Showing 21001 words to 24000 words out of 38445 words

Chapter 8 - MAKARANTAR MATSAFA COMPLETE NOVEL By Shamsiya Lauwali Rabo.txt

numfashi,ta tashi ta je can gaban wani babban teburi ta ɗauko min zuma ta bani na karɓa ina washe baki saboda ina son zuma kullum sai Uncle Salem ya bani ita tun ina ƴar yarinya.

Zumar na soma sha muna kallon juna ni da Kaka kafin ta ce “ban san dalilin Deborat ba da ta zaɓi ta ɓoye miki baiwarki,amma na so a ce kin zama tamkar Kakarki Ayodele ciwon idon Mayu...” sai kuma ta yi shuru yayin da ni kuma na tsaya da shan zumar na ce “wai Granny Mamar Daddyna?”

Ta jinjina min kai kafin ta ce “eh sosai ita fa! Kin san ita ma ba ta da tsoro kamar ke take,sai dai ita dukkan aikin da alloli da magabata suka saka ta yi tana sane da komai ba kamar ke ba da yake zuwar miki siffar mafarki”

“Yanzu mafarki ne nake yi kenan?”
“Kusan haka ne! Sai dai wannan muna kiransa da balaguron ruhi,wasu suna yinsa cikin bacci yayin da wasu kuma ke yinsa ido farke ”

“Ita Kakata Ayodele ya take yi?” na tambaye ta,sai da ta saki wani murmushi kafin ta ce “in na tsaya baki labari ai ɓanar lokaci ne kuma ba za ki fahimta ba,amma MRS SADAUKI ta fi kowa iya bada labarinta shi yasa ta fitar da littafi na musamman dominta ungo” ta faɗa tare da miƙo min wani littafi ban kai ga duba sunansa ba na ji muryar Inna A'i na ce “Nafisa ki tashi ki shirya ƙarfe bakwai fa har ta wuce” da sauri na ware idona tare da yaye abin rufa.

“Littafin mene ne wannan babu kyawun gani?” Inna A'i ta faɗa tana yamutsa fuska.

Sai a yanzu na farga da littafin da ke riƙe a hannuna,an yi masa cover da hoton matattu har da fatalwa na motsa bakina dakyar “MUTUWARE(Duk mai son jin labarin Ayodele sai ya tuntuɓe ni)”

“Ki bar kirawo min mutuwa don Allah ” Inna A'i ta faɗa ,na yi dariya ina saboda na daɗe da sanin babu abin da take tsoro a duniya kamar mutuwa da kuma fatalwa,haka duk kusancinta da mutum ba za ta iya kwana da gawarsa ba.

Sai da na yi dariya mai isata kafin na saka littafin cikin jakata sai na shiga toilet,ruwa na sauka a jikina mafarkin da na yi na yanzu ya faɗo min a rai abin da ya fi bani mamaki ta ya aka yi littafin ya bayyana gare ni alhalin cikin bacci aka bani shi? A nan take wani tsoro ya kama ni wanda zan iya cewa wannan ne karon farko da na taɓa jin tsoro game da ire-iren abubuwan nan.

A gaggauce na yi wanka na fito na shirya, breakfast ɗina ma cikin kwano mai murfi Inna A'i ta saka min shi kafin na wuce can makaranta.
Tuni kuwa dalibai sun soma zuwa,sai da na je na ajiye jakata a cikin aji kafin na fito na yi tsaye.

Abun mamaki duk malamin da muka haɗa ido da shi sai ya harare ni,ciki kuwa har da Adama wacce ajinmu ke manne da na juna.Ina son yi mata magana amma sam ba ta bani fuska ba sai wani cijewa take.

A haka har lokacin shiga aji yayi,na shiga ina mai yin tsaye tare da fiddo takardar liste ɗin ɗalibai na soma kiran sunayensu bayan na gama na ce “ akwai wanda bai ji sunansa ba?”

“Madam ni ” na ji wata murya wacce ta min kama da wacce na sani,na juya inda na ji sautin sai idona ya sauka kan ɗalibina na jiya da dare amma fa sam ban gane wai shi ne ba saboda mafarkin da na yi na manta shi.

“Mene sunanka?” na tambaye shi.
“Abdul” ya bani amsa,hakan na nufin sunansa na cikin jerin farko na masu A .“Abdul wa me sunan mahaifinka?” nan ya faɗa min amma abin mamaki sam babu sunansa a liste ɗin.

Na ce “kuma jiya da na yi kiran sunan ɗalibai ka ji naka?”
“Eh Madam ” ya bani amsa.
Ban ƙara cewa komai ba sai na fita zuwa ofis ɗin Grand Maa kamar yadda aka ce in wata matsala ta samu can za mu je.Tun daga bakin ƙofa na ji jinin jikina ya daskare yayin da kuma numfashina ya canza salon tafiya,dakyar na danna belt na neman izini ta bani izinin shigowa.
Ina buɗe ƙofa na ci karo da lamba ɗaya ɗan headmaster shi kuma zai fita,yayi min wani mugun kallo kafin ya fice ni kuma na ƙarasa na gaishe da Grand Maa.Ciki-ciki ta amsa kafin ta ce “ me kika zo yi kuma?” tambayarta ta ce ta yi min wani iri amma na watsar da ita kafin na ce “ an manta ba a rubuta sunan ɗaya daga cikin ɗalibaina ba bisa liste ” sai na faɗi cikakken sunansa .

Wani irin kallo Grand Maa ta yi min na kar ki raina min hankali kafin ta ce “ ai ba mantawa aka yi ba,ki duba liste ɗin da kyau” yanzu ma furucinta sai ya yi min wani iri,amma sai na yi kamar yadda ta ce ɗin na nutsu da kyau na duba liste ɗin sai na ga liste ɗin ta fara da lissafin lamba biyu,sannan a can sama ga sawun rubutu nan mai ɗauke da lamba ɗaya sai dai sam ya goge ba ka ma ganin abin da aka rubuta.

“Me haka ke nufi?” na tambaye ta ina mai ɗaga kai ina kallon ta .

“Kin ga Malama fitar min daga ofis ki bar yin kamar ba ki san komai ba,ni ba za a yi comedy da ni ba” ta faɗa cikin ɗaga murya tare da nuna min ƙofar fita,ganin yadda tuwon fuskarta ya kumbura har yana motsi ga idonta da suka rikiɗe suka zama kamar na Zombie yasa da sauri har ina tuntuɓe na baro ofis ɗin.

Ina shiga aji sai na ɗauki biro na rubuta sunan yaron daga sama,sai na soma yi masu darasi har lokacin shan iska yayi.Kamar yadda aka sanar da mu cewa iya ranar Monday kawai a ba za mu fitar da yara aji ba a nan za su ci abincin da makaranta ta dafa musu,to yau suna da damar fita wannan yasa na ce su je su sayi abin da suke so amma da zarar sun ji ƙarar rawa su dawo.

Kowa ya fita daga aji amma banda Firdausi,na dube ta tare da cewa “ke me yasa ba za ki fita ba?”
“Babana ya ce bai da kuɗi” ta bani amsa.Abincina na buɗe muka ci tare bayan mun gama na bata chocolat tare da cewa “kullum zan dinga kawo mana abinci mu ci kin ji ko?” kai ta gyaɗa min alamun to.Haka ta yi ta mini surutu har lokacin dawowar ɗalibai yayi.


Bayan sun shigo waƙa na soma koya musu sai na ga sun fi mayar ma da hankali a kanta,yadda duk suka shiga nishaɗi sai abun yayi min daɗi.
Lokacin tashi ya gabato sai na yi zaune tare da fiddo liste ɗin sunaye,abun mamaki sunan Abdul da ni ce na rubuta shi ya goge babu shi.Shuru na yi ina sauraren bugun zuciyata da yake wani harbawa fiye da ƙa'ida,dakyar na aro jarumtar sake rubuta sunan nasa sai kuma na soma kira ɗaya bayan ɗaya har na gama duk sai aka zo fara ɗaukarsu har kowa ya watse.

Ina fitowa muka yi kiciɓis da Adama na ce “madam Adama Barka da warhaka fatan kina lafiya?”
“Bayan kin kusa kashe ni shine kike tambayar ina lafiya ? To nan sani ba” ta bani amsa tare da yin gaba fuuu.Na yi tsaye cak ina kallon ta kafin dakyar na ɗaga ƙafata na wuce zuwa gida,sai na tarar da Jabeeru direba muka gaisa a mutumce nan Inna A'i ce ke faɗa min Ammy ta aiko shi ya kawo mana abubuwan buƙata har ƙatuwar frigine wacce aka cika da kaji zuƙu-zuƙu.

Bayan ya tafi ne na shiga na yi wanka na fito,ina zaunawa Inna A'i ta miƙo min kofi cike da madara tana cewa “ungo ki shanye ƴar autata ” ganin yadda ta yi min abin cike da soyayya yasa na karɓa na sha ba tare da na tambayi na mene ne ba.

Sosai na yi ƙoƙari wurin watsar da duk abin da ya faru da ni a makaranta muka sha hira da Inna A'i kafin ta kawo min naman kaza wanda ta yi wa wani romo na musamman dama tun da na dawo ban ci komai ba sai na zauna na soma ci sai na ji tamkar ɗanɗanon magani amma ban yi magana ba na ci na ƙoshi.

Inna A'i ta ce “zan fita na je kasuwa akwai abubuwan da zan sayo ”
Na ce “kin san kasuwar ne?”
“Taxi zan shiga,ba zan jima zan dawo”
“To a dawo lafiya” na faɗa nan ta fice ni kuma saboda kaɗaici yasa na jawo wayata sai dai sam babu network a dole na ajiye ta na ɗauki littafin MUTUWARE ,tun a page ɗin farko na soma jin kaina na juyawa yayin da nake ganin kamar abin da ya faru ya taɓa faruwa da ni,da na tsananta tunani ne kawai idona suka hasko min abin da ya faru da ɗalibina Abdul a daren jiya.Na dafe saitin goshina da ya soma tsira min,ba tare da na shirya ba na kwanta baccin dole wanda ban yi niyya ba.

Cikin wata kasuwa na tsinci kaina,sai tafiya nake ina waige-waige kamar mai neman wani abu.Yayin da hankulan ƴan cikin kasuwan duk ya dawo kaina kamar sun ga sabuwar halitta,har tambayar kaina nake mene ne suke kallo a jikina.Ban ɗauki dogon lokaci ba kuma na samo amsar,wato dogayen fuka-fuka ne a bayana sai motsa kansu suke.Ban kuma ɗauki lokaci ba na tashi sama ina baza idona ta ko ina ,can na hango Inna A'i tana ta sauri yayin da wata matsafiya ke take mata baya tana naɗe inuwar Inna A'i tamkar wata tabarma.Shuuu na dira a tsakiya cak matsafiyar ta tsaya tana kallona,“bani abin da ke hannunki ” na faɗa saboda kusan rabin kurwar Inna A'i na hannunta.
Da sauri ta saka abin cikin kwagiri (wata jaka ce da tsofi ke ɗaurawa a ƙugu don zuba kuɗi)

Ihun Inna A'i yasa da sauri na juya ta ɓangarenta,sai na ga ta faɗi na je da guduna ina kiran sunanta na tallabo ta.Ko da na waiga sai na ga babu matsafiyar babu alamunta,daidai nan na tashi daga baccin saboda kakarin mutuwa da na ji ana yi kusa da ni.


Na buɗe idona a hankali da suka yi min nauyi,sai na ga Inna A'i ce kwance tana kakarin mutuwa jini na fita ta hancinta.Hankali tashe na ce “me ke damunki Innarmu?”

Numfashinta kamar zai fita take min jawabi “a kasuwa ne wata mata ta bani ƙananun kifi na ci shine kawai na soma jin jiri,jikina kuma kamar ana cire min wani abu”

Fatarta na kalla na ga ta yi wani mugun ja ga wasu sawun halittu tamkar dai kifin.Tsam na miƙe tare da saka takalmi,idona har wani rufe wa suke saboda ɓacin rai,ni kaina ban san wa nuna min kasuwar ba haka dai na samu kaina da tunkarar wata hanya har na isa.Allon sanarwar na duba inda aka rubuta ƘWARGWAM MARKET wato kasuwar matsafa,ƙafata na ɗora da niyyar shiga sai dai tamkar akwai wani abu da ke jana a baya wanda ya hana ni shiga ciki.Na gwada hakan ya fi shuren masaki amma na kasa,a ƙarshe ma dai sai zube wa na yi ƙasa a gajiye numfashina na shirin tsinkewa.

Nan na kawo ƙarshen free page duk mai son ci gaba zai biya 500 via

2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

Sai ya turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822

NB: Yanzu nake rubuta shi ,so don Allah kar ki zo kina ce min ke complet kike so Ni kaina banda shi.
In kuma ya kammala 1k ne kuɗinsa.

30 Janairu 2025
[30/01 08:49] MRS SADAUKI: *SURUKATA*🪽🪽🪽

Na
*Chamsiya Laouali Rabo*
```{MRS SADAUKI}```💫✍️

*FCWA* ☀️

*SADAUKARWA Ga:*. Shamsiyya Manga, My Namecy 😊

___________________________________

01


A duniya akwai wata babbar illa wacce ba kowa ke fahimtar illa ba ce sai wanda abin ya faru da shi kamar dai ni da duniya ta yi juyin waina da ni.
Farinci;kalma ce da ban san me take nufi ba ballantana na more ta,na taso cikin matsin rayuwa mai cike da ƙalubale da rikitacen al'amari wanda da ace ba a kaina hakan ta faru ba da ko shakka babu ba zan taɓa yarda kan cewa Uwa na iya cutar da Ƴar da ta tsugunnai ta haifa ba.


Sunana Janiki,ƴar asalin ƙasar Yuganda ce a wani ƙauye da ake kira da Norobi,ƙauyen ya shahara wurin bai wa al'ada haƙinta.Ni ce ta farko wurin iyayena,sai ƙannaina uku Ayo mai shekara goma sha bakwai,sai Sarah mai 13years sai kuma ƴar autarmu Natasha mai shekara goma.Dukkansu baƙaƙe ne sai ni ɗaya tal ke fara sol kamar zabaya,da wannan jama'ar ƙauyen suke tsokanata da ƴar fara mayya.Tun ina da ƙanannun shekaru ake kirana da haka har zuwa yanzu da nake cikin shekara ta ashirin da biyar.

A hankali nake wanke kwanukan da zan zuba abincin rana,ina rera waƙoƙin da ake koya mana a Coci.Saukar dundu na ji a bayana kafin ashar ta biyo,“ to daƙunanna haihuwar asara,kin kama kwanuka kina shafa kamar mai yi wa jariri wanka sai sun sauko daga makaranta ba ki gama ba ko?” muryar Mama ce wacce a kullum nake fargabar jin ta.

Jikina na kyarma na ce “ na kusa ida wa Mam...” ko rufe baki ban yi ba ta gwaɓe mini haɓa tare da shure ni da ƙafa tana mai cewa “ don ubanki kar ma ki gama zauna nan ki yi ta shafar kwanukan in ƙannan ubanki ne” ban ce komai ba sai sauri da na ƙara ina mai ci gaba da tsiyayar da hawaye,ina gama wanke wa daidai ƙannaina na shigowa su duka ukun a tare kowacce riƙe da jakar makarantarta.


Kamar wasu jarirai haka Mama ta soma tarairayar su tana tambayar su makaranta, sai washe baki take tana fara'a kamar ba ita ce ta gama haɗe mini fuska tana zagina haɗi da dukana ba.


“Shegiya mayya ta wani zubo mamu shegun ƙattin idonta tana kallo,ba za ki je ki fidda abincin ba sai na kare miki ƙafa?” Mama ta faɗa a lokacin da na shagala ina kallonsu,sumi-sumi na wuce zuwa mafada.Kamar yadda na san kowa shi ɗaya yake cin abinci haka na ɗauki kwanuka ina zuba abinci har na fidda shi duka,haka na jera kwanukan kan ƙaton faranti na kai gaban Mama.

Nan kowacce ta ɗauki nata ni ma na ja nawa tare da komawa gefe na fara ci kenan sai ga Sallamar Hajiyar Lubabatu ƙawar Mama wacce a duniya in akwai wacce ta tsane ni bayan Mama to ita ce ta biyu.


Ina ƙoƙarin sunne kai don gudun mugun kallon da za ta watso mini,amma sai ta shammace ni ta sakar min murmushi har da tsarabar furuci mai daɗi.

“ Ah ƴata Jakini abinci ake ciki?” ta faɗa .

Da sauri na gaishe ta “ ina wuni Tanti?”

“Lafiya lau alhamdullah” ta amsa kafin su soma taɓawa ita da Mama,can kuma suka miƙe suka shiga ɗaki.Da wannan damar yasa na matsa kusa da ƙannan nawa ina mai cewa “ yawwa ku koya min karatun”


Ayo mai mugun hali ta miƙe ta shige ɗaki,sai Sarah ce ta fara koya min duk da ba a rubuce ne ba amma ina fahimta sosai.


“Janiki ashe har yanzu kina ta ƙoƙarin koyon karatu?” Hajiya Lubabatu ta faɗa bayan ta fito na tsawon lokaci da suka ɗauka ita da Mama a ɗaki.Na ɗan saki murmushi tare da jinjina kai,ta ƙara yin ƙasa da murya ta ce “ yawwa ki daure ki koya kin ji ai ana son mace ta waye ta fannin karatu,in kina so ma zan turo malami na Musamman don koy...” maganar ce ta yanke saboda fitowar Mama.


“Kin ga fa Ayo ce da rigimar da ta saba ashe ta ji hirar da muka yi” Mama ta faɗa tana murmushi kafin ta janye Hajiya su nufi ƙofar fita da alamu rakiya za ta yi mata.


Ina nan zaune sai ga Ayo ta fito tana hararena,wanda kuma ban san dalilin haka ba sai da Mama ta dawo.

“To Janiki sai a fara shiri lokacin aurenki yayi,yanzu nan Hajiya Luba ta zo min da shawarar arziki kuma na yi amanna da ita” sai kuma ta yi shiru tana kallona kamar yadda ni ma ita nake kallo.


“Ai kin san babban ɗanta Aliyu ko?” Mama ta tambaye ni,na jinjina kai tare da sunne kai ina jin zuciyata na mugun bugawa da sauri.

“To da shi muka yanke shawarar haɗa ki aure,tun da dama ba wani karatu kike yi ba sannan ba saurayi ne da ke ba” Mama ta ƙara faɗa .Idona ne suka kawo ruwa,na ɗaga kai dakyar na ce “ Amma Mama tsoho ne fa,ya kai shekara arba'in duka-duka nawa nake?”

“Yanzu na haifo ki Janiki!” ta faɗa cikin ƙaraji kafin ta ci gaba da yi min masifa “ wato kin samu zai rufa miki asiri ya aure ki shine za ki wani tsiro min da wani iya yi,a'a ba tsoho ne ba shine tuwo tashi ki bani wuri” ta yi min wata uwar tsawa tare da kai min duka.


Da mugun sauri na tashi na shige ɗaki,kan katifa na haye na ci kuka sosai har na gode ma Allah.A haka na samu bacci ya ɗauke ni,haniyar mutane ce ta tashe ni da bushe-bushe.

“Me kuma ake yi a gidan?” na tambayi kaina,shigowar da Abba yayi ce ta bani amsar tambayar hannunsa riƙe da alawa da goro.Bakinsa kamar gonar auduga tsabar murna,miƙo min yayi kafin ya ce “ kuɗin an gani ana so ne aka kawo miki Janiki,ina taya ki murna ke ma za ki je ɗakinki?”

“Duk yaushe aka tsara wannan ban sani ba? Yanzu fa na kwanta bacci” na yi furicin ina duba tsohuwar agogon ɗakinmu sai na ga ƙarfe wajen biyar har da rabi na maraice alhalin lokacin da na kwanta duka-duka ƙarfe ɗaya ne.


Abba bai wani damu da tashin hankalin da na shiga ba ballantana ya bani amsar tambayar da na jefo,kawai ya ajiye goro da alawar ya fice.Ban iya fita ba saboda har yanzu ina jin hayaniyar mutane da saura ba su watse ba,sai bayan gari yayi duhu ne gidan yayi tsit sai a halinsa kawai.Dakyar na je na yi wanka na sauya kaya na zauna tare da rabka uban tagumi ina tunanin zuciya ‘ yanzu dai gaske Umar za su aura min? Mutumin da kullum fuskarsa a haɗe take bai fara'a ? To shi ya ce yana sona ko shi ma dole za

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login