Showing 18001 words to 21000 words out of 48171 words

Chapter 7 - BASO BANE CUTA CE BOOK COMPLETE BY Usaina B Abubakar.doc

*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYU DACE BA*
*BA SO BANE*...

*RUKKY MAMA INA TAYA KI MURNAR KAMALA NOVEL DIN KI, NA MUMINA SADDIQA ALLAH YA BIYA KI DA MAFIFICIN ALHAIRI, KURAKURAN DAKE CIKI ALLAH YA YAFE MANA BAKI D'AYA, MUNA GODEYA KWARE DA GASKE..*


_CONGRTULATION MAMA QUEEN ALLAH DA YA BAKI IKON KAMALA NOVEL DIN KI, ALLAH YASA KI FARA SABO A SA'A, INA MUKU MURNA KWARE DA GASKE._


*Book 2*


5????~ 8???


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Tana zuwa wajen bata damu da mutane dake wajen ba, tayi hugging din IMRAN ciki kirsa da kisisi na, tace"My Brother kana nan kenan? tun d'azu nake ta fama neman ka." tayi maganar muryar ta na raurawa, tamkar zata fashe da kuka..


IMRAN dai har ga Allah bai san nufin ta ba, amma ko kad'ai baya son wannan aladar ta ta, amma sai ya basar gani mutane dake tare dashi yau bai ture ta ba, sai ma hannu da yasa ya d'ago ta daga jikin sa yana mata murmushi yace" sister kema kin koyi k'iriniya irin na k'annen ki ko? na sha gaya miki ki rage wannan aladar ba irin tamu bace mu hausa fulani amma bakya ji." yayi maganar yana ja mata k'unne..

Yar kara ta saki tana tura baki gaba tace"na kula a gidan nan ni kad'ai kake ma haka." ta fad'a har cikin ran ta..

Murmushi kawai yayi baiyi magana ba...

can tace"miji na na gobe ni zan wuce kayi mini addu'a." tana fad'ar haka ta wuce abun ta tana aikawa da Nabila harara ta wutsiyar ido..


wani irin bakin ciki ya mamaye zuciyar Nabila, take taji wani mugun kishi ya taso mata, "dama Imran yaudarar ta yake yana da wace zai aura tun can, dan ko tantama ba tayi wannan daga gani akwai wata ala'ka me 'karfi tsakanun su, duba da irin kallo da jameela take mata, aiko wallahi bazai yuyuwa.." ta fad'a a zuciyar ta ga wani zafi da take ji tunda take dashi ko hannun su bai tab'a had'uwa ba amma yau a gaba ta wata ta rungume shi, har da wani yi mata wasa aiko dole ta tashi tsaye...
bata bari Imran ya sake magana ba ta wuce d'aga waje cikin sauri wasu hawaye na zubo mata...


Imran da ido ya rakata yana gani ikon Allah, tunanin sa d'aya ita kuma wannan me akayi mata haka da tayi zuciya? gani bai da amsar tambayar sai ya d'aga kafad'a cikin halin ko in kula tunda ya san shi bai da wani laifi...


Abdul dake zaune mamaki ya hana shi magana, sai yanzu ya samu damar bude bakin sa, yace"Aboki tarkon ka fa ya kama kurciya dan ko ban fad'a maka ba kai ma zaka fahimta kishin ka akayi, yana da kyau kafin tayi nisa ka bita ka shawo kan ta.." yayi maganar cike da tsokana dan ya san ko zai kwana yana rok'on sa ba zuwa zaiyi ba...

Imran ya maka mai harara yace"ka ga nayi ma kalar bin mace da tayi fushi, kishi kuma ai ita ta ga zata iya, tunda duk unguwar nan babu wanda bai san jameela ba da kuma al'kar mu da ita, kishin banza ma take har me akayi mata?" yayi maganar cike da jin haushin ta dan dama shi a takure yake da ita dan dai kawai baya son b'acin rain jawahir ne...


Abdul yayi dariya yace"Aboki baza ka gane ba, Nabila bata san kan gidan ku ba ko kad'ai, dan ko jawahir bata san ya kuke da ita ba, bare kuma jameela amma ni zanje na same ta na wayar mata da kai..."

"Allah kar ka soma dama ni wallahi na gaji da wannan suntirin da take mana a gida, kuma ina gudun wata rana Baffa ya ganta ta jik'a muni aiki, bata kawai ta kara gaba Allah ya bata wani dai ni dama tausayin ta nake ji wallahi da kuma son gani farin ciki my k'albi, amma ba dan haka ba banga dalili da zai sa na bata ma kai na lokaci ba." yayi maganar yana son barin wajen..

"Lallai Imran yanzu dama duk wannan soyayyar da kuke zubawa ba son ta kake ba? kayi ne kawai sabida wata k'albi din ka. to ko dai ita din kake so??" yayi maganar idon sa akan Imran..

bai fasa tafiya ba yace"kai dai ka jiyo ni ra'ayi na fad'a kuma bana so a tursasani.." Yana zuwa nan ya wuce abin sa..

Khadija dake zaune tsalam ta mik'a ta bar wajen...

Ranar Nabila ta sha kuka, musamma in ta tuno da irin kallon da jameela tayi mata, abin bakin ciki ko ya biyo bayan ta tunda ai ya san dashi take wannan fushi...


Jawahir ta dube khadija tana murmushi tace"da gaske anty? ni dama Allah yarinyar ta jima da fitar mini a rai shi yasa zaki ga yanzu ban cika zama ba in dai tana wajen da ta cika za'kawa da yawa, ai gara da big sister tayi mata haka gobe ma ta sake biyo mana shi gida.." ta fad'a tana wani munafikin murmushi..


Khadija tace"Anyya k'anwa ta ba so Brother din nan kike ba, na jima da fara hango kishin sa a face din ki, amma ki kayi mini gardama?"

Murmushi tayi mata tace"ke kika ga haka, amma da gaske ina son My dinna sosai, haka kuma ina kishin sa sosai musamma in ganshi da wannan duluwar yarinyar me jar face, amma duk wannan abun da na fad'a miki ba wai kishin aure ba nake ji aa haka kawai nake ji kuma bana son shi a matsayi miji, in kin yarda fa kenan." ta fad'a tana mik'awa tsaye.

Khadija tayi dariya tace"yarinya kenan bari na zuba ido na gani to in da gaske kike.."

Jawahir bata sake magana ba ta fice a d'akin..


wasa-wasa kusan satin biyu Nabila na zuba ido taga Imran yazo amma shiru babu shi babu dalilin sa, ga Abdul yanzu bata cika had'u dashi ba, haka ma jawahir abu kamar had'i baki duk yanzu bata gani su, abun ya fara damun ta...


Bayan sun gaisa, sai kuma shiru ya biyo baya gani bata da niyyar magana Abdul yace"Nabila ni zan shiga daga ciki kin san halin rayuwar yanzu ba kamar da bane, in wani ya fahimce mu wani bazai fahimta ba, ga dare daya sako kai.." yayi maganar a d'arare.

Nabila tayi murmushi tace"kay hakuri na kasa jurewa, dama na zo ne kan abinda ya faru kwanaki baya ai na san baka manta ba, wai abokin ka wanan irin mutane? sannan ina so na san wai wannan yam matam da nake yawan gani su tare dashi wai ya suke ne? Haka wace ta fito din nan har tayi hugging nashi, har da cewa mijin ta na gobe wai me take nufi ne?"
ta fad'a idon ta na kan Abdul..

Ajiyar zuciya ya sauke kana yace"abu mafi sauki da za muyi yanzu shi ne kiyi hakuri mu barwa safiya in Allah ya ka mana rai da lafiya, zan zo har gida nayi miki bayani yanda zaki gane, kamar ke da kuma irin kallo da mutane suke miki bai kamata ki fito daga gidan ku ba a irin wannan lokacin ba, mu barwa safiya kinji." ai yana kawo wa nan bai jira amsar ta ba ya wuce cikin gidan su da sauri...

Nabila ba wai rain ta yaso ba ta wuce gida....


"My wai ina 'yar farar yarinyar nan ne?" Jawahir tayi tambayar lokacin da take d'aura kan ta bisa cinyyar sa.

hannu yasa bakin ta yana d'an bige mata baki a hankali kana yace"lallai ma matar da zan aura kike cewa yarinyar to daga yanzu anty za kina cewa." ya fad'a cike da tsokanar ta.

ta kame bakin ta cikin takaci, tace"to Allah yanzu bana son ta dama ai ni nace ka so ta, to yanzu na fasa ka rabu da ita, tunda akan ta har da marar mini baki kayi." tayi maganar cikin shagwab'a da siraran hawaye..


Murmushi yayi kana yace"naki din ni kuma naga matar aure ai."

ta sake narke mai da shagwaba, haka suka yi ta fama daga wanna sai can daga 'karshe dai har sai da ya amsa....


Washe gari har gida Abdul yaje yayi ma Nabila bayani duk bata ji dadin yanda abun yazo ba amma da tuna wace yake ji da ita, tana son ta sai taji sauki, amma fa ta dauki d'amar duk wanda yace zaija da ita a fagen soyayyar sa, sai ya k'washi kashin sa a hannu...


Murmushi naga Jameela nayi....


Khadija tayi d'aki da sauri haka kuma face din ta na dauke da damuwa me tsanani...



?x? *wannan wanne irin birkitacen gida ne wai??.*


Haka suka ci gaba da rayuwa kullum da kalar matsalar da zata fito daga cikin wannan gidan, kuma babu wanda yake fara ankara da ita sai Imran, Nabila da kan ta ta dawo wajen Imran duk da yanzu bama ta samu face kamar dah, amma na damun ta sosai gashi ko tazo waje k'albin nashi bata samun wata ishashewar kulawa, bincike ta shiga kusfa kusfa..

Tafe take akan hanyar ta koma wa gida ta dawo daga islamiya. jameela ce a cikin motar ta ta fanno ta da mugun gudu kamar ba cikin unguwa ta shigo ba, Nabila bata san wake cikin motar ba amma tabbas ta san motar ta kusa daf da ita. tunda daga nesa Jameela ta sheda dai kayan ranar nan ne ajikin ta wani dadi ya mamaye mata zuciya.........




*ina barar addu'ar ku my hasseena tana kan hanyar ta na koma wa gida Allah ya kai su lafiya ya tsare hanya.*


Comment
And
Shared
Please

Mrs Abubakar ce
[8/18, 1:55 PM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*?x  ?xR?BA SO BANE ?xR??x  *
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAU??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????TAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYU DACE BA*
*BA SO BANE*...


*HAUWA A JIDDAH, INA MUTUK'AR TAYA KI MURNAR KAMALA NOVRL DIN KI ME SUNNA RASHIN SANI, AHMDULILLAHI MUYI MUTUK'AR FARIN CIKI SOSAI DA SOSAI DA JIN KARSHEN WANNA CAK'WAKIYAR ALLAH YA BIYAKI DA MAFIFICI ALHAIRI KUSKUREN DAKE CIKI ALLAH YA YAFE MANA BAKI D'AYA, MUNA JIRAN KI A NEW NOVEL DIN KI ME SUNNA RABO AJALI, ALLAH YA SADAMU DA ALHAIRIN DAKE CIKIN SA, MUNA TARE DAKE AKO DA YAUSHE.*


*Book 2*



9????~ 1???0???


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Saura k'iriss ta mak'eta Allah ya taimaka Nabila tayi tsalle ta dire gefe guda, babu abinda take sai huci da sauke ajiyar zuciya akai-akai...

Jameela wani bakin ciki ya mamaye mata zuciya, ta ciza lips din ta ido ta yayi jawur ko me ta tuno kuma oho kawai sai ta saki murmushi kana ta taka car din ta tsaya cak..


fitowa tayi cike da alamar firgici ta nufi Nabila hankali a tashe tace"ya rabbi baiwar Allah ba dai abinda ya same ki ko?" ta fad'a tana ware idon ta akan Nabila bayan ta san ko wacece..

Nabila ta d'ago suna had'a ido a tare suka wani ce "ke dama ke ce?" suka fad'a suna nuna junan su..

Nabila ta b'ata face cikin jin haushi tace"ai dama ke din nan daga ganin ki ba sai an fad'a ba zaki aikata fin haka, yan, u da kin bigeni me zaki ce ?"

Jameela tayi wau rau-rau da ido tace" a'a Allah ma ya tsare ni sam ba da niyya nayi ba, kuma tunda ban bige ki ba ai na goda Allah kiyi hakuri kiji matar brother.. " ta fad'a amma har ciki ran ta zafin Nabila take ji...


Nabila ta wani ya mutsa fuska tace"ok ya wuce amma ki kula nan gaba gaskiya, yanzu ma dan kina da dangantaka da abinda nafi so ne, amma wallahi da wani ne sai ya gane kuren sa.." ta fad'a amma har ciki ran ta, taji dadi yanda aka ce mata matar brother...


Lips din ta ciza kana tace"dama ina neman ki tun ran da abun nan ya faru, in babu damu mu d'an shiga ciki car din na ak'awai abinda zan nuna miki.." ta fad'a tana tsare ta da idanu...

"Ok."


kamar abin arziki haka suka shiga motar, da farko Nabila ta tsorata amma da tuna yanda suke da Imran sai take gani Jameela baza ta cutar da ita ba...

Jameela ta jima sosai bata ce mata k'ala ba sai can ta d'auko wayar ta yan shige-shige tayi a cikin ta kana ta mik'a mata wayar tace"kalli ki gani banyi dan na had'a ki da ita nayi ne kawai dan kin kwata mini a rai kuma ina tunani zaki kula mana da d'an uwan mu da kyau.."

Hannun Nabila har rawa yake wajen amsar wayar jin abinda suke cewa yasa idanun ta ya ciciko da kwallar bakin ciki

"Yanzu dama yarinyar nan duk abinda take mini *Ba so bane* ita ce fa reshan da na kama wajen kafowar soyayya ta amma shine har take iya cewa wai sai ya rabu dani, ashe *ba so bane cuta ce* me nayi mata da zafi haka?" ta fad'a cikin kuka wiwi...

Jameela ta saki wani mugun murmushi gani ta samu abinda take so, take face din ta sauya zuwa tsantsar damuwa tace"sai fa kin tashi tsaye dan yawanci duk budurwar da zata so Brother to Jawahir ke shiga tsakanin su, kema yarda dake ne da nayi yasa na nuna miki wannan abun amma ba dan haka ba ma ba zaki sani ba, ki gode wa Allah ma da har ya fad'a da bakin sa yana sonki haka kuma ya ga matar aure, abu d'aya za kiyi shi ne ki shiga tsakanin sa da jawahir wannan shi ne kawai mafita..."

Nabila bata sake magana ba ta fice a motar zuciyar ta na zafi..

Jameela ta saki wata munafikar dariya tace"lallai yarinyar baki san wacece ni ba, kin koma huta she dani wajen share ki a zuciyar abun kauna ta, da kan ki zaki dishashar da soyayyar ki kin d'ibo ruwan dafa kan ki dan tab'a jawahir tamk'ar b'arar da soyayyar ki ne baki d'aya muje zuwa yam mata.." ta fad'a cike da nishad'i kana tayi gaba abin ta zuciyar ta k'al...



Abinda ta nuna mata kuwa hirar da Jawahir tayi da Imran ne ranar da take cewa ya rabo da Nabila bata son ta, abinda basu sani ba shine gaba d'aya jameela tayi musu video record amma bata bari sun k'arasa ba tayi gaba abin ta...



Shiru tayi gani kukan bai da wani alfanu tunanin mafita ta shiga bata wani jima a haka ba ta saki murmushin mugun ta a fiti tace"yara kenan gaba d'ayan ku baza ku sha a waje na ba, jin sunnan kawai kuke amma baku san ko ni din wacece ba a zahir Jawahir kin tafka babban kuskure dole ki amshe hukuci a waje na dan ba'a tab'ani a zauna lafiya, jameela kenan na jima da sani ko ke din wacece dan na fiki hatsabibanci haka kuma na shallake tunanin ki mu zuba mu gani ni da ku shegi ka fasa..." ta fad'a tana wani juya ido...



Bayan su 'kwanki duk da Imran ya sauya mata sosai hakan na damun ta amma bata bari ya gane ba, kullum burin ta shi ne ta had'u da jawahir amma kashe ko a harabar gidan bata gani ta haka ma jameela abu kamar had'i baki...



Yau duk yanda Imran yaso tazo suje yawo Jawahir tak'i bisa a cewar ta ita d'aya zata tafi koma da kan ta take son ta tuk'a car din, gani ta fara kuka babu yanda ya iya haka ya rabu da ita duk da lokaci yamma ce sosai dan 5:24 fitar ta babu jimawa naga jameela ta fice ita ma..


Haka kawai yaji bai baya jin dadin zuciyar sa haka hankali sa yaki kwanciya, sai tunani yake bark'atai marasa ma'ana gani zaman gida baya mai dadi sai ya shirya ya fice shima duk da bai san ina jawahir tayi ba...


Nabila tayo wani mugun murmushi gani wuce war su kuma ko wane inda ya nufa daban, waya ta ciro ta shiga latsi-latsi babu jima wa ta kara wayar a k'unne ta fara magana ban ji me tace ba haka kawai naga ta sauke wayar har yanzu face din ta da fara'a...

yayi nisa a tafiyar sa haka kawai yaji fad'uwar gaba wayar sa dake gefe ya duba hannu yasa ya d'auka number jawahir ya shiga kira amma shiru ba tayi picking waje ya samu ya tsada car din ya ci gaba da kira gani bata niyyar d'auka sai ya koma mota ya fara tafiya duk wani waje da ya san zata iya zuwa sai da yaje amma babu ita babu dalilin ta ran sa ya b'acci tuna yanda tayi mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login