Showing 27001 words to 30000 words out of 38445 words
Chapter 10 - MAKARANTAR MATSAFA COMPLETE NOVEL By Shamsiya Lauwali Rabo.txt
ban ƙoshi ba.Sai na soma kallon su Ayo da har yanzu suke cin abinci suna hira hankali kwance,ni kuma yatsuna na soma siɗewa ina jin hanji cikina na yin ƙugi alamun dai abincin bai ishe su ba.
Mama ta tashi ta ɗauki buta ta shiga banɗaki,da sauri Sarah ta cika hannu ta zuba min a farantina har sau biyu.Jikina har rawa yake wurin soma ci.
“Tukunyata kika buɗa kenan?” Mama ta faɗa cike da masifa,na girgiza mata kai.Uwar masu mugun hali ta ce“ cikin namu ta damtsa ta ƙarawa kanta”
Mama ta sa hannu ta buge farantin abincin ya juye ga ƙasa,ta dungure min kai ta ce “ ke da baki jin kunya abincin ƙannan naki za ki ci?”
Sarah ta ce “ Mama ni fa na zuba mata na ga ba ta ƙoshi ba”
Da sauri Ayo ta ce “ ƙarya ce Mama Janiki ce ta ɗeba da kanta kin ga sawun ƙaton hannunta ma”
Da harara Mama ta bi ni kamar idon za su faɗo kafin ta shige ɗaki,ni kuma da sauri na kwashe abincin na je wurin pampo na wanke shinkafar.Yunwa ce ta saka ni na ci haka nan,sai kuma na sha ruwa na fita na zauna kan dakali.
Tunanin abubuwan da Mama ke yi min na soma,hawaye suka zubo min na ce “ ban san me zan yi don na faranta ranki ba Mama da tabbas sai na yi shi” sai kuma na goge hawayen kafin na ci gaba da cewa “ duk kai ne ka ja min da ace ba ka kusance ta ba da tabbas ba za a samu cikina ba,na tsane ka! Ban sonka!” na furta kamar ina gaban shi mahaifin nawa.
Idona na ji an rufe min ta baya,na saki ɗan murmushi na ce “ Rahila ce” da sauri ta buɗe min idon tare da dawowa gabana ta yi tsaye.
“ Kukan mene kike?”
“Babu komai daga ina kike da tsakar rana?”
“Umma ta aike ni na karɓo ɗinkunanmu,bari na nuna miki ” Rahila ta faɗa tare da ajiye ƙatuwar ledar kan dakali ta buɗe ta soma nuna min ɗinkunansu kala uku ita da Mamarta duk zanuwan iri ɗaya ne gwanin sha'awa.
Ban san lokacin da na ce “ kin ji daɗinki Rahila ke Umma na son ki”
Ta ce “ haba Janiki wace irin magana ce wannan? Ke ma ai Mama na son ki kawai dai don kuna da yawa ne shi yasa kike ganin kamar tana nuna banbanci ni kuma kin ga ni ɗaya ce kawai mace ga Umma”
Na girgiza kai na ce “ wannan bai isa yasa Mama ta ƙi ni ba,kullum tana hantara ta.Kin ga mu bar hira nan zuciyata na ƙara ciwo”
“Ya maganar aurenki?”
Na taɓe baki na ce “ har yanzu dai Hajiya ba ta sake zuwa ba”
“Shi Aliyun ya zo?”
“A'a fa,Rahila ga Umma can ta leƙo ki je kar ta yi miki faɗa ” na faɗa ,da sauri kuwa Rahilar ta tafi saboda in ka ga Umma na yi mata faɗa to a kaina ne kawai kwata-kwata ba ta so ta gan mu tare.
Ni ma tashi na yi na koma gida,masarar tuwo na fidda a ruwa kafin na je ɗaki don karɓo kuɗin niƙa.Mama tana kwance na kira sunanta,shiru ba ta amsa ba sai a na biyun ta tashi da ta yi min wata uwar tsawa har sai da na firgita.
“Na ce mene?”
“Kuɗin niƙa” na bata amsa.
“Saboda kuɗin niƙa sai ki tashe ni ina bacci? ”
“Ki yi haƙuri ban san bacci kike ba” na faɗa tare da fita waje,Ayo wacce suke exercices ita da sauran ta tuntsire da dariya kafin ta yi min gwalo sai ta miƙe ta shiga ɗaki.
Babu jimawa ta fito tare da cillo min kuɗin niƙan,na duƙa na ɗauka tare da zuwa na ɗauki robar masarar na fice.Ina isa mashin na tarar da layi,na ajiye nawa kafin na koma can nesa da mutane na zaune.Idona suka ciko da hawaye,tunanin shan maganin ɓera ya zo min a kwanya na mutu kowa ya huta.
“In kin gama kukan ungo ki ci” na ji muryarsa kamar daga sama,na ɗaga na dube shi kafin na dubi abin da yake miƙo min.A take yawuna ya tsinke,hannu na rawa na karɓa ba tare da jira ba na soma ci.
Ya ja ajiyar zuciya tare da zama kusa da ni,bai ce min komai ba har sai da na ci rabin abin da ya kawo min wanda ban san taƙamaimai mene ne ba amma a tsakiyar akwai niƙaƙen nama.
Gorar ruwa ya miƙo min na karɓa na sha,na yi ajiyar zuciya tare da dubansa cikin ido.
“ Shikenan sai kika gudu kika bar ni?” ya faɗa .
Na sunne kai kafin na ce “ da gaske wannan shi ne tarihina?”
Ya saki murmushi mai sauti ya ce “ eh sosai”
“Amma kai ya aka yi ka sani?”
“Saboda ba ki san ni ba shi yasa har kika yi wannan tambayar,amma ni da nake yarima mai jiran gado jinin masarauta ai wannan ba abin mamaki ba ne?”
“Kenan tsafi kake?” na samu kaina da tambaya.Bai ce komai ba ya miƙe tsaye,“ ina za ka je ?”
“Zan koma gida mana” kafin na kai ga cewa komai mai yin niƙa ya kira sunana na waigawa don na amsa masa kawai ban farga ba Prince Mahadi ya ɓace.
Niƙana na je na ɗauka tare da biya sannan na wuce gida,ragowar abincin da ya bani sai na kaiwa Natasha ta karɓa cike da murna ta shiga ɗaki.
Ina tsaka da hura wuta Mama ta shigo madafar ta yi tsaye kaina,“ gidan uban wa kika samu gurasa da nama?”
Gabana ne ya bada wani rasss ,na dubi Mama kawai ina zarar ido ga kuma Natasha gefenta tana cin abincin.
“Da ke nake!” ta ƙara faɗa a dake tana haɗe rai.
Murya na ɗan rawa na ce “ bani aka yi ”
“Na sani ai,uban wa ya baki shi nake son sani?”
Idona ya kawo ruwa na ce “ sadaka aka ban” ban rufe baki ba ta shure ni da ƙafa tana cewa “ almajira ce ke ballantana a baki sadaka? Wato daga jin za a yi miki aure shine kika fara biyar maza? ” nan ta rufe ni da duka kafin ta ce “ taso ki biyo ni don ubanki sai na duba ki” haka na tashi ina kuka na bi bayanta har banɗaki.
“ Ki cire pant ɗinki na duba ki” ta faɗa ,jikina ne ya ƙara ɗaukar mazari yayin da kukan da nake ya ƙaru na buɗe baki da niyyar yi mata rantsuwa amma marin da ta sauke min yasa na yi yadda ta ce.Na rumtse ido gam,ina jin kamar zuciyata za ta fashe tsabar baƙin ciki yadda Mama ke duba ni har da gwada saka min yatsa ta yi kafin ta fita ta bar ni nan cikin banɗaki ina marayan kuka.
Sai da na yi mai isata kafin na miƙe na fito,Ayo ta bi ni da kallon tausayi kafin ta je kusa da Mama tana cewa “ Mama kin san halin Janiki ba za ta taɓa aikata abin da kike zargi ba,kuma sam hakan da kika yi gaskiya bai dace ba”
“Ki rufe min baki ko na ci mutuncinki,so kike na zuba mata ido ta je ta lalace?” Mama ta faɗa .
Madafa na shige ban ƙara jin abin da suka tattauna ba,haka na yi musu girkin duk raina a dagule.Bayan na gama na ɗumama ruwa na je na yi wanka,amma duk da haka zazzaɓin da nake guje ma sai da ya saukar min.Haka na je na shige ɗakinmu na kwanta kan katifata na duƙunƙune na soma rawar sanyi,har aka kira sallar isha'i ban fito ba.Ina jin muryar Natasha na cewa ga lemu da ayaba da Abba ya kawo amma ban iya ɗaga kai na dube ta ba ballantana na karɓa,tana fita kuma Ayo ta shigo tana tambayata.
“ Janiki ba ki sha ne?” dakyar na buɗe fuskata na ce “ banda lafiya ” sai ta matso kusa da ni ta zo ta ɗora hannunta kan wuyana kafin ta fita.Babu jimawa shi ma Abba ya shigo kafin ya ce na tashi ya bani magani.Haka ya ɗebo ruwa a kofi ya bani na sha cike da tausaya wa ,sai dai kamar ma an ƙara wutar ciwon sai abin ya ƙara ƙamari.Da gudu na fita na soma kelaya amai kamar raina zai fita,na zube nan cikin rumfa ina jan numfashi.
Ina jin Mama na masifar ita dai ba da kuɗinta za a kai ni asibiti ba,amma a haka Abba ya fito yasa na wanke baki ya kai ni asibiti.Ina tsoron allura hakan yasa sai da ya riƙe ni sannan aka yi min,bayan mun dawo ne na samu na ci ayabar sai na kwanta na lumshe ido babu jimawa bacci ya ɗauke ni.
Washegari na yi ranar tashi,ko da na farka har sun share ɗakuna da kuma tsakar gida.Girkin ma sun ɗora,haka na je na gaishe da Mama da Abba shi kaɗai ya amsa ita kuma banda saƙon mugun kallo babu abin da ta yi min.
“ Munafuka yanzu da aka gama aikin gida ai ga shi can ta fito,kuma wallahi ba za ki je coci ba gida za ki zauna” na tsinkayo furicin Mama ina ƙoƙarin shiga banɗaki.Daga nan ina jin yadda Abba ke cewa “ daga yau ba ta yi aikin ba shikenan ta zama munafuka? To nan gaba ayyukan gidan raba su za a yi ita da sauran danginta su rinƙa yi a tare,wankin kaya kuma kowa ya wanke nasa”
Ina jin Ayo na cewa “ Abba mu da muke zuwa makaranta”
“Ai ba ku yin ta maraice sabka guda kuke yi,don haka in ta yi aikin safe ku sai ku yi na maraice ke da Sarah.Ita ma da zarar an bani kuɗina zan mayar da ita makarantar ta ci gaba da karatunta”
“Auren fa?” wannan karon Mama ce ta yi maganar.
“Aure ai bai hana karatu”
“Amma dai ka san yanzu ta kusa shekara goma da barin makaranta ko? To wane aji za a saka ta?”
“Daga inda ta tsaya za ta ci gaba,ai shi karatu bai da girma ko ke yanzu kika ce kina son komawa sai na mayar da ke” Abba ya faɗa cikin tsokana.
Daidai nan na fito daga banɗaki sai na ga Mama na murmushi muna haɗa ido kuma ta gimtse fuska tare da kawar da kai.Ni kuwa ji na yi kamar na je na rungume Abba tsabar farin ciki,dama can mugun hali na Mama yasa na bar zuwa makaranta kawai don na kula da su Ayo ita kuma ta fice wajen kasuwancinta wanda a ƙarshe jarin ya karye ta zauna gida.
Abincin kari muka ci,yau na ci na ƙoshi saboda a gaban Abba ne.Bayan haka aka soma shirin zuwa Coci ni ma na shirya kuwa sai dai yau ba kaya iri ɗaya muka saka ba saboda banda irinsu su da Mama sai suka yi anko.
Da muka fito fuskar Abba ta nuna bai ji daɗin yadda aka ware ni ba,amma sai bai ce komai ba muka fita waje har muka shiga taxi Mama ba ta yi ƙorafin don me na biyo su ba.
Da muka je can coci sai na hangi Momy,gudun fitina yasa na zauna a nan gaba yayin da su kuma suka je can wurin ta.Da lokacin yin sallah da addu'a yayi haka na lumshe ido na ta kai kokena wurin Yesu cike da yaƙini.Bayan nan aka soma gwajin fasaha ,tambayoyi ne akan rayuwar Yesu duk wanda ya sani sai ya ɗaga hannu ya bada amsa,yau ma kamar waccan satin na fi kowa bada amsa wanda a ƙarshe har Father ya buƙaci na je can kan dandamali.
Lasifika ya bani tare da cewa na bada tarihin Yesu,ai kuwa haka na soma zayyanowa har ina haɗawa da wasu baitoci.Liƙen kuɗi aka soma yi min kamar ba gobe,Sarah ta zo tana tattare min har na kammala shi ma Father sai da ya bani kyauta ta musamman tare kuma da yin selfie da ni.
Bayan an tashi dukkan kuɗin da na samu sai na miƙawa Abba ,ina ganin Mama kamar ta fashe da alamu ta ji haushin haka.Da muka isa gida kuwa Abba ya sake jaddada alƙawarinsa na mayar da ni makaranta,a ranar ya sayo min uniform da kuma Books da duk abin da zan buƙata.
Washegari sai da na yi aikin da na saba yi kafin na yi wanka na shirya.Mama dai sai cika take tana batsewa amma wannan bai hana Abba kai ni makaranta ba,duk da ina da shekaru dayawa hakan bai dame ni ba musamman da na ga akwai wanda suka kai ni da girman jiki.Ina da ilimina dama,hakan yasa sosai nake fahimtar abin da ake koyawa wasu kuma dama tuni Sarah ta koya min su.Kamar a mafarki nake jin kaina haka na yi shawagi a filin makarantar da muka fito shan iska,abinci ma kasa ci na yi saboda shauƙi har muka taso na nufo gida.
Ina shigowa Mama ta ce “ sai ki ɗauki cefane ki ɗora girki tun da baƙin ciki ya rufe miki ido sai da kika koma makarantar” ban ce mata komai ba na ɗauki cefanen sai da na cire uniform na je na hura wuta ,babu jimawa na haɗa jalob ɗin taliya.Na sauke tukunya na shiga wanka,bayan na fito na ɗauki kasona wanda Mama ta zuba min na ci na wanke hannu ba don na ƙoshi ba.Amma na share tare da ɗauko kayan makaranta na soma dubawa,sallamar Hajiya Luba ta saka gabana faɗuwa.Kamar yadda na yi tunanin kuwa zancen auren ne ya ƙara kawo ta inda take shaidawa Mama ranar juma'a za kawo lefe kenan sai ta sanar da dangi waɗanda za su tarbi kaya.Tun kafin ta fita kuwa Mama ta soma kiran wayar na kusa da ita tana sanar da su za a kawo lefen Janiki,har wani murmushi take tana nuna tsantsar farin ciki wanda ni kuma tuni zuciyata ta aminta Mama ba za ta taɓa yin farin cikin akan abin da zan amfani da shi ba sai dai in wanda zai cutar da Ni ne.....
[19/12 à 04:41] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽
Na
*Chamsiya Laouali Rabo*
```{MRS SADAUKI}```💫✍️
*FCWA* ☀️
*SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊
___________________________________
06
Shirye-shiryen kawo lefena bai sa na ƙi zuwa makaranta ba,sai dai sam na kasa nutsuwa na yi karatun yadda ya kamata.Tsorona guda shine kar bayan auren mijin da za a aura min ya hana ni karatu, wannan na samu Abba na kai masa kokena ya kuma alƙarwanta min abu ne da ba zai taɓa faruwa ba.
Ranar juma'a ce suka tsayar don kawo lefe,yau ta kama Alhamis tuni kuwa dangin Mama sun cika gidan sai gyaran kayan da za a yi miya da su gobe suke.Abin da ya fi ban mamaki kuwa bai fi yadda na ga ana jiƙon ruwan lalle ba,wanda a al'adar garinmu ranar da aka ɗaura aure kawai ake yi wa amarya wanka da su.Amma sai na yi shiru na ja bakina,ina rakuɓe na kasa cin komai sai ga Rahila ta shigo.Kusa da ni ta zauna,kamar yadda ba na farin ciki da wannan auren ita ma haka.
“ Ashe har da ɗaurin duk za a yi a goben?” Rahila ta faɗa ,sai na yi rau-rau da ido amma na kasa cewa komai yayin da ita kuma ta ci gaba da cewa “ an ce gobe bayan sallar juma'a za a ɗaura a masallaci,irin na shari'ar Muslunci za a yi tun da wai mahaifinki ma musulmi ne” sai a lokacin na lumshe ido kafin na maimaita kalmar “ musulmi?” cikin wata irin murya Rahila ta ce “ eh wai! Kenan Abba ba shi ya haife ki ba?” na buɗe idona hawaye na masu surnano min na dubi Rahila da kyau na ce “ ni ma ban sani ba,ƙila hakan ne.Amma ke wa ya faɗa miki?”
“Umma na ji suna yin hirar ita da ƙanwar Hajiya Luba ” ta bani amsa,sai na sunne kai ina wani irin huci.“Mahaifinki Balarabe ne wai,kuma fari ne tasss kamar ke,sai yanzu ni ma nace ai sai larabawa irin wannan gashi naki tubarkallah ”
“ Kaina yana ciwo Rahila ki taimaka min da magani” na furta tare da yin kwanciya.
“To bari na je na siyo” tana fita na je na buɗe jakar kayana na ɗauko hankicin da Prince Mahadi ya bani na soma goge hawaye da shi ina shaƙar ƙamshinsa.Ba ta wani jima ba ta dawo ta kawo min maganin,na karɓa na sha sai kuma duk muka yi shiru.
Mama ta shigo ta dube ni kafin ta ce “ Rahila ko kuna da buƙatar yin wani ɗan shagali ne?”
“A'a Mama” ta bata amsa.
“To ki yi mata ko dilka ne kafin gobe a yi mata lalle,kitso dai kam sai dai ta zauna da gashinta don babu ƴar wahalar da za ta kitse mata wannan tulin gashin” Mama ta faɗa tare da jefo wata baƙar leda.Rahila ta ɗauka tare da buɗewa sai ta kalle ni kafin ta ce “ kayan gyaran jiki ne,bari na haɗa sai ki shafa a dukkan jikinki” kanzil ban ce mata ba har ta ɗauko wani ƙaramin kwano ta haɗa kayan sai da suka yi kamar minti goma kafin ta matsa min na tashi na shafa.
Wani tsohon zanena na ɗaura zuwa ƙirji kafin Rahila ta soma shafa min dilkan a kaf jikina.Sai da na yi kusan awa ɗaya kafin ta je ta kai min ruwan wanka,dakyar na iya fita saboda idon mutane.Bayan na fito daga wanka haka suka ta yaba yadda na ƙara kyau,ita kanta Rahila haka ta yi tsaye tana kallona kafin ta taɓe baki ta ce “ wannan ɗan tsamin ran ko an yi dilkan ma ai ga banza”
“In ma dai iya tsamin ran ne kawai da sauƙi,in ɗayar maganar ba ta tabbata ba” na faɗa kamar zan yi kuka.Rahila ta ja numfashi kafin ta ce “ to da yake an ce iya ƙarar alburushi ne ya taɓa masa ƙwaƙwalwa,ƙila haukan ba yadda muke tunani ne ba”
“Sani dai sai Allah ” na faɗa kafin mu soma yin hira jefi-jefi.Da Rahila ta tafi gida sai na ji kaɗaici ya ƙaru amma haka na daure,sai wuraren magrib su Ayo suka shigo gidan ashe wurin kitso da lalle suka je .Abin da na fahimta hatta su sun san gobe ake ɗaura min aure amma ni banda darajar da za a sanar da ni.
Natasha ta zo ta faɗa jikina tana nuna min kitson da aka yi mata har da duwatsu,yadda take murna da nishaɗi sai na ji sanyi a raina.
“Hum! Sai wani murmushi take kamar wani auren ƙwarai” Ayo ta faɗa wacce ita ma ta yi kitson da