Showing 15001 words to 18000 words out of 48171 words

Chapter 6 - BASO BANE CUTA CE BOOK COMPLETE BY Usaina B Abubakar.doc

ta cike da rauni ta isa gare ta tana tangad'i tamkar yar kwaya.

A jikin ta jameela tayi mata ma sauki, tana jin ta jikin yar uwar ta, ta saki wani marayan kuka duk rashin imani ka sai ka tausaya mata sai da tayi me isar ta sannan ta dawo tana ta sauke a jiyar zuciya akai-akai, jameela ko babu abinda take sai auki shafa mata kai alamar rarashi.


Yan uwan Zainab da makota gaba d'aya sun zo haka yan uwan mijin ta dama akwai yan tsirari, sai ragowar da suke iso su ma, duk wanda yaji labarin mutuwar ta sai ya girgiza, haka baffa dangin ta in suka gan ta sai su ce ba ita bace sam, maza da mata sun had'u a babban falon gidan kowa yana jimamin abinda ya faru..

Adam ya dawo gida inda aka bar Imran a can yana kula da Baffa Nafi'u, Allah sarki abin tausayi sai a time din Jawahir ta fito jikin ta sai rawa yake tana wani irin kuka, Anty Nafeesa ta kama ta har gaban gawar tace" kiyi shiru 'yata Zainab addu'ar ki take buk'ata yanzu ba kuka ba." ita ma ta fad'a cikin kuka.

Jawahir kasa tab'a gawar tayi ban da nishi da take sama-sama sabida tsabar kuka, ko wa sai da ya share k'walla saboda tausayin ta, bakin ta na rawa tace"Allah ya jikan ki." ta fad'a tana fad'uwa kasa, domin kafar ta ta gaza d'aukar ta, ji take kamar ba mome bace wannan dan sam bata ji a jikin ta tayi wani rashin ba, me yasa Imran zaiyi mata karya me yasa zai ce wannan mama ce... sai ta fara wani kalar tari idanun ta nayi sama da wani kalar fari kamar me shirin tada isaka. babu wanda hankali sa bai tashi ba gani yanayi da take ciki gwani ban tausayi.



Imran kuwa hankali sa ya gaza kwanciya, tunanin sa d'aya halin da ya bar gida a ciki gashi doctor yace yana so mutun d'aya ya zauna a wajen sa domin yana gaf da farkawa, duk da sun sha walaha kafin dai-daituwar numfashin...


Allah sarki Zainab kamar yanda ake ma ko wane mamaci gata in ya mutu a kashi makwancin sa haka ita ma akayi mata...


suka dawo gida maza sun daga harbar gidan in da mata suke daga cikin gidan, duk wanda ka kalla take zaka hango tsananin damuwa, jawahir tayi zuru-zuru da ita bata um bata umum sai ido kawai, bata da burin da ya wuce tasa idon ta akan imran ba, dole ya gaya mata gaskiyar ina momen din ta take...


Baffa Nafi'u sai da yayi kwana biyu asibiti sannan ya farfado, yana tashi babu abinda ya farayi sai sallolin dake kasa, bayan ya idar ya jima a zauna sosai yana ta addu'a sannan ya tashi, maganar farko da ta fito a bakin sa shine" ina take?" Abinda yace ma Imran kenan time din su baffa basu jima da tafiya ba..

Kan sa a k'asa yace"an kai ta gidan ta na gaskiya." ya fad'a yana share k'wallar da ta zubo mai...



Mrs Abubakar ce?x ?
[8/13, 10:21 PM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*?x  ?xR?BA SO BANE ?xR??x  *
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYU DACE BA*
*BA SO BANE*...

*ina ma kowa barka da sallah Allah ya maimai ta mana da rai da lafiya, my fan's a ci nama a hankula dai kar zawo ya kama ku.*?x? ?x? ?x?


*Book-2*



1????~ 2???


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Baffa yayi shiru zuwa wani time, can yace"Imran ka fad'a mini gaskiya ka tabba Zainab ta baka wanna letter da hannun ta,, Imran ina ji a jiki na Zainab tana raye sai da tana buk'atar Addu'ar mu, zan iya rantsuwa akan Zainab din na bata mutu ba, sai dan ina tsanan mamaki me yasa duk wani abu da zai faru, baya faruwa akan kowa sai akan iyali na?

Imran ba fa mu kad'ai bane a cikin gidan mu, abin duba wa a nan shi ne ka mayar da hankalin ka akan, jameela da khadija, tunda muke da su a cikin gidan nan ka tab'a jin wani abu ya faru dasu?? Jawahir tun tana k'arama take had'uwa da masifo kala-kala, kafi kowa sani abubuwan da suka faru da ita, kuma duk a cikin gida d'aya abin yake faruwa, yanzu abi yaci tura har ta ka ga kisa kan, ina tsanmani wannan matar ma macece me girma da kuma mu'kami, ban so aka bunne ta ba zan so nayi bincike akan ta, amma Allah bai nufa ba, zan amshi kaddara domin Allah ne yayi hakan zai faru haka kuma zan ci gaba da Addu'a har karshen numfashi na, bazan tab'a gajiyawa ba har abada, ka tayani da Addu'a Imran dan ita kad'ai zaka mini a yanzu na ji dadi, ka d'age da Addu'a ka kula mini da kanwar ka wanna shine buri na, zan so ka cire wannan kud'irin naka akan bazaka iya bata matsayi mata ba, ko ba yanzu ba Jawahir taka ce ka sa haka a ranka kaji d'a na sanna ka taya ni bincike har na gano bakin zaren." yayi maganar hawaye na zubo mai.

Shi ma Imran kuka yake sosai dan duk abinda baffa ya fad'a gaskiya ne, haka kuma maganar mama gaskiya ce makashin su yana tare da su..

cikin murya kuka yace"Insha Allahu Baffa ba zan sake bari kayi kuka ba, zayi iya yi na wajen gani na binciko gaskiya, Baffa karka damu za saka ido akan kowa na gidan ba mata kad'ai ba gar mazan, amma sai kayi hakuri da sawu abubuwan." yayi maganar cikin sha'kewar murya.

da kai kawai ya amsa mai amma babu bakin magana...

doctor ya shigo ya sake duba jikin Baffa, cikin murmushi yace"Alhamdulillahi jiki yayi kyau, sai dai dan Allah ka rage damuwa a ran ka." sannan yayi yan rubuce-rubuce ya basu sallama..


Gida suka dawo abu kamar wasa, suka tarar da mutane jingin a cikin gidan na su, Baffa baiyi mamaki ba dan ya san za'ari na yan uwan Zainab duk sun hallara, kuma babu wanda bai je ya gano halin da yake ciki a asibiti ba, ko da suka ganshi sai gaisuwa suke mai da kuma kara bashi hakuri zuciyoyin su cike da tausayin sa.

Imran tunda ya shigo gaba d'aya hankali sa yana ga neman Jawahir sai kalle-kalle yake, can idon sa ya fad'a kan khadija cikin sauri ya karasa wajen ta duk da tana ciki mutane hakan bai sa ya gaza zuwa wajen ta ba, cikin muryar sa me rikitar da ita..

Yace"my k'anwa, ina kika gani mini 'kalbi na?" yayi tambayar yana bin ta da kallo.

cikin murya kasa-kasa tace" tana part din su Anty jameela tun shekaran jiya." ta fad'a tana nuna mai hanyar da hannu ta..

kai tsayi part din yayi cikin sauri, da sallama a bakin sa, ya karasa nama cike yake da mutane, Adda samira ya gani a falo cikin girmamawa ya sunkuya har k'asa, yana gaida ta.

cikin sakin face ta amsa mai, tana sakin wani malalacin murmushi..

Yace"Adda Jawahir fa?"

Dumm taji kirjin ta ya buga amma sai ta d'aure tak'i nunawa ko a face din ta, tana yak'i tana komai tace"aiyya tana cikin d'aki 'kanwar ka, har yanzu tak'i yarda cewa Zainab ce ta rasu, amma ka shiga ciki ko zaka iya shawo kan ta."
tana zuwa nan tayi waje duk da zuciyar ta ba tai mata dadi...

kai tsayi d'akin ya wuce bakin sa d'auke da sallama, kamar shi take jira dama, da sauri ta mik'e tsaye wasu kalar hawaye masu zafi suka zubo mata, tana karkata kai gefe game da yi mai wani irin kallo...

shi ma ita yake kallo cike da tausyin ta, cikin takun k'asaita ya isa gare ta, hannu ya daura kan kafad'ar ta yana had'e face din su waje d'aya duk kan su, suna jin numfshin juna, hancin su yana gogar na juna, cikin wata siririyar murya yace"Sorry 'kalbi na!!.."

jikin sa kawai ta fad'a tana me k'ank'ame shi, kukan ta na tsana ta, cikin murya kuka tace"kai kad'ai ne zaka gaya mini na yarda My, shin da gaske ne abunda idanu na suka gane mini? zuciya ta ta gaza aminta da abinda naji bakin ka ya fad'a tun farko, kayi mini rantsuwa da Allah madukakin sarki cewa da gaske wanna matar da na gani mome nace?" ta fad'a idon ta na gan sa.

Cike da tsantsar tausayin ta, yace" please ki kwantar da hankalin ki, mubi komai a sannu tabbas ita din mama ce da ido na, na ganta har mu kayi magana da ita, amma sai dai ban fahimci abinda take nufi ba, abu d'aya na gane a cikin maganganun ta, shine na je na kula da ke.
Jawahir ki bani hankalin ki nan, a yanzu mama addu'ar mu kawai take bu'kata ba wai kuka ko jan zance ba, kiyi hakuri kinji Allah ya jikan mama." ya fad'a yana dan bubuga bayan ta.

da sauri ta ture shi, har yanzu kuka take tace"bazan yarda ba mome na bata mutu ba, ni ina ji a jiki na tana raye wallahi, kuma sai na nemo ta Allah bazan barta haka ba." ta fad'a tana yin hanyar fita da sauri.

cikin zafin nama ya fanciko ta da duk kan k'arfin sa yace "ki nitsu mana su nawa zan fada miki mama ta rasu cikin. karaji ya fad'i maganar sannan daga baya ya suma yi mata magana cikin nitsuwa da kwantar da murya yace" haba kanwa ta kin san dukan mai rai mamaci ne toh ke me yasa baza ki d'auki Kaddarar ki ba wanda yafi mu san ta ya amshe abar sa a irin wannan lokaci Addu'ar ki take buk'ata,

idan har kika kasance kina mata Addu'a da fatan samun sallam a makwancin ta toh hakika za tayi farin ciki da haka kuma kin san burin ko wace uwa ta haifi Da' na gari wanda ko bayan ranta zatayi mata Addu'a, please jawahir kema ki zama daya daga cikin wa yan nan ya'yan, ki manta hankalin ki ba akan ki aka fara mutuwa ba, ki dube ni da kyau bani da kowa, kuma gani ina rayuwa ban mutu ba, haka ban zauce ba, kamar yanda kika fara rasa mahaifiyar ki nima ita ce ta fara tafiya ta barni, kuma gani ina rayuwa ta kamar kowa, haka na rasa uba nan ma na ci gaba da rayuwa, me yasa bazaki gwada irin hakurin da nayi ba? haba jawahir ke fa macece kuma uwa zaki zama nan gaba, yana da kyau ki koyi juriya da hakuri, Allah ne ya bamu mama a matsayi uwa, sanna ya amshe ta a lokacin da ya kamata, sai da muyi hakuri mu rungume k'addar mu, Allah ya jikan mama." ya fad'a shima hawaye na bin kuncin sa, domin abinda ya jima yana damun sa yau ya taso mai a lokaci guda...

Duk da zuciyar ta batayi wani laushi ba, amma sai tayi kasa da kan ta, hawaye na zuba mata.

Hawaye yake share mata, da hannu sa yana cewa"Allah yasa abinda na fad'a miki kiyi aiki dashi, yanzu abinda nake so kiyi wanka kizo d'akin baffa yana son ganin ki kinji." ya fad'a yana ware idon sa akan face din ta...


_nasan na kund'i ma muku laifi to kuyi mini uzuri, aikin sallah ga kuma yawan sallah amma na kusa dawa gaba daya, insha Allah._


Mrs Abubakar ce?x"! ?x"!
[8/14, 11:33 AM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*?x  ?xR?BA SO BANE ?xR??x  *
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYU DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*


3????~ 4???


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


gaba d'aya ta kasa tsayiwa da kafar ta, tunanin ta d'aya shine yanzu in da gaske mome ce ta mutu ya zatayi da rayuwar ta, wa zai sata farin ciki? wa zai rarashe ta in tana kuka, wa zata kalla a matsayin uwa taji dadi? lallai ko in hakan ya faru da gaske sai tafi kowa bakin ciki mafi muni a rayuwar ta.

take ta fashe da wani mahaukacin kuka tana fad'i " No No No bazai yuyuba wallahi bazan yarda ba, Allah ba mome bace yasi wannan ba uwata bace..." ta fad'a a haukace cikin gigitacen kuka...

Imran ya dafe kai sa da duk kan hannuwan sa biyu, yana juya shi cikin tsananin damuwa, kukan ta na tab'a shi fiye da zaton masu karato, idanun sa suyi jawuri dan tsananin tausayin ta da kuma jin kukan ta da yake har cikin zuciyar sa, k'in magana yayi sai ido kawai da ya zuba mata, ganu bata da niyyar yin shiru yasa yayi gaba abin sa zai bar mata d'akin...

tana kallon sa har ya fice a d'aki, ta kasa tsada shi...



A gaba Baffa yasa sai fad'a yake mata, cike da taushin murya, daga nan kuma ya koma yi mata nasiha me ratsa jiki, cikin sanyin murya yake mata..
.

tun Jawahir na kuka har ta dayna, sai sharar kwalla kawai da take..

Imran shi ma ya shigo nan suka saka ta a gaba da nasiha, ko wanne da irin abinda yake ce mata..



Bayan sati biyu,


tun da Zainab ta rasu, jawahir bata sake dariya ko murmushi ba, kullum tana d'aki a zaune bata da wani aiki da ya wuce tunanin, duk yanda iyayen ta suka so ta rage damuwa abin yaci tura.

Imran duk wani abu da yasan yana sanya ta farin ciki yayi mata amma a banza, dan yanzu ko magana ba sosai ta cika yin ta ba, tashin hankali iyayen ta sun shige shi mutuk'a.

Adda Samirra kuwa dadi kamar ya kashe ta, haka ma jameela.

A hankali Imran ya fito da wani saban salo na fita da ita, yawo duk wani wurin sha'katawa da ya sani sai ya d'auke ta su wuce tare, wannan abun da ya fara ba k'aramin, d'aga wa su Adda hankali yayi ba, a irin wannan fitar ne ya had'u da abokin sa Abdulrahman.

Abudlrahman mutun ne me hakuri da barkonci, gashi da sany hali, duk fushin mutu ko hancini sa in suka had'u sai ya shi yayi dariya...

sun sha'ku sosai kuma kullum sai sun had'u ar da jawahir cikin aminci Allah ta fara sakewa dashi har wani lokaci takan d'anyi murmushi...



A nan kasan layin su, akwai wata yarinyar Nabila, yarinya ce kyakykyawa me hankali da nutsuwa, kusan rabin layin ansan da nutsuwar ta, zaman da Imran ya fara a waje shima ya fara sani ko wacece ita, had'uwar su ta farko sanadin abdulrahman, tun a kallon farko Nabila ta fad'a tarkon son Imran amma babu fusaka dan ko kallon ta baiyi ba...



Haka suka ci gaba da rayuwar su cikin huk'unci Allah, inda Nabila ta mayar da wajen da su suke zama wajen wuce warta, kullum sai tazo tun basu gane abinda take nufi ba har sai da suka baro jirgin ta....



An d'auki lokaci me tsaho, tun Imran bai kula Nabila da tursasawa Jawahir da Abdul suke sa shi ya fara kula ta....


A hankali so Imran ya fara shigar Nabila, ya zama duk duniya bata da abun so sama dashi, shiko gogon naku bai ma san tana yi ba, dan ya dauki kular duniya ya d'aurawa Jawahir.

Jameela ce tazo wuce kamar yanda ta saba kullum yau ma fita zatayi cikin shigar ta, ta fida tsiraici cak ta tsaya tana k'arewa Nabila kallo ta cikin medical glasses din ta, gani suna ma juna murmushi take wani takaici bakin ciki ya taso mata lokaci d'aya cikin zafin rai ta karkata akalar ta zuwa gare su, zuciyar ta na kuna....



Comment

And

Shared

Please

Mrs Abubakar ce?x?"!
[8/17, 6:34 PM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*?x  ?xR?BA SO BANE ?xR??x  *
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login