Showing 9001 words to 12000 words out of 33266 words

Chapter 4 - YAN UBANCI COMPLET BOOK By Maman Afrah.doc

a ledoji. Tsayuwar motar Aliyu suka ji, can sai gashi ya yi sallama ya shigo takaici ya ishi Umma Kande dak'er ta amsa gaisuwarsa dan takaici har tambayarta ya yi ya taro ta ce
"Mun gode Allah"
Leda ya miko yace "Ga wannan ba yawa,"
wani kamshin kuli ne ya ziyarci hancin Umma Kande nan take ta washe baki ganin ledar kusan cike take yasa yawunta tsinkewa da k'ara taso mata da yunwarta, Allah kad'ai ya san illar da cin muguntar da za ta yiwa tsiran nan .

"Ikilima d'an zubo min soyen kayan cikin a d'an kwano in tab'a, ki kawo min d'akina"ya ce yana mik'ewa ya musu sallama ya fita daga d'akin.

"Maza kula ki kai masa ki dawo mu ci tsiran nan, dan wallahi ba dan tsiran da ya siyo ba da ba mai bashi naman nan "Umma Kanden ta fad'a tana had'iyar yawu. Jiki a sanyaye Ikilima ta d'auka masa naman ta fita zuwa d'akin nasa dan ta san me zai biyo baya. Umma Kande da sauri ta bud'e ledar da duk kamshin ya cika musu ciki, tana gama bud'ewa aikwa ta kawo wani ashar ta dankara wani rogo ne irin na kasuwa da aka yankawa albasa aka barbad'a kuli -kuli akai. Wani takaici sai da Umma Kande ta ji kamar ta yi kuka, gashi an bashi naman da babu ko kwandalarsa a ciki.Aikwa Ikilima na dawowa sai da Umma Kanden ta yi kamar ta cinyeta d'anya wai dan munafurci ta san rogo ne a ledar amma bata fad'a mata ba.Washe gari kwa haka aka soye uban jikin ragon haka Umma Kande ta raba har dangin mijin ta ba su shima Aliyu ta d'auka masa a cewarta su ba matsiyata bane, amma ni nasan ba haka bane kawai dai dan ba yadda za ta yi na.


*BAYAN SHEKARA BIYAR*

A lokacin IMRAN yana da shekara biyar, a lokacin ne kuma Mama Ikilima ta kuma samun ciki duk da har yau ba ta canja zani ba tsakaninta da Aliyu duk da abin da ya ke mata bai yiwa IMRAN domin yana k'aunar d'an nasa sosai .A lokacin ne kuma Allah ya had'a Hindatu da Dector Ayuba, a lokacin har sun gaji da gorin rashin miji da kuma dariyar k'eta daga wurin Umma Kande, ita dai Ummi Ishalle ko a jikinta dan ta san lokacine bai yi ba ,kullum tana addu, a akan Allah ya sa jinjirin ya zama alkairi.Dector Ayuba iyayen sa y'an asalin k'auyen kukayasku ne. kasuwancine ya mai da iyayensa garin Kano, kuma gidan kakaninsa na mak'otaka da gidan Malam Buba dan gida hud'u ne a tsakaninsu. Tunda iyayen Dector Ayuba suka koma Kano da zama acan ya k'arasa karatunsa na secondary school, dan da a makarantar kwana yake ta maza da ke garin maigatari. Zamansu a Kano ya k'ara hab'aka arzik'in mahaifinsa dan dama gonakai ya siyar ya kama kasuwancinsa, hakan ne ma yasa ya k'aura Kano d''a zama ta sanadin abokinsa da suke harkar kasuwanci tare ya siyi gida ya koma can da iyalansa ya sanya yaronsa d'aya tilo wato Ayuba a makaranta mai kyau da tsada dan ya samu ilimi mai inganci. Bayan ya kammala karatunsa Babansa ya sama mishi admission a kasar chaina. Nan take ya koma can domin yin karatunsa a b'angaren likitanci ,tun da ya tafi sau d'aya ya zo hutu sai dai su iyayen nashi su je su ganshi. A yanzu haka ya kammala karatunsa a Inda manyan asibitoci d''a dama da ake ji da su a kasar chaina suna maraba da shi suna so su d'aukeshi aiki sabo da k'warewarsa.Dan sai da ya yi musu aiki na tsawon shekara biyu, Yanzu kud'in da suka biyashi kad'ai ya isheshi ya k'are rayuwarsa da su. Likita ne na abin da ya shafi k'wak'walwa. Amma dai har yanzu bai yanke shawarar yin aiki da su ba yana so sai ya zo k'asar haihuwarsa wato Nigeria ya yi shawara. Yau kwanansa biyar da dirowa Nigeria shi ne ya je kaiwa kakaninsa ziyara garin kukayasku. A sannan itama Hindatun ta zo gida domin ganin iyayenta, zuwan da sai da ta yi da ta sani sabo da irin gori takura da Umma Kande ta kad'e mata hankali ,ita ba dan komai abin ke damunta ba sai dan Umminta da Baba Malam duk da ta san sun yarda da k'addara amma kuma su ma za su so su aurar da ita dan ba Umma Kanden kad'ai ke mata gori ba hatta y'an k'auyen na su suna yada mata magana akan rashin aure dan yanzu sa,anninta daga mai y'ay'a uku sai masu biyu da wani cikin amma ita har yau duk wanda ta had'u dashi sai ta nemeshi ta rasa kamar wanda aka yiwa wani abun.


A yau ma da yamma nan haka ta sanya su gaba da gore gore na rashin auren Hindatu da kuma rashin haihuwar yaya Nana, ita Hindatu da ta gaji da jin rashin tauhidin Umma Kanden shi ne ta tashi ta fita daga gidan dan ta dan zagaya gari duk da shi ma garin ba tsira ta yi ba. Dan ko wurin wani mai tukufar tsire da ta zo wucewa kamar ta yi kuka yadda maza ke aibata girmanta ba aure sai bokoko a wuta gashi yanzu ta kasa auruwa.Haka ta danne zuciyarta ta wuce ba tare da ta san in da za ta je ba, dan haka kawai sai ta yi hanyar bayan gari, tana tafiya tana jin karatun Qur, an mai girma a wayarta sai dai ta sa headphone a kunnenta. Dr Ayuba da ke kwance akan saman mota ya hango Hindatu tana tafiya duk da hijab d'in da ke jikinta hakan bai hana kyanta da kyawun surarta bayyana ba.Dr Ayuba kallonta kawai ya ke daga inda ya ke, ita kwa Hindatu ba ta san ma yana yi ba, sai da ta gaji da tafiya ta juyo domin dawowa gida dan dama rashin wurin zuwa ne ya sa ta yo bayan gari. Tana tafiya a nutse har ta zo za ta wuce Dr Ayuba da ke jiran dawowarta ya diro daga saman mota ya iyo tattaki zuwa kan y'ar siririyar hanyar da Hindatu ke tafiya .

"Assalamu Alaikum "ya ke rangad'a sallama dan shi da ganin yarinyar ya san kwata-kwata ba ta yi kama da y'ar k'auyen nan na su ba. Jin shiru bata amsa ba ya kuma sallamar amma dai tafiya take dan bata san yana magana ba, Dr Ayuba Har ya fara tunanin ko dai kurma ce sai kuma ya tari gabanta. Hindatu bata ankara ba sai ganin mutum ta yi a gabanta.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji, un "ta ce ganin mutum a gabanta fari dashi kyakkyawa kamar wani bature dan duk farinta ya fita haske.Hannu ta sanya ta cire headphone d'in daga kunnenta, Dariya ce ta so k'wacewa Dr Ayuba ganin ta yi wuri -wuri da ido .
"ina ta sallama kin kyaleni "yace yana murmushi jin karatun Qur, an na tashi daga wayar,data zare headphones d'in, kashewa ta yi sannan ta fuskance shi.


"Ban ji ba "

"OK ba damuwa nima sai yanzu na fahimci haka "

shiru ta yi bata ce komai ba.

"Am ni sunana...... "

"Ba na tsayawa a hanya ka je gidanmu ka sameni "

"wane gida Kennan kuma wa zan ce
"ya ce yana yaba tarbiyar yarinyar

"Gidan Malam Buba, Hindatu"Haka kawai ta ce ta juya ta ci gaba da tafiya,haka ya zuba mata idanu yana jin wani nishad'i har sai da ta b'acewa ganinsa.

Kande na ganin Hindatu ta fita itama ta fice daga gidan dan dama tanaso ta fita dan ta yi kwalli da motar nan ta bak'on da ya zo daga Kano jikan Hamza yaron da akace a k'asar waje ya yi karatunsa, gashi an ce kud'i kamar ya watsar a bola. Shi yasa take so ta je ta kashe kwarkwatar idonta .Amma rashin sa, a bata ga dank'areriyar motar da ake labari ba wai ya tafi zagayen bayan gari haka ta dawo tana sababi wai duk bak'incikin mutum dai sai ta ga motar kafin ya tafi. bayan sallar magriba Umma Kande tana zaune tana cin tuwo, a daki Ummi Ishalle da Hindatu kuma suna kofar d'aki suna hira.

"Assalamu Alaikum "wani yaro ya yi sallama, Ummi Ishalle ce ta amsa masa.

" Wai ana kiran Hindatu a waje"Gaban Hindatu ne ya fad'i dan ita har ga Allah ta manta ma sun had'u da mutumin.

"Hindatu kuma d'an nan?? "Ummi Ishalle ta tambaya da mamakii sanin duk garin ba mai zuwa kiran Hindatun dan sun ce ta yi kwantai.
"Eh yana waje "
"Je ka ce tana zuwa "Ummi Ishalle ta ce dan duk tunaninta ko dai daga maigatari aka biyo ta.

Umma Kande da ke cin tuwo har neman k'warewa ta yi, jin ana kiran Hindatun ture kwanan tuwon ta yi gefe ta tashi ta wanko hannunta, a lokacin har Hindatun ta fita, zaunawa Umma Kande ta yi tana jiran Hindatu ta dan jima da fita kafin ta bi bayanta ta je ta b'atata a wurin saurayin. Murmushi ta yi tana tunanin irin kuncin da zasu shiga idan ta kori saurayin, tana nan zaune har dai ta ga lokaci da ya kamata ta fita ya yi.

Tana fitowa ta yi arba da wata dank'areriyar mota da bata tab'a ganin irin ta ba tun da take a rayuwarta, motar sai daukan ido take a hasken farin wata da ganin motar kasan sabuwa ce dal, k'arasawa jikin motar ta yi ta sanya hannu tana shafa jikin motar, ita tama manta da abin da ya fito da ita daga gida,sannan ba ta yi tunanin me ya kawo motar k'ofar gidansu ba. Su Hindatu kwa ita da Dr Ayuba basu lura da Umma Kanden ba dan a gefe suke a tsaye, ita kuma Hindatun bata ma san motar ta Dr Ayuba bace dan ita dazu ma da su ka had'u bata ganshi da mota ba dan haka yanzu ma bata san motarsa bace.

"Yauwa nagode sosai Hindatu da amincewa da soyayya ta da ki ka yi, kuma insha Allah da mun fahimci juna auren mu ba zai d'auki wani dogon lokaci ba "Wannan maganar da Dr Ayuba ya yi ita ta tunawa Umma Kanden abin da ta fito yi, sakin baki ta yi tana kallon Dr Ayuba da yake sanye da wata ubansun shadda wacce ko a jikin Aliyu sirikinta bata tab'a ganin makamanciyarta ba. Ga wata tafkekiyar wayarsa da ta haske fuskarshi anan ta ga tsagwaron kyau da haiba da kuma kwarjini da yake dashi.

"To shikenan bari in shiga gida "Hindatu tace tana juyawa ta shiga gidan ganin Umma Kande tsaye tana kallon su.

Shima juyawa ya yi ya nufi in da motar tashi take tsabar razanar da Umma Kande ta yi daker take jan numfashinta, idonta kwa k'i ta yi ta k'iftashi dan kawai son ta ga inda mutumin nan zai shiga ,ganin ya fiddo Mukulli ya sanya a jikin motar ya sa Kanden ta zauna a k'asa ta yi zaman y'an bori cewa take

"Ba dai jikan Hamzan bane?? ?"shi kwa Dr Ayuba da ta masa kama da mahaukaciya saurin shiga motarsa ya yi ya mata key ya manna a guje dan kar ta masa rotse a glashin mota.. Ganin ya ja motar ya sa Umma Kanden tabbatar da jikan Hamza ne, nan take ta hau bori tana abu kamar mahaukaciya sabon kamu Kuma ba komai bane Illa bak'incikin Hindatu ta samu wanda ko kafarsa mijin Ikilima bai kama ba daman y'an magana sun ce ""Hassada ga mai rabo taki "" Haka mutane suka taru ana tambayar Kanden lafiya sai ta ce


"Ba dai jikan Hamzan bane, wayyo Allah in shine na shiga uku"




Wasu matane guda biyu da suka zo wucewa aka sa su kama Umma Kanden su shiga da ita cikin gida, dak'er suka kama ta dan sai tirtirjewa take tana fad'in

"Ba dai jikan Hamza bane"wannan Abu da take ta fad'a shi ya sa mutane suka d'auka ko gamo ta yi.

Ummi Ishalle suna d'aki suna tattaunawa akan wanda ya zo wurin Hindatu,dan daga Hindatun har Ummi Ishalle babu wanda ya san jikan Hamza ne, ya dai gabatar mata da sunansa da buk'atarsa kuma ya fad'a mata shi d'an asalin garin nan ne amma dai ba, a garin yake da zama ba.Itama kuma da ba,a garin take yanzu ba sai bata wani dameshi da tambaya ba ta dai ji hankalinta ya kwanta dashi.

"Assalamu Alaikum, ina Ishallen maza fito k'anwarki ta yi gamo "D'aya daga cikin matan ta fada tana wani rirrik'e Umma Kanden da karfi kamar za ta saka ta a turun mahaukata. Ummi Ishalle ce ta fito da daga d'aki da saurinta jin abin da matar ke fad'a.

"Subhanallah Allah mai iko yanzu fa ta fita daga gidan nan, oh shi yasa ba,ason fita da magriba, musamman yara ma "ta karashe fuskarta da nuna alamar tausayawa.

"Ke dalla rufewa mutane baki, wane shegen ne ya ce na yi gamo, kuma ta ina muka had'a dangi da ita da za, a kirani da k'anwarta"Umma Kanden tace tana wani zare ido.

"Allah baki lafiya, yanzu muma fitowa muka yi domin zuwa gidan Hamza za mu yi mu baiwa idanmu nama dan ganin motar nan da ake ta bada labari,mun zo wucewa mu ka ga maza sun taru ana cewa Kande ta yi gamo shine aka ce mu shigo da ita, gata nan idan Malam d'in ya shigo kya masa bayani dan suna cikin masallaci suna karatu"Matar d'aya ta fada.

Hindatu da tun dazu take saurarensu ta kamo hanya ta fito daga d'aki,ai Kande na ganin Hindatun ta daddage k'arfinta ta hantsilar da matan nan ta tunkaro inda Hindatun ta ke, matan nan ganin ta yi kan Hindatu tana cewa "wlh yau sai dai wata ba ke ba sai na lahantaki karshe in zama ajalinki" wannan dalilin ne yasa matan suka k'ara bin ta suka rik'eta aikwa ta dage ta naushesu d'aya a ciki d'aya a baya. Suma basu yi wata wata suka kai mata kamar yadda ta kai musu nan take dambe ya kaure Ummi Ishalle na k'ok'arin rabasu. Ana haka Malam Buba da labari ya iskeshi bayan ya fito daga masallaci ya shigo gidan ya ga abin da ke faruwa, kafin a raba fadan Kande ta ci d'an uban duka. Malam ya dakatar dasu ya sallamesu dan said baya son sabgar mata amma Kande kullum bata rabuwa da neman fad'a, amma tsabar masifa da hassada da ke cin ta bata saduda da neman dukan Hindatu ba duk da ta ji jiki.

Hindatu bayan Ummi Ishalle ta je ta lab'e ganin Kanden da gaske za ta iya mata abin da ta ambata.Malam Buba ne ya ce

"Wlh kika tab'a yarinyar nan a bakin aurenki "Juyawa ta yi da mamaki take kallonshi jin wai ita zai saki. Kuka ta fashe da tana jin kamar zuciyarta za ta fito tsabar bak'inciki so take ta huce haushinta akan Hindatun ko ta ji dama -dama.

"Haba Malam shin ka san me shegiyar yarinyar nan ta min da ka ke hanani dukanta, ko dan ba ni na haifeta bata shi...

"Rufe min baki ke dai wallahi na ga randa za ki yi hankali, ace kin zauna a waje gaban maza kina bori kina kiran ba dai jikan Hamza bane, ke kullum sai kin zubar min da mutunci a garin nan yanzu dambe har cikin gida kamar wasu k'ananan yara"

"Haba Malam me yasa ba za ka goyi baya na ba,ace sabo da tsabar munafinci da asiri ace duk k'asar waje duk garin Kano ace jikan Hamza bai ga macen so ba sai Hindatu? ya d'akko dank'areriyar mota ya zo wurin wannan wacce ta yi kwantan, ita ba budurwa ba ita ba bazawara ba, amma ta samu saurayi kamar wannan wanda ko Ikilima bata samu irinsa ba"ta fad'i haka wani kukan takaici na taho mata.

"Subhanallah ke dai Allah shiga lamuranki yanzu akan Ayuba ya ce yana son Hindatu shine ki ke bak'inciki ni na yi mamakin abin da zai saki kuka ashe dai hassada ce da bak'incikin ace kirasa wa za ki yiwa hassada sai yarki ke ba abin farinciki bane ace namiji kamar Ayuba ya ce yana son Hindatu ba"Malam Buba ya fad'a cike da takaici.

"sai dai abin bak'inciki Ayuba jikan Hamza yace yana son Hindatu, tunda ai Hindatu ba Ikilima ba ce"Umma kande ta ce tana zare ido.

"Allah kyauta "Ummi Ishalle ta ce tana juyawa ta shigewarta d'aki. Itama Hindatun bin bayan Umminta ta yi aka bar Umma Kande tana b'ab'atu da sababin aure bazai iyu ba sai dai ta dawwama a haka ba aure. shima Malam juyawa ya yi ya barta tana bala, i dan abin ya fi k'arfinsa dan yanzu ko kukan ma bata yi sai masifa.


Washe gari sai ga Malam Hamza ya zo gidan Malam Buba domin isar da sakon Ayuba na neman auren Hindatu, tunda daman Malam Hamzan ya san irin tarbiyar Hindatun dan haka ya yi farinciki sannan ba komai ya sa ya zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login