Showing 18001 words to 21000 words out of 38445 words
Chapter 7 - MAKARANTAR MATSAFA COMPLETE NOVEL By Shamsiya Lauwali Rabo.txt
da shi kafin ta yaye fatar,da sauri na kawar da kai ganin yadda ciwon nasa yake buɗe har yanzu.
“Ki matso ki soma ɗinke masa cikin ” ta faɗa .
Na juyo da sauri na ce “ni kuma?“
“Eh kin zata wa zai yi miki aikin?” ta faɗa tare da miƙo min wani mashi mai kamar wuƙa da kuma baƙin zare.
Jikina ne ya soma rawa haka na zauna ina kallon yadda ta ƙara wanke cikin nasa tare kuma da zuba wani magani,hannu na kyarma na soma ɗinki yayin da ita kuma take faɗar wasu surkullen da ita kaɗai ta san ma'anarsu a haka har na ida.
Na yi baya ina mayar da numfashi,ta tashi ta je can gaban wani babban teburi ta ɗauko min zuma ta bani na karɓa ina washe baki saboda ina son zuma kullum sai Uncle Salem ya bani ita tun ina ƴar yarinya.
Zumar na soma sha muna kallon juna ni da Kaka kafin ta ce “ban san dalilin Deborat ba da ta zaɓi ta ɓoye miki baiwarki,amma na so a ce kin zama tamkar Kakarki Ayodele ciwon idon Mayu...” sai kuma ta yi shuru yayin da ni kuma na tsaya da shan zumar na ce “wai Granny Mamar Daddyna?”
Ta jinjina min kai kafin ta ce “eh sosai ita fa! Kin san ita ma ba ta da tsoro kamar ke take,sai dai ita dukkan aikin da alloli da magabata suka saka ta yi tana sane da komai ba kamar ke ba da yake zuwar miki siffar mafarki”
“Yanzu mafarki ne nake yi kenan?”
“Kusan haka ne! Sai dai wannan muna kiransa da balaguron ruhi,wasu suna yinsa cikin bacci yayin da wasu kuma ke yinsa ido farke ”
“Ita Kakata Ayodele ya take yi?” na tambaye ta,sai da ta saki wani murmushi kafin ta ce “in na tsaya baki labari ai ɓanar lokaci ne kuma ba za ki fahimta ba,amma MRS SADAUKI ta fi kowa iya bada labarinta shi yasa ta fitar da littafi na musamman dominta ungo” ta faɗa tare da miƙo min wani littafi ban kai ga duba sunansa ba na ji muryar Inna A'i na ce “Nafisa ki tashi ki shirya ƙarfe bakwai fa har ta wuce” da sauri na ware idona tare da yaye abin rufa.
“Littafin mene ne wannan babu kyawun gani?” Inna A'i ta faɗa tana yamutsa fuska.
Sai a yanzu na farga da littafin da ke riƙe a hannuna,an yi masa cover da hoton matattu har da fatalwa na motsa bakina dakyar “MUTUWARE(Duk mai son jin labarin Ayodele sai ya tuntuɓe ni)”
“Ki bar kirawo min mutuwa don Allah ” Inna A'i ta faɗa ,na yi dariya ina saboda na daɗe da sanin babu abin da take tsoro a duniya kamar mutuwa da kuma fatalwa,haka duk kusancinta da mutum ba za ta iya kwana da gawarsa ba.
Sai da na yi dariya mai isata kafin na saka littafin cikin jakata sai na shiga toilet,ruwa na sauka a jikina mafarkin da na yi na yanzu ya faɗo min a rai abin da ya fi bani mamaki ta ya aka yi littafin ya bayyana gare ni alhalin cikin bacci aka bani shi? A nan take wani tsoro ya kama ni wanda zan iya cewa wannan ne karon farko da na taɓa jin tsoro game da ire-iren abubuwan nan.
A gaggauce na yi wanka na fito na shirya, breakfast ɗina ma cikin kwano mai murfi Inna A'i ta saka min shi kafin na wuce can makaranta.
Tuni kuwa dalibai sun soma zuwa,sai da na je na ajiye jakata a cikin aji kafin na fito na yi tsaye.
Abun mamaki duk malamin da muka haɗa ido da shi sai ya harare ni,ciki kuwa har da Adama wacce ajinmu ke manne da na juna.Ina son yi mata magana amma sam ba ta bani fuska ba sai wani cijewa take.
A haka har lokacin shiga aji yayi,na shiga ina mai yin tsaye tare da fiddo takardar liste ɗin ɗalibai na soma kiran sunayensu bayan na gama na ce “ akwai wanda bai ji sunansa ba?”
“Madam ni ” na ji wata murya wacce ta min kama da wacce na sani,na juya inda na ji sautin sai idona ya sauka kan ɗalibina na jiya da dare amma fa sam ban gane wai shi ne ba saboda mafarkin da na yi na manta shi.
“Mene sunanka?” na tambaye shi.
“Abdul” ya bani amsa,hakan na nufin sunansa na cikin jerin farko na masu A .“Abdul wa me sunan mahaifinka?” nan ya faɗa min amma abin mamaki sam babu sunansa a liste ɗin.
Na ce “kuma jiya da na yi kiran sunan ɗalibai ka ji naka?”
“Eh Madam ” ya bani amsa.
Ban ƙara cewa komai ba sai na fita zuwa ofis ɗin Grand Maa kamar yadda aka ce in wata matsala ta samu can za mu je.Tun daga bakin ƙofa na ji jinin jikina ya daskare yayin da kuma numfashina ya canza salon tafiya,dakyar na danna belt na neman izini ta bani izinin shigowa.
Ina buɗe ƙofa na ci karo da lamba ɗaya ɗan headmaster shi kuma zai fita,yayi min wani mugun kallo kafin ya fice ni kuma na ƙarasa na gaishe da Grand Maa.Ciki-ciki ta amsa kafin ta ce “ me kika zo yi kuma?” tambayarta ta ce ta yi min wani iri amma na watsar da ita kafin na ce “ an manta ba a rubuta sunan ɗaya daga cikin ɗalibaina ba bisa liste ” sai na faɗi cikakken sunansa .
Wani irin kallo Grand Maa ta yi min na kar ki raina min hankali kafin ta ce “ ai ba mantawa aka yi ba,ki duba liste ɗin da kyau” yanzu ma furucinta sai ya yi min wani iri,amma sai na yi kamar yadda ta ce ɗin na nutsu da kyau na duba liste ɗin sai na ga liste ɗin ta fara da lissafin lamba biyu,sannan a can sama ga sawun rubutu nan mai ɗauke da lamba ɗaya sai dai sam ya goge ba ka ma ganin abin da aka rubuta.
“Me haka ke nufi?” na tambaye ta ina mai ɗaga kai ina kallon ta .
“Kin ga Malama fitar min daga ofis ki bar yin kamar ba ki san komai ba,ni ba za a yi comedy da ni ba” ta faɗa cikin ɗaga murya tare da nuna min ƙofar fita,ganin yadda tuwon fuskarta ya kumbura har yana motsi ga idonta da suka rikiɗe suka zama kamar na Zombie yasa da sauri har ina tuntuɓe na baro ofis ɗin.
Ina shiga aji sai na ɗauki biro na rubuta sunan yaron daga sama,sai na soma yi masu darasi har lokacin shan iska yayi.Kamar yadda aka sanar da mu cewa iya ranar Monday kawai a ba za mu fitar da yara aji ba a nan za su ci abincin da makaranta ta dafa musu,to yau suna da damar fita wannan yasa na ce su je su sayi abin da suke so amma da zarar sun ji ƙarar rawa su dawo.
Kowa ya fita daga aji amma banda Firdausi,na dube ta tare da cewa “ke me yasa ba za ki fita ba?”
“Babana ya ce bai da kuɗi” ta bani amsa.Abincina na buɗe muka ci tare bayan mun gama na bata chocolat tare da cewa “kullum zan dinga kawo mana abinci mu ci kin ji ko?” kai ta gyaɗa min alamun to.Haka ta yi ta mini surutu har lokacin dawowar ɗalibai yayi.
Bayan sun shigo waƙa na soma koya musu sai na ga sun fi mayar ma da hankali a kanta,yadda duk suka shiga nishaɗi sai abun yayi min daɗi.
Lokacin tashi ya gabato sai na yi zaune tare da fiddo liste ɗin sunaye,abun mamaki sunan Abdul da ni ce na rubuta shi ya goge babu shi.Shuru na yi ina sauraren bugun zuciyata da yake wani harbawa fiye da ƙa'ida,dakyar na aro jarumtar sake rubuta sunan nasa sai kuma na soma kira ɗaya bayan ɗaya har na gama duk sai aka zo fara ɗaukarsu har kowa ya watse.
Ina fitowa muka yi kiciɓis da Adama na ce “madam Adama Barka da warhaka fatan kina lafiya?”
“Bayan kin kusa kashe ni shine kike tambayar ina lafiya ? To nan sani ba” ta bani amsa tare da yin gaba fuuu.Na yi tsaye cak ina kallon ta kafin dakyar na ɗaga ƙafata na wuce zuwa gida,sai na tarar da Jabeeru direba muka gaisa a mutumce nan Inna A'i ce ke faɗa min Ammy ta aiko shi ya kawo mana abubuwan buƙata har ƙatuwar frigine wacce aka cika da kaji zuƙu-zuƙu.
Bayan ya tafi ne na shiga na yi wanka na fito,ina zaunawa Inna A'i ta miƙo min kofi cike da madara tana cewa “ungo ki shanye ƴar autata ” ganin yadda ta yi min abin cike da soyayya yasa na karɓa na sha ba tare da na tambayi na mene ne ba.
[30/01 08:07] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️
```LoVe aNd HoRrOr story```👽
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}
*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.
*FCWA*☀️
________________________
Last free page 10
Ganin Grand Maa ta ɗauki wuƙa za ta tsaga cikin yaron na yi saurin rumtse idona,ina jin sautin kururuwarsa yadda yake kuka yana cewa “madam ki cece ni kar ki bari su cutar da ni ” na buɗe idona da suka yi jawurrr na sake zuba su kan Grand Maa wacce ke zuba jinin yaron nan a kofi ta hanyar saka ludayi tana wani kwaso shi.
Bayan ta gama sai ta kai kofin bakinta ta sha sannan ta miƙawa principal shi kuma da ya sha ya bai wa headmaster daga nan sai vice principal da kuma vice headmaster.Grand Maa ta ƙara karɓar kofin ta ce “lamba ɗaya sha ka bai wa lamba biyu,haka za ku dinga yi har kowa ya sha” wanda aka kira da lamba ɗaya na duba, kyakkyawan saurayi ne irin sosai ɗin nan kuma sai na ga yana kama da headmaster da dukkan alamu ɗansa ne,bayan ya sha sai ya miƙawa lamba na biyu shi kuma ya miƙo min na karɓi kofin ina kallon yadda jinin ɗalibina yake kwance a ciki mugayen matsafan nan sun mayar da shi lemun sha .Na kai kofin kusan bakina na yi kamar na sha kafin na miƙawa Adama wacce ita kuma ita ce lamba huɗu,so nake na ce mata kar ta sha amma idon Grand Maa ƙurrr suke kanmu ina ji ina gani Adama ta sha jinin kafin ta ba na kusa da ita a haka har kowa ya sha aka mayar da kofin.
Daga nan sai Grand Maa ta yi wani siddabarun sai ga yaron da aka feɗe cikinsa ya tashi zaune daram da buɗaɗen ciki idonsa na shatatar da hawayen jini yana kallon tsakiyar idona har yanzu kuma bai gushe da neman taimakona ba sai dai sam ban san ya za a yi na taimake shi ɗin ba.
Wasu kwalabe ta jera saman table ɗin,ta yi wani alama da hannu a nan take duk suka buɗe kansu.Bakinta na furta ɗalasiman tsafi ta dinga umartar ruwan da ke cikin kowacce kwalba da su je su shiga buɗaɗen cikin yaron,nan ya soma yin wata irin zabura kamar an jona shi da lantarki abin da na kasa jura kenan na ce “ōvovār̃ī” hakan yana nufin komai ya tsaya wato stop cak duk komai ya tsaya kuwa yayin da dukkansu suka soma amayo jinin da suka sha suna wani waro ido kamar za su mutu.Sam ban wani damu ba sai ma zuwa da na yi na ɗauki ɗalibina ,kamar yadda uwa ke gudun matsala ta samu ga ɗanta ko kuma in ta ga wani abu zai cutar da shi take ɗauke shi tare da ɓoye shi haka na yi wa ɗalibina na ƙanƙame shi gam a ƙirjina ina kallon Grand Maa wacce ke yin ƙarfin hali tana cewa “lamba uku ki ajiye shi kar lokacin kaddamarwa ya wuce duk ki ɓata mana shiri ki maido mu baya”
Na girgiza mata kai na ce “ba zan bayar da ɗalibina ba”
“Lamba ɗaya je ka ƙwato min abin farauta” Grand Maa ta basa umarni ai kuwa sai ya miƙe tsaye ya tunkaro ni,muna kallon juna cikin ido sai na ga tamkar na san shi yana dab da kawowa wurina kuma sai na tuna a inda na san idon,wato tsakakar ranar nan ce da na bugewa bindi.Na dubi ƙafarsa sai na ga yana yin ɗingishi,“kār̃bās!” na furta nan take kuma ya ɓangwale ya faɗi yana ihu,nan kuwa na ga hankalin headmaster ya tashi ya nufo shi duk da kuwa ƙoƙarin tsayar da shi da Grand Maa ta yi don ba a so kowa ya gusa daga wurinsa sai da umarni.
Ta yo kaina za ta ƙwace shi da ƙarfi ni kuma da mugun sauri na bi ta rufin ɗakin na tashi sama cikin iska muka bar wurin.Ban san inda na ɓoye yaron ba amma tabbas na kuɓutar da shi kuma na basa tsaro,daidai nan kuma na tashi daga baccin saboda kiran sallar asubah da aka yi.
Dukkan cinyoyina na ji suna yi min ciwo kamar wacce ta yi wasar tsere,dukkan abubuwan da suka faru da ni kuma sai na manta da su .Wanka na yi tare da alwala na zo na yi sallah,bayan na gama na soma yin Azkhar ina lumshe ido alamun bacci ne yake son ƙara yin gaba da ni amma kiran Uncle Salem ya shigo wayata na je na ɗauka tare da yin kwance na kara wayar a kunne.
Yau shine ma ya gaishe ni da farko,na amsa cikin mayen bacci ina jin yana cewa “ mafarkin me kika yi Naf ?”
Baccin da nake ji ne ya sake ni a nan take tuna na yi mafarkinsa mun haɗa shimfiɗa da shi muna mu'amalar aure ,amma me yasa yake yi min tambayar nan shine abin dubawa .Cike da gyatse na ce “kai wane iri ka yi?”
Sai da ya saki murmushi kafin ya ce “mafarki na yi ga shi nan an kawo min ke gidana,muna kwance kan bed duk babu sutura a jikinmu ina yi miki zazzafan romance ke ma kina maido min da kuma na fara kusantarki sai kika fara yi min kuka kina kiran sunana Uncle Sal zafi ka bari ban so.Amma sai na soma rarrashinki har kika yi shuru kika bar kuka,Naf na ji daɗin mafarkin nan sosai kin ga yanzu ma da zan yi sallah sai da na yi wanka”
Tun da ya soma magana na rumtse ido,wato shi ko kunya bai ji yayi mafarkin suna sex da ƴarsa sannan har wani labari yake bani.Ina ƙoƙarin kashe kiran ya tsayar da ni,“ Please Naf kar ki kashe min kira faɗa min yau ma kin yi mafarkin tsoro?”
Jin ya canza akalar zancen yasa na yi shuru,sosai na tuna na yi mafarkin ban tsoro amma na kasa tuna abubuwan da suka faru.
“Faɗa min me kika gani?” ya sake faɗa .
Na ce “ni na manta komai”
“Kin sha maganinki kuwa kafin ki kwanta?” ya jefo min tambaya,ni sam na ma manta da ya bani magani.Na ce “eh a'a...”
“Baby ina ga ke ma kina son na zo kusa da ke shi yasa kike wasa da shan magani,amma babu damuwa duk weekend zan dinga zuwar miki” da sauri na ce “a'a ban so ka yi zamanka ”
“Saboda me? Naf me yasa kike son hana cikar burinmu ne ? Haƙurina ya ƙare fa ina buƙatar kulawa kin san abin da nake ji duk dare? Da zazzafan feeling ɗinki nake bacci ina tuna surar jikinki na matsu na ji komai na jikinki a hannuna yana sarrafa shi ...” kuka na saka masa ina roƙonsa don Allah ya bari ban son irin wannan zancen daga ƙarshe na ƙara da cewa “uncle ka je asibiti don Allah likita ya duba ka”
“Ke ce likitata domin ke kaɗai kike da maganin ciwona,kin ga yanzu ma duk kin tayar min da hankali ji nake...” ban bari ya ida ba na kashe kiran ina mai ci gaba da yin kuka.
Inna A'i wacce ta fito daga toilet ta ce “in kin gama kukan sai ki tashi ki yi sallah”
Na ɗaga kai na dube ta ina mamakin yadda aka yi ta canza min,na turo baki gaba na ce “Innarmu kin bar sona ” na faɗa ,ba ta kula ni ba ta haye dadduma.Ni ma tashi na yi na shiga toilet na yi wanka sannan na ɗauro alwala na zo na gabatar da sallah,ina Azkhar ina tuna mafarkin da na yi da Uncle Salem nan take kuma na soma jin jikina na saki har wani sanyi-sanyi nake ji yana rufe ni.Na je na ƙara haye katifa tare da jan bargo na rufa ina lumshe ido,karon farko da na ji ina muradin yin saurayi mu yi soyayya sannan aure ya biyo baya sai yayi min duk abin da Uncle ɗina yayi min cikin bacci.Da wannan tunanin bacci ya sake yin awon gaba da ni sai kuma na ci gaba da mafarkina daga inda na tsaya wato cikin wani daji na tsinci kaina.A gabana kuma wani ɗaki ne na kara,a bakin ƙofa wata tsohuwa ce zaune tana hura wuta amma ban ganin fuskarta.
Na matsa kusa da ita na ce “Kaka jiya na yi ajiya a wannan ɗakin cikin dare” ko kafin ta ɗago idona ya sauka kan ƙusumbinta.
Ta ɗago tana kallona,ganin mun san juna sai na sakar mata murmushi na ce “Kaka dama ke ce? Nan ne gidanki?” na faɗa ina nuna ɗakin.
Ta jinjina kai kafin ta ce “ki shiga ciki yana nan yana bacci amma kar ki tashe ”
Na shiga ɗakin sai na tarar da ɗalibina kwance bisan kunnuwan ganye yana bacci,fuskarsa kawai ake gani saboda yadda aka yi masa rufa da wata fatar dabba.
“Ya samu rauni sosai Allah yayi sa'a ma kin kawo shi nan kan lokaci da saura ƙiris ya rasa ransa” Kaka ta faɗa wacce ta shigo hannunta riƙe da ƙwayar sai tururi ke tashi.
Zama ta yi kusa da shi kafin ta yaye fatar,da sauri na kawar da kai ganin yadda ciwon nasa yake buɗe har yanzu.
“Ki matso ki soma ɗinke masa cikin ” ta faɗa .
Na juyo da sauri na ce “ni kuma?“
“Eh kin zata wa zai yi miki aikin?” ta faɗa tare da miƙo min wani mashi mai kamar wuƙa da kuma baƙin zare.
Jikina ne ya soma rawa haka na zauna ina kallon yadda ta ƙara wanke cikin nasa tare kuma da zuba wani magani,hannu na kyarma na soma ɗinki yayin da ita kuma take faɗar wasu surkullen da ita kaɗai ta san ma'anarsu a haka har na ida.
Na yi baya ina mayar da