta miko miki ita ki ganta, ABIDA Milo min shi nima in ganshi " Ta ce fuskarta na nuna ainihin tsantsar farincikin da take ciki.

"A, a kar ma a miko min ita ba sai na ganta ba, kuma shima ba sai kin ganshi ba, yo da Allah na tuba dan kin haifi mace ma har wani abin murna ne, ai da namiji ne sai ki yi wannan d'aga kan tunda mun san namiji shi ke da rabo me talla idan tsoronsa mutuwa ta riskeshi"

Wani daci da rad'ad'i ne suka ziyarci zuciyar Hindatu jin kalaman da suka fito daga bakin Ikilima.

Wai dan Allah Aunty Ikilima me na miki ne a rayuwa da bakya son ko kad'an ki ganni ina farinciki?" Hindatu ta fad'a wasu hawaye masu zafi na zubo mata, tabbas tana jin ciwon abinda iko ke mata amma na yau ya dara na kullum kuma hakan ba ya rasa nasaba da ciwon haihuwar da ta ji sannan kuma Ikilima ta nuna bama ta k'aunar ganin abin da ta haifa d'in kuma itama ba za ta bata nata d'an ba tare gani. Lallai k'iyayyar ba k'arama ba ce.

"Dalla can malama kar ki dameni, kuma wa ya ce miki sai ka yiwa mutum abu ya ke tsanarka, ko kad'an ba haka bane duk wanda ba ya k'aunarta to kwa baya kaunarka har gaba da abada! dan haka ki rik'e yarki na rike d'ana " Ta ce tana mike kafarta akan gadon.

Juyawa Hindatun ta yi tana kallon Hanne, jin maganar da y'ar uwarta ta fad'a har zuwa lokacin hawaye basu bar kwaranya ba idanunta ba.

"Ki yi hak'uri Hindatu komai mai wucewa ne wataran sai labari, ke labarin mai ba,a ji ba" Cewar Hanne tana dafa kafadar Hindatu don lallashinta domin ta ga sauran mutane da ke d'akin sun fara ankara duk da kowa sabgar gabanshi ya ke.

"To munafuka da ki daurewa munafurci tsantsa ai dai y'aruwata ce kuma ba, a canjawa tuwo suna " Ikilima ta ce dan zuwa yanzu ta gama k'uluwa domin ta fahimci cewar Yaya Nana ta tafi ma,ana magani ya fara aiki sabo da ta san sun manta da ita kamar yadda boka ya ce, amma daman mantuwar banda ita, dan haka ji take kamar ta je ta shak'e Hindatun har sai ta mutu MI's, dan yanzu ne yan ubanci ya fara tunda ta haihu.

Daga Hanne har Hindatu babu wanda ya k'ara tanka mata, ana haka ta ce Hanne ta miko mata waya dan so take ta kira Dr ta sanar dashi dan direbobin da suka kawosu ma ta ce su koma gida kuma kar su sanar da kowa halin da ake ciki. Ana miko mata waya ta ga 16 miss call na Dr sai 4Miss call na Ummi Ishalle ,Umminta ta fara kira ta sanarwa sosai ta yi murna da godiya ga Allah, kafin daga bisani ta kira Dr.


"Haba ina ki ka shiga tun dazu na sa a duboki cikin taron nan ba, a ganki ba, kuma na kira waya baki d'auka ba?"



"Albishirinka" Ta ce cike da farincikin, daga can Dr yana jin irin zak'uwa da son sanar da shi albishir d'in a muryarta.

"Amma dai duk albishir d'in da za ki min ba kamar ganinki ba, na fi so in ganki ko hankalina zai kwanta "

"To nima ina son ganinka,bari in kwatanta maka in da na ke sai ka zo "

"OK ba damuwa, kina nufin bakya wurin taron nan "

"Eh ban je wurin bama yanzu haka ina government Hospital Allah ya saukeni lafiya na samu...

"Babu irin wannan wasan tsakaninmu, dan Allah kar ki sa zuciyata ta tsinke wallahi har kin sa na d'ora rai akan zan ga jinina a yau! "Dr ya katseta cikin hanzari.

"Wallahi da gaske nake,ka kwantar da hankalinka ka....
Ai kafin ta kai k'arshen maganar tata ba ya kashe wayar, daman lokacin an kammala komai sai abubuwan rabo da ake rabawa, a hanzarce Dr ya kira direban da ya kawo su key d'in motar ya karb'a ,ya nufi in da aka ajiye motar ya bud'e yana k'ok'arin shiga IMRAN ya hangoshi da sauri ya nufi inda ya ke dan ya san ba karamin abu bane da zai sa Daddyn ya bar wurin taron ba kuma ba tare da kowa a tare da shi ba, direba bai yi driving d'inshi ba sannan kuma bai nemi IMRAN d'in ba. Ya kusa k'arasawa wurin Dr ya figi motar ya fita daga harabar asibitin. Wurin direban abokan Daddyn ya nufa ya karb'i aron key d'in mota ya marawa Dr Ayuba baya dan ko kad'an bai yi tunanin kiransa a waya ba.

A asibiti kuwa Hindatu jin da ta yi Dr ya kashe wayar ta kasa daina murmushi dan ta san yanzu zai bayyana a asibitin, itama Hanne murmushin take, jin an doka wani tsaki ya sa Hanne da Hindatun kallon Ikilima da ta yi tsakin, kallon ido cikin ido sukayi itand da Ikilima kafin ta mik'awa Hanne jaririyar ta sakko da kafafunta k'asa a hankali dan har lokacin bata gama dawowa dai-dai ba tana d'an jin jikinta na ciwo hakan ma ba zai rasa nasaba da rashin wanka ba, dan da ta yi wanka da ruwan zafi da ciwon jikin ya barta .A haka ta lallab'a ta k'arasa gadon y'ar uwarta duk da harara da Ikilima ke aiko mata, tana zuwa ta ce

"Haba y'ar uwata bai kamata wannan kalaman da ki ka yi yanzu ya fito daga bakin ki ba,ni fa y'ar uwarki ce wallahi har cikin raina nake kaunarki ban tab'a miki Y'AN UBANCI ba...

"Dan Allah Hindatu ki kyaleni kaina ciwo yake banason hayaniya "Ikilima ta katseta cikin hanntara.

" Shikenan Allah baki lafiya "

"To na ji ai sai ki koma gadonki"

"Toh bari na ga jinjirin,, kawo shi ABIDA " Ta ce tana mik'a hannu ya za ta karbeshi.
Da kamar ABIDA ba za ta bata shi ba, kuma koda me ta tuna ta mik'a mata shine.
"Tabarakalla Masha Allah"cewar Hindatu ganin yaron kyakkyawa da shi ta jima tana kallonshi shima tana jin kaunarsa kamar dai yadda ta ji kaunar jaririyarta, dan ita duk d'aya ta daukesu duk da ba kamar wanda ka haifa ba amma shima zai sai ta ji shima tana kaunarsa. Addu, a ta tottofa masa har sai da Ikilima ta ce ta daina tofeshi da matan, sannan ta yi murmushi ta mik'awa ABIDA yaron ta koma gadonta. Zamanta ke da wuya sai ga Dr ya shigo da shi da Likita da kuma nurse guda d'aya, suna shigowa sai ga IMRAN ya shigo hankali tashe kana ganinsa ka san akwai matsala dan duk ya rud'e da ganin Dr Ayuba ya nufo asibitin a tunaninshi ko Mamansa da ABIDA ne suka mata wani abu dan barin su da akayi a gidama hankalinsa bai kwanta ba dan ya gama sanin halin Mama Ikilima. Dan haka ma dak'er ya kawo kansa asibitin,Yana shigowa idanunsa suka sauka akan babyn =?v? da ke rungume a hannun Mummynsa, zaro idanu ya yi baki sake yake kallon Hindatu wani irin farinciki da annushuwa ya ke ji,bai gama mamakin ba ya ga Daddy (Dr Ayuba) ya je ya rungumeta ita da =?v? babyn sai godiya da kirari ya ke yiwa Ubangiji, akan kyautar da ya masa.

"Sannu my Hindy kin min komai a rayuwa Allah ne ya bamu amma tabbas kece sila Nagode miki kwarai da gaske sannan kuma albishir d'in nan da ki ka min na mallaka miki day'a daga cikin asibitocina, kuma hajjin bana ku shirya ke da Ummi ,Umma da kuma Malam" Ya ce yana kallonta.

"Masha Allah muna godiya Allah k'ara bud'i mai albarka da nisan kwana mai amfani, ya barmu tare, amma kuma su dai sa je ni kuma idan na yaye babyn mu sai in je" Ta ce tana kashe masa ido d'aya.

"Hindatu ni mantawa da tawa haihuwar ki ka yi baki fad'a masa ba"Ikilima tace tana dariyar da ta fi kuka ciwo ,sabo da hajjin da aka biya musu a kokon ranta duk da har mahaifiyarta aka biyawa hakan bai sa ta ji dad'i a ranta ba.

Wannan maganar da Ikilima ta yi ita tasa IMRAN ya lura da su dan daga shi har Dr babu wanda ya gansu, ita kuma Hindatu ganin mai gidanta cikin wani irin yalwataccen farinciki ya sa ta manta da su a wurin.

" Ayya walllahi aunty Ikilima na sha,afa ne, sweet heart tare fa aka kawomu da aunty Ikilima ita kuma baby boy muka samu "ta ce tana sakar masa baby da suka rik'eta tare.

"Kai Masha Allah haihuwar har biyu to bari in gama ganin wannan sai in ganshi ko" yace lokacin da ya sanya bakinsa jikin kunnen baby zai mata kiran salla.

Shi kuma IMRAN gadon da Mamansa ta ke ya nufa yana cewa

"Wallahi Mama bamu lur??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a da ku ba,ashe har ABIDA ma kuna tare amma bata min magana ba " Yace sanda ya ja wata kujera ya zauna a gaban gadon Ikilima.

"Eh ni na hana ABIDA ta maka magana sabo da na ga hankalinku ya tattara akan Hindatu shi yasa, ka ga idan kun gama murnar sai ka dawo wurina nima ka mini sannu "Cewar Ikilima tana wani yatsina fuska, dan daga Dr har Hindatu babu wanda ya san me take yi hankalinsu na kan babyn. Bare Hanne da tun shigowar su Dr ta fita waje.





Haka aka sallamesu daga asibitin dan dama lafiya k'alaw sulast haihu. Ran kowa fari kal amma ban da ran Ikilima da ta ke jinshi cike kuma cunkushe da tarin bak'inciki, sabo da cikinta da bai ci akan wacce ta sa aka mata aikin dominta ba, gashi yanzu mafarkinsu ba zama gaskiya ba domin ita ko kad'an bata damu da maganin da Yaya Nana ta taka ba, hankalinta ya karkata ne ga cikar burinsu wato Hindatu domin ita ce yanzu gaba d'aya y'an ubancin ya karkata akanta sabo da ita ce ta had'a komai na rayuwa wanda su ba su samu ba. Duk da k'ok'arinta na ganin ba su yi rashin komai ba a rayuwa amma hakan bai sa sun raga mata ba. Dan ko zancen da sukayi wato Ikilima da ABIDA akan b'atan Yaya Nana, da ABIDA ke bata shawara akan asa bokan ya karya maganin ta dawo tunda ba ita akayi niyyar yiwa ba Ikilima cewa ta yi

"Ke dalla k'yaleta ta karata can an rage mugun iri"

"Kuma hakane fa mama" ABIDA ta ce, suka fashe da dariya.


Bayan sun dawo gidan Hindatu daga asibitin, komai da komai na baby aka siyowa Ikilima Hindatu ta sanya IMRAN ya iyo shopping babu abinda babu wani abun ma Ikilima bata san amfaninsa ba, amma haka Hindatun ta yi list aka soya komai. Hatta da kayan shayi an ajiye mata manyan gwangwanaye isassu ga nama Kala-kala kafin a d'auke wata kulan naman an kawo wani. Dan Hindatu ta hanasu tafiya wai sai ta warware. Ko su Malam Buba da Ummi Ishalle da kuma Umma Kande nan suka zo ganin baby anan har Malam ke yiwa Iko fad'a akan ta zo ta zauna a gidan k'anwarta menene amfanin hakan. Haka dai Hindatun ta Lallab'a Malam Buba wai kai ta dan huta sabo da d'anyen jiki na jego, da haka suka tausheshi ita da Ummi Ishalle har dai ya hak'ura. Amma ita Umma Kande cewa ta yi karta yarda ta tafi ta zauna anan ayi suna tare da na Hindatun dan Dr Ayuba ya yankawa d'an nata abin yanka dan ta san ba lallai Aliyu ya bata yanka ba, sabo a sunan ABIDA ma wasu d'an akuyabin ya siyo sai Hindatu ce ta bayar ask siyo manyan raguna guda biyu dan haka yanzu ma gwara ayi sunan tare yanda Dr zai mata duk abin da ya yiwa Hindatun.Sun yiwa Dr Ayuba godiya akan biya musu makka da ya yi, ya nuna musu babu komai kawai su godewa Allah domin shi ne ya kirasu, shi Dr sanadi kawai ya yi. Sun ji dad'i da karamcin irin na sirikinsu Dr amma umma kande a cikin ranta haushin Dr Ayuba ta ke ji saboda bai biyawa Ikilima ba


Ranar da suka cika kwana biyar da haihuwa, Dr ya bada buhun shinkafa 2 taliya cartoon 3 buhun nikarkiyar masara dana hatsi sai kuma kud'in raguna guda biyu. Duk taurin rai irin na Ikilima da ABIDA sai da suka ji dad'i kuma suka ji a ransu lallai Hindatu mutumce kuma tabbas tana da kyan zuciya, sai dai hakan bai sa sun ji cewa Wataran za su janye mugun nufinsu akanta ba. Suna ya kama guda biyu anayi a Kano ana kuma yi a Gumel, Dr ya kashe kud'i sosai an ci an sha an raba kaya na gani a fad'a yarinya ta ci suna Fadila kowa ya yi farinciki da wannan rana. A can Gumel ma ana ta buduri su kande anci shinkafa an ci nama har sai da aka kwana zuwa bayi ana gudawa, y'an garin kukayasku kwa sun sha gori wai k'walamar shinkafa suka zo.Yaro ya ci suna SAFWAN an rak'ashe sosai su Ikilima manyan makwadaita wai Allah sa ta k'ara haihuwa a Kano, in ji umma kande da ta ke sud'in hannu tana cin naman kai >?u?


Yaya Nana tun da ta tafi daga kan wata bola haka ta kama hanya tana ta tafiya har sai da ta gaji sosai k'arfinta ya k'are ta galabaita sosai ga yunwa ga wahalar tafiya,haka ta fita daga cikin gari ta fara fita wajen gari gajiyar ce ta mata yawa ta samu wata bishiya zauna tun tana zaune har ta fara gyara gyad'i har dai barci ya d'auketa a wurin cikin barci ta zame ta kwanta a wurin. Bayan kamar awa biyu ta farka tana farkawa ta ji yunwa sosai dan dama itace ta tasheta. Wahiawa ta yi ta ga babu wani abun da za ta ci sai kawai ta fara cirar ciyawa tana sawa a baki,tana ta cirar ganyen ciyayi tana ci sai ga wata mota ce hilux ta tsaya daga can baya daga in da ta ke mutane biyu ne suka fito daga motar d'aya daga mazaunin direba d'aya kuma daga gefen me zaman banza,nan kowa ya lura da Yaya Nana da ke cin ciyawa, cikin hanzari suka k'arasa wurinta, suka dakatar da ita daga cin ciyawa amma ta k'i anan d'aya ya koma cikin motar ya d'akko biredi da pure water guda biyu tana hango biredin nan ta dena cin ciyawar da gudu ta nufi mutumin me d'auke da biredin ta warce biredin ledar ta yaga ta fara ci kamar bata tab'a cin abinci ba. Tausayinta ya kamasu, ganin ta zauna ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login