Showing 27001 words to 30000 words out of 48171 words

Chapter 10 - BASO BANE CUTA CE BOOK COMPLETE BY Usaina B Abubakar.doc

mutune kuma shima har da farin gashi kamar yanda na Nafi'u yake, duk wata hanya da suka san za'abi domin bincike su sai da suka shafe ta kafin su tafi, Nafi'u yayi bakin ciki sosai amma duk da haka yaki yarda yayi abinda suke buk'ata yana ji yana gani suka raba shi da gidan sa da kuma ahalin sa baki d'aya...

Da safe kowa ya tashi cikin walwala da jin dadi amma banda Jawahir da take jin ta kamar marar lafiya, gida ya kaure da hayani da aike-aike jama'a suka fara taruwa haka su Baffa Abdullahi su ma suka d'au wanka kowa ya k'afe a mazauni sa, duk wanda ka kalla a gida farin ciki ne akan face din sa duk da mutanan gidan basu san mak'asudin taron ba...


Jawahir na hango ta d'au wanka kyau iya kyau, ta sha wata doguwar riga marar kafad'a pink cool kai fan's Jawahir fa ta had'u irin sosai din nan wallahi ga wata kwaliya da akayi mata abin ka da farar mace take ta haska wajen tana wani d'aukar ido, tubarkala na iya cewa kawai..


IMRAN KENAN kyakykyawan matashi meji da iza da k'asai ta yaro me zamani wanda kaf garin kano babu wanda bai sanshi ba, dan yaro ne wanda kudi ya zaunawa ga kyauta da taimakom tallakawa burin ko wace budurwa taga tayi taraiya dashi..
shine ya fito ciki wata shiga ta manya kaya masha Allah domin IMRAN ya wuce tunanin me tunanin dan ni kai na sai da na girgiza da _amma fa duk had'uwar sa bai ka Abubakar din na ba domin shi din.na daba ne yasin. lozzz

idanun kowa ya koma kansu, sai kallon su ake ana sanbarka..

Suma iyaye fitowar su ta musamma ce ko wanne su ya d'au wanka, iyayen su mata kenan ga kaya masu tsada da suka saka ko wace sai wani yauk'i take da bud'e hanci su a lallai ga masu gida...

Jameela ma tayi kyau mutu'ka ita da Khadija kayan su irin d'aya suma masu tsadar bala'i domin ta kanas IMRAN ya siyo musu haka kayan dake jikin Jawahir da kan sa ya zab'a mata, iri d'aya dashi...

Maza sun gama shiryawa amma shiru babu NAFI'U Abdullahi ya kalli 'kanin sa ciki soyayya yace" ka sa IMRAN ya kira mana sirikin sa.." shima cikin murmushi yace" angama.."

Comment

And

Shared

Na Gode sosai kawayen kirki da iyaye na Allah ya biya ku...



Mrs Abubakar ce
[9/2, 11:43 PM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*?x  ?xR?BA SO BANE ?xR??x  *
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYi DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*


1???8????~ 1???9???


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Baffa Adam da kan shi yaje ya fad'awa IMRAN dake hard'e akan kujerar girma, babu musu ya amsa da to, bayan tafiyar sa har zai tashi sai ga wasu abokan sa da suka jima basu had'u, sanni domin shi suka zo sai ya koma wajen JAWAHIR cike da so da kauna yace" k'albi na, in babu damuwa ki kira Baba na mana su Baffa na son ganin sa.." ya fad'a yana kashe mata ido d'aya.

Bata ce komai ba sai kallon sa da take face din ta cike da murmushi ta mik'e tsaye, sai da suka tsaya gaf da gaf numfashin su na gogar na juna, tana wani layi da kuma aladar ta na kar kata kai gefe.

Tace" insha Allah abin k'auna ta mud'in za kayi farin ciki to ni ko zan cika maka burin ka..." ta fad'a tana shagwab'a face.

Cike da nishad'i ya kama kumatun ta ya ja cikin wasa kana yace" shi yasa ban saka kowa ba sai maradin rai na.." shi ma ya fad'a yayi mata alama da ido akan ta wuce..


Har taje gaf da part din su wasu k'wayen ta suka tare ta da hira, ganin haka yasa ta kalle inda Khadija take cikin girmamawa tace" My Anty na dan Allah ki kira Abba a d'aki suna jiran sa.." duk da akwai wani abu a ran ta haka ta daure tayi d'akin ba tare da tace komai ba...

Da salama a bakin ta shiru baa amsa mata ba, sake k'walla salama tayi iya 'karfin ta amma shiru ciki tashiga gaba d'aya, tana sake rad'a salama har ta juyu zata wuce sai taga kamar kafar mutun ne daga gefen gado cikin ta ya d'uru ruwa cikin rawar jiki ta isa waje, ai idanun ta na sauka akan wanda yake kwance take ta saki wata ingataciyar k'ara me firgitar wa. sosai ta shiga kururuwa da ihu dan ta kasa tsayawa waje guda sai ihu take gashi ta kasa fita...


Gani shirun yayi yawa yasa Baffa Adam shiga da kan aa domin kiran sa, tunda ya fito gaban sa yake fad'uwa amma haka ya d'aure har ya isa ga 'kofar part din ihu da yake jiyowa daga nesa shi ne yasa ya karayin sauri cikin azama ya tura kai d'aki cikin tararabi, shi ma cak ya tsaya gani abinda take ma ihu cikin firgici ya shiga girgizata yana fad'i " ke tsaya menene? wannan haukar ta meye??" yayi maganar cike da rud'ewa dan gaskiya ba k'aramin so yake ma yar tashi ba...


Bude ido ta sakeyi da kyau gani tabbas babban ta ne yasa ta k'ank'ame shi cikin muryar kuka da firgici tace" Baffa Baffa Baffa ya mutu shima an kashe shi.." ta fad'a tana mai nuni da hannu ta wajen da gawar take..


Adam jiki ya hau rawa idanun a waje, take wani masifafan tashin hankali ya d'ire mai a lokaci guda, tamkar wawa haka ya dawo bin hannun ta da kallo, har idon sa ya d'ire akan gawar dake kwance samb'ala har ta sandare, gaba d'aya k'wa'kwalawar sa dai na aiki tayi na d'an sakani..

Khadija ce gani ta samu mafita yanzu yasa tayi waje a guje cikin rud'ewa, da ihu game da fad'i shikenan shi ma sun kashe shi, shikenan mu kuma a haka zaa k'arar damu..." Tayi maganar cikin zautuwa a haka ta isa ga jama'ar dake cike da gidan tana surutai aiko dan da nan jama'a suka rufar mata, masu tambaya nayi masu kuka har sun fara...

Jawahir dake tsaye kallon su kawai take har sai da taga su baffa sun shiga d'aki kana tabi bayan su, jikin ta dai gashi nan ne, IMRAN yama kasa ko da motsi har sai da Abokin sa ya kama shi suka shiga d'aki duk da jama'ar dake wajen haka suka k'utsa kai ciki...



Tsayawa fad'a muku irin tashin hankalin da akayi a wannan ranar b'ata baki ne dan iya mashifa da bala'i su shige ta daga IMRAN har JAWAHIR kusan haukacewa su kayi sai a d'aki aka rufe su ko wa yayi mamaki da alajabi abun kamar almara nan baffa Abdullahi yaki bari kowa ya tab'a gawar har sai da yan sanda da likitoci suka zo suka d'auke ta game da wucewa da ita domin ayi bincike dan wannan karan shi da kan sa yaki yarda da cewa wannan gawar dan uwan sa ce, baffa Adam yayi?? ?yayi da Abdullahi akan a binne gawar amma yaki ko da kula shi bare ya sa rai...


Nan yan sanda suka shiga bincike babu kama hannun yaro Allah da ikon sa kuma suka gano abubuwa da dama, haka suka aka binne gawa amma kowa ya san ba baffa Nafi'u bane ya mutu, Jawahir Imran sune kawai basu da masani sabida gudun tashin hankali su...


Bayan kwanna bakwai, har yanzu basu ciki nutsuwar su gashi kuma Baffa Abdullahi yace dole ne ya fad'a musu dalili taron da kuma abinda ke tsakani su ko hakan za sa damuwar dake cin su ta ragu, bayan dogon jan k'unne da yayi ma jama'ar gidan akan kar wace ta gaya musu Baffa bai mutu ba...


Duk wanda suke gidan sun wuce gidan su, inda yan sanda bincike su har cikin gida da d'aku nan matan gidan...


A yau ne kuma bayan an fito daga masallaci baffa Abdullahi ya bu'kaci gani kowa dake cikin gidan, da kyar da sud'in goshi su Adda suka shawo kan jawahir ta fito dan har yau taki sakewa da kowa duk zuwan da Imran zayi da kuma rarashin ta da zayi duk a banza bata kula shi bare ma yasa ran zata saurare shi, wannan abun da take shine ya sa shi muguwar rama shima kullum cikin tunanin da hange me zai mata wanda zai sa ta dawo yanda take, duk da shi ma kwana yake kuka da tunanin mafita, to sai gashi baffa yayi mai kiran gagawa haka ya taso jiki babu kwari ya taho wajen sa...


A falo suka had'u gaba d'aya ko wane yana zaune bayan kowa ya mik'a gaisuwar sa wajen manya, baffa abdul ya bude taro da addu'a daga bisa ni ya koma kan su Jawahir da nasiha me ratsa jiki da jini, a take suka ci gaba da kuka na ban tausayi a wajen babu wanda baiyi kuka ba..

Yace" ya isa haka yanzu dai abinda mahafin ku yake buk'ata a wajen ku shine addu'a domin ita kad'ai ce mafita a gare shi ina fatan zaku kasance masu biyayya ga umarni na? " bai jira amsar su ba ya daura da cewa" sannan abu na gaba dama na kira ku ne domin na fad'a muku musababin taron da akayi ya zama na makoki, IMRAN JAWAHIR ku bani hankalin ku nan, a yanzu dai tsakani ku din nan babu wata maraba ko nesan ta bare cancanta, duk kan ku kuna cikin matsayi d'aya wanda bana son fad'ar sa amma ya zama dole.

Domin ku din *marayu ne duk kan ku baku da iyaye* sai mu ne yanzu kawai muka rage muku a yau kuma nake sake d'aukar ma kai na al'kawari mudin ina numfashi a doran kasa bazan tab'a bari kuyi kukan maraici ba insha Allahu, abu nan gaba kuma shi ne a yau zan fad'a muku abinda na san dole za kuyi farin ciki dashi, haka za kuyi alfahiri da mahaifan ku na har abada. sai kuma yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya game da share kwalla ya daura da cewa" na so dan uwa na yana kusa na si yana zaune agaban idon sa na cika mai burin sa na fad'a muku cewa *ku din ma'aura ta ne* tun filazala, tabbas da zayi mutu'kar farin ciki domin wanna shi ne burin sa, Adam miko mini suga zahiri.." yayi maganar yana kallon Adam dake share tashi kwalla.

Cike rawar jiki ya tashi zuwa ciki, har ya kai zai shiga cikin d'akin sa sai kuma na ga ya tsaya ya kura ma waje d'aya idanu na wani lokaci can kuma ya kutsa zuwa ciki duk ko da yanayi yanda yake jin jikin sa...

_Allah yasa kai ma ba kashe ka za suyi ba_


*my fan's na gode 'kware da gaske da addo'in ku Allah ya saka da alhairi naji sauki sosai domin gashi yanzu har na fara typing, Ahmdulillahi Allah ya bawa d'aukaci musulmai marasa lafiya lafiya yasa kaffa ne, ina taya ku murnar shigar sabuwar shekara musulci Allah ya maimaita mana Ameen gobe insha Allah ina asibit kar kuji shiru..*

```amma fa ban sauya ba sai na ga commten sannan zan yarda kunyi missing din na da gaske.```


Commten
And


Shared

Please

Mrs Abubakar ce?xR?
[9/4, 8:08 AM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*?x  ?xR?BA SO BANE ?xR??x  *
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYI DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*


2???0????~ 2???1???


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Cikin sauri ya shiga d'aki duba d'aya yayi ma wayar sa ya d'auka bai tsaya wani jan lokaci ba yayi waje zuciyar sa fas...

Ko da ya dawo falo jikin TV yaje a nan yayi yan jone-jonen sa, kana ya 'kunne ta duk abinda ya faru a ranar jumma'a da yanda d'aurin auren ya kasance babu abinda basu gani ba hata dawo war su gida da zaman da suka ringayi babu wanda bai baiyana ba, har yanda Baffa Nafi'u ya bada amanar yaran sa duk sun gani...

Tashin hankali da ba'a saka mai rana a falo babu wanda yake cikin nutsuwar sa duk kan su, rud'ani suka shiga yam mata falon kuwa kuka suke sosai kamar ran su zai fita ko wace da tunanin dake ran ta.

Adda Samira wani irin gume ne yake karyo mata ta ko ina sai zare ido take..

Adda mairo tayi wani murmushi me ciwo take wasu hawayen bakin ciki suka biyo 'kuncin ta, amma babu damar nunawa haka ta danne abinda take ji..

Jawahir tashin hankali da ta tashiga yafi na kowa dan gaba d'aya ta rud'e sai zare ido take tana maimaita kalmar aure ni kuma..

IMRAN yayi kasa da kan shi yana tuno maganganu da su kayi da baffan sa, sai yanzu ya fahimci inda zance sa ya dosa tausayin baffa ya kama shi, wasu hawayen bakin ciki ya kama shi babbar damuwa sa bai wuce me yasa bai gaya mai da bakin sa ba, dole zai cika mai burin sa ko da ko shi zai zamo sanadin rushewar na shi farin ciki, sai maganar da su kayi a daren ranan da abun zai faru, *ku din kuna da alak'a me karfi a tsakani ku gobe insha Allah za kuji komai fatana ku kasance masu biyayya a gareni da ma magabatan ku.* shine maganar karshe da zai iya tunowa ya rantsi ido da karfi, cikin kasalaliyar murya yace" tabbas abba na ya gaya mini ya fad'a mini amma ban fahimta sai yanzu na gane innalillahi wa'innailaihi raju'un Allah ya jikan ka Abba Allah ya kai haske ka barin ka.." ya fad'a cikin matsananci kuka, baffa Abdullahi ya taso cikin tausayawa ya kama IMRAN zuwa jikin sa yana shafa mai kai alamar rarashi ga wani tausayin su da yake ji..

Allah sarki Jawahir ta kasa yarda babu wanda ya kula da ita cikin rud'e taje gaban TV ta sake dawo da komai baya kana tayi zaman dirshen a k'asa tana zare ido hankalin ta tunanin ta gaba d'aya ta mayar dashi a tv kuma har yanzu bata dai na kuka ba hawaye kam ba'a maganar sa idanu ta yayi jawur dashi, yana zuwa k'arshe ta mik'a zata sake maidowa baya aiko baffa Adam ya damk'e ta nan ta fara zullu da ihu tana fad'in" kayi ma Allah da manzon sa ka bari ni na sake gani zuciyata ta kasa yarda na gaza aminta da abinda idanuna suka gane mini, me yasa za kuyi mini haka iyayye na ? me nayi muku da zaku zar tar mini irin wanna hukucin, wallahi bana son shi, ni ba son aure nake mai ba a yaya na d'auke shi, in na aure shi wa zan ringa kai wa kuka na? wa zai shige mini gaba a duk kan lamari na? *ni gaskiya ya sake ni kawai*..." Tass tass tass wani ingantace mari ya dawo da ita cikin nutsuwar ta jin ta da ganin ta ya d'auke lokaci daya.

Cikin bacin rai ya suma magana dama "bamu isa da ke ba ba zamu iya zaba miki abokin rayuwa ba ki amshe shi hannu bibiyu? wato zaki nuna mana mu ba iyayyan ki bane? kin san zafin da nake ji akan yan uwana kar ki manta yau kwana sshi bakwai da barin duniya shine zaki saka mu gaba da ihu kamar wasu k'annan yara ? toh su kansu mahaifan nake sunfi kuwa farin ciki da auran ku kuma sune nan suka had'a ki aure da shi mu abin da ya rage maka 'karasa ba san zuciyar mu maka yi ba,


Cikin sanyin jiki ta zubi a gurin tare da taren nadamar abinda ta aikata tace" Baffa kayi wa Ubangijin rahama kayi ha'kuri wallahi banyi dan ranka ya bace ba kuma zan nuna mu ku ni yar' kuce na karbi zabin ku zanyi biyyaya iyakar iyawata amma Baffa dan Girman Allah kayi hakuri kar kayi fashi da ni.." ta k'arasa fada ciki da shashi shiyar murya me raurawa..

Take tausayin ta ya kama baffa adam sai ya kalli hannun da ya dake dashi wata nadama ta kama shi, ya runtsi ido can yayi ta maza ya sunkuyi ya d'ago ta daga durk'ushin ya rungume ta yana shafa bayan ta a hankali yace" kukan ya isa haka 'yata Allah yayi miki albarka Allah ya jikan iyayen ku.." ya fad'a cikin sanyi jiki.


Adda Samirra cikin tashin hankali ta mi'ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login