Showing 21001 words to 24000 words out of 33266 words

Chapter 8 - YAN UBANCI COMPLET BOOK By Maman Afrah.doc

maida hankalinta kan cin biredin suka ajiye mata ruwan suka juya suka koma mota ruwa dama Malam Habu zai kama shine dalilin Tsayuwar ta su, lokacin da Malam Habu ya taho daga Inda ya kama ruwa, a lokacin har Yaya Nana ta cinye biredin tas tana shan ruwan, dede zai shiga motar dan dama shi Malam Inuwa yana cikin motar wani mutum da motarsa ta tsaya ne ya k'ara so wurinsu ya musu sallama tare da neman alfarmar su daure su tura masa motarsa ta tsaya. Bin bayansa sukayi suka je suka tura masa motarsa dak'er ta tashi,haka suka dawo wurin motar tasu,amma sai ba su ga wannan mahaukaciyar da su ka baiwa biredin nan ba, sai su ka d'auka ta tafi, motar suka tafi dama Kano suka zo suka kawo buhhunan hatsi da na rid'i domin Malam Habu manomine da ke zaune a wurin, yana kai kaya cikin Kano ya siyar, yanzu ma kayan suka kai shi da abokinsa Malam Inuwa ya rakashi .Suna tsayawa suka fara musabiha domin kowa zai shiga gidansa sabo da Malam Habu da Malam Inuwa mak'otane kuma abokan juna, Motar nan ma ta Malam Inuwa ce amma a cikinta aka kai buhhunan.

"Lah Malam Habu ka manta da sakon Talle na barkonanta so ka ke ta koroka idan ka shiga gidan" Cewar Malam Inuwa yana dariyar tsokana.

"Ka ga kwa na manta kwata -kwata amma kuma ai kasan ko zaure ba ta koroni ba" Shima ya ce yana dariya.

Nufar bayan motar ya yi zai d'akko buhun barkonan, yana lekawa me zai gani

"Malam Inuwa ka...ga... wannan...... "

Ai kafin ya k'arasa fad'a har Malam Inuwa ya k'araso, shima mamaki ya lullube shi.

"Ikon Allah to daman nan ta shiga " Malam Habu ya ce cike da mamaki.

"Nima abin da na ke tunani kenan, ina ga lokacin da muka tafi mu turawa wannan mutumin mota ta shiga bayan motarmu.

"Tabbas shi ya sa da muka dawo muka rasata"

Suna ta Al, ajabin ganinta kwance a bayan motar amma ita Yaya Nana barcinta ta ke hankali kwance. Haka aka tasheta daga barcin dan Talle matar Malam Habu da Rabi matar Malam Inuwa aka kira suka kamata dak'er ta yarda ta shiga gidan Malam Habu dan anan aka yanke shawarar ta zauna, tunda gidan ba yara bare su dameta dan Malam Habu bai tab'a haihuwa ba.


BAYAN SHEKARA BAKWAI



Yaya Nana na gani zaune akan tabarma tana karanta Qur, an ita kuma Talle tana bakace hatsi dan wannan bakacen ma dak'er Yaya Nana ta barta take yi dan komai na aikin gidan ita ta ke yi. Yanzu Talle ta d'auki Yaya Nana da suke kira da Amina dan ba su san sunanta ba itama kuma Yaya Nana ta manta da sunanta kai ba sunanta ba hatta komai nata ma ta manta.Dan tun sanda ta dawo gidan Malam Habu da zama Talle ta ke kula da ita sai Rabi da ke shigowa wani lokacin tana tayata kula da ita duk da hauka tuburan ta ke yi dan wani lokacin ma sai an daureta amma a haka suka ci gaba da kula da ita, suke nema mata magani dan sun fahimci sammu ne abin ba wai mahaukaciya bace tun asali. An sha wahala sosai kafin a samu maganin dan sun kashe kudade masu yawa wajen neman maganin ,har dai aka dace lafiya ta fara samuwa kad'an kad'an har dai ta warke sai dai kuma ta manta da komai ta manta Wacece ita cigiya har gidan TV dana rediio su Malam Habu suke zuwa su yi ko Allah zai sa a samu y'an uwanta amma dai har yau shiru.



Gidan Aliyu mijin Ikilima na hango k'ofar gidan an masa penti rangad'a d''a d'au, cikin gidan na shigo shima na ga an yi gini a inda filine da a wurin mata sai shige da fice su ke, wasu na Jere a kicin wasu kuma suna ta gyara abin da be yi ba a falo da d'aki,dan yau za, a kawo amarya shema,u sai Shirye Shirye ake dan karfe biyar na yamma za a kawota sabo da dokar da Alhaji Ahmad Muhammad sani, wato sarkin Gumel ya sanya ta hana d'aukan amare da daddare. Duk wannan buduri da ake Ikilima bata sani ba suna can sun tafi wani k'auye cikin Niger wurin wani boka da zai musu aiki akan Hindatu, ko SAFWAN ma can kukayasku ta kai shi dan dama ya fi zama a can dan ita kullum tana yawon barbad'a .Yau kwanansu goma a can ita da ABIDA dan auren nan ma bata san Aliyu zai yi ba,.


Dan sahu ne ya tsaya a k'ofar gidan Aliyu, Mama Ikilima ce da ABIDA suka fito suna yiwa gidan na su kallon mamakii ganin ya sha penti ga kuma mata na shiga suna uzurinsu dan tuni an tafi a taho da amarya, gidan suka shiga dan sanin me ke faruwa, Ikilima ido biyu ta yi da ginan nan b'angaren da ya fi shekaru biyar a gine amma a d'an kwana goma da sukayi basa nan har an yi plasta an yi penti har Jere an yi kafin ta gama tantance abin da ta ke gani sai jiyo muryar mata ta yi suna rangad'a gud'a ana cewa amarya ta k'araso. A take Ikilima ta ga gidan na juya mata kafin me wannan sai kiji ka ke gif ta fad'i kamar wata tsohuwar saniya.




"Wayyo Allah mamana ki zo ku taimakeni " ABIDA ta ce tana jijjiga mama Ikilima

"Subhanallah me ya sameta, ta fad'i ko dai tana da aljannu ne" wata mata ta fad'a lokacin da ta k'araso wurin.

"Wallahi bata da aljannun komai kawai fad'uwa ta yi " ABIDA tace tana kallon matar.

" Ya za ki ce bata da aljannu bayan gata kwance magashiyyan, da ta san bata da cikakkiyar lafiya ta zo tsegumi sai ki kamata ku tafi gida " Matar ta ce tana musu wani yatsina fuska.

"Dalla dakata malama ya za ku zo har gidan ubana ki ke fad'a min magana, da ki ke cewa mun zo tsegumi ki ga mata a gidanta ki ce ta zo tsegumi sai dai in ke ce ki ka zo tsegumin"cewar ABIDA.

"Lah wai kina nufin wannan ce uwar gidan Shema, un? Ikon Allah ashe labari ya sameta akace Niger ta tafi shine yanzu daga zuwa kishi ya sa ta fad'i Hehehehe " Matar ta fad'a tana tuntsurewa da dariya.

"Ke uwartawa ki ke fad'awa haka, nima fa fitsararriya ce" cewar ABIDA tana nunawa matar yatsa.

"Jama, a ina ku ke ku zo ku ga uwar gida ran gida yashe a tsakiyar gida, ina masu cewa ba su san uwar gidan Shema, u ba ku zo gata "Matar ta fad'a da k'arfi dan matan duk hankalinsu na kan amarya da aka shigo da ita yanzu duk ba su ankare ba, da abin da ke faruwa ba. Aikwa kamar an hankadosu kunsan mata akwai son ganin tsegumi nan fa aka fara ka ce na ce gaba d'aya y'an d'akin amarya sai suka dawo ganin Ikilima da ke kwance shame -shame.

"Lah kun ganta kwa a sume " wata ta ce tana kama hab'a.

"Tabd'i yo Allah na tuba suma ma ya miki, abinda ba fasawa ba za, ayi, dan ga amarya nan ta sauka a d'akinta, dan mu da za mu wuce ma bamu lura da ke ba "wata ma ta ce tana yin shewa.

"Dalla ya isheku malamai ya za ku zo har gidanmu kuna fad'a mana magana "Nan aka shiga kace nace da ABIDA da y'an kawo amarya, ana cikin haka wata ta tafi ta d'akko ruwa a bokiti ta taho ba tare da kowa ya lura da ita ba tana zuwa ta shake ruwan bokitin gaba d'aya akan Ikilima, ai Ikilima sai gata a zaune tana kuka tana kiran an cuceta an ci amanarta, wannan kuka shi ya maido da hankalin mutane kan Ikilima ciki kwa har da ABIDA ,da hanzari ABIDA ta nufo mahaifiyarta dan ganinta cikin halin k'ak'anikayi.

"Mama tashi mu shiga d'aki kin ga mutane y'an gulma sai kallonki su ke yi " ABIDA ta ce tana musu kallon hadarin kaji.

"Ke su waye magulmatan, ai ita ta yi abin kunyar da za, a kalletan"Wata cikin matan ta ce tana dariyar k'eta .

Ai nan ABIDA ta hau yiwa matar masifa ita da wacce ta shekawa Ikilima ruwa, amma Ikilimar cewa ta ke ta k'yale wacce ta sheka mata ruwan dan taimakonta ta yi dan bai kamata ace tana sume ba kamata ya yi ace tana can ana fafatawa da ita a d'akin amarya. Hankalin ABIDA na kan matan nan, Ikilima ta tashi a wani hargitse jikin nan jagaf kamar ta yi iyo a ruwa ta fito,k'ofar amarya ta nufa gadan gadan ruwan nan sai d'iga yake daga jikinta, mutane da ke falo wanda ba su je wurin suman Ikilima ba, suka zubo mata na mujiya ganin ta da kaya a jik'e ga kuma hawaye na zuba duk sai suka tsorata dan sun d'auka ko ba hankali a tattare da ita, itakwa Ikilima tsabagen kyan kayan da ke falon amarya ne ya dad'a tunzurata, bedroom ta wuce inda amarya ke zaune kan gadonta an lullube ta da mayafi, sai kawayenta da basu san wainar da ake koyawa ba a waje.

"Ina bak'ar munafukar da ta aure min miji, an rasa maahinshini, macijiya wacce ba ta ramin kanta sai dai wani ya yi ta shiga"
wannan kalaman da suka fito daga bakin Ikilima su ne suka tabbatarwa y'an matan wacece me magana.

"Haba iya yaushe rabon duniya da yin irin kashin nan da ki ke, ai mu kin zama iyarmu dan duk kin haifemu, sannan ma wannan abin da ki ke yi class d'inki ne ki ke gani a matsayinki na babba "

"Wallahi tsakanina da ku Allah ya isa, zagin da ki ka min kwa gyatumarki ce keelass d'in (class) banda wulak'anci ace kin zageni da girmana, dan kun ga ban yi karatu ba, wallahi dan ABIDA batayi makaranta ba da ita zan saka ta zageku tass da yaren nasara har sai kun d'auka baku iya turanci ba, sannan nesa bata maganin kusa da IMRAN ya turanceku da turanci da baku isa ku gane ba dan a kasar waje ya yi karatunsa. Allah sarki Hindatu kin huta da kikayi karatunki yanzu ko baturiya Ayuba zai aure sai ku kara da ita a turanci " Ta fad'a tana share hawayen takaicin tashin yin karatu da ta yi karatu wallahi ko Hausa d'aya ba za ta saka ba a maganar.

"Ah lallai nikwa na gane baki yi karatu ba, tunda gashi ko sunan mazaunin da ake zama ayi karatun baki sani ba (class) Gashi an fad'a kin ce zagi ne. D'aya daga cikin y'an matan ta fada.

"Kun dai ji kunya matsiyata kun bar ballagazar kawarku ta auri mijin wata "

"Ke dai ce matsiyaci....

"Plss Salma don't tell her anythings again, you.....

Wallahi Allah bazan tab'a yafe muku ba, munafukan banza da wofi in Allah ya yarda sai kin fita kin bar min gidana " Ikilima ta katse amarya daga maganar da take k'ok'arin yiwa kawarta Salma, sai kuka take wiwi, a haka ABIDA ta zo dakin ta kamata suka tafi d'akinsu, ganin mahaifiyarta na kuka haikam yasa itama zuciyarta ta karaya, ita kuma Ikilima abin ne ya hade mata goma da ashirin dan bata tab'a zaton Aliyun zai mata kishiya ba dan ta dad'e da baiwa boka kud'in ya mata aikin akan kar a mata kishiya har abada ,sai kuma gashi an gallo budurwa sabuwa fil a leda. Waya ta dauka ta dannawa Umma Kande kira da sunayen da aka yi serving da alamomin da za ta gane. Umma Kanden na d'auka Ikilima ta fashe da kuka tana mata bayani sosai abin ya dagawa umma kande hankali dan bata tab'a zato ko tsammanin hakan ba, sannan hakan ya fara bata tsoro akan burukansu da suka sanya a gaba anya kuwa burinsu zai cika a rayuwa. Da haka ta daddanne Ikilima akan za ta koma ta yiwa bokan nasu bayani a samo mafita, wannan tausan da umma kande ta mata ne jin za a nemo mafita wurin boka yasa ta ji hankalinta ya dan kwanta.





Haka dai rayuwar gidan Aliyu ya kasance cikin farinciki da kwanciyar hankali dan gaba d'aya Shema, u ta kawo gyara mai wuyar fasaltawa, wanda hakan ya yi mugun sauya rayuwar Aliyu. Wanda hakan yasa Ikilima cikin mugun tashin hankali da damuwa
sun yi neman yadda za su fidda Shema, u daga gidan amma hakan bai samu ba sai kallo da ido. Shema, u macece mai kyau ilimi tarbiya da sanin ya kamata, gashi ta d'auki SAFWAN kamar d'an da ta haifa tana kula da shi yadda ya kamata, dan yanzu da Hindatu ta sa aka mayar dashi private school ita ke daukan duk d'awainiyar karatunsa kuma ta yi hakan ne dan kar Ikilima ta hanashi karatu duk da Ikilima ta fi k'aunar SAFWAN duk cikin y'ay'anta, kuma bata ma da niyyar hanashi karatu sabo da itama yanzu tana danasani dan yanzu gashi mijinta ya auro mata, wacce ta fita komai da komai kuma mai matakin karatun N. C. E. kuma yadda Shema, u ke kulawa da SAFWAN ya sa ta ji rad'ad'in kashinta ya ragu dan sosai take k'aunar SAFWAN Allah ya jarabceta da son SAFWAN fiye da kowa a y'ay'anta kai har ABIDA da take mace.


Fadila ta taso cikin gata da kulawa, mummy Hindatu, IMRAN da kuma daddy Dr kenan kowa kullum kulawa da soyayya yake nuna mata babu wani abu da ta nema ta rasa hakan bai sa an yi sake da tarbiyarta ba. Duk in da ake neman y'ar gata to FADILA ta kai masu mata hidima ma da ban suke, gashi yanzu ana Shirye Shirye na auren IMRAN da wata budurwarsa ILHAM kanwar abokinsa da suke aiki tare. Amma shak'uwar IMRAN da FADILA ta sa IMRAN na tunanin yin nisa da FADILA.........





Gatan da FADILA ke samu wannan shine abu na farko da ya sa Umma Kande ,Ikilima da ABIDA suka fara shirin maida y'an ubancin da suke yiwa Hindatu ya koma kan FADILA duba da yadda suke ganin IMRAN na kyautata mat mata, sai Ikilima ke ganin duk wani samunsa akan FADILA ya ke k'arewa. Bata duba da yadda mahaifan yarinyar ne suka masa komai sannan itama Hindatu ce ke d'aukan d'awainiyar SAFWAN dama su kansu su Ikilimar, hakan ya sa Ikilima ke tura ABIDA Kano lokaci zuwa lokaci dan ta ke ganin abin da ke wakana, tana samo rahoto dan su san ta in da za su bullowa al, amarin. Kuma sosai ABIDA kan samo musu labarai akan komai ko dai ta yi lab'e ko kuma idan ta leb'e da FADILA ta ke tambayarta a wayance dan kar ta gane kun san yaro sai ta yi ta fad'a mata duk abin da ta tambayeta. Cikin bin k'wakkwa'afin da ta ke ne ta samo labarin su Hindatun za su je umara ita da FADILA Dr ya biya musu, bayan daman bayan Hindatun ta yaye FADILA ta je wacce ya biya mata a matsayin goron albishir d'in haihuwar FADILA bayan wannan ma zuwanta hajj biyu. Wannan zancen umarar shi ya dagawa musu hankali suna ganin Ikilima bata je ba amma har za,a kai wata kanakanuwar yarinya makka banda asarar kud'i, dan su biyawa Umma Kanden ma da akayi ba burgesu aka yi ba. Haka sukayi ta soki burutsun su da biye biyen malamansu amma Allah ya rubuta zuwan haka suka gaji suka bari.

Bayan sun je Umara sun dawo mummy Hindatu ta tafi Dubai, soyayyar kayan lefen d'an lelenta IMRAN daga Dubai ta je Cairo ta k'ara wata siyayyar dama ma kuma a makka ta siyo sarkokin daham dan gwal d'in da ta siyo ba kad'an bane. Haka aka had'a lefe na gani na fad'a haka Hindatu da za ta je kukayasku aka lode akwatunan set biyu ta kai kowa ya gani sannan ta ta wuce da su Gumel ta kai wa Mama Ikilima budar bakinta sai cewa ta yi sai ka ce y'ar gwal wannan uban kayan sunyi yawa, kawai dai na sa IMRAN kashe kud'i dan d'an abin da ya ke dashi ya k'are. A nan Hindatun ta ce ita da Dr ne suka had'a lefen amma dai Ikilima ko ta ce an gode, sai ma cewa da ta yi abar kayan anan dangin Aliyu su gani.A nan aka bar kayan suka kwashi na kwasa, da aka kai kayan sai da Hindatu ta k'ara dan dama akwai ragowa da akwatin suka cika aka ajiye.

An yi taron biki an watse, aka kai amarya gidanta da Dr Ayuba ya baiwa IMRAN, amarya ta tare yarinya y'ar mutunci mai hankali da sanin ya kamata, tabbas IMRAN ya yi dace. FADILA ce ma ta yi ta rigima da ta ke ganin baya kwana a gidan shima kuma baya kwana biyu bai lek'o gidan ba, sannann kuma ya kan kai ta ta yiwa ILHAM weekend itama kuma ILHAM d'in sosai ta ke son FADILA dan yarinyar duk da yar gata ce hakan bai sa an k'i bata tarbiya ba.


BAYAN SHEKARA BIYAR


A lokacin FADILA na da shekaru goma sha biyu, lakacin Hindatun y'ar gidan IMRAN na da shekaru hud'u wacce suke kiranta da (AFNAN) lokacin da aka haifi AFNAN da aka sanya da IMRAN ya sanya mata sunan Hindatu Ikilima kamar ta yi cinyeshi d'anye dan fad'a wai akan me zai sanya sunan Hindatu bai sanya nata ba, itama Hindatu gori

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login