Showing 39001 words to 42000 words out of 48171 words

Chapter 14 - BASO BANE CUTA CE BOOK COMPLETE BY Usaina B Abubakar.doc

tashi shine kayi mini lik'imo in har barci gaske ne kake bai ci a ce har yanzu kana nan yanda kake ba to wallahi sai ka tashi..." ta fad'a tana haye wa kan shi, hannun ta duk biyu ta zuba acikin sa tana mai cak'ul'kuli had'i da sakin dariya...

IMRAN ya saki dariya shima ya shiga tare ta game da kama hannun ta duk biyun, shi ma ya shiga ramawa, dariya suke suna shewa alamar duniya tayi musu dadi.

Haka suka cigaba da yi, tunda suka fara har ya dawo suna yar d'anne d'anne, ta murgi shi ta haye kan shi, shi ma ya murgi na ta ya haye kan ta, cak'ul'kuli kuma ba su fasa yi ba, IMRAN ya rungume ta tsam a jikin sa a hankali cikin wata murya yace" INA SON KI JAWAHIR SO NA HAK'IK'A INA MUTU'KAR K'AUNAR KI MATA TA..."


JAWAHIR ta sak'e ta k'asa cewa komai, sai tayi luf a kirjin sa tana jin wani iri a zuciyar ta...

D'ago ta yayi yana had'e fuskar su waje d'aya, hancin su na gogar na juna yana kallon yanda ta runtsi idon ta cikin kasataliyar murya yace" K'albi na, ki kalle cikin idon na ki gaya mini abinda kike ji, please Jawahir ki gaya mini gaskiya ko zuciya ta zata samu nutsuwa, shin me kike ji a kan a yanzu...?"
yayi maganar yana sake d'ago kan ta wanda ta ke k'ok'ari kawar wa gefe...

Jawahir ta shigar mutsu-mutsu tana son k'wacewa, cikin murya me raurauwa tace" My!! yunwa nake ji..."

"Ok.." ya fad'a duk da ran shi bai mai dadi ba..

Sakin ta yayi ta tashi, inda ta jera abinci nan ta koma ta zauna tana jiran sa, shi kuma shiga yayi k'imtsa kana ya fito cikin shirin fita, ta gaba ta yazo zai wuce cikin wata murya tace" My!! ga abinci fa a nan.." ta fad'a tana mi'kewa tsaye..

" Eh na gani sauri nake zanje inda za'a gaya mini abinda nake bu'katar ji, kin san akwai Nabeela!!.". ya fad'a yana kashe mata ido d'aya...

Jawahir ta kar kata kan ta gefe, tana kallon shi sannan ta tab'arb'are fuska tana shirin fara kuka tace" amma fa domin ka nayi duk wanna hid'imar ka bari in ma zuwan ne kaci abinci tukuna..." tana maganar ne hawaye na zubo mata...


IMRAN ya kalle a gogon bango yana k'ank'ance ido yace" gaskiya zan makara kuma kin san Nabeela yanzu zata iyayin fushi, so kici kawai in dai nine na gode, in kuma kina so naci to sai kin gaya mini abinda na tambaye ki...""" ya fad'a yana kawu da kai gefe...

Jawahir tayi shiru kamar baza ta sake cewa komai ba zuwa can kuma tace" tom naji kaci abinci.."

"" Kinyi alk'awari...""" ya fad'a yana mik'a mata hannu..

Ita ma hannu ta mik'a mai suka sark'e yatsun hannu su waje d'aya kana suka saki ko wanne ya nemin wajen zama, cikin nutsuwa da kwanciya hankali suka fara cin abinci IMRAN yana ta kod'ata da zuzuta dadin abinci, Jawahir dadi kamar ya kashe ta sai murmushi take tana dariya, a haka har suka kamala...

" Tom ina jinki.." ya fad'a yana kama hannun ta had'i da matse su a cikin nashi hannu...

Jawahir t???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a mik'e cikin tsantsar shagwab'a ta Haye cinyar sa tana wani langwab'ar da kai tace" My ba ka yarda da k'aunar da nake maka bane? a tunanin ko ban fito fili na gaya maka ina k'aunar ka ba, baza kayi sha'ku ko tunanin ba sabida so ko ban fad'a kana ganin shi a aikace My!! ina mutuwar son ka da k'aunar ka domin kai ne jinin jiki na, bana ji zanji dadi rayuwata idan babu kai a cikin ta My!!! ILOVE YOU SO MUCH MY heart, ban san ya zanyi da soyayyar ka ba, dan Allah kar ka guje ni ko da nan gaba domin kai ne gata na abin alfahari abin tun'kaho na bani da wanda zan gani naji dadi fiyya da kai my heart..."
ta fad'a cikin matsananci kuka domin jin son shi take har cikin mak'wararar zuciyar ta da ran ta game da gangar jikin ta...


Comments

And

Shared


Mrs Abubakar ce
[9/18, 11:29 AM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*?x  ?xR?BA SO BANE ?xR??x  *
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYI DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*



3???6????~ 3???7???


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Tsananin tausayin ta yasa IMRAN fitar da wasu siraran hawaye, shi me cike da zallahr k'aunar ta ya shiga goge mata hawaye yace" idai duk duniya zasu taru a kai na, bazan iya rabuwa dake ba Jawahir domin ke ce jina da gani na, haka kuma ke amana me gare ni tsakani baffa da mama babu wanda bai bani amanar ki ba, haka kuma nayi musu alk'awari kula dake har k'arshen numfashi na, Jawahir ina so ki d'auke ni kamar yanda na d'auke, kiyi min alkawari duk wuya duk runtsi bazaki tab'a rabuwa dani ba, haka kuma bazaki tab'a cutar dani ba, haka kuma duk wata matsala in ta taso zaki zo gare ni mu magance ta duk wuyan ta da tsaurin ta, Jawahir ki rik'e mini alk'awari na kamar yanda zan rik'e miki..." ya fad'a yana shafa fuskar ta..

Hannu ta saka ta had'e fusakar su waje gudu hancin su na gogar na juna, kamar yanda yake mata, ta lumshe idanun ta tana cusa hannu ta cikin sumar kan shi, a hankali tace" insha Allah duk abinda kake tunani bazai tab'a faruwa ba a rayuwar auramu ba, auren mu babu CUTA babu cutar wa zanyi iya baki k'ok'ari na, na gani na baka duk kani wata kulawa ta musamma fata na Allah ya k'ara mana lafiya da fahimtar juna..." sai kuma ta sake shagwab'a fuska tace" My!! bana so na sake jin ka ambata mini wani sunna me kama da Nabeela bare kuma ita kan ta, kar ka manta dama na baka ka ja ra'ayi na, kar ka bari wannan damar ta kub'uce maka..." ta fad'a tana jamai hanci alamar jan kunne..

IMRAN ya had'e jikin su waje gudu, yana mata wani salo wanda yasa ta kusa fad'uwa domin kafafun ta gaza d'aukar ta sukayi, fahimtar hakan da yayi yasa shi had'e bakin su waje d'aya yana aika mata da wasu mahimma sak'oni cikin kwarewa da iyawa, duk da shi ma dan koyone a fanni amma haka ya zage damtsi, JAWAHIR taji bak'on lamari domin tunda suke dashi hakan bai tab'a faruwa a tsakani su ba sai yau duk da ba wani abu bane, kissing ne kawai..
?x?0


A hankali ya sake ta yana sauke numfashi yace" sai na dawo ko..". ya fad'a yana 'kauda kai gefe domin shima din tunani yake me kuma ya kai shi nan, ya san za'a rina aiko tayi shiru kamar ruwa ya cinye ta, har ya ficce a d'akin bata ce k'ala ba..


Sun Adda suna zaune suna jiran fitowar su ko wace sai sintiri take a falon da kallon kofa, ga tsaki da suke ja akai-akai, suna cikin haka IMRAN ya fito fuskar sa d'auke da murmushi, ido suka zuba mai ko wace da abinda take sak'awa a ran ta, shi bai ma kula dasu ba har sai da ya kusa k'ulewa sannan Adda mairo tace" IMRAN manya sai yanzu aka fito...?" ta fad'a yanda zan jiyo ta, aiko tayi sa'a domin jin maganar yayi tamkar saukar aradu ya juyo a su'kwane, gani irin kallon da suke mai yasa shi fara sosa keya yana sunna kai gefe, bai dawo ba a nan inda yake tsaye ya sunkuwa yana gaida su. ciki-ciki suka amsa mai ko wace zuciyar ta kamar ta faso jirkin ta ta fito tsabar bakin ciki...

Har ya mik'e zai wuce Adda Samira ta sake jeho mai wata tambaa da cewa" lafiya ya baku fito dinner ba? sannan ihun me najiyo jiya da dare..?"" ta fad'a cikin murya tausayi kamar gaske gaba d'aya tayi wani iri...


IMRAN har ga Allah baiyi niyya dawowa ciki ba, amma gani yanda ta tashi hankalin ta dole ya dawo da baya, cikin biyayya ya zaunar da ita akan kujera yana me kama hannu ta yace" kwantar da hankalin ki Adda ba wani abun damuwa bane, kawai tsorata tayi, kuma alhamdulillahi an shawo kan matsalar yanzu ma na baro ta tana barci, maganar dinner kuma da kan ta tayi mana a ciki, please addas kar ku damu kan ku ta iya yuyuwa ma yanzu ku gan ta fito, ni zan wuce na gode da kulawar ku..." yana kawowa nan ya fice a d'akin ya tafi neman halali...


Babu wace zuciyar ta ba tayi mata nauyi ba a cikin su, ga wani kululun bacin ciki da ya gauraye musu jini da tsuka, sai nishi suke su kad'ai sabida tsananni b'accin Rai...


Jawahir gado ta fad'a tana sake ajiyar zuciya akai-akai ji take kamar har yanzu yi mata yake, hannu ta same ta tab'a bakin a hankali ji tayi yayi laushi tashi tayi ta nemi mirro ta haska gani tayi lips din ta yayi ja had'i da kumburi sabida tsabar tsotsa da ya sha, zare ido tayi cike da tsoro a fili tace" wayoo me yasa banji komai ba lokacin da yake shanye mini jini.." ta fad'a tana tura baki gaba kamar yana kallon ta...

Dariya nayi nace kaji shirme..

" Ai ko yau babu wanda zan ganni sai lips din na ya sab'e..". ta fad'a tana kwantawa akan bed din sa..


Zaune suke suna tataunawa, a tsakani su Ni da nake gefe banji me suke cewa ba amma da duk kan alamu hira ba tayi musu dadi ba, dan ran kowa ya b'accci Adam ya mik'e Rai a b'acce ya fice a office din Dan uwan nashi..

Abdullahi ya bishi da kallo cike da k'unar zuciya..


_me kuma yake faruwa shine abinda nace kawai.._


Adda mairo ta wuce d'akin ta domin rarashin 'yarta, ida Adda Samira ta k'asa ta tsare sai taga fitowar Jawahir...

Ko da rana tayi da kan tayi girki iya wanda zai ishe ta, taci ta koshi tana yi tana kallo mirro...


IMRAN ko da ya fita wajen Abokin say ya fara zuwa sun d'an tab'a hira har yana tambayar sa amarya ga mamaki sa sai ya ga yana dariya yana komai yace mai tana nan lafiya kalau, a hakan suka rabu bayan tafiya IMRAN babu jimawa sai ga Nabeela tazo ita zama tayi kusa da Abdullahi Nan suka fara hira ya sanar mata da iya abinda ya sani ita ma ta wuce abin ta..


Haka rayuwar su ta kasance tsakani makiya dama da hago amma har yanzu basu fahimta ba domin zallar k'auna ake nuna musu a zahiri amma a bad'ili tsanani k'in su ake, sun fifita su akan y'a'yan su domin gani idon au sautari za'ayi ma su Khadija abin b'accci rai su kuma a dad'a musu, wanna abu yana damun su ainu amma basu da damar magana..


Kamar yau gaba d'aya su suna zaune a falon JAWAHIR NA JIKIN IMRAN a kwance sai shagwab'a take zubawa shi ko sai biye mata yake , inda su Adda suna zaune sai dariya suke musu amma a bad'ili kukan zuci suke.

Jawahir ta dawo kusa da Adda ta zauna tana tura baki gaba tace" nayi fushi tunda abun haka ne..". ta fad'a har da Yar k'wallar ta..


Bakin ciki ne ya kama Jameela gani tsagwaran raini wayo batayi tunani komai ba ta mik'e a fusace tazo inda Jawahir take ta sa hannun ta duk biyu ta d'ago ta sannan ta hankad'a ta tana nuna ta da yatsa cikin fushi da fusata marar amfani tace" 'yar iskar yarinya kawai marar kunya da cikakiyar nutsuwa, na sake gani k'afar ki a jikin uwa ta sai na koya miki hankali doluwa kawai.." ta fad'a tana wurga mata harara...

Jawahir tayi sororo tana kallon ta tausayin kan ta ya kama ta hawaye ya shiga ambaliya a kuncin ta, ta kasa cewa komai sai kuka mai ban tausayi domin ita ta sa haka nee a ran ta kawai dan anga babu tata uwar ne a gidan.. tana cikin wanna kukan ne taji saukar mari me firgitar wa da hargitsi tunani...



Comments

And

Shared

Mrs Abubakarusaeenah@gmail.com
[9/21, 11:07 AM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*?x  ?xR?BA SO BANE ?xR??x  *
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN MARUBUCIYAR.!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYI DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*


3???8????~ 3???9???


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Adda ce rai a mutu'kar b'acce tace" ko da wasa kika sake gigin tab'a mini 'ya da zumbar wulak'aci ko tozarci, ki sa a ranki sai na nuna miki koranki wawuya kawai.." tana kawowa nan a zancen ta sai ta koma ga Jawahir dake tsaye tana ruwan k'walla ta, tallafo ta zuwa jikin ta cikin kasataliyar murya tace" kiyi shiru kinji yarinya ta, rabu da anty nayi mata fad'a bazata sake ba kinji..". ta fad'a tana shafa gadon bayan ta..

Jawahir tayi shiru abubuwa da dama suna dawo mata amma haka ta jure bata sake magana ba.

Allah sarki Jawahir da kin san marin nan da akayi ma Jameela abun zai zameki bala'i da baki bari an mare ta ba..



Bayan wasu mak'oni.


Izuwu yanzu soyayya tayi bala'in k'arfi tsakani IMRAN DA JAWAHIR har ta kai ko wajen aiki zai tafi tare da ita yake zuwa, wannan dalilin ne yasa sam maso son cutar da ita basa samu dama, k'auna ce zallah wace ko a gaban waye basa jin kunyar nunawa juna haka ne ya jawo hankali iyaye maza akan IMRAN ya koma sabon gidan shi da ya gina tun kwanakin baya, Amma sai ya nuna musu shi baida ra'ayin haka wanna abun yayi wa su Adda dadi...


Bayan 3 day's

Kwance take akan cinyar sa tayi malimali abin ta, inda shi kuma sai aukin shafa mata gashi yake, face dinta kawai zaka kalla ka san tana jin dadi wanna shafar, cikin shagwab'a tace" My! gobe in Allah ya kai mu ina so naje gidan su Aina'u in babu matsala..?"

Hankalin sa ya mayar gare ta cike da k'auna yace" maganar gaskiya banji zaki fita gobe sabida akwai inda nake son zuwa kuma ba tare zamu fita ba, so ki bari sai na dawo in yaso sai kije.." ya fad'a cike lalashi...

Jawahir ta tura baki gaba alamar tayi fushi, Imran sarai ya gani Amma shima yayi fuska dan haka kawai yaji hankalin sa bai kwanta mai da fitar da za tayi ba, gani ya'ki rarashin ta yasa ta mik'e cikin bubuga kaf'a a k'asa tace" My ban fa tab'a tambayar ka zuwa ko ina ba, kuma wanna Aina'u da zani wajen ta kafi kowa sanin ta dan Allah ka barni..." ta fad'a had'i da k'walla.

" Ya rabbi K'albi me yasa kike da taurin kai ne, tunda kike na tab'a hanaki zuwa duk inda kike buk'ata, yau d'aya dan nace bazaki ba shine zaki fara kuka to babu inda zakije..." yana fad'a ya tashi ya bar wajen..


Jawahir tayi shiru ran ta duk a dame na gani ta bata goma bata gyaru ba..

Washe gari da wuri ya tashi bai tashe ta ba har sai da ya kamala shirin s ana tafiya sannan ya tashe ta, har yanzu fushi take cikin turo baki tace" Ina kwana..?"

Bai amsa mata ba ya ajiye mata kudi had'i da cewa" gashi nan ni na wuce, in na dawo yau to in kuma ban dawo ba sai gobe..." ya sa kai yayi fice war sa..

Jawahir tayi shiru tana tunani can kuma ta mik'e, ita ma shiryawa tayi abin ta bayan ta kamala ta wuce falon gidan babu kowa domin safeya ce sosai kewar mijin ta ne ya kamata ta lumshe ido tana sauke a jiyar zuciya a fili tace" ya zanyi ne to? me yasa na bari ya tafi da fushi ne? Anya na kyau ta kuwa..??"

" Menene abun rashin kyau tawa? ai ke yar golace, shalele ta gaban goshin kowa, kinga ko ai bakya laifi, tunda a kan ki uwa ta mari 'yar ta, to wa zaki yi wa laifi a gidan na a hukunta ki, duk da ban san menene ba amma ko ma me kika yi kiyi dai-dai
tunda ke komai naki me kyau ne.." cewar Jameela tana zama a d'aya daga cikin kujerun falon..

Jawahir tsalam ta mik'e zata wuce d'akin ta Jameela ta daga murya tace" in zakije 'yar tsuntsuwa ? ai yau tafiya bata kama ki domin duk inda kike shiga sai na biki, zamanki a nan ne ma kawai yafi miki alhairi.." ta fad'a tana kai coffee bakin ta..

Jawahir bata ce komai har ila yau kuma bata fasa tafiya ba.

" Kashi bani da hankali in rai na ya b'accci, 'yar tsuntsuwa ki dakata naci.." ta fad'a fusace..

K'in tsayawa tayi baifi taku biyu ta shigo part din su tayi anyi mata wani tsinke, a tsakiyar kai dafe kan ta tayi cikin tsananin tashin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login