Showing 6001 words to 9000 words out of 38445 words

Chapter 3 - MAKARANTAR MATSAFA COMPLETE NOVEL By Shamsiya Lauwali Rabo.txt

hannuna zuwa inda aka jera wayoyin manyan masu tsada Iphone na ɗauka sai muka zo nan ya biya kuɗi muka wuce mota yayin da kuma aka kawo min kayana har mota.

Tun a hanya aka soma kiran sallah ga shi wurin da ɗan nisa, Uncle ya ce “ Jabeeru ɗan tsaya mu yi sallah kar jam'i ya wuce mu,dama da alwala ta” wuri direba ya samu ya parker suka fita suka bar ni nan,ina duba sabuwar wayata na ji an ƙwanƙwasa gilashin mota.Da sauri na dubi wurin sai na ga wata tsohuwa mai ƙusumbi a tsaye tana kallona da manyan idonta da suka shige can ciki tsabar tsufa.
Banda ko dala a hannuna tun da ban fito da jaka ba,duk a tunanina almajira ce wannan yasa na buɗe ƙatuwar ledar chocolat da sauran kayan maƙulashe na ɗauko mata cake guda biyu da kuma jus,ina buɗe murfin motar sai ta ɗan matsa gefe na fito .Fuskata ɗauke da murmushi na ce “ ga wannan Kaka banda kuɗi hannuna”


Cike da murna ta karɓa kafin ta ce min “ ki san yadda za ki yi ki hana mijinki tafiya dajin nan rayuwarsa na cikin haɗari tarko ne aka yi masa”
Na yi dariya na ce “Kaka ai ni budurwa ce banda aure”


“Naf shiga mu tafi kin wani fito waje duk ana kallon ki“Uncle ya faɗa tare da buɗe min ƙofa na shiga ina kallon tsohuwar wacce ke tsaye tana yi min murmushi amma abin da ya bani mamaki yadda aka yi sam Uncle bai gaishe ta ba alhalin na san shi da girmama tsofi don shine ya koya min yin sadaka musamman masu rauni irinsu.

Sai bayan na shiga motar ne na lura da ashe tun tuni shi Jabeeru ya zauna kan mazauninsa.Har muka iso gida da tunanin tsohuwar nan danƙare a zuciyata amma sam ban faɗa wa kowa ba sallah kawai na yi na fito na soma buɗe kayan ina nunawa Ammy da kuma ƙannaina biyu Abdul da Mubarak,sai kuma sauran ƴan uwana waɗanda suke cousin ɗina ne.Wayar iphone ɗin dai ce duk suka yi ta taya ni murnar mallakarta don su duk sun jima da yinta in aka cire ƙannaina.Bayan an yi sallar isha'i Daddy da Uncle suka shigo a tare nan ne na ji yana faɗar cewa gobe in Allah ya kai mu Jabeeru direba zai kai mu can ƙauyen Ƙwargwam ni da Inna A'i saboda shi zai wuce can mission.Sam kwata-kwata ban kawo zancen cewa akan Uncle Salem wannan tsohuwar ke magana ba shi yasa kawai ban wani damu ba sai ma rigima da na ɗora masa na cewa to dole da zarar ya sauko ya fara zuwa can inda nake kafin ya zo gida.

A cikin daren ma sai da na yi mafarkin tsohuwar nan ta sake ce min kar na bar mijina ya tafi,amma na share batunta na soma shirin tafiya don tuni tun jiya ka saka komai namu a cikin mota.


Ƙarfe tara tuni mun yi breakfast,sai duk muka fito.Uncle Salem motarsu ce ta wurin aiki ta zo ta ɗauke shi yayin da ni kuma ta gidanmu ce.Duk lokaci guda motocin suka tashi muka hau titi,ta windown mota muke kallon juna ni da Uncle muna sakarwa juna murmushi har aka zo mararrabar hanya motocin namu suka rabu.Sai a lokacin na maido dubana kan titi ina jin abu biyu,kewar Uncle da kuma murnar cikar muradina ba tare na san abin da ke can yana jirana a ƙauyen Ƙwargwam.....
[25/01 20:21] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️


```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.


*FCWA*☀️

________________________


05

Sosai Jabeeru ke sharara gudu kan titin da yake tsit babu kowa kamar an yi ruwa an ɗauke.Kamar daga sama haka na ga tsohuwar nan mai ƙusumbi daga can nesa ta yi tsaye tsakiyar kwalta amma duk nisan tazarar bai hana ni ganin ƙwayar idonta ba wacce ke yi min magana kuma raɗam nake jin sautin muryarta kamar waccan lokacin.
“ Me kike jira da har yanzu ba ki sanar da Uncle ɗinki saƙona ba? In wani abu ya samu ɗana sai na ɗanɗana miki azabar da ba ki taɓa tunani ba ballantana gani a duniya” na shagala sosai da kallon ƙwayar idon nata sam ban san lokacin da Jabeeru direba ya kawo dab da ita ba,cikin ƙaraji na ce “ Jabeeru ka taka burkiiii!” sai dai ko kafin in rufe bakina tuni ya ratsa ta jikinta amma abin mamaki sam bai kaɗe ta tamkar dai iska wannan mai kaɗawa haka gangar jikinta take.



Jabeeru ya tsayar da motar,ina haƙi ina ƙari na ɓalle murfin motar na fita na je na yi tsaye na duba can gaba a zatona ko zan ganta sheme a ƙasa sai dai wayam ba komai.Kamar wata mahaukaciya haka na ƙara yi a guje na duba bayan motar nan ma babu kowa ko ɗigon jini babu.Da na leƙa ƙarƙashi ma babu komai,tuni sun fito suna tambaya ta lafiya.Kai na dafe kafin na koma cikin mota na ɗauki wayata don na kira Uncle Salem sai dai sam babu network.Zuwa wannan lokacin hankalina ya soma tashi ji nake kamar dai gaske wani abu zai same shi.


“ Wai Nafisa lafiya duk kike wannan kai komon kamar mai saffa da marwa?” Inna A'i ta tambaye ni.
Ba tare da na dube ta ba na ce “ network nake nema ina son kiran Uncle ne”
Jabeeru direba ya ce “ Hajiya fatan dai lafiya?”
“ Jabeeru ina son samun network don Allah,mu je ko cikin dajin nan ne mu duba ko zan samu tsauni na hawa” na faɗa kamar zan yi kuka.

Inna A'i ta ce “ a'a gaskiya ba zan bari ki shiga daji ba,daga ganin wannan ciyayi ba za su rasa maciji ba.Ki yi haƙuri mu ƙara gaba na san za a samu”
Jabeeru direba ya yi caraf ya karɓe zancen“ eh Hajiya wallahi sosai ake samun macizai zo mu ƙara gaba ai mun kusa shiga inda ke da network tun da ga ƙarfen falwaya can ina tsinkaye” jin yadda suke ta tsorata ni yasa na yarda muka koma ciki sai dai juyin duniya motar ta ƙi tashi a dole kuma muka sake fitowa Jabeeru ya soma dubawa.


Da wani irin gudu na ratsa cikin ciyayin saboda wasu manyan duwatsu da idona suka hango min.Ina jin Inna A'i na kirana amma ko waigowa ban yi ba ballantana na amsa mata,da isa ta na hau can ƙoli ai kuwa sai ga network ya shigo ko kafin na kira Uncle text ne birjit irin waɗanda ake turowa in an so a kira mutum amma ba a same shi ba.Hannu na rawa na rubuta lambar Uncle Salem wacce ke zaune raɗam a kwanyata,sai na ji yana cikin kira amma ba a ɗauki lokaci ba ya ɗaga yana mai jan ajiyar zuciya yayin da ni kuma na saka masa kuka tare da soma magana “ Uncle Please kar ka tafi tarko suka haɗa maka duk ƙarya ce babu wani kashe sojojinku da aka yi, Please ka koma gida”

“ Naf lafiya kike kuwa? Wane irin zance ne wannan? ” ya faɗa .Na ce “ ni ma ban sani ba wata baƙar tsohuwa ce ke son haukata da farko ta ce mijina,yanzu kuma ta ce kai”

“ Ya siffarta take?” ita ce tambayar da ya jefo min.
Na ce “ tana da ƙusumbi...” ko kafin na ida koro masa sauran bayanan ya ja wata ajiyar zuciya kafin ya ce “ Ok to” yana faɗar haka aka shaida min kuɗina sun ida,daidai nan kuma na ji muryar Inna A'i tana cewa “ Nafisa zo mu wuce motar ta tashi” tuni na sauko na kama hannunta muka fito daga cikin ciyayin don sai da ta biyo sawuna.

Muna shiga motar muka ci gaba da tafiya cikin gudun da ya saba,sai da muka yi wajen awa uku kafin ya tsaya mu ci abinci da kuma fitsari sannan muka ɗora tafiya .Ba mu kai ƙauyen Ƙwargwam ba sai wuraren sallar azahar lokacin rana ta zo tsakiya,muna shiga garin gabana ya soma faɗuwa ina jin wani irin yanayi kamar wacce ta taɓa zuwa dama har da wasu tsofin moments nake gani wanda na rasa daga ina suke ziyartar kwanyata sam ban taɓa kawowa cewa suna ɗaya daga cikin ire-iren mafarkan da nake yi ba tun ranar da na soma ganin period.


Kamar yadda tun kafin mun tawo Uncle ya bani duk wasu takardun sheda da ya karɓo daga can makarantarmu haka muka samu wani yaro ya kai mu can gidan shugaban makarantar wanda yake cikin ƙatuwar school ɗin wacce sosai na yi mamakin yadda aka yi ma aka gina ta.

Da isar mu can sai muka taras da wasu malaman da alamu suma zuwansu kenan .Tarba muka samu daga wajensa kafin ya nuna mana ɓangaren jerin flat/appartement ɗin da aka tanada domin malaman ƙetare waɗanda ba ƴan ƙauyen ba.Kowane daga cikinmu ya bamu key ɗin ɗakinsa kafin mu wuce ,Jabeeru ya tuƙa mota har zuwa ƙofar ɗaki mai lamba uku wato nawa.Shi ne ya kai mana kayanmu ciki,ɗakin tsaf yake bai da datti kamar an sa da zuwanmu.Ciki guda ne sai toilet da kuma ƴar ƙaramar kitchen,haka duk muka jera komai wajensa Inna A'i ta cire zanen da muka tarar shimfiɗe kan ƴar madaidaiciyar kafitar ta shimfiɗa wata,na shiga toilet bakina ɗauke da addu'a na yi wanka tare da alwala sannan na fito sai na tarar tuni Jabeeru ya tafi ko sallama bai yi min ba .Dadduma na shimfiɗa na gabatar da sallah yayin da ita kuma Inna A'i ta shiga toilet ita ma don yin wanka.Ina zaune ina lazumi na ji ihunta haɗi da yin ƙara,kafin kuma na ji tana magana da alamu akwai abin da take kora can kuma ta fito kamar wacce aka jefo.


Cike da kulawa na ce “ Innarmu lafiya?”
Cikin masifa ta ce “tsakaka ce na gani kin san ban son ganinta“ ta bani amsa.
Na ce “ ai kuwa inda kashe ta kika yi da kin samu lada ”

Ba tare da ta ce komai ba ita ma ta zo ta yi sallar bayan ta gama ne muka soma taɓa hira kafin kuma mu ji bugun ƙofa,ita ce ta je ta buɗe sai kuma ta dawo hannunta riƙe da kwanon abinci tana mai cewa “ kin ga shugaban makaranta ya aiko mana da abinci”

Na ce “ ban jin yunwa amma in kina ji kawai ki ci ki rage min”

Inna A'i ta ce “ ai kuwa ina ji tun da a mota abin turawa ne kawai kika bamu ” tana nufin cake.Na yi dariya tare da ɗaukar wayata na soma saita app don jiya ban samu na yi ba.Ita kuwa Inna A'i hankali kwance take cin shinkafa da miyar kajinta tana santin cewa ashe ƴan ƙauye ma sun iya girki,ashe ba ta san guba ce take ciwa kanta ba.



★ Uncle Salem

Tun jiya da ya rabu da zoben hannunsa yake jinsa wani iri tamkar gangar jiki babu ruhi amma babu yadda ya iya haka ya haƙura ya bar wa Naf ɗinsa.Tun asali zoben Inna Delu ce ta basa shi a ranar da ta sanar da shi za ta koma can maƙabarta makwancinta,sam bai san amfanin zoben ba amma yau da Nafisa ta kira shi ta sanar da shi cewa ta ga tsohuwa mai ƙusumbi kawai ya fahimci wato sirrin ganin Inna Delu da yake a duk lokacin da wata matsala ta tunkaro shi ya ta'allaka ne da zoben.Suna tsaka da gudu ya cewa direban da ke jansa yayi su koma gida,cike da mamaki direban ya juyo ya dube shi sai dai babu damar tambaya don bai ma ga fuskar tambayar ba .
Suna tafe yana tunanin yadda Naf za ta ɗauki wannan lamari mai kama da wahayi don gudu yake abin ya bata tsoro don ya fahimci har zuwa yanzu kamar ganin abin take a mafarki.

Tunani ya soma ta yadda zai bi ya karɓe zobensa ba tare da ya ɓata mata rai ba,a haka har suka isa Company.Ya fita cike da izzarsa wacce ba kullum yake bayyanar da ita sai in yana cikin fushi ko kuma yana son gwada ƙarfin ikonsa akan wasu.Ofis ɗinsa ya nufa tare da buɗe shi,yana shiga ya duƙufa yin bincike.


★Ƙwargwam

Sallah kawai ke raba ni da wayata wacce bayan na kira gida mun gaisa na shaida musu mun sauka lafiya sai na soma chating da ƙawayena a whatsapp.Hira sosai muke a group ɗinmu na ƴan makaranta har dare yayi,sam ba mu yi girki ba saboda akwai abinci shi Inna A'i ta ƙara ci kafin ta kwanta ni kuma sam ban jin yunwa saboda dama haka nake muddin ina maƙale da wayata.

Kiran Uncle Salem ya shigo a lokacin ne kuma na yi alwala na canza kaya ina shirin yin shafa'i da witiri na kwanta.Na ɗauka tare da yin sallama na gaishe shi cike da girmamawa sannan ya soma tambaya ta hanya ina basa amsa har muka yi hirar yadda muka samu tarba mai kyau.

Ya ɗan jan numfashi kafin ya ce “ ina kewarki Naf”
Na yi ƴar dariya kafin na ce “ Uncle tun da ka fasa tafiya me zai hana ka zo nan ɗin ka yi kwana biyu?”
Ya ce “ kika ce ɗaki ɗaya ne tal inda aka sauke ku”
Na ce “ eh amma ai ba za a rasa wurin da za ka kwanta ba ko da hotel ne”
Yayi ƴar dariya kafin ya ce “ to zan duba na gani,amma Please ki kula min da kanki sosai banda magana da maza ko da kuwa shugaban makarantar ne ban so”
Na ce “ to Uncle in sha Allah,amma yaushe za ka zo?”
“ Sai zuwa wani satin Naf,yanzu akwai binciken da zan yi”

Kafin na basa amsa sai da na juya na dubi Inna A'i wacce ta zagaya toilet a karo na uku tun lokacin da na soma waya,ina son tambayarta lafiya amma saukar numfashin Uncle a kunnena yasa na ƙara mayar da hankali wurinsa.
“ To Uncle zan fara lissafin kwanaki tun yanzu”
“Faɗa min me za ki shirya min na special?” tambayar da yayi min kenan wacce na ji wani banbarakwai don har wani salo na daban amon muryarsa ke fitarwa.Kamar zai yi kuka na ji yana cewa “ Please Naf faɗa min mana kar ki ji kunyata ” hakan kuwa ya ƙara ɗaure jijiyoyina na rasa amsar da zan basa,daga can toilet na soma jiyo saurin nishin Inna A'i cikin azaba babu wani tunani na kashe kiran Uncle ɗin tare da nufar toilet ɗin ina tambayar lafiya.Ba ta bani amsa ba sai ƙofar toilet ɗin da ta buɗe ƙiiii da kanta,daga inda nake tsaye na hangi Inna A'i zaune kan wc tuni ta fita hayyacinta don da alamu gudawa ce take ta yi.
Tsakaka na gani kan katanga tana saukowa kamar za ta faɗo bisa kanta da mugun sauri na ɗauki takalme ina kiran sunan Allah na kashe tsakar,ta kuwa faɗo ƙasa bindinta ya rabu da gangar jikinta da mugun sauri kuma ta bi ta ƙafafuna shuuu ta fice ta bar guntun bindin wanda sai motsi yake.

Daidai nan Inna A'i ta soma kelaya amai kamar hanjinta za su faɗo,ba tare da tsantsani ko ƙyanƙyaminta ba na taimaka mata ta yi wanka ,bayan nan na sa abin kwashe shara na saka bindin tsakakar sannan na wanke toilet ɗin na rufe ƙofa.Ina zuwa tuni Inna A'i ta yi bacci,ni ma sai na raɓa gefenta na kwanta.
Washegari bugun ƙofar ɗakinmu ne ya tashe mu,yadda ake jijiga ƙofar kamar za a ɓallata yasa muka kalli juna kafin na miƙe na je na buɗe,da sauri na yi baya ina kallon shugaban makarantar da mamakin abin da ya zo nema a yanzu ko ƙarfe shidda ba ta yi ba.Yadda kuma yake yi min wani kallon tsaf yasa na sha jinin jikina......


Ga mai son shiga paid group 500 ne via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

Sai ya turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
[26/01 13:14] MRS SADAUKI: *MAKARANTAR MATSAFA*☠️


```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA :* Ga dukkan Malaman makaranta.


*FCWA*☀️

________________________

6-7


Na haɗiye wasu yawu muƙut, Allah na gani ba na cikin mutane masu mugun tsoron nan don za a iya kirana jaruma kai tsaye amma kallon idon headmaster kaɗai sai da suka hautsana hanjin cikina.

“ Barka da warhaka shugaba!” na samu bakina dakyar ya furta.
Ya saki wani murmushi wanda kana gani ka san ba na jin daɗi ba ne kafin ya ce “ lafiya! Ina son duba toilet ne don ganin ko gyaran da aka yi yayi” ya faɗa cikin wani irin amo.
Kamar na ce masa wane gyara kuma amma sai na basa wuri ya shigo,cike da girmamawa ya gaishe da Inna A'i wacce ke zaune har yanzu a inda na bar ta kafin ya shiga cikin toilet ɗin na take masa baya kuwa.Dube-dube na ga yana yi kamar mai neman wani abu amma ban kawo komai ba don na yi tunanin ko gyaran ne a gaske yake dubawa .

Fuskarsa duk ta nuna alamun ƙin jin daɗi har zai fito sai kuma ya tsaya cak yana cewa “jinin mene ne can?”
Inda ya nuna na duba sai na ga daidai wurin da na kashe katsakakar jiya ne,amma ai na wanke toilet ɗin sosai ta ya aka yi jinin bai fita ba.

Yadda ya watso min idonsa masu matuƙar dafi yasa na soma inda-inda,“ dama...dama jiya ne da Innarmu ta shiga ta ga tsakaka...” da sauri ya katse ni “ kenan ita ce ta buge mata bindi? ”
Tsuru-tsuru na yi don ina tsoron kar ya kore ni ya ce ba zan koya ba,ya ƙanƙance ido ya ce “mu nan garin ba a kashe ƙwari ban san daga wane wajen kuka fito ba” sai kuma ya fita ni ma na take masa baya,ina kallon yadda ya bi Inna A'i da wani mugun kallo kafin ya fita.


Ɗakin na rufe bayan na gama kallon yadda har a wajen sai da yayi ta dube-dube.
Ko da na juyo sai na ga tuni ta shiga toilet,sai na jira ta fito sannan na shiga ni ma na yi alwala na fito na yi sallah sannan na zauna na yi Azkhar ɗin safe.

“ Ina kwana Innarmu? Ya ƙarfin jikin naki?” na faɗa bayan na gama komai.
“ Alhamdullah ai na ma warware,ina ga kajin jiya ne suka buga min ciki don na yi doguwar tafiya” ta bani amsa .
Na ce “ ai kuwa dai ,yanzu ki kwanta ki huta dai zuwa an jima sai ki yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login