Showing 33001 words to 36000 words out of 38445 words

Chapter 12 - MAKARANTAR MATSAFA COMPLETE NOVEL By Shamsiya Lauwali Rabo.txt

sai ya riƙe min tsintsiyar hannu.Wani irin kallo ya soma aiko min kafin kuma ya sakar min hannun,da sauri na shige toilet ina mamakinsa ko me ya shiga kansa yau.
Bokiti na tara a pampo kafin na soma yin wankan,ana buɗe ƙofa na san da shi ne.Ko juyawa ban yi ba haka na ci gaba da yin wankan a takure ina jin idonsa gare ni.Na jawo towel zan ɗaura yayi saurin fizge shi daga hannuna,daidai kunnena ya min raɗa “ ina so mu yi wanka tare” ban kai ga yin magana ba ya buɗe shower ruwan suka zuba gare mu.Na ja wani numfashi saboda sanyin ruwan ina shirin guduwa ya riƙe ni gam tare da juyo ni muna facing juna,“ mene ne?” yayi min tambayar a dake .Idona suka kawo ruwa na ce “ ban so na jiƙa gashina” sai ya sa hannu ya cire hullata wacce ko bacci bai raba ni da ita yayi cilli da ita.

Gashina da na laulaye na yi masa naɗin tayar mota ya warware tare da cire ribob ɗin,ido ya waro ganin sumar kaina.Kamar wani sakarai ya soma shafa ta yana jan ta cike da mamaki,yana tallabo fuskata na lumshe ido.

Wanka muka yi cike da salon romantic,yadda Aliyu ya tafi da ni cikin shauƙi da tausasawa kamar ba shine na jiya ba da yayi ta yi min tsawa.Yadda ya manne ni a ƙirjinsa yana sauke min huci a kunne shi ya fi ɗaga min hankali,kamar wata ƴar baby haka yayi min wanka.Karon farko da na ga soyayya gun ɗa namiji don ban taɓa yin saurayi ba,bayan ya gama yi mana wankan muka ɗaura towel har zan taka da ƙafata amma sai ya ɗauke ni.A zuci na ce ‘ ka ga wani sabon salo’ kan bed ya shimfiɗe ni,yana shirin warware min towel na ce “ ka rufo ƙofa”

“Na ru..fe ta ca..cccan falo ” ya faɗa muryarsa na rawa,haka kawai na ji tausayinsa saboda tsantsar buƙatuwa da na hango cikin ƙwayar idonsa amma na san ba za a je ko ina ba saboda bai da wani ƙarfin.

Ido kawai na lumshe tare da yin shiru ina karɓa saƙonsa,ko ta ina yake min sumba jikinsa na yin rawa.Ɗumin hawayensa ne suka sa na buɗe idona,da dukkan alamu ya ji takaicin yadda yanzu ma da ya so kusantata kawai komai ya tsaya cak babu biyan buƙata.Fuskarsa na tsure ina kallo ,kyakkyawa ne shi duk da yana baƙi hakan bai ɓoye kyawun nasa ba.Ya koma gefe tare da kai hannu ya kashe ƙwan lantarki,ɗakin sai yayi duhu.

“Zahra!” yayi furicin ,ban amsa ba don ba haka ne sunana ba.Ya jawo ni ya maido ni kan ƙirjinsa tare da cewa “ shine kika yi shiru?”
“Ni sunana Janiki” na faɗa .
“Ban sonsa ne shi yasa na zaɓa miki sunan Zahra shi ya fi yi miki kyau,tun da kin ga kai tauraruwa ce”

“ Zahra na nufin tauraro?” na tambaye shi.
Ya ce “ eh mai mugun haske ma kuwa”

“Kenan ni tauraruwa ce?” na sake jefa masa tambayar.Shiru yayi kafin can ya ja numfashi ya ce “ eh ”
“Saboda me?”

“Me yasa kika aure ni?” shi ma ya jefo mini tambayarsa.Sai na kasa cewa komai,hasken ɗakin ya kunna kafin ya ƙara maimaita min tambayar yana kallon cikin idona a dole na amsa masa da “ Mama ce ta ce na aure ka”

“Hajiya Mama?”
Na girgiza kai na ce “ a'a Mamana”
“Kafin su aura miki ni sun yi miki bayani kaina ba?”
“Wane bayani?”
“ Komai!” ya faɗa tare sake kashe hasken,ina jin yadda bugun zuciyarsa ke tafiya da sauri-sauri.

A hankali na ɗan janye daga jikinsa kafin na juya masa baya,amma kamar wani ƙaramin yaro haka ya zo ya ɗora min ƙafarsa ɗaya tare da zagaye cikina a dole dai ya mayar da ni cikin ƙirjinsa.A haka muka yi bacci kafin lemar fitsarinsa ta tashe ni,na janye jikina da sauri tare da kunna hasken ɗakin shi ma ya farka sai muka fara ƴar kallon-kallon kafin kuma ya sauka ya je ya shiga toilet.Ni kuwa tsaye na yi ina kallon gadon da yayi shaɓe-shaɓe da fitsarin,a yau maimakon takaici sai na ji tausayinsa....



My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822
[26/12 à 09:10] MRS SADAUKI: My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822



Last free page 10


Zanen gadon na cire ,sai na dubi ƙofar toilet da nake ta jin ƙarar zubar ruwan shower da alamu wanka ne yake don dole sai wankan tun da uban fitsarin nan da ya shashaɓa min.Ganin ba zan iya jiransa har sai ya fito ba kawai na yi niyya fita waje na ciko bokiti da ruwa na goge ledar da ke kan katifa.Ba tare da wani tunani ba na suturta jikina kafin na je na buɗe ƙofa na fita tsakar gida.Wani irin mugun haske ne na jar wutar mai kamar ta murhu ya min maraba,kaf tsakar gidan ya ɗauki kalar ja yayin da sararin samaniya yayi baƙi ƙirin kamar bayan tukunya sai giza-gizai ke gudu .

A tsorace nake kallon giza-gizan masu kamar zanen fuskokin mutane,na toshe kunnuwana saboda wata gurɓataciyar murya da ke rera waƙa cikin wani kiɗa marar daɗin sauti kamar ana kiɗa goge.

Baya-baya na soma da na ƙasa na darewa tana tsagewa kamar yadda in an yi girgizar ƙasa za ka ga wuri na ɓaɓarewa.Ihu nake son yi amma tamkar wacce aka riƙewa murya na kasa,hatta motsa ƙafafun haka na kasa gusawa saboda yadda nake jin tamkar an ɗinke fatata da kuma ƙasa.

Wani haske ne ya tawo daga sama kamar tauraro ya hankaɗa ni na yi baya tare tashi sama ban dira ko ina ba sai cikin ɗakina,yayin da kuma ƙofar ɗakin ta bada ƙiiii tare da rufe kanta.

Na dafe saitin zuciyata ina jan numfashi kafin na tashi dakyar na koma bedroom,sai na tarar tuni Aliyu ya fito daga wankan yana tsaye kan dardduma yana Sallah.Toilet ɗin na shiga na ciko bokiti da ruwa na goge ledar tare da saka wacce ta ɓace cikin bokitin,tun a cikin daren na wanke ta sannan na yi wanka na fito.Har yanzu yana kan dardduma ,kayan jikina na saka sannan na shimfiɗa wani zanen gadon.Can ƙarshen gado na hau na kwanta ,abubuwan da suka faru yanzu da na fita suka faɗo min a rai.


‘ To wannan ɗin duk na mene ne? Ko dai gamo na yi?’ sai kuma na watsar da tunanin don banda wanda zai ban amsa.Ina nan kwance shi ma ya zo ya kwanta tare da kashe hasken ɗakin.A tsorace na tashi na ce “ Please ka kunna haske tsoro nake ji”

“ Zo nan ” ya faɗa tare da jawo ni cikin ƙirjinsa,ido na rufe ruf ina jin zuciyata na bugawa da ƙarfi.“ Me ya tsorata ki?” ya tambaye ni.

“Babu komai kawai ban son duhu ne” na basa amsa.
“To ko ma mene ne ba zai taɓa zuwa nan ba don cutar da ke muddin kina kusa da ni” ya faɗa tamkar ya shiga raina ya ga abin da nake tsoro.
Lamo kawai na yi ina sauraren bugun zuciyarsa,a hankali yake dadaɓa ni alamun na yi bacci.Na yi murmushi ina tuna can gidanmu yadda nake bacci ni ɗaya,ga shi kuma yanzu na samu abokin kwana duk da auren ba mai moruwa ba ne amma da ɗan sassauci kan rayuwata ta gida.

Kalamansa ne suka katse min tunani inda yake cewa,“ Zahra na san ba ki sona an aura miki ni ne bisa dole,sannan kuma yanzu da aka kawo ki sai kika ƙara tsanata saboda larurar da kike tarar ina da ita.Ki yi haƙuri da sannu za ki saba za ki ga kamar ma yana ɗaya daga cikin aikin da kika fi so na wankin kayan fitsarina,abu guda na sani kina da lada don ni mijinki ne sannan aure dukkansa bauta ce.Allah ne ya ɗora min babu yadda na iya,ba wai zaɓina ba ne duk da farko abin ya addabi ruhina har ya taɓa aikin da nake saboda ina tsoron yin bacci a cikin abokai na yi fitsarin kwance.Shawarar Mama ce da nake bi nake ganin canji,ita ce ta ce min kar na damu da duk halin da zan samu kaina Allah bai ɗorawa bawa abin da ba zai iya ɗauka ba,sannan in na je can mission inda zan yi bacci cikin mutane na saka a raina ba zan yi fitsarin ba,kuma kin san abun mamaki hakan take faruwa fa sosai nake jin daɗi” ya ƙarashe maganar yana sakin murmushi mai sauti yayin da kuma yake shafa gadon bayana.


“Amma kuma sai in ka zo nan gida ne kawai fitsarin yake dawowa?” na samu kaina da tambayar shi.

Ya bani amsa da “ eh! Amma ko a gidan ba kullum ba ne nake yi”

“Ita kuma ɗayar matsalar fa?” na tambaya a kunyace,shiru yayi bai bani amsa ba sai da aka ɗauki lokaci kafin ya ce “ wace matsala kenan?”

“A'a ko ɗaya ,zan yi bacci” na faɗa jin yana son raina min hankali wato fitsarin kwance kawai ya ɗauka a matsayin matsala shi rashin kusantata da ya kasa yi ba matsala ba.


“Zahra don Allah kar ki guje ni kin ji?” ya faɗa yana wani ranƙwafowa kamar mai leƙen fuskata.Na turo baki gaba kafin na ce “ kar ka damu Janiki ba ta taɓa yin farin ciki ba dama,ina tabbacin cewa sanin zan iya zama da kai suka haɗa aurenmu” na yi furicin hawaye na surnano min.


Hasken ɗaki ya kunna tare da yin zauna ,sosai nake jin idonsa a kaina duk da na juya masa baya.
“Ki bani labarinki” ya faɗa .
“Aliyu ba ka jin bacci ne halan?” na faɗa
[30/01 08:49] MRS SADAUKI: MAFIYA*☠️

01

‘ Lokacin da muna yara,da zarar an ce MAFIYA kawai abu guda kwanyata ke bani ƙungiyar shan jini ce mai sa a yi kuɗi.Amma yanzu da na girma,na kuma tsinci kaina a ciki sai na fahimci cewa MAFIYA na nufin cikar muradi.
Sunana HAROON matashi ne ni ɗan kimanin shekara talatin da takwas a duniya,maraya na uba ,shalelen mahaifiyata.Na taso cikin matsin rayuwa ta talauci kafin kuma na tsinci kaina cikin daula...... '


“Haroon sakatariyarka ta ce yau ba za ka fita ba ko zan san dalili?” muryar Ammy ta katse mini ɗan taƙaitaccen tunanin zucina wanda kusan lokuta da dama nake zama haka kawai ina bai wa kaina labarin kaina.

Na saki murmushi ina kallon sanyin idaniyata abar alfaharina,“ ban jin daɗi ne Ammy shi yasa,amma kar ki damu ciwon kai ne kawai”

“Kamar ya kar na damu ? Ciwon kan ne kake faɗa ƙaramin abu? Jira ni ina zuwa” ta faɗa tare da yin gaba.

Na bi ta da kallon ƙauna,Ammyna kenan uwa ta gari wacce a idonta sam ba na girma kullum tamkar ƙaramin yaro haka take ɗauka ta.Ina nan zaune ta dawo hannunta riƙe da wata tasa da kuma ƙaramin towel,na lumshe ido lokacin da ta soma tsoma towel ɗin a ruwa tana matse shi sai kuma ta dinga dadanna shi a kaina.Cikin ikon Allah na ji ciwon kan yayi sauƙi,“Ammy ya isa haka je ki huta mana ban san yaushe za ki daina ɗawainiya da ni ba,kamar wani ƙaramin yaro dai sai ririta ni kike” na faɗa ina mai riƙe hannunta mai ɗauke da towel ɗin.


Ta dungure mini goshi cikin faɗanta da ta saba yi min ta ce “ sai ranar da ka kawo matar aurenka a gidan nan.Wai HAROON yaushe za ka yi aure ?”

Da sauri na miƙe ina mai cewa “ aure! Aure dai kullum shine zancenki Ammy,duka nawa nake?”

“Yanzu na haife ka” ta bani amsar da ta saka ni dariya,sai kuma na ce “ kar ki damu zan nemo miki suruka kafin ƙarshen shekarar nan in sha Allah!” na furta ina mamakin furucina na ƙarshe da na ambaci sunan maƙagina,wanda a ƙalla zan kai shekaru biyar da muka yi hannun riga ni da umarninsa.Yanzu haka ambaton sunansa sai da na ji maƙogorona yayi min wani zafi,halshena kuwa tamkar an saka reza ne an tsaga shi.



“Allah ya nuna mini wannan babbar rana, Ubangiji yasa ina da rai albarkacin Manzon Rahama Ya Rabb ka dubi Harunana ka basa mata ƴar aljanna mai haska duk wani duhun gidansa” ita ce addu'ar Ammy gare ni,ban ko amsa ba na yi gaba abina.


Ina fitowa harabar tsakar gida direbana yayi saurin tashi tare da nufar motar da a yau ita ce zan shiga.Da kansa ya buɗe mini gidan baya na zauna,sannan ya ja motar. Hanyar babban ofis ɗina ya ɗauka amma na yi saurin dakatar da shi.“ Ka ga kai ni wurin da zan ɗan shaƙi iska yau ban ra'ayin aiki ko kaɗan ” na faɗa don haka kawai nake jin yau raina a dagule babu daɗi ga wani irin bugawa da zuciyata take.



Gudu yake da ni amma hankalina ba ya ga hanya na lula sosai cikin tunani,ƙiiiii ya ja wani uban burki sai a lokacin na dubi gabana.Wata kyakkyawar budurwa na hango tana tsallakar da yara ƴan makaranta,yayin da duk ababen hawa suka tsaya suna jiran sai yaran sun gama wucewa.


“Yi haƙuri yalaɓai bari na canza hanya” cewar direba ,da sauri na ce “no ! Jira” ido kawai na tsura mata yadda take ta zulumniya cikin ƙaton hijabinta ,yayin da hannunta kuma wanda ya sha jan lalle ke faman kamo na yara.


Ido na lumshe sa'ilin da ta game dukkan hannuwanta alamun godiya ,ban san mun bar wurin ba sai da na ji direba yana cewa “ba don Malam Zainab ba ce da ƙila mutanen nan ba su tsaya ba sai an samu waɗanda za su ce sai sun wuce”

“Ka san ta ne dama?” na samu kaina da tambayarsa.

Yayi ƴar dariya ya ce “to wane ne zai ce bai san Malama Zainab ba,yarinyar da duk shekara ita ce ke cin gasar musabaƙa ta duniya.Makarantar can ma gwamnati ne ya buɗa mata ita da sunanta,yalaɓai in ka ji yadda ɗalibanta ke yin larabci kai kace ƙyanƙyasar Saudiya ce uwa uba ita in tana yi.Zaƙin muryar.....”


“Ya isa haka juya ka mayar da ni gida” na yi saurin katse shi saboda bugun zuciyata da na ji sai ƙara hauhawa yake.Muna isa gida ko wani burki mai kyau bai yi ba na yi saurin fita daga motar ba tare da na jira ya buɗe min ba.


Ammy na falo ta ga na shigo a hargitse,ta yo kaina tana tambayar lafiya amma ban bata amsa ba na haye step ina taka shi bibiyu yayin da ita kuma ta mara min baya tana faman kiran sunana.Ina isa ɗaki kuma na rufe shi gam da key,ga ƙofar na jingina ina sauke numfashi kafin dakyar na ƙarasa na je na zauna kan kujera ina kallon kaina cikin baƙin madubin da shine silar canza rayuwata daga jiya zuwa yau.A zahiri ni mutum ne complet,amma a cikin madubi ba komai ne ba face ƙwarangwal ba tsoka saboda da kaina na sayar da ruhina ga MAFIYA.........
[26/12 à 09:33] MRS SADAUKI: *MAFIYA*

02

Karon farko kenan da na yi da na sanin shiga MAFIYA,a tsawon shekarun da na yi a ciki na yi su ne cikin farin ciki.Hawayen takaici nake yi yayin da ƙwarangwal ɗin da ke cikin madubi ke ƙyartata dariya,ita ƙwarangwal ɗin nan ba kowa ba ne face Ni,inuwata ce ko kuma na ce ruɓaɓen ruhina.Daga can bakin ƙofa ina jin Ammy na buga wa tare da kiran sunana amma na kasa tashi ,zuciyata ta yi rauni ba zan iya tsayuwa gabanta ba na shaida mata alƙawarin da na yi mata na samo matar aure ne ya cika sai dai kuma baƙin ruhina da farin ruhin kyakkyawar budurwar nan sam ba za su iya zama a inuwa ɗaya ba saboda rayuwar da ta rage min ƙalilan ce.



Wayata ce ta ɗauki ruri,ina dubawa na ga sunan Oga.A dole na ɗaga,“ ka zo muna da meeting ɗin gaggawa” shine abin da ya faɗa kafin ya kashe.

Jiki babu ƙwari na miƙe na shiga toilet na wanke fuskata na goge ta da towel sannan na fito.A bakin ƙofa na ga Ammy idonta sun yi jawur,na sakar mata murmushi na ce “ kar fa ki damu kan ki zan nemo wata tun da wannan ɗin ta fi ƙarfina”

“Wa kenan?”

“Budurwar da na gani yanzu da muka fita,kin ga Ammy kar ki damu zan cika miki alƙawarin da na ɗauka” ina gama faɗa na soma tafiya,ta biyo bayana har muka sauko ƙasa sannan ta ce “ ƴar wace ce ita da har ta fi ƙarfin ka?”

“Ba kowa ba ce kawai malamar makaranta ce” na bata amsa,“ mi sunanta?”

Na juyo muna facing juna sannan na bata amsa da “ zan fita yanzu in na dawo za mu yi maganar”

“Allah tsare ka ya maido mini kai lafiya”

Dakyar na amsa da “Amen ” .Ina fita na karɓi key ɗin mota,don in magana ta shafi Oga ban bari a yi draving ɗina.Tuƙi nake amma idona ita suke hasko min,dakyar na samu na kai kaina can inda muka saba meeting ɗin.


Tuni mutane sun fara taruwa,na samu wuri na zauna muka ɗan soma cacabke wa da sauran members.Sai da kowa ya hallara sannan wurin yayi tsit,Oganmu sai a lokacin ya miƙe ya soma jawabi.“ Kamar yadda kuka sani wannan Association ɗin namu yana da tsari,ba a shiga kudin sirrin kowa hakan ne yasa wasu informations ɗin ba mu samunsu kai tsaye ta yadda za mu fahimci daga ina suka fito.Sai dai sosai dakarun bayar da kariya suke iya ƙoƙarinsu wurin ganin babu wata ƙungiya ko baƙin haure da za su kawo mana hari.To yau ma ɗin mun samu labarin cewa wani mummunan al'amari na tunkaro ƙungiyarmu ,kune ƴaƴanta kune kuka san yadda kuke gudanar da rayuwarku don haka ku nutsu ku yi nazari a cikinku babu wanda ya tsokano faɗa ko kuma yayi wani kuskure wanda bai dace da tsarin ƙungiya ba?” Oga na kawowa nan da zancensa sai duk ya soma bin mu da ido ɗaya bayan ɗaya.


Ko kaɗan ban kawo a raina cewa malam Zainab da na soma jin ƙaunarta ita ce matsalar da Oga ke magana a kai ba wannan yasa sam ban ma nuna damuwa ba.Har aka gama meeting babu wanda ya ce ga wata matsala sai Oga ya sallami kowa.Har zan fita ya tsayar da ni,sai da ya kalli tsakiyar idona kafin ya ce “ HAROON ka shekara biyar a cikinmu”

“Ai na sani Oga” na faɗa don ban ga amfanin sanar da ni ɗin ba.

“Eh tuni ne na yi ma don kar ka shagala” ya faɗa yana ƙara yi min kallon nan da ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login