Showing 36001 words to 38445 words out of 38445 words
Chapter 13 - MAKARANTAR MATSAFA COMPLETE NOVEL By Shamsiya Lauwali Rabo.txt
sa mutum ya tsargu,shiru kawai na yi masa.Can ya ce “ kana iya tafiya” na jinjina kai.
Bayan na fito daga can direct wani gidan shaƙatawa na tsaya Park,wuri ne da iyaye suke kawo yaransu don shan iska da kuma buɗe ido.Karon farko da na ji sha'awar ajiye yara,yadda suke wasa gwanin ban sha'awa sai ya sake tuna min da Malama Zainab.Hoton fuskarta nake gani a kan fuskar duk iyayen da ke wurin,sai nake ganin tamkar ma a nan ita ce ke kula da su.Na ɓata lokaci sosai kafin na bar wurin,ina draving ina tunaninta har na isa gida.Cak na tsaya bakin ƙofa ganin Malama Zainab ɗin tare da Ammy a zaune.Na girgiza kai tare da dariyar kaina a zuci na ce ‘ HAROON ka haukace tun da har a cikin gidanku Malama Zainab kake gani ’ sai na yi gaba har na hau step ɗin farko sai na tsinkayo muryar Ammy na cewa “ HAROON zo ku gaisa da malamar da za ta dinga koyar da ni karatu”
Da sauri na juyo sai muka haɗa ido da ita amma ta yi saurin kawar da kai,tamkar wani gumki haka na tsaya ina kallon ta .Sanye take cikin pink ɗin hijabi,tafin hannunwata a waje suke ta riƙe litattafai da su.Kamar wani sakarai haka jan lallen yatsunta ya ja ra'ayina har ban san lokacin da na taka can inda suke a zaune kan salon ba,“ mu ga littafin da za ku soma” na faɗa tare da kai hannuna zan karɓa amma wani azababen suraci da ban san na mene ne ba ya daki hannuna da bala'in sauri na yi baya har ina shirin faɗuwa.
“Yi sannu mana,Malama miƙo min na basa” cewar Ammy ta karɓo littafan ta miƙo min sai dai sam na kasa amsa saboda wani irin haske da nake ganin yayi min katanga da littafafan.Na girgiza kai na ce “ a'a Ammy ba sai na gani ba” sai kuma na nufi step da mugun sauri na haye can sama,ina shiga ɗaki na ƙargame shi da key ina jin wani tsohon ilimina na baya na dawo min.A nan take a inda nake na fahimci wani abu,ina cikin fushin Allah mai tsanani ta yadda har har littafai masu kalmomin saninsa suka yi min tawaye suka haramta gare ni........
MRS SADAUKI ce 💫✍️
[26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
03
Duk yadda na so nuna wa zuciyata ruwa ba a sa'an kwando ba ne amma sam sai ta yi min bore ta ƙi aminta akan muradinta.Soyayyar Malama Zainab ɗin dai ta zaɓa ,duk da tunanina ya ƙi bata haɗin kai wannan bai canza zane ba.Dakyar na cira ƙafafuna zuwa toilet,kayana na cire kafin na shiga ƙarƙashin shower na buɗe pampon duka.Ruwa suka soma jiƙa ni,sanyinsu na rantsa sumar kaina ina jin wata ƴar nutsuwa na sauko min.Rabon da na ji yanayin buƙatar mace har na manta,zan iya kai wata biyu haka ban yi lalata da ƴar kowa ba amma yau soyayyar Malama Zainab ta motso mini da tsimin.
Pampon na kashe ba tare da na yi wankan sabulu ba,towel na ɗaura a ƙugu kafin na fito ina tsane gashina da ɗan ƙarami.Bayan na gama na saka ƙananun kaya na fashe jikina da turare kafin na sauko ƙasa ,sai na tarar tuni ta tafi sai Ammy kaɗai zaune a falo tana duba littafi.
Na ƙaƙalo murmushin dole na ce “ Barka da yamma uwa ta gari”
Ta ɗago ta ɗan dube ni na wani lokaci kafin ta ce,“ meke damunka HAROON ? Ina ce ganin Malama Zainab zai sa ka nutsu amma sai na ga saɓanin haka”
Kusa da ita na zauna kafin na ce “ wai aka yi kika nemo ta? Ko dama kin san ta ne?”
“To wane ne bai san Malama Zainab ba duk Yamai? Na san ta mana har gidan marayun da take kula da shi ina zuwa duk ƙarshen wata”
Na ɗan saki murmushi,taimakon al'umma yana ɗaya daga cikin halin kirki na Ammy.Duk wata ƙungiya mai kula da marayu sun san ta sannan ba wata ɓoyayya ba ce a garin Yamai don kusan duk wani abu da ya shafi Islam sai an kawo mata takardar gayyata irin taron ci gaban addini da sauransu,amma ko kaɗan ban yi tunanin ta san Malama Zainab ɗin ba.
“Bayan fitarka ne na tambayi direba sai yake sanar da ni,shine fa muka je har can inda take na nemi alfarmar ta dinga zuwa tana min karatu a gida ” Ammy ta faɗa murmushi kan fuskarta.
Ita ɗin tana da son Addini sai dai ba tada yawan karatu,kuma samun ilimi na ɗaya daga cikin burinta sai dai ta karaya ne tana ganin ai shekarunta sun ja.
“To Ammy sai ku yi ta karatun,yaushe da yaushe za ta zo?”
“Duk bayan sallar magrib in sha Allah,zan dinga aika direba ya ɗauko ta in kuma ta gama sai ya mayar da ita”
“Amma iyayenta sun bari?”
“Eh sosai,ai a gabansu na nemi alfarmar shi fa mahaifinta gani yayi ma kamar zunubi ne ƙin yarda da abin da na roƙe su ɗin.Iyayenta ƴan mutumci ne kamar dai ita” ta ƙarashe zancen fuskarta na canzawa,da sauri na kamo hannunta ina mai cewa “ mene ne kuma Ammy? Don Allah kar ki tuna shi,kar fa ki manta kin yi mini alƙawarin haka”
Kai ta jinjina mini kafin ta ce “ zan shiga ciki sallar magrib ta gabato zan yi wanka” sai kuma ta miƙe,na bi bayanta da kallo kawai.Ina nan zaune mai aiki ta kawo min abubuwan motsa baki,ko kallon ta ban yi ba na soma ci ina tunanin abar ƙauna.Na kurɓi lemun zoɓo kafin na miƙe na fita harabar gidan,mota na shiga na ƙara ficewa.
Ban yi nisa ba kuwa aka soma kiran sallah,amma ban wani damu ba na ci gaba da tuƙina har na isa inda nake tunanin zan samu macen da za ta sama min nutsuwa.
Daidai wurin bada hannu na tsaya,almajiran suka fara miƙo min robobinsu duk da kuwa gilashin motata a rufe yake ruf.Dayawansu ba za su wuce shekara ashirin zuwa da uku ba,ganin ban buɗe ba yasa duk suka tafi sai ɗaya ce ƴar jaraba ta tsaya .Sai a lokacin kuma na yi ƙasa da madubin motar,cikin daƙiƙa biyar na ƙare mata kallo fara ce ita amma dauɗa ta saka ya disashe sannan irin kamar Fulanin nan na daji.
“Alhaji ka taimaka mini ina son kai Mamana asibiti ne” ta faɗa cikin marairaice murya.
“Nawa ne farashinki? ” na samu kaina da furta wa,ido kawai ta zuba min da alamu ita sabuwar zuwa ce ba ta san tabi'ar nan ta ban manda na baka gishiri ba.
“Za ki bi ni mu je in kina son na baki kuɗi” na faɗa a karo na biyu,sai na ga tsoro ya bayyana a fuskarta.A hankali na soma mayar da madubin motar amma ta yi saurin dakatar da ni ta hanyar saka hannunta daga sama ,sai na ƙara yin ƙasa da shi.
“In mun je da gaske za ka bani kuɗin?” ta jefo mini tambayar cike da yarinta.
Kai kawai na jinjina mata,sai na ga fuskarta ta faɗaɗa da murmushi.Gaban mota na buɗe mata kafin na yi mata key,tuni gari ya ɗauki duhu sai hasken fitilun kan hanya.Gudu nake sosai ta yadda ta soma yi min magana cikin tsoro “ don Allah Alhaji ka yi haƙuri kar ka sayar da ni ”
Na ja tsuki ban tanka ta ba,sai dai na rage gudun motar sai ta saki ajiyar zuciya.Gidana na kai ta wanda babu kowa a cikinsa hatta mai gadi ban sa ba,a waje na yi parking duk muka fito.Na buɗe gidan na shiga sai na ga ita ta tsaya bakin ƙofa,“ki shigo”
“A'a ba sai na shiga ba ka ɗauko kuɗin ka bani” tsabar takaici ban san lokacin da na wani jawo hannunta da ƙarfi ba na shigo da ita ciki tare da rufe gidan.
“In kika ce ihu ko kuka za ki yi min zan sayar da ke ɗin tun da haka kike so” na faɗa tare da yin gaba,a dole ta take min baya har cikin falo.Na kunna wutar ko ina sannan na haɗe rai tare da nuna mata toilet na ce “ ki shiga ki yi wanka” jikinta na kyarma ta shiga ɗin,sama da minti goma amma ta ƙi fitowa sai na mara mata baya ina shiga na ja wani uban burki zuciyata ta soma bugawa fat! Fat! Fat! Sakamakon ganin Oga cikin shigar kayan yarinyar da na ɗauko a mota.
Waige-waige na fara sai dai babu ita sai shi ɗin dai,kamar ƙyaftawar ido yarinyar ta dawo normal ta soma magana amma muryar oga ce ke fita.
“ Tun da na soma meeting ɗin yau hankalina yake kanka,wato a fuskar kowa na lura da damuwa saɓanin kai.HAROON ka fara soyayya faɗa mini wace ce ita?” yana gama faɗa sai ya ɗauki siffarsa ta namijin kayan yarinyar nan suka zube a ƙasa sai nasa kayan jajaye masu kamar jini.
Kasa furta komai na yi,don in na ce in yi magana ƙarya ce zan faɗa kuma tsaf zai gane.To mene ne ma abin yi wa mutumen da yake da ƙarfin power ɗaukar siffar mace? Shirun dai ne ya fi alkhairi a gare ni.
Kafaɗata ya dafa sai na ji wani zuuut,sai muka ɓace daga cikin toilet zuwa daularsa wacce kusan a can muke taro masu muhimmancin sosai ko kuma in wani sabon members ya shigo.Ban fita daga wannan mamakin ba na ji na yi sama cikin iska kafin kuma in ji ni gammm,bayana ya bugu da bango yayin da hannuwana kuma aka banƙare su tare da ɗaure su da kacar tsafi.
“Babu soyayya a tsarin ƙungiyarmu,amma kai ka karya doka! Zaɓi biyu zan baka ko dai ka sadaukar da budurwar da kake so,ko kuma na aika ka ɓoyayyar duniya yanzu nan tun kafin wa'adin shekarunka su cika”
Ido na rumtse gam,a cikin zaɓin biyu babu mai sauƙi a gare ni.Shekara biyar ta rage mini a doron duniya kamar yadda muka yi yarjejeniya a ranar da zan sayar da ruhina,an bani shekaru goma na rayuwa a wannan duniya kafin na isa ɗayar,a cikin goman kuma na yi biyar saura biyar suka rage mini.‘Wane zaɓi zan ɗauka?’ na tambayi kaina a zuci.......
[26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*☠️
LoVe aNd HoRrOr StOrY☠️
*Mallakar:* Chamsiya Laouali Rabo
(MRS SADAUKI💫✍️)
*Lambar waya:* +22795045822
*FIRST CLASS WRITER ASSOCIATIONS☀️*
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation.
_____________________
04
“Wato soyayyar da kake yi mata har ta kai ka kasa sadaukar da ita kai tsaye shi ne ka tsaya shawara? Hahaha! Ōgāfōr̃!” Oga yayi lafazin ƙarshe cikin Yaren matsafa a nan take kuma na ga tile ɗin ɗakin na darewa wata jar turɓaya na bayyana kuma sai girrrr kake shi tamkar ƙatuwar tirelar ɗan danƙarau mai yin gina.
A inda nake can sama ɗaure a jikin bango nake kallon duk abin da ke faru,gidan ƙasa ne ya bayyana sai a lokacin kuma kacocin hannuna suka kwance kansu yayin da na soma yawo cikin iska ina kaɗawa kamar wata leda.
Wasu ɗalasiman tsafi Oga ya soma kafin ya ce “ je ka ɓoyayyar duniya ka yi ziyara na tsawon kwana uku,in ka fito daga ciki sai ka bani zaɓin ka” rufe bakinsa ke da wuya na soma ji na ina yin ƙasa har na shiga dogon ramen mai ɗauke da wata daular .
Ina shiga ciki komai ya soma komawa normal ya ɗinke,sai da na ja wani numfashi sa'ilin da na ji ƙafafuna sun dogane da ƙasa.
Baƙar ƙofar na kalla ta gabana wacce nake da tabbacin ita ce za ta sada ni da ainahin abin da ake kira da ɓoyayyar duniyar.Na shagala sosai ina kallon ƙofar tare da tunanin da na san ba zai fishe ni dare ba,kawai sai na ji ƙiiiiii ƙofar ta buɗe da kanta.
Ido na tsura ina jiran ganin wanda zai fito,amma sai na ji wata murya na cewa “ Barka da zuwa duniyar Ruhaniya ” ban amsa ba haka ban gusa daga inda nake ba .
Sai na ji an kamo dukkan hannuwana biyu ana jana amma ban ganin masu jan nawa,a dole na soma taka ƙafata har muka bi ta ƙofar nan a take kuma ta rufe ji kake gammm.Duhu ne ya turniƙe wurin,sai a lokacin kuma na ga inuwar masu jaye da ni saboda wani jan haske da goshinsu ke fitar wa kamar wuta.
Ci gaba suka yi da ja na izuwa ciki,matakala muka soma takawa muna daɗa yin can ƙasa.Har muka ainahin duniyar,nan ɗin ko ina da haske tamkar goshin azahar haka.
Duk masu bi suna wuce wa na soma duba,dayansu siffar mutane ce da su yayin da sauran kuma suke ɗauke da sifofin dabbobi iri-iri.
Irin inuwar nan gani ta waɗanda suka yi min iso,a zuci na ce ‘ ko su waye su?’
“Dōr̃ānī! Masu kula da shige da ficen duk al'ummar nahiyar nan.Ko da wasa wani ya tsaya hutawa dangane da aikin da yake yi za su hukunta shi ne” na ji muryar ɗazu ta faɗa wacce ta tarbo ni tun a bakin ƙofa.
Saitin inda murya ta fito na duba,sai na ga yanzu ana ganinsa da kyau sai dai muninsa ma ba zai bari ka ci gaba da kallonsa ba.
“Amma kuma ƴan Adam ne?” na tambaya.
“Duk faɗin nan babu mai ruhin bil'adama sai kai ,duk waɗanda ka gani da irin siffarka to mutum ne da rigar aljan.Bima'ana gangar jikin ce ta mutum amma ruhin aljani ne a ciki”
“To ya ake hakan tana faruwa?” na sake jefo masa tambayar.
“Mutanen da suka sayar da ruhinsu ga MAFIYA ,bayan wa'adin shekarun da aka ɗibar musu ya cika za a aiko da su izuwa nan.Ruhikansu za su dinga yin bauta ,yayin da gangar jikinsu kuma aljanai za su ɗauke ta su dinga amfani da ita.” yana kawo wa nan sai yayi shiru yayin da ɗaya abokin aikin nasa ya ɗora da cewa “ dayawan jinnu na son ganin kansu a duniyar bil'adama sai dai babu damar yin haka don ba za su iya bayyana da siffarsu ba,wannan ya sa suka ƙulla yarjejeniya da manyan masu ƙungiyoyin asiri da su dinga sayar musa da gangar jiki”
“To mi za su yi da ita?” na yi tambayar cikin zaƙuwa zuciyata na bugawa jin ni ma
********************** **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
************************* **********************
DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.
Visit > https://www.aihausanovels.com.ng
Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.
Email > aihausabooks@gmail.com
******* FOLLOW US ******
Facebook: Ai Hausa Novels
Twitter: Ai Hausa Novels
Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels
WhatsApp Number: 08138873799
Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.
********************** **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** **************************