Showing 6001 words to 9000 words out of 33266 words

Chapter 3 - YAN UBANCI COMPLET BOOK By Maman Afrah.doc

ga ana zuwa binni amma su da binni sai a labari "

"Yauwa shi ya sa nake sonki, ki bud'e k'aramar jakata ki irgi dubu biyu "

"Yauwa y'ar albarka Allah k'aro miki masoya amma a binni "Umma Kande ta ce tana wata dariya.

*Bayan wani lokaci*

Rashin zama lafiya da ya ke gudana a gidan Malam Buba ya sa Nana ta nemi izinin mijinta ya zo ta d'auki Hindatu ta tafi da ita Maigatari domin cigaba da zama a can dan dama tana da burin haka dan ta san zaman gidansu sai a slow, kuma ta samu miji mutumin kir ki ya amince mata, dan har lokacin Allah bai ba ta haihuwa ba.Sosai Ikilima da Ummarta su ka yi bak'inciki dan kuwa bak'inciki sa son Hindatun ta bar gidan dan sun fi so ta zauna su cigaba da nuna mata Y'AN UBANCI, haka dai su ka hak'ura da wani k'udurin na da ban. Tun da ta koma Maigatari aka sanyata a islamiya amma ba ta allo ba, sannan an sanyata a boko a in da ta fara zuwa makarantar jeka ka dawo ta cigaba daga S. S 1 nan ta cigaba da karatun ta hankali kwance ba tare da damuwa ba.




Tun da Hindatu ta koma hannun y'ar uwarta gaba d'aya rayuwarta ta canja, domin sai lokacin ne ta san menene y'ancin d'an adam sabo da irin rayuwar da suka tsinci kan su a gidan mahaifinsu sanadin kishiyar uwa wato Kande,yanzu damuwar su ita da Nana bai wuce halin da mahaifiyarsu ta ke ciki na duk da Hindatun ta baiwa Nana labarin yadda abubuwa ke kasancewa, yanzu ba komai mahaifiyar ta su ke d'auka ba itama tana yin takar-takar wajen ganin ta rama cin kashin da Kanden ke mata, duk da kasancewarta mace marar son tashin hankali. Wannan dalilin ne ya sa hankalinsu ya d'an kwanta A b'angaren Ikilima ma kwa suna can suna yin duk yadda za su yi dan ganin itama Ikilima ta koma can maigatari da zama domin Ikilimar ta sake takura mata amma Malam Buba ya k'i amincewa da zuwan Ikilima maigatari a cewarsa ba za a je a tare musu a gida ba, a d'auki yara har biyu a kai musu gida ai abin ya yi yawa .Wannan dalilin da Malam ya Fad'a shi ya sa Kande ta yi ta bala,i wai dan ya ga ba ita ta haifi Nana ba shi ya sa ya nuna Ikilima ba za ta je gidan Nanar ba sabo da ana so a nuna mata Y'AN UBANCI haka dai tai ta masifa ba bu wanda ke kulata. Amma ita Ikilimar kamar ma dan ita aka yi domin a halin yanzu ba ta so ta bar garin na kukayasku da zama sanadin wani saurayi bafulatani d'an gidan wani hard'o ne da ke wata riga da ta ke mak'otaka da garin kukayasku. Soyayya su ke kamar me dan dai shi d'in ma kamar itane ba wani na kir ki bane amma abin da ke sanya Ikilima ta ke yin baya -baya da shi ,shi ne yana so ta bashi kanta amma kuma ta k'i hakan ya sa ya ke mata barazana da zai rabu da ita, dan ya ga tana bala, in son shi.

Abin da gaba d'aya ya sanya Ikilima ta fad'a tunani da damuwa kenan domin bata so ta rabu dashi sabo da son shi ya yiwa zuciyarta k'awanya.Amma dai duk da haka har yau ba ta tab'a yarda cewa za ta bashi kan ta ba dan duk rashin ji na Ikilima da rashin tarbiya iyakarta tab'e -tab'e amma tunda ta ke bata tab'a yin zina ba. Kuma ba komai ya sa ta ke k'yamatar zina ba sai maganganun Ummi Ishalle da ta ke fad'a mata akan ta gaji aikata zina domin zina ba k'aramin sab'o bane, kuma zina bashine, komai daren dad'ewa sai ka biya bashin zina .wannan abin ne idan ta tuna ta ke jin ba za ta tab'a iya kusantar zina ba amma abin mamaki lokacin da Ummi Ishalle ke mata irin wannan maganganun ko kallonta ba ta yi bare ta sa ran za ta yi aiki da shi amma hakan bai sa Ummi Ishalle ta gajiya ba wurin fad'a mata hakan ba??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????, sabo da ba ta da mugun nufi a ranta. Haka ta hak'ura da shi, suka rabu da juna ya ke daman shi ba son gaskiya ba ya ke mata ba ko a jikinshi ita ce ta shiga damuwa sosai duk wanda ya ga Ikilima ya san akwai damuwa a tare da ita.



*BAYAN SHEKARA BIYU*

Lokacin Hindatu tana aji shida a secondary school, a sannan ne kuma Ikilima ta je maigatari domin ta yi kwana biyu,Malam ya barta ta ne sabo da ya ga ta d'an nutsu. Ranar laraba ta je dan haka washe gari ya kama alhamis sai su ka shirya yaya Nana ta aikesu kasuwa kamar yadda Hindatu ke kiranta amma ita Ikilima Nana ta ke cewa, ranar alhamis d'in itace ranar kasuwar garin kasuwa ce babba da ta ke ci duk ranar alhamis, mutane daga jahohi da dama suna zuwa cin kasuwar ta maigatari. Kasuwa ce da ake siyar da rak'uma, shanaye, dawakkai ,jakuna, da duk wasu nau, i na dabbobi, kai kana iya samun komai ma a kasuwar .Sun shirya tsaf inda Hindatu ta sanya doguwar rigar atamfa ta dora hijabi akai itakwa Ikilima riga da sket ta sanya ta yafa mayafi aka fante fuska, a haka su ka shiga kasuwar suka gama siyayarsu da Nana ta aika su. A hanyar su ta komawa gida ne wani me mota golf ya sha gabansu, har sai da suka tsaya, fitowa ya yi yana dariya ya rufe k'ofar motar ya k'araso gabansu ba wani babbane ba, sai dai gaskiya ba saurayi ba ne, za, a iya kiranshi da tuzuru. Ganin ya nufosu amma hankalinsa akan Hindatu ya ke hakan ne ya sa Ikilima ta yi sauri ta d'akko wani k'ullin maganin farin jinin da Ummarta ta bata, daga cikin bra d'in ta, tun tahowar su ta so ta yi amfani da shi amma bata ga namijin da ya mata ba, sai yanzu da ta ga wannan sannan dad'in dad'awa ta ga ba ta ita ya ke ba hankalinsa akan Hindatun ya ke nan take ta ji wani Y'AN UBANCI ya taso mata. Tana fito da maganin ta damk'e shi a hannunta na hagu kamar yadda Ummarta ta fad'a mata, ai nan take wannan mutumin ya maida akalar dariyarsa ga Ikilima sosai dad'i ya rufeta ganin mutum d'an birni harda mota yana mata murmushi.

"Barkanku dai y'anmata, ina fatan ban takuraku ba"ya fad'a yana yiwa Ikilima wani kallon.

"Barka amma dan Allah ka k'yalemu ka ga nan titi ne ko ma in ce kasuwa tunda gaba d'aya garin nan ko ina kasuwa ce ta ke ci, ka ga kwa bai dace.....

"Barka babu wata damuwa, wanda ya damu da kai shi ya ke kulaka"Ikilima ta yi saurin katseta ganin za ta mata riga Malam masallaci. Bin Ikilima Hindatun ta yi da kallo baki a sake.

"Yawwa aikwa nagode da wannan tarb'a da ki ka min" Ya ce yana jingina da motarsa.


"Kar ka damu ai wannan ba komai bane "ta ce tana wani farfara ido.

"Yauwa nagode "

"Yaya Ikilima ni na tafi sai kin taho "Hindatu ta ce tana kama hanyar tafiya gida.Banza Ikilimar ta mata har sai da mutumin ya mata magana sannan ta wayance wai bata ji ba. Shiru ne ya biyo baya kafin saurayin ya fara magana ganin Ikilima ta tsareshi da idanu ko kiftawa ba ta yi.

"Ni sunana Aliyu Abubakar, ni d'an asalin garin Gumel ne, iyayena sun rasu yanzu ina gidan wan mahaifina ne. Ina hayar mota ne da ita na dogara.Aliyu ya ce yana maida hankalinsa kan Ikilima, dan yadda ta nutsu sai kawai ta burgeshi gashi dama yana da burin ya auri mace a garin maigatari.

"Allah jik'ansu "ta ce da nuna tausayawa.

"Amin nagode ya sunan malamar "ya ce yana kallonta da murmushi.

"Sunana Ikilima ni y'ar garin kukayasku ce iyayena acan su ke, na zo nan ne jiya wurin yayata da ta ke aure anan garin"ta k'are d'ago kai ta kalleshi, amma me sai ta ga fuskarsa ta canja ya wani had'e rai.

" K'auyen Kukayasku kuma?




"Eh acan nake wlh" ta fad'a kamar za ta fashe da kuka ganin yadda ya ke wani yatsina fuska, alamar ba lallai bane ya amince da ita ba. K'ara damk'e maganin nan ta yi a karo na biyu da mugun k'arfi .

Aliyu da ke shirin juyawa ya koma cikin mota amma sai ya ji wani iri a ransa ji yake idan ya rabu da ita zai iya shiga damuwa.

"Lah meye na b'ata rai kukayasku ma ai gari ne kuma mu ma duk asalinmu k'auye, ni
ke nake so dan haka kar ki damu idan Allah ya sa ke mata ta ce za mu yi aure, idan kuma ke ba mata ta bace, haka Allah ya kaddara"

"Allah ma zai sa mu yi aure "ta ce a zuciyarta a zahiri kuma ta ce. "Allah zab'a mafi alheri"

"Amin" yace ,anan dai suka d'an tab'a hira kafin daga bisani Aliyu ya karb'i phone number d'inta suka yi sallama ya d'auki 3k ya bata wai ta sanya kati.Murna wurin Ikilima ba, a cewa komai burinta da na Ummarta zai cika za ta yi aure a binni.Tana zuwa gida ta d'auki jakar da ta zo da ita ta ce ta tafi gida za ta koma, su Nana fatan sauka lpia suka mata dan yaya Nana har 500 ta hau mota, haka ta tafi domin tana so ta je ta kai wa Ummarta wannan labarin mai mugun dad'i domin asan yanda za,ayi kada Aliyun ya kufce musu.

Umma Kande ta yi murna sosai da labarin da Ikilima ta kai mata, dan gud'a ta ringa rangad'awa wai y'arta ta yi goshi ta samu miji d'an birni mai mota .Haka ta je wurin Malami ya musu abin da suka kama Aliyu a hannu.

*BAYAN WATA UKU*

An yi bikin Aliyu da Ikilima, an kai amarya garin Gumel, a unguwar k'ofar saja, gida madaidaici ciki da falo sai kicin da bayi sai kuma d'akin mai gidan mai bayi a ciki. Amarya ta yi sa,ar gida amma abin da bata sani ba shine bata yi sa,ar miji ba, domin kuwa Aliyun irin mazan nan ne da su ka yi hannun riga da mutunci ga shi da mak'on tsiya.Ansha amarci lafiya a in da daga baya hali ya bayyana dan kuwa sai a sannan Aliyun ya san Ikilima ko aji bata tab'a shiga ba aikwa daga nan salon ya sauya, itama kuma ta gama gane waye shi amma son zaman birni da son ace ta auri mai mota ya sa ta watsar da duk wasu abubuwan da yake mata.Bayan auren da wata biyu Umma Kande ta kawo mata ziyara anan ta tarar da y'ar tata babu lafiya amma ko d'igon kulawa babu daga miji dan idan ya fita ma da safe sai dare ya ke dawowa sabo da jinyar da take yi cikine da ita.Tunda ya san tana da ciki sai rashin mutuncin ya k'aru. Dan haka ita Umma Kande da ta zo ta samu kud'ad'e a wurin Ikilima sai ta tarar da ita a halin buk'atar kud'in itama, dan sai da ta zo ta kai ta asibiti aka rattabo mata magunguna ta biya dan gaba d'aya babu magungunan a wurin da ake ba da magunguna kyauta. Haka duk kud'in hannunta ya k'are, b'acin rai da bak'inciki duk sun isheta sai kwashewa Aliyu albarka ta ke wai ya cucesu dama ya san shi ba namijin da zai d'auki d'awainiyar iyali bane ya auri y'arta. Haka dai ta koma da damuwar halin da y'arta take ciki, ga babu kud'in hannunta dak'er kud'in hannunta ya maidata gida. Wannan kenan.

Rayuwar ta ci gaba da gudana babu dad'i a wurin Ikilima, dan kullum Aliyu abin nashi gaba ya ke dan yanzu idan ya ajiye kayan abinci ko kud'in cefane bai bayarwa, haka zai bar gidan dama shi ba a gidan yake cin abinci ba, dan haka yanzu komai ya cab'e mata sai wayoyinta ta had'a ta siyar ta kama sana, ar siyar da itace da haka ta ke samun d'an abin rik'ewa a hannu.


A haka har dai Allah ya sauketa lafiya ta haifo d'an tab'a namiji, haka y'an k'auyan kukayasku su ke ta murna zasu je su sha suna acii dad'i amma tsabagen mugunta irin ta Aliyu ko k'wayar shinkafa bai kawotq ba, sai garin masara da kub'ewa d'anya wai ayi tuwo tunda su y'an k'auye ne ai tuwo ya kamata su yi. Haka Umma Kande ta k'uk'uta ta auno shinkafa y'ar tsinta dan a futa kunya kuma dan ta lullube k'aryar da ta ke na suna sai Gumel gidan Ikilima.Ana gobe suna Aliyu ya cewa Ikilima bashi da halin yiwa yaro yanka sai dai daga baya idan ya samu ya yanka, haka ta sha kukanta ta sanar da Ummarta haka Umma Kanden ta harhad'a wasu kud'ad'enta da wasu a wurin Ikilima aka siyo tunkiya dan gudun abin kunya. Ran Umma Kande in ya yi dubu ya b'aci sai cewa tayi ke.

"Wannan an yi kudurarran yaro uban shegen mak'on tsiyar jarraba, ni da nake so ka zama bawanmu mu yi ta wankarka amma sai gashi mu ka ke wanka banda tsagwaron wulak'anci ace yanka ma ya gagareka sai ni zan yiwa d'an na ka yanka dan jaraba shinkafa ma ka kasa aunowa wai ta yi tsada ga buhariyya sai dai mu yi tuwon masara san ka sa y'an k'auyenmu su sani a waka, kai Allah wadai da wannan abu wallahi "take ta Fad'anta kamar ta kaiwa Ikilima duka duk haushi ya isheta. Ita kwa Ikilima sai kukanta ta ke dan itama abin ya fara shallake tunaninta, su ma dangin mijin ba son ta suke ba, dan haka matar wan baban Aliyun ma cewa tayi ai komai d'an akwai ne in babu sai hak'uri.

Ranar suna yaro ya ci suna IMRAN gidan suna ya cika mak'il da mutanen kukayasku, Hindatu ma sun zo ita da yaya Nana, amma Ummi Ishalle ba ta samu zuwa suna ba sabo da Malam baya jin dad'i. Ta dai zo barka ta kawo atamfa turmi da rigar yaro guda biyu, amma dan bak'in hali ko d'an ba,a bata ba.An gama jalof d'in shinkafa duk an zubawa Jama, a sai ci suke suna santi suna yaba kyan gidan Ikilima da dace da miji da ta yi wata ta ce.

"Gaskiya mijin Ikilima ya yi k'ok'ari a wannan marrar da ake ciki amma aka dafa shinkafa ga wata dank'areriyar tunkiya hak'ik'a Ikilima ta samu miki na nunawa sa, a"ta ce tana aika lomar shinkafa bakinta. sai wata ma ta karbeta.

"Eh wallahi kalli gida dai ya kai gida, ko a birnin ma ai ta kerewa sa, a, ga atamfofin da take ta sawa kyatsa -kyatsa ai abin sai sam barka"

Umma Kande da ke gefe tana jinsu ta doka musu wata uwar harara, ba tare da sun ankara ba, hango Ikilima da ta yi da d'aya daga cikin atamfofin da ta ciyo bashi dan a samu a fita kunya. Tunda dama bai mata lefe ba kud'i kawai suka karb'a.

"Kande gaskiya kin yi dacen siriki Allah sa a dad'e anayi "cewar wata tana sud'ar hannu dan ko gudun muwa bata bada ba, kai hasali ma y'ar aranni muje biki ce dan ba gayyatarta akayi ba. Dariyar yak'e Umma Kanden ta yi ranta na k'una kafin ta daddage ta ce

"Walllahi kwa, sannan ta k'ara da amin amin"




Haka dai taron suna ya watse ba tare da sun samu wani abin arzik'i ba, bare ayi zancen biyan bashi..Dan wasu ma barkar naira hamsin ce suke bayarwa. Takaici duk ya ishi Umma Kande dan wasu ma da su na mata sallama kai kawai take gyad'awa ,su yaya Nana ma a ranar suka koma domin ba,a basu fuskar kwana ba, dan daga mai jego har uwar babu wani sakin fuskar da suka nuna musu, sai dai sun karb'e kayan da suka kawo masu uban yawa dan itama Hindatun da nata kayan dan tun da ta kammala secondary school ta ke sana, ar ruwan sanyi zobo,kunun aya da kuma jinger. Mijin yaya Nana ya siya musu wata tsohuwar freezer y'ar hannu sai kankara kwa sana, a suke kuma alhamdulillah suna samu musamman ranar kasuwa. Da dare bayan kowa ya watse sai Umma Kanden kawai da wata y'ar uwarta, lissafi suke su uku ne a d'akin gaba d'aya abin da aka samu bai taka kara ya karya ba. Ran Umma Kande duk ba dad'i ga wata muguwar yunwa da ke addabarta, dan ko abincin da za ta ci babu dan ko tuwon da akayi da garin masarar da Aliyu ya kawo a matsayin abincin dare, gaba d'aya y'an garrinsu sun kwashe dan wasu dashi suka tafi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login