Showing 33001 words to 36000 words out of 48171 words

Chapter 12 - BASO BANE CUTA CE BOOK COMPLETE BY Usaina B Abubakar.doc

ta fito dashi ba imran kad'ai ba hata iyayen sa maza abun na damun su domin sun gani da idon su ba labari aka basu ba.

Kamar yau kowa na gidan na falo a zaune amma banda Jawahir tana d'aki tana sana'ar ta wato kuka da kallon pic din iyayen ta, Baffa abdullahi ya kalli Imran yana murmushi yace" yaro na kirawo matar ka mana, ka zauna babu abokin hira.." ya fad'a yana me murmushi..

Kunya ta hana Imran tashi ba??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????llai amsawa kawai sai ya fara wasa da yatsun hannun shi yana murmusawa..

Adda ta d'ago kai tana aunawa miji na ta harara cikin wani yanayi tace" Allah sarki yarinya ta har yanzu ba wai ta gama warwarewa bane , Jameela maza jeki kuyi fira da Imran Jawahir bata jin dadi sosai bare kuma har ta iya wata hira me tsaho.." ta fad'a tana dariyar mugunta.

Abdullahi yayi mata wani kallo me wuyar fassarawa..

An'nurin face din Imran ya d'auke gaba d'aya jin an ambaci sunnan Jameela, amma sai ya d'ake bai nuna ba..

Jameela dadi kamar ya kashe ta jiki na rawa ta nufo wajen sa kallo d'aya za kayi mata ka gano abubuwa da dama a ta tare da ita, bai fi taku hudu ta isa inda yake ba, sallamar Jawahir ya tsada ta cak kamar an dasa ta a wajen ga wani irin bakin ciki da ya mamaye mata zuciya ta farat d'aya domin ta san 'karshen zance...

Jawahir gaida kowa na falon tayi sannan ta nemi kusa da Adda Mairo tana shirin zama Baffa adam yace" yauwa 'yata dama yanzu nan za'a aika a kiraki sai kuma gaki wanna abu yayi mana dadi, IMRAN tashi kuje gata nan tazo..". ya fad'a yana sakin wani murmushi..



Jawahir baza ta iya musuwa ba amma har cikin ranta hakan bai mata dadi, cikin girmamawa tace" to baffa.." ta mi'ke jiki a sanyaye ta bi bayan sa, duk da shi ma bai san dalilin cewa suje da baffan ya fad'a ba..

Inda suka saba zama da nan ya nufa, ya jima a zaune har ya fitar da rai ganin ta, kawai sai ya ji sallamar ta murya can 'kasa abun ma dariya ya bashi haka ya daure cike da k'asaita yace" barka da fito wa My k'albi ?"

Tunda yake kiran ta da wannan sunnan bata tab'a jin ta tsani sunna ba irin na yau, cikin jin haushi sa tace" ba sunnan da iyaye na suka rad'a mini ba kenan in zaka iya kirani da Jawahir din na kawai, kayi sauri aiki nake a ciki.."

Tabbas ko bata fito ta fad'a mai ba ya sani yanzu bata son wata ma'amala a tsakani su, amma sai ya daure cikin tsokana kamar yanda suka saba, ya sa hannu ya jawo ta jikin sa aiko ta fad'o jikin sa babu shiri caraf ya rungume ta a kirjin sa yana sauke wata ajiyar zuciya dan babu karya yayi missing din ta.

Jawahir ta zaro ido waje cike da jin haushi duk da ita ma taji wani ba'kwan lamari amma sai ta hana zuciyar ta baiyanawa, ta shiga ture shi tana dukan sa game da cewa" ni ka sake ni, bana son irin wannan wasan banzan.."

Hakan yayi dai-dai da zuwan Jameela wajen cak ta tsaya zuciyar ta na mata zafi a take idanun ta suka kad'a su kayi jawur dasu...


IMRAN ya juyo da ita saitin face din sa yana mata wani kallo ido cikin ido cikin wata murya me rauni da sanya kasala yace" K'albi na ni ko? dama akwai ranar da za tazo kina gudu na tamkar wanda ya aika ta miki wani babban laifi? to wai shin ni na sa aka aura mini ke ta karfi ko ko? menene laifi na dan na amsawa iyaye na abinda suka umarceni dashi? shin laifi ne dan nayi biyaya a gare su duk da basa raye? mudin kika bani amsoshin tambaya ta a yanzu ni kuma nayi miki alkawari baki takadar ki tunda na jima da sani menene burin ki, ko da ko hakan za sa su baffa suyi fushi dani, Ina sauraron ki Jawahir..." ya fad'a yana tura ta domin ya gaji da wannan halin da take nuna mai...


Jameela ta rab'e a gefe gudu addu'ar ta d'aya Allah yasa Jawahir ta gaya mai abinda zai sa ya sauwak'e mata baki d'aya.



_nima na gaji a yau za'ayin ta kawai my Fan's Dan Jawahir ta Kai mu bango.._

_masha Allah na dawo lafiya kalau insha Allah yanzu zaku na jina akai_akai amma fa sai na ga yanayi comment din ku_


Comment

And

Shared

Please

Mrs Abubakar ce?x ?
[9/13, 10:13 AM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*?x  ?xR?BA SO BANE ?xR??x  *
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYI DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*


2???6????~ 2???7???


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Cikin tsoro da d'imuwa take kallon shi dan ko a mafarki bata tab'a zaton IMRAN din ta zai iya ture ta haka ba, har da guzirin tambayoyi masu wuyar gaske..

Idon ta har ya ciko da k'walla cikin murya kuka tace" a'a My!! a cikin abinda ka lisafo mini gaba d'aya baka da laifi ko kad'ai hasali ma kamar yanda ban san auren nan ba haka kai ma baka san dashi ba, gaba d'aya mu muyi rayuwa ne a cikin rashin sani har sai da aka faiyace mana komai, zuciya ta kasa aminta da kai a matsyin miji dalili kuwa shine, a baya kai ne abokin shawara ta farin ciki na walwala ta annuri na hasken idaniya ta, haka in Ina cikin damuwa kai nake fad'awa damuwa ta in an bata mini rai kake sani farin ciki, to yanzu da ka zamo miji a gare ni Ina zan kama ? In ka bata mini rai wajen wa zani na fad'a mai damuwa har yayi mini maganin ta kamar yanda kake mini?
in min samu sab'ani wazai sasantamu? My gashi har yanzu bana maka kallon so ko k'aunar irin na miji da mata har yanzu a matsayi Yaya na nake kallon ka, kala k'aunar da nake maka tana nan amma fa ta yan uwan taka, ka fad'a mini ya zanyi..?" ta fad'a cikin kuka..

Imran ya zuba mata ido gani yanda take zaffga yarinta k'arara, cikin wani yanayi me wuyar fassarawa yace" kukan ya isa haka, ki sani duk abinda kika lissafo a yanzu ne ma na sake samun wata dama wace zan baki kulawar da baki tab'a samu ko tsammani ba, amma fa dole sai kin bada had'in kai, maganar wa zaki gaya ma damuwar ki ki cire ta a ranki domin babu wanda yafi cancanta da ya san damuwar ki sama da mijin ki, a zaman auren mu ma babu damuwa ko sab'ani ki kasance me mana fatan alhairi a ko yaushe kinji my K'albi, Jawahir Ina so ki amshi wannan auren hannu bibiyu kiwa iyayen mu biyayya ta yanda ko nan gaba za suyi alfahari dake, ki fad'a mini abinda kike so ni kuma nayi miki alkawarin cika shi mudin bai zarce k'ainda ba, sanna karkiyi magana akan auren mu, dan ni biyaya zanyi fad'a mini zaki amince dani a matsayi Miji...?"


Tana hawayen tausayin sa gani yanda zai ma iyayen ta biyaya duk da basa raye sai ita da suka sha wahalar ta tana neman bijire musu, wata k'aunar sa take ji na taso mata cike da so tace" insha Allah nima zanyi biyayya kamar yanda kayi My zanyi k'ok'ari na gani na koya wa kai na son ka da k'aunar ka..." ta fad'a murya ta na rawa...

IMRAN ya sakar mata murmushi me taushi sannan yace" abubuwa zasu fara sauya tun daga yau ina fatan a shirye kike ...?" ya fad'a yana mata alama da ido..

Jawahir ta sunna kai k'asa zuciyar ta wani irin, tunanin ta d'aya ta ya zata fara son shi? taya zata kalli shi a matsayi miji, Amma kamar yanda yace insha Allah zata bashi dama ta farko ko zayi nasara sauya mata tunani...


Jameela kuka take game da jiri gani abinda take tsamani bai faru ba, lallai ma Jawahir munafika ce yanzu duk irin yanda Addata ke bata kula da shawarwari akan auren nan ashe ba dauka take ba? dole ne ko nayi magani ta ta yanda ko mafarki baza sake gigin cutar damu ba.. da wannan tunani ta bar wajen jiri na d'ibarta..


" My zanje na kwanta dare nayi." ta fad'a kan a k'asa..

" Ok har kin gaji da hira dani? ba damuwa kije amma kafin nan ina so daga yau ki dawo kwanna a part din mu, domin zuciya ta bata aminta da kwanna ki a part din su Jameela ba, sannan bana so duk wani abu da zai faru tsakanina dake kije ki fad'awa kowa, ki barshi tsakani na dake Ina fatan ki fahimce ni..?"

"Eh insha Allah..". data nan su kayi sallama ta wuce ciki abinta, kamar yanda yace ma haka ne ko ya kasance domin tana zuwa ta shiga had'e kayan ta waje gudu, sai da ta gama d'aukar duk wani abu nata, tana shirin fita Adda ta shigo d'akin face din ta babu yabo babu fallasa, tayi mata wani kallo wanda ita kad'ai ta san ma'anar sa, kana ta saki wani malalacin murmushi..

Tace" Jawahir lafiya naga kina had'a kaya ina zaki kuma?" ta fad'a cike da alajab'i.

Cikin mutuntawa tace" Adda zan koma part din mu ne ko hakan zai rage mini kewar su mom da Abba.."

" Allah sarki komawar ki bazai rage miki komai ba face ya k'ara miki damuwa, Jawahir zaman ki a nan ya fiyye miki komai akan komar ki can, shin bakya tunani Imran ya takura miki a can tunda baya gani ido kowa a tare dake? bazan so ki sake shiga damuwa ba Jawahir domin ke din nan abar tausayin ce kina buk'atar uwa a tare dake, shi yasa nayi uwa na makarbiya a duk kanni lamarin ki bana so wani abun b'accci da zai shafeki ko ya rab'e ki, amma in zaman kad'aici kike so Jawahir bazan hannaki tafiya ba, kuka dole ki zab'i d'aya a matsayin ki na d'iya mace dole sai da babba a kusa dake duk da gaba d'ayan ku yara ne, zaki tafi amma dole sai dai na had'aki da yayar ki Jameela tana d'eb'e miki kewa kije zata biyo ki daga baya...". ta fad'a fuskar ta cike da zallar tausayin jawahir...

Jawahir har cikin ran ta taji kamar kar ta wuce amma tunawa da abinda ke gaban ta yasa dole sai ta kawar da wanna tunanin,. Tace" na gode Adda nima ba jimawa zanyi ba zan dawo Anty Jameela dama tayi zaman ta kawai bana buk'atar kowa..". ta fad'a har cikin ranta..

Adda ji tayi kamar ta watsa mata ruwan zafi amma sai ta d'anne tace" 'yata abinda babba ya hango yaro ko ya hau rimi bazai gano ba, kiyi mini biyayya kawai shine mafi alhairi.." ta fad'a cikin Yar tsawa-tsawa..


"K'arshen biyayya nayi ma iyayye na da suka bar duniya da maradin aurar dani a ga wanda yafi cancanta da rayuwa ta, Amma tun a Karin farko nayi watsi da duk burin su, bana ji akwai abinda za'a sake sakani nayi shi kai tsaye ba tare da tunanin ba, Adda ki bar ni nayi rayuwata ni d'aya zuwan Anty babu abinda zai hana ko k'ara wa face b'accci rai da nadama ni zan wuce duk da har yanzu ban gama sani komai ba.." tana zuwa nan a zance ta taja akwatin ta sai part din su...


Adda Samira tsoro da firgici ne ya taro yayi mata k'atutu, har ya sa ta k'asa magana balle motsi tana ji tana gani Jawahir ta bar part din ta, ba komai ya hanna ta ai watar da komai ba face tunani yanda Jawahir tasha kama su dumu-dumu suna had'a makirci amma sai ta nuna bata ji komai ba, anyya yarinyar nan ba munafirtar mu take ba?? tana ciki wannan halin ne Jameela ta shigo a hargitsi...



Comment

And

Shared

Please

Mrs Abubakar ce?xR?
[9/14, 3:12 PM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*?x  ?xR?BA SO BANE ?xR??x  *
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYI DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*

_Comment din ku nayi mini Dadi irin sosai din nan muje zuwa my Fan's_


2???8????~ 2???9???


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Cikin hargitsi da b'accci rai tana haki ga hawaye tace" Adda Jawahir munafika ce ta cuce mu, ta juya mana baya yanzu dama duk irin hud'ibar da kike mata ashe ba d'auka take ba, Adda ni ganau ce ba jiyau ba gani ido na ganta a jikin sa suna soyayya yarinyar nan to kunyar idanu na bata ji.." ta fad'a hawaye masu zafi suna zubo mata..

Adda tsoro ya sake kama ta ga wata zufa dake karyo mata ta ko ina a jikin ta, cikin rawar murya tace" ai komai ya kusa rushi mana Jameela domin yanzu nan Jawahir ta gaba gaya mini magana san ranta haka kuma ta kwashi kayan ta kaf ta koma part din su, amma in ta sam wata ai bata san wata, dani take zance sai ta gammace kid'a da karatu yanzu wasan namu za fara da kan ta zai ta nemin takadar saki.." ta fad'a cikin 'kunar Rai..

Jameela da kukan kishi kawai take...

_Ni ko nace shine zayi ajalin ki yarinya_


Jawahir ta koma kamar yanda yace mata, a tare su ka gyara wajen duk da bai wani yi datti ba, agogon bango ta ciro ta goge sannan ta sake hawa kan kujerar da nufin mayar wa, Imran nan d'aga gefe yana goge su TV basu da ta zara me yawa, tunda ta sa kafar farko ta kujerar ta fara rawa ko a jikin ta haka ta d'aura ta biyun, aiko ta zame tayo k'asa zata fad'i gama d'aya ta gama sada'karwa sai ta kai k'asa, ta saki wata yar k'ara game da rauntsi idon ta, cikin zafin nama Imran yayi wata sufa had'i da bud'e hannuwan sa a haka ya iso gare ta, saukowar ta k'asa yayi dai-dai da zuwan sa saitin wajen aiko ta fad'o a fafad'an taffukan hannayen sa carf ya rungume ta a kirjin sa had'i da sakin wata b'oyayyar ajiyar zuciya haka ita ma ta zagaye shi da hannuwan ta masu taushi da santsi, tamkar dama ta san inda zata fad'o haka ta lafe a kirjin sa, gashin kan ta ya rufe mata rabin face, IMRAN ya zuba mata lafiyaye idanun sa baya ko kifftawa..


Jawahir jin kamar ana kallon ta yasa ta bude idon ta a hankali ako carf idanun su ya sark'e da na juna, wani kallo suke ma junna su me tatare da zallar tausayin, soyayya, k'aunar, an'nashewa, Jin dadi, gaba d'aya abinda kallon ya k'unsa kenan, kusan a tare suka sakar ma junna su wani malalacin murmushi me d'auke da ma'anoni daban-daban na tsantsar k'auna da shak'uwa, Jawahir tayi k'asa da kan ta tana jin wata irin kunya, har yanzu fa tana a hannu sa bai sauke ta ba haka ita ma bata cire hannun ta dake kaffadar sa ba, IMRAN ya saki 'yar k'ara yana ya mutsa face. Jawahir ta d'ago da sauri tana kallon shi dan so gani abinda ya same shi, sunna had'a ido ya kashe mata ido d'aya kana yace" hannu na zai sage.." yayi maganar yana mata nuni da ido.

Jawahir ta zaro ido waje gani halin da suke ciki aiko tayi saurin tashi tsaye, tana ka re face din ta da hannun ta dan kunyar sa take ji..

Gani haka IMRAN ya sake saki k'ara a karo na biyo, Jawahir ta d'ago da sauri tana kallon shi sai ta ga ya kama kafar sa d'aya dake lank'washe yana yamutsa face alamar tana mai zafi, cikin sauri ta isa inda yake gaba d'aya ta rud'e sai wani shafa shi take yana juya shi game da cewa" sannu My!! Ina ne yake ciwo.." ta fad'a arud'e..

Shiko kallon ta kawai yake bai ce komai ba, a hankali ya matso kusa da ita ba tare da ta ankara ba, sai da yazo saitin face din ta sanna tajiyo saukar numfashin sa a wuyan ta aiko tayi suman tsogone ta k'asa ko da motsi sai raba ido take, cikin wata wahalaliyar murya Imran yace" K'albi na!! har yanzu baki fara k'ok'ari sauya mini matsayi ba...??". ya fad'a cikin wani sabon yanayi dashi kan shi bai san yanayi ba..

Jawahir jiki ya fara rawa ta k'asa cewa komai sai auki matsa hannu..


Wallahi na so nayi muku me yawa sai kuma gashi an kawo mana nepa bye..

Comment

And

Shared

Please

Mrs Abubakar ce
[9/14, 7:38 PM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login