Showing 3001 words to 6000 words out of 48171 words

Chapter 2 - BASO BANE CUTA CE BOOK COMPLETE BY Usaina B Abubakar.doc

ga saurin fahimtar mutane, duk da har yanzu babu a wace ta fito da maitar ta a fili, haka kawai yaji basu kwanta mai a rai ba.


Comment
And
Shared
Please


Mrs Abubakar ce?x ?
[7/29, 11:07 AM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*?x  ?xR?BA SO BANE ?xR??x  *
( *CUTA CE* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*








LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYU DACE BA*
*BA SO BANE*...

_momyn mufeedah na gode Allah ya saka da alhairi_



6????~ 7???

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Haka suka ci gaba da rayuwa, har Allah ya sauki Adda Zainab lafiya, murna a wajen IMRAN har ba a magana, ta samu mace kyakykyawa da ita tubarkala, Ranar sunna yarinyar ta ci sunna JAWAHIR, kishin saurin ta babu wanda yaji dadin wannan haihuwar da tayi, musamma ganin yanda IMRAN yake rawar jiki akan abinda ta haifa, sai gaba d'aya bakin ciki ya taro yayi musu yawa, gaba d'aya tunanin su ya tsaya akan yarinyar da uwar ta na gani sun bar duniya gaba d'aya, su ka shiga yi musu bita da k'ule kuma ko a fuska basu tab'a nuna wa ba, sai ma tsantsar kauna da suke nuna mata haka su mayar da bangaren su wajen zaman su, ba dan komai ba sai dan ganin suncin ma burin su akan ta.

Matar Abdullahi sunnan ta ADDA SAMIRA, tana da d'iya mace me sunna JAMELAT, sai matar ADAM, me sunna ADDA MAIRO tana da d'iya mace ita ma me sunna maman su BASHIR, wato KHADIJA, a tsakanin SAMIRA DA MAIRO babu wanda ya san abinda dan uwan sa yake 'kullawa, akan IMRAN, ko wace burin ta ya so yar ta, yara tun su k'anna, duk da shi ma lokaci ban mallaki hankalin kan sa ba, amma babu wace take gaban sa kamar JAWAHIR duk wata kula war duniya ya d'aura akan ta, ko abu zai siya to sai ya had'a da ita.

wannan dalilin yasa suka k'ara tsanar ta a zuciyar su domin ji suke tamkar su sha'keta a take ta mutu..

A hankali yarinya tana kara girma da wayo, ga shak'uwar dake kara shiga tsakanin su, tsakanin ta da yan uwan ta kuwa su ma ba'a bar su a baya ba, duk da sun girme ta sosai dan ko wace ta bata shekara biyar-biyar, tsakanin jameelat da khadiji babu wani tazara me yawa 'yan kwanaki ne kawai.


bangaren Adda Mairo da dan sausauci dan ita bata uzura kamar yanda Sameera ta dage ba, a cewar ta zata bari yara su girma a lokaci ita ma zata nuna ikon ta..



IMRAN ya mai da hankalin sa kan karatun sa sosai, ta wani bangare kuma yana kula da 'kanwar sa kamar ran sa, shi kan shi BAFFA na sa yana mamaki irin wannan kaunar dake tsakanin su, haka ma Zainab abin nayi mata dadi sosai, kuma ta sa a Ranta ko bayan ranta IMRAN zai kula mata da 'yar ta, haka rayuwar su ta ci gaba,

kullum da kalar sharin da Adda Samira ke bibiyar su, amma wani ikon Allah babu abinda yake samun su, dan duk lokacin da za tayi wani abin sai Allah ya taima ki IMRAN shi ke warware wa, duk da bai da wani ishashan hankali a lokacin, kamar yau;


gaba d'aya su mutanen gidan suna babban falo a zaune, duk da ba wata hira ake me tsayi ba, amma an zaune har mazan ko wane na wani abu daban, IMRAN ne ya na ta kallon kowa dake zaune a wajen sam ba kula da JAWAHIR bata wajen ba sai yanzu, ya mayar da kallon sa ga Adda Zainab yace"MAMA NA, wani ina k'albi na ne?" yayi maganar da murya sa me rik'i tar zuciya yam mata.

ita ma sai a lokacin ta kula bata wajen tace"ha'a!! ina kuma tayi? muna tare da ita a nan wajen fa." ta fad'a hankali tashe.

Adda Mairo tayi mata wani shi'umin kallo kana tace"ban da abun Zainab yarinyar da ta fara dabo, ai bai yuwa ta zauna waje d'aya in kin bibiya ta koma cikin gida." ta fad'a tana wata yar dariya.

Adda Samira tace"yaro da ba'a raba shi da k'iriniya, yanzu haka tana wani wajen tana ta'adi, karki wani d'aga hankalin ki, muna nan dake zaki ga ta dawo tunda tayi kafa."

haka kawai Zainab taji bata yarda da abinda suke cewa ba, gaba d'aya hankalin ta yayi ga y'ar ta, amma saboda kawaici da ake cewa irin nata sai tayi yak'e tace"kuma haka ne Allah yasa lafiya." ta fad'a tana ci gaba da jin fad'uwar gaba.

IMRAN ya kalle ta yace"Mama na ni bari na dubo ta dan ina ji a jiki na kamar bata cikin k'oshin lafiya." yana zuwa nan ya fice ya bar d'akin gaba d'aya.

Maza da suke gefe a zaune, ba su ce komai ba, amma gaba d'aya hankalin NAFI'U shi ma yana kan su jin IMRAN zai dubo ta ne sai yayi kamar bai jiba..

IMRAN na fita Adda ta bi bayan sa da harara a zuciyar ta tace"zama ka dawo sarkin iyayi." ta fad'a tana wani saki murmushi.

Shashin su yaje, yana ta kiran ta, da duduba wa ko zan hange ta, shi ne taik'a can d'aga can, duk inda yake saka ran gani bata wajen, gaba d'aya hankalin sa ya tashi, sai zufa yake yana haki, yazo komawa babban falon ne dan sheda musu, sai yaji karar fad'uwar abu kamar k'arfe ta bangaren Addan jameela, haka kawai yaji hankalin sa bai kwanta ba dan haka yace"waye a nan ?" ya fad'a dan k'arfi.
shiru babu amsa, har ya fara takawa zai shiga shashin yaji murya Adda ta bayan sa tace"IMRAN tana ina kuma naga zaka shiga nan?" ta fad'a tana kallon bayan sa.

Shi ma kallon ta yayi yace"bangan ta a can bane shi ne na fito na fad'a miki, ko kinga wani ya d'auke ta a cikin su khadija? "

Zainab tayi d'an shiru can tace"aa gaba d'ayan su suna zaune babu wanda yaje ko ina, amma tsaya na duba waje ko ta fita.""
tana fad'ar haka ta fice daga wajen da sauri.

shima falon ya koma bai shiga sashin ADDAN ba.

Gayen dake tsaye jikin labulayen d'akin rik'a da JAWAHIR jin sun matsa daga wajen, ya sauke wata wawuyar a jiyar zuciya, kana ya mai da duban sa ga yarinyar da ta jima da suma tun matsi mata baki da yayi, cikin sauri yayi hanyar kicin din gidan dan tana ne kawai zai samu hanyar wuce wa, ba tare da an kama shi ba.


hankali a tashe yace"Baffa na ba'aga JAWAHIR ba fa har yanzu." ya fad'a cikin sammatsi.

gaba d'aya mutane falon suka mi'ke tsaya ido waje cikin had'in baki suka ce"me!!?"

"ce Baffa's tun d'azu nake duba ta, kuma na duba ko ina bangan ta ba wallahi ina ga kamar hannu ne ya d'auke ta."

kafin kowa yayi magana ADDA Mairo tace"kaji yaro da wata magana duk tsagerancin mutun ai bazai shigo har cikin wannan tangamemen gidan ma cike da matak'an tsaro ya saka hannu ya d'auke yarinyar ba, ka dai ka sake duba wa da kyau me yuwa ta shiga wani wajen ta kasa fito wa." ta fad'a cikin manyen ce.

Adam yace"kware kuwa da ido na, naga wuce war ta, ta nan waje ka shiga sashin ADDA SAMIRA dan nan naga ta nufa." ta fad'a yana nuna mai da hannu.

Samira taji kamar ta k'utuntumawa Adam zagi, amma sai ta d'aure tace"ta iya yuwa yaro kuma, shi ga ka duba ko nace muje tare naga ko ta shige waje ne." ta fad'a tana yi gaba su Baffa na bitan a baya, har suka shigo falon ta, IMRAN bai jira cewar kowa ba ya fara k'walla mata kira da *k'albi na!!* kina ina!! ? *k'albi na!!*." yana maganar yana duba duk inda yaci karo dashi,

IMRAN babu ko kara har cikin d'akin barci su ya shige yana duba ta, had'i da 'kwalla mata kira, amma shiru kuke ji tamkar bata wajen, aiko hankalin sa ya tashi jijiyoyin kan sa suka furfuto, gaba d'aya ya hautsine a d'an k'an'kanin lokaci idanun sa su kayi jawar dasu, babu wanda bai tsorata da yanayi da ya shiga ba, sun duba ko ina bata wajen.

hankalin kowa ya sake tashi Baffa ya gigice ya manta da yar fari ce, bako kunyar yayin sa yace"na shiga uku yanzu ina kuma yarinyar ta sake shiga, haka ma fa kwanaki aka d'auke ta kuma har d'akin barcin ta, yanzu ba dare bane bare nace, ana nema ta an rasa YaYa Abdullahi ku taimaka mini kar na sake rasa ta a rako na biyo, su biyu gare ni a rayuwa ta." ya fad'a cikin gigita.

Abdullahi ya kama shi yana girgiza mai kai yace"ka nutsu Nafi'u ina ji a jiki na 'yata tana cikin gidan nan babu abinda zai faru kaji zamu gan ta." ya fad'a da sigar kwantar mai da hankali.

Adam dai babu bakin magana dan har ga Allah yana son Jawahir, jin ta yake kamar khadija.

gaba d'aya sun suka fito daga shashin, suka nufi na ADAM lokacin Zainab ta dawo nan ta tare da mumunan labari Allah yaso ta fad'a ma'aikatan gida kuma sun bazu a ko ina na gida har ta bayan gidan kuwa, duk nacin mutun da taurin ran sa bai isa ya wuce ba tare da angan shi ba.

ko da suka duba na ADAM nan ma bata ciki, dan har kicin suka shiga ba su ganta ba.

IMARN yayi shiru na d'an wani lokaci yace"ina zuwa." yana fad'ar haka ya wuce da sauri sai shashin su jameela, yana shiga bai zarce ko ina sai kicin dan nan ne basu shiga ba, cak ya tsaya ganin hular ta ya she a k'asa babu komai a kicin din sai hayak'i da turiri da ya rasa ko na menene. gaba d'aya ji yayi kafar sa ta kasa d'aukar gangar jikin sa, cikin tashin hankali da rud'e wa, ya zube a wajen yana fitar da wasu zafafan hawaye, zuwa can ya zafga wani mahaucin ihu!! game da k'walla mata kira cikin hargitsi da tsabar rud'u.

gaba d'aya mutane gida wajen sa su kayo hankali tashe.

jikin Baffa har ruwa yake sabida tsabar rud'ewa, Adam ne ya shige gaba ganin kowa ya gara duba wa, cak ya tsaya cikin tsantsar kid'ema da rawar jiki.......


*a nan zan daka ta sai naga comment din ku sannan zan ci gaba*

Comment
And
Share
Please

Mrs Abubakar ce
[7/29, 1:25 PM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*?x  ?xR?BA SO BANE ?xR??x  *
( _cutar ka za suyi_ )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*








LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYU DACE BA*
*BA SO BANE*...


_Rashin comment din ku ya fara yawa gaskiya_ ?x? ?x?
8????~ 9???

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

A sandare take, a kasa babu alamar rai a tare da ita, tayi wani duhu a cikin d'an k'ank'anin lokaci, Baffa Adam ya kasa k'arasawa gare ta, banda rawa babu abinda jikin sa yake, gani haka ya sa kawu Abdullahi 5a kawa a hankali kamar wanda k'wai ya fashe mai a ciki ya k'arasa gare ta, gani halin da take ciki, jiki na rawa ya d'auko ta bakin sa na ambata sunnan Allah, bai jira cewar kowa ba yayi waje da ita cikin sauri da mazarin jiki.

sai da ya kai waje sannan ya bud'e murya yana kiran IMRAN da k'arfi, kafin ya gama sauke numfashin sa, har ya iso waje duk da irin kukan da yake kuwa, ba su zarce ko ina ba sai asibiti gaba d'aya gidan sunyi carko-carko a bakin d'akin da aka shiga da ita, sun d'auki lokaci mai tsaho sannan Doctor ya fito yana share gumin da ya zubo mai, office ya wuce suka bi shi a baya, sai da yayi wasu yan rubuce-rubuce, kana ya d'ago rai a b'acce yace"maganar gaskiya ban ji dadi yanda akayi sakaci da yarinyar k'arama irin haka ba, yanzu ba dan Allah yayi tana da saurin numfashi a duniya ba, dashi kenan sai da ace tsautsayi ne, bayan babban ganganci aka mata...."

IMRAN yayi sauri k'atse shi ta hanyar cewa"daka ta dcotor ina so naji tana raye ko-ko, ban son d'ogon zance, yanzu in tana raye menene abinda ya same ta?" ya fad'a dan son sani abinda ya faru da ita.

Dcotor ya sau'ke a jiyar zuciya kana yace"binciken mu ya nuna mana, ta jima da suma ta sanadin taushe mata hanci da baki da akayi, dan ko ba'a fad'a kuna kallon fuskar ta za ku gane haka, duk da babu shatin hannu a jikin face din ta, da alama anyi amfanin da wani abu ne, sannan an sake yun'kurin cutar da ita ta hanyar sha'ke mata wuya wanda har sai da ta farfad'o ta sake d'ogon suma, wanna shine abin da muka gani kuma muka shida dan Allah a kiyayye domin tasha wuya da yawa." yana maganar ne lokacin da yake k'ok'arin fita a office d'in.

IMRAN ya saki wata muguwar kara yana cewa"Ya rabbi, wai me yarinyar nan ta tsare musu ne? ko da yaushe basu da burin da ya wuce su cutar mini da ita, da zan kama mutun ko waye da hannu zan harb'e shi, wallahi da bazan raga mai ba ko k'ank'ani ne." ya fad'a cikin muryar nan tasa me dad'in sauraro duk da yana cikin tashin hankali amma hakan bai hanata dadi ba..

Adda samira tayi mai wani kallo sannan ta kawar da kan ta gefe, ta sake d'ago tana kallon sa, ta kasa jurewa har da tayi magana tace"umm ni kam IMRAN abi ka yana d'aure mini kai mutuk'a, haka kuma bazan boye maka ina gani kamar da sa hannu ka a sace yarinyar nan da ake..." maganar ce ta mak'ali gani irin kallon da kowa yake mata...


Abdullahi yayi mata wani mugun kallo kana yace"ke!! har kina da baki magana akan haka? amma tukuna dai menene dalilin ki na fad'ar hakan?" ya fad'a rai a mutu'kar b'ace..

"kayi hakuri Baffa jameela kawai na kasa yarda ne da abin da zuciya ta take raya mini har sai da na maganun, a cikin gidan nan dai gamu nan da yawa mu, kuma ba ita d'aya yarinya ba, ga su jameela da khadija amma tunda nake da su ba a tab'a d'aukar ko d'aya daga cikin su sai ita, kuma duk lokacin da wani abu zai faru to shine yake zuwa dashi akan bai ganta ba, ko yace an sace ta, haka kuma shine yake nemo ta, abin duba wa nan mudin ba wai ya san inda take ba ya akayi yake d'auko ko? kuma ya akayi ya san an sace? gaskiya yana da kyau a bincike shi, dan ni sam nafara zarewa da alamarin sa, kullum shi ne yake fito mana da matsala kuma in an duba sai aga haka ne, tabbas akwai ayar tambaya a tare dashi." ta fad'a cike da ya'kini.

IMRAN kukan sa ya tsaya tunanin sa ya tsaya gaba d'aya ya rasa inda kalaman ta suka nufa, haka kowa na d'aki ya mayar da kallon sa gare shi, ana mai kallo zargi.

Abdullahi yayi wani murmushi irin nasu na manya yace"ai in da wanda ya cancanci a saka ma ido, bai wuce ke ba domin duk lokacin da wani abu zai faru to a part din ki ake samun ta, yarinyar nan tun kan tayi kafa ana same ta a part din ki ya kai sau biyar kuma duk cikin mumunan yanayi, kin ko kece alamarin ki akwai abin duba wa a cikin sa, dama shi gwano bai jin warin jikin sa, amma ba damuwa kin d'aura mu akan hanya zamu bincika kamar yanda kike ce tunda shawara ce kika bayar.?" ya fad'a yana mata murmushi..

ADDA SAMIRA bata yi tsamani akwai wanda zai zarge ta ko yayi tunanin ita ce ke kula komai ba,, bare kuma har a fad'a mata irin abinda mijin ta ya fad'a mata, a yanzu take taji cikin ta yayi wata irin hautsi nawa, cikin kid'ema tace"me kuma zai kawo wannan maganar tsakanin da Allah, banda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login