Showing 24001 words to 27000 words out of 33266 words

Chapter 9 - YAN UBANCI COMPLET BOOK By Maman Afrah.doc

babu wanda Ikilima bata mata ba wai ta shanye mata d'a bayan ita kanta Hindatun bata san zai sanya sunan ba sai da ya rada sunan ya sanar mata. Aikwa yarinya ta sha kaya kamar ba gobe.


Wata ranar juma, a ne mummy Hindatu na zaune a falon kasa tana kallo sai ga ABIDA ta yi sallama, amsa mata ta yi cike da nuna jin dad'in zuwanta, duk kuwa da su suna nuna mata basu son ta ita kuma bata tab'a jin bata son su ba ko da kuwa a ranta ne balle a fili. Nan ta sa mai aiki ta kai mata kayanta d'aki sannan aka gabatar mata da aminci da da lemo, anan ta ci ta koshi ta bi lafiyar gado dan mummy Hindatu ta ce ta je ta kwanta ta huta.


Washe gari ya kama weekend dan haka Dr yana gida, idan kwa yana gida to ya kan zauna da iyalansa su yi hira cikin farinciki da kwanciyar hankali. Yau ma hakan ce ta kasance dan itama FADILA ranar bata je gidan Auntie ILHAM ba daman idan ta je ta kan tafi da uniform d'in islamiya daga can a kaita makaranta, domin karfe uku ta ke tafiya islamiya, dan haka yau tana gida. Sun zauna part d'in Dr a falon k'asa suna ta hira FADILA yar gata tana ta shagwab'a abin ta, suna cikin haka ABIDA ta shigo da sallama duk da Hindatun ta yi mamakin ganinta dan basa shiga b'angaren Dr ko gaisuwa ce sai dai in ya shigo part d'in Hindatu su gaishe shi,amma haka ta danne mamakin ta, amsa sallamar ta yi da walwala a inda ABIDA ta zauna a k'asan capet akayi -akayi ta hau kujera amma ta k'i ta zauna a k'asa. Gaishe da Dr ta shiga yi dan dama sun gaisa da mummy Hindatu, sannan ta sa FADILA ma ta je har d'akin da ta sauka ta gaisheta. Nan ABIDA ta ce

"Dama Mamata ce tace in zo in gaisheta idan na zo " tace tana sadda kai k'asa.



"A lallai Nagode da wannan sako da ta iyo mini, nima kuma idan kin koma ki isar min da sakon gaisuwata a gareta.

"To in Allah ya yarda zan fad'a mata "Cewar ABIDA tana murmushi ganin ya amsa mata ba tare da ya nuna komai ba ko da kuwa a fuskarsa ne. Jimawa kad'an ta yi kafin ta musu sallama ta tashi za ta tafi, Mama Hindatu ta ce da FADILA.

"Ku je ki zauna a d'akinta man ki tayata hira kin game ita kadaice babu wanda za su yi hira"


"Lah Aunty ki barta ta yi zamanta, nima barci nake so na d'an koma"ABIDA ta yi saurin katseta dan bata son FADILA ta biyota daman dan ta yi lab'e ta ji me suke cewa shi yasa ta zo, yanzu kuma in ta fita za ta lab'e kinga =?
? da kamata akayi tana da dalili amma idan aka ganta dole za ayi tunanin me ya kawota sashen me gidan.

"To shikenan "Mummy Hindatu ta ce tana murmushi...

ABIDA kwa na fita ta samu wuri ta lab'e, ta dad'e tana sauraren hirarrakin nasu ,har za ta tafi dan babu wata muhimmiyar magana da suke sai kuma ta ji Dr ya ce

"" Ah my hindy dama inaso in sanar da ke cewa na tattara gaba d'aya takardun manya manyan kadarorin da nake da su anan Nigeria da ma wanda na tsiya a cairo zan sanya sunan FADILA a jiki domin zan mallaka mata su a matsayinta na y'ar dana haifa kwaya d'aya a duniya,sannan kuma kin san gaba d'aya takardun kadarorina akwai sign d'ina sannan akwai naki dan haka nakeso zan d'akko idan mun samu lokaci in sanya hannu kema ki sanya " Ya fad'a yana kallonta ganin ta zuba masa idanu tana masa wani kallo na mamaki.

ABIDA kwa da ke lab'e saurin sa hannu ta yi a bakinta ta rufe dan gudun kar karaji ya fito dan ta tsorata da jin maganar, ace duk wannan uban kud'in mutumin nan ya tara amma zai damkawa yarinya k'arama kamar wanna duk abin da ya mallaka? lallai Mama Ikilima ta cuceta da ta auri talaka da yanzu itama mahaifinta na da kud'i shima ita zai mallakawa.

"Haba daddyn IMRAN ya za, a yi ka ce za ka mallaka mata komai bayan......

"Dakata Hindy menene dan na mallaka mata kar ki manta fa ita kad'ai Allah ya mallaka min, kuma yanzu bawai tsufa na yi ba bare k'i ce zan dena nema a, a sanin kanki ne ina da tarin dukiya da kadarorin da ko da na mallaka mata bazan rasa wasu ba, kema kuma kina da naki, sannan IMRAN ma yana da nashi bare kice babu komai, kuma na shawarci mahaifana sun min fatan alkahiri kema ki min in mallaka mata ko hankalina zai kwanta " Dr ya dakatar da ita daga maganar da take k'ok'arin yi"

"Toh shikenan na yarda amma dai inaso ka mallaka mata wasu daga ciki, ba duka ba"

"To shikenan hakan za, a yi wani satin zan had'asu wuri d'aya sai in waro wanda zan bata tunda haka ki ke so ko" yace yana mata wani kallo

"Hakan ya yi Allah sanya alkairi " itama ta ce tana maida masa kallon da ya mata.

FADILA kwa da bata san ma me suke cewa ba tana ta rubutun home work d'inta, ko a jikinta. ABIDA kuwa jin an kai k'arshen maganar yasa ta juya za ta bar wurin cikin hanzari, tuntub'e ta yi ta dan bugu da jikin kofa, k'aran k'ofar ne ya ankarar da su akwai wani a wurin, tasowa Dr ya yi da sauri dan ganin wanda ke wurin dan bayaso kowa ya san maganar da suka tattauna dan yanzu duniya tak'i da dad'i makusancinka shi ke cin amanarka,ABIDA jin alamun tafiya yasa ta koma bayan kofar ta lab'e, dan haka da Dr ya zo bai ga kowa ba a wurin sosai ya dudduba har can k'ofar part d'in amma bai ga kowa ba hakan ya sa ya dawo. Yana shigewa ABIDA ta fito da sand'a ta koma part d'in mummy Hindatu ta koma d'akin da aka sauketa, tana shiga ta sa Mukulli ta rufe ta d'auki waya ta kira Ikilima ta shaida mata duk abin da ya faru Ikilima kamar ta zauce jin, za, a mallakawa kanakanuwar yarinyar kadarori wanda ita ya kamata ta mallaka ta ji dadinta, umarni ta yiwa ABIDA akan ta zauna kar ta taho har sai kwanakin da ta dauka sun cika dan kar ta ce za ta taho ayi zaton wani abun.


Yau ya kama juma,, a kuma yau ne kwanakin da ABIDA ta zo yi suka cika, dan har gidan Yaya IMRAN ta je ta musu kwana biyu, amma ita ILHAM sai kawai bata sakar mata fuska sabo da ta ga renin wayon ABIDA da iyayi sun yi yawa ga shegen sa idon jaraba, duk abin da IMRAN zai shigo dashi akan idonta kuma ta sha kamata tana waya tana fad'ar abin da ke faruwa a gidan wannan dalili yasa basa jituwa ita da ILHAM. Bayan ta shirya mummy Hindatu ta sa direba ya kaita Gumel, haka aka sanya mata kayanta a mota aka kai ta har gida da sha tara na arzik'i.

Dama tun a waya ABIDA ta gama sanya wani wanda sukayi primary ta re kafin ta gagara ta daina zuwa, to shima dai hakan ta ke bai yi karatum ba sai shashanci da sace-_sace kai daga baya ma ya zama dan fashi da makami, a Kano ya ke hannun iyayensa dama Gumel d'in hannun kanwar mahaifinsa ya ke da ya gagareta ta maida shi hannun iyayensa, suma yanzu asibitocin dais su masa addu, a dan sai ya bushi iska yake zuwa ya gansu. Sun had'u ne da ABIDA wani lokaci na zo Gumel ganin y'ar uwar mahaifinsa anan suka karb'i number juna dan ya bata labarin irin rayuwar da yake data tambayeshi labarin karatu, shine ta karb'i numbersa wait idan bukatan hakan ta taso. Dan haka yanzu tun a waya ta sanar dashi kuma shi tun jiya alhamis yake Gumel d'in dan yanaso ayi a gama dan ta sanar dashi irin mak'udan kud'ad'en da suke cikin tafiya.




Direban yana sauketa ya shigar mata da jakarta cikin gidan ya fito ya yi tafiyarsa, tana shigowa gidan ga Shema, u na bakin famfo tana ta shek'a amai kallon hadarin kaji ta mata ta shige d'akin Mama Ikilima .Jim kad'an suka fito daga d'akin ko sallama ba su yiwa Shema, u ba suka fice daga gidan, waya ta yiwa Okasha ya fad'a mata inda za su had'u, d'an sahu suka tare suka shiga suna dab da zuwa wurin suka sauka suka sallameshi yayi tafiyarsa, da kafa suka k'arasa wurin da Okasha ke jiransu suna zuwa suka gama tsara abin da za ayi, sun kwatanta masa gidan da kuma asibitin da Dr ayuba ke aiki daga K'arshe ABIDA ta tura masa hotunnansu ,dan sun ce ko kisa ne ya kama ayi matsawar dai za, a zo musu da takardun kadarorin, sun gama tsara komai Okasha ya ce su bar komai a hannunsa haka suka rabu da Okasha ran su fari kal shi kuma ya dawo gida ya yiwa y'ar uwar mahaifinsa sallama ya kama hanyar kano domin su fara aiwatar da aikinsu.


Tun da Okasha ya sauka a garin Kanon dabo ya je suka tsara yadda za su aiwatar da aikin, tun a ranar juma, ar suka fara bibiyar duk wani motsin Dr ayuba ta haka ne suka gane cewar takardun basa tare da shi amma kuma tabbas suna bin diddigin motsinsa ba tare da ya sani ba.



Ranar asabar da misalin karfe sha biyu na rana, Dr Ayuba ne a bayan mota sai direbansa da yake jan motar, hanyar asibinsa da ya ke aiki suka nufa, motar su Okasha na biye da su a boye ba tare da sun fahimta ba har dai direban ya yi parking Dr ya fito, mutane da damane suke ta gaishe da shi yana amsa musu cikin sakin fuska, Office dinsa ya nufa ya bude sannan ya maida k'ofar ya sanya key ya k'ulle, wata loka dake cikin office din ya janye sannan ya d'aga capet wasu takardu ya fiddo na kadarorinsa, da ya boye in bashi ya fad'a maka ba babu yadda za ayi ka fahimci cewa akwai wasu takardu a wajen. Daman ya rarraba takardun ne saboda samun akasi shi yasa ya bar wasu a gida wasu a office, yana dauka ya maida lokar mazauninta ya ajiye, toilet ya shiga ya wanke hannunsa da kura ta taba garin dakko takardun, daukan takardun ya yi ya sanya a wani file ya bude k'ofar ya fito ya k'ulle, Okasha da ke lab'e a windon office d'in daga bayan can ya yi murmushin mugunta, jujjuyawa ya yi ya ga babu wanda ya ganshi dan haka ya fito ya shiga motarsa ya bari sai da su kamar Dr suka fita sannan ya tada motar ya bi bayansu, danja ta tsayar da su Okasha yana saitin motar Dr yana satar kallonsa lokacin da yake saka wasu takardun da ya fito da su daga gida shine yake had'asu a file d'aya .Waya Okasha ya yiwa abokansa ya sanar da su kan cewa su je layin hanyar gidan Dr wanda Dr ke bi su tsaya in da ba mutane motar na zuwa su aiwatar da aikinsu, yana gama fad'a musu ya yi hanyar gidan da suke ajiye mutane in buk'atar hakan ta taso. Dr suna zuwa layin suka ga mota ta sha gabansu kafin me wannan sai ganin mutane sukayi fuskokinsu a rufe, salati Dr da direban suka fara yi kafin mutane su nuna mu su bindiga, shiru sukayi aikwa aka sa direban ya baiwa d'aya daga cikin mutanen tuk'in shi kuma ya shiga d'aya motar suka ja suka tafi,ana fara tafiya suka shak'a musu powder nan take suka fara barci, wata hanya suka d'auka suna gudu kamar masu barin k'asar sai da suka yi tafiya mai d'an nisa can bayan gari kafin suka tsaya a k'ofar wani gida, shiga akayi da Dr da direba aka sanyasu a wani d'aki.


Bayan kamar awa d'aya Dr ya kawo hankali nan suka tisa keyarsa akan ya sanya hannu akan takardun da sunan da suke so, ya musu gardama suka hau dukansa da ya ga suna neman halakashi sai ya ce zai yi abin da suke so nan Okasha ya ce ya sanya hannu da sunan SAFWAN kamar yadda su Ikilima suka buk'ata dan suna so idan SAFWAN ya taso wannan tarin dukiyar ya zama mallakinsa, yanda zasu mora dan basa so a sanya sunansu dan kar a gano su amma SAFWAN ba lallai ne a gane ba kuma sun san dole ba za a saida kadarorin ba sai da takardun to kafin lokacin da SAFWAN zai girma maganar b'atan takardun ta lafa ka ji tunani irin na Ikilima da y'ar ta ABIDA. Bi ya yi ko ina ya sanya sunan SAFWAN ya sa hannu sai wurin da Hindatu za ta sa hannu ne kawai ya rage, anan suka buk'aci ya sa hannu ya nuna musu wurin suka ga ansa sunan Hindatu dan haka suka karb'i takardun suka sakesu dan shima direban ya farfado sai dai shi basu masa komai ba. Mukullin motar Dr suka baiwa direban daga nan suka sallamesu haka suka fito jikinsu sanyi k'alaw ,motar suka shiga direba ya mata key suka bar gidan suka kamo hanya ,sun hau kan kwalta kenan direban na baiwa Dr hak'uri shi dai Dr bai cewa komai dan ba kowa ya ke tunani ba sai Hindatu ya san tunda suka san akwai wurin da za ta sa hannu to tabbas kamar yadda suka kamoshi to tabbas za su nemo ta itama dan haka ma baya son ya kirata a waya so ya ke sai ya je gida ,dan dole ma a sanya tsaro mai tsanani a gidan sannan duk inda suke sai an nemo su, yana cikin ayyana maganar a ransa sai ji ya yi motar tana tangal tangal

"Yallabai motar nan birkinta ba yi kwata-kwata "direban ya ce a kidime dan sai auna arzik'i suke.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji, un kar dai sun kunce birkin ne? "shima Dr ya ce hankali tashe.

"Walllahi inaga sun since dan bayaji"

"Ya salam ni daman na yi mamakin da suka barmu sikau dan sun san dole za, a sanarwa tsaro ashe su mana abun da suka yi...ai kafin me wannan motar ta tintsira kawai gangarawa suke har dai ta hantsila ta fad'a cikin ruwa.




Hindatu kwa ganin Dr bai dawo ba har sha biyu ta wuce gashi ta yi ta kiran wayarsa bata shiga hatta wayar direban ma in ta kira a kashe ake cewa. Ganin haka sai hankalinta ya tashi dan cewa ya yi ta bashi yan mintoci yanzu zaije ya dawo, daga K'arshe dai ta yanke shawarar bin bayansu zuwa asibitin dan hankalinta ya kwanta, bata yi tunanin kiran IMRAN ba dan ta san yanzu yana gida batas???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?o ta d'aga masa hankali, fitowa ta yi ta tura FADILA wurin wasa Inda kayan wasanta suke birjik ita da masu kula da ita, direba ta sa ya d'akko mota suka fito dan direbobi ne birjik a gidan suna fitowa, su Okasha da ke lab'e suna lura da duk wani shige da fice na gidan dan ko hatsarin da su Dr suka yi akan idansu dan kwa suna biye da su. Haka suka ringa bin motar har suka kai layin da suka kama su Dr anan suka musu yadda suka yiwa su Dr haka suka kai su gidan da suka kai su Dr,har dai suka farfado daga K'arshe bayan sun sa Hindatu ta sanya hannu a. jikin takardun, tana ta kuka da rokonsu su fad'a mata inda mijinta yake amma suka k'i, haka suka baiwa direban Mukullin motar ya tafi dan Okasha ya hana a barta su tafi da direban. Domin sun shirya shi da abokan aikin nasa za, a yiwa Hindatu allurar poison in yaso sai su jefer da gawar a wajejen gidan a tsinceta wannan plan d'in Okasha ne ya shirya musu shi, haka aka mata alluran haka suka d'auki gawar suka kai ta bakin titi suka yarda suka k'arawa. rigarsu iska. Yan sandan da suka je d'akko wanda aka ce sunyi hatsari da motar ambulance su ne suka tsinci gawar Hindatu,, sun samu motar Dr da gawar direban amma ba a samu gawar Dr ba, sannan an samu gawar direban da ya d'akko Hindatu wanda ya je ya bugu da bishiyar maina dan itama motar sai da suka since mata burki suka bashi.


Yan sandan sunyi bincike akan gawarwakin amma basu gano komai ba, dan su Okasha sun san aikinsu ba su bar wata alama da za a gano su ba dan tuni ma sun bar garin Kanon dabo amma in kere na yawo zabo na yawo watarana za, a had'u. Itama gawar Hindatu haka aka gama bincike bincike akanta aka je aka binneta acan in da kowa sai ya je Allah sa mu cika da imani ameen. Yanzu dai tsaro sun ce za su tsaurara bincike akan gano wanda suka aikata haka, dan sun gano cewa wasu ne suka aikata haka Ummi Ishalle sai kuka take amma har gwara Hindatu an ga gawarta an sallaceta akan Dr da ko gawarsa ba, a gani ba, ya nitse a cikin ruwan.






Wani matashi na gani cikin dare ya nufi makabarta, ciki ya shiga yana waige waige alamar rashin gaskiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login