Showing 42001 words to 45000 words out of 48171 words

Chapter 15 - BASO BANE CUTA CE BOOK COMPLETE BY Usaina B Abubakar.doc

hankali domin iya buguwa ta bugu ga wani zugi da yake mata, a hankali ta kalla k'asa dan fahimtar abinda ka jefe ta dashi, coff din dake hannu Jameela ne har yanzu tana nan zaune inda take, bata motsa ba..

Ran Jawahir ya b'accci amma gani yayar ta ce bata da damar ramawa komai za tayi mata sai tayi shiru ta wuce..

Adda samera ce ta fito wace ta jefe ta da coff din tana murmushi ta zauna kusa da 'yar ta tace" me kuma kike jira? yau gidan nan babu kowa sai mu kad'ai ina so naji ihun 'yar tsuntsuwa ya cika ko ina.." ta fad'a tana shafa mata gefen fuska..

Jameela ta sake narkewa a jikin uwar ta game da cewa" kwantar da hankalin ki mama na barewa baza tayi gudu ba Yar ta tayi rarafe ba, mudin ni jiniki ce yau zan saki farin ciki.." ta fad'a cike da ya'ki ni..

Tana zuwa d'aki ta fad'a kan gado ta saki wani kuka me tab'a zuciya, a hankali tace" ina kike mome ne? a 'yan kwanakin nan rashin ki na damu na mome, wait yaushe zaki dawo gare ni ne mome..?" ta fad'a cikin kuka..

A dai-dai lokacin da take kuka a lokacin ne kuma IMRAN ya dafe saitin zuciyar sa game da cewa" me kuma ya saki kuka K'albi? ko dan na hana ki fita ne? Allah ya ka kare mini matata Allah ka tsare ta da tsarewar ka.." ya fad'a cikin rauni, domin yaji a jikin sa bata cikin dadi..


" Wanda ya mutu ai baya dawo wa 'yar tsuntsuwa, me kike tunanin ne kina gani an dake ni akan ki a dake bulls ne? Hhhhhhhh lallai yarinya to ki maza ki farka domin bazan kyali ba.. cewar Jameela dake tsaye bakin kofa..


Jawahir dai bata kula ta ba sai kuka kawai da takeyi.. gashin kan ta taji ana damk'e mata da masifar karfin har sai da ta saki yar k'ara sabida zafin da taji, cikin kuka tace" Anty dan Allah kiyi hak'uri in wani laifi nayi miki, nima ba'a son rai na Adda ta hukuntaki ba, domin kina da gaskiya babarki ce ba tawa, haka ke d'aya kike da ikon hawa kan ta bani ba to na yarda nayi karn bani amma kiyi ha'kuri ki sake mini kai na kar yayi mini ciwo.." ta fad'a tana dafe kan na ta da dukan ni hannun ta biyu...

Jameela ta sake matse mata gashin da kyau, Jawahir ta saki k'ara game da sakin wani rikitacen kuka tace" na rok'eki da Allah Anty kiyi hak'uri wallahi ko kusa da Adda bazan sake zuwa ba.." ta fad'a cikin kuka..

Dariya tayi kana ta same d'aya hannu ta damk'e mata k'unne da masifar k'arfi ga gashi ga k'unne, Jawahir ta gigice ta Ware murya iya karfin ta ta saki kuka me gigita cikin kuka tace" wayoo Allah na zata kashe ni, My!!!.." ta fad'a da masifar k'arfi..

Cak ya taka kan motar ta bada kirr.kiirrr. a fili yace" JAWAHIR!!!..." yana me dafe kirjin sa dake buga mai da sauri_da sauri,. wayar sa ya d'auka ya shiga Neman layi ta, Kira yake tayi amma anki d'auka, tsoro ya kama shi cike da fargaba ya juyo kan motar sa zuwa gida zuciyar sa bata mai dadi...


" Wato MY ko dan ubanki, yau ko uban My din zaki Kira naga me kwatarki shegiya me suffar kwad'i..." ta fad'a tana had'e kan ta da garu..

Jawahir ta lumshe idon ta sabida tsananin wuya, wata k'walla me zafi tana zubo mata izuwa yanzu ta daina ihu sai nishin wahala kawai take..

Bari kiji wallahi bake d'aya ba mudin kika fad'awa mutane abinda ya faru tsakani na dake sai na gigita Miki rayuwar bake kad'ai ba har da ta IMRAN wawuya kawai marar ajiya...". tana fad'ar haka ta hankad'a ta gefe da k'arfi...

Jawahir ta fad'i a k'asa goshi ta ya bugo, ta dafe wajen tana girgiza kai sabida tsananin wahala a nan ta zama sumammiya hannun ta dafe da goshin ta..

Jameela tana ganin haka ta tsalle ke ta wuce zuciyar ta fess fatan Allah yasa ta wuce karta tashi..

Wani irin bugu zuciyar sa tayi da masifar k'arfi ya dafe kirjin sa ga wasu hawaye da bai san da zaman su ba suka shiga rubo mai, ya Kara giyar motar sa da masifar gudu, a hankali ya furta'' ki tashi JAWAHIR please Jawahir kar ki zama raguwa mana.." ya fad'a cikin wani yanayi..

Jawahir ta wani motsa a hankali idanun ta ya bude yayi jawur, tamkar yana gaban ta ne yayi maganar, ta shigar jan jiki tana son d'aukar wayar ta dake ruri, sabida buguwar da tayi bakin ta na jini ta tofar da miyau me had'e da jini ta sake Jan jiki, ta dauko wayar hannun ta rawa tana gani dishi-dishi, My heart naga ana sa tana d'aukar wayar jiri ya d'auke ta ta fad'i warwas a wajen, tana nishi sama-sama,

Gani ta d'auki wayar ya shi cewa" kina jina Jawahir?? fad'a mini meke faruwa yanzu? sannan kina Ina?? a wanna hali kike cikin?" yayi maganar a rud'e.

Jawahir ta sake bude ido cikin jigata ta sake jawo wayar kusa da it's duk da Bata gani sosai tace" MY!!! ZAN MUTU, ZATA KASHE NI.... sai kuma ta kama tari babu k'wak'wautawa can kuma tayi dogon summa..

IMRAN YA SHIGA KWALLA MATA KIRA IYA KARFIN SA JAWAHIR JAWAHIRRR!!!..

_na rantsi zanyi shara domin yanzu kun rage comments masu comments din kad'ai ne, in kuma bakwa so sai a dai na_

COMMENTS AND
SHARED

MRS ABUBAKAR CE?x???? ??"!?
[9/22, 11:07 AM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*?x  ?xR?BA SO BANE ?xR??x  *
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYI DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*



4???0????~ 4???1???

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Gudu yake sosai bai ma cika gani gaban sa, dan ma Allah ya taimaka safeya ce babu motoci da yawa a titin, ikon Allah ne kawai ya kawo shi gida ko rufe motar bai tsaya yayi ba ya cikin gidan da gudu, lokacin shigar Adda Samira part din ta kenan, shi kuma ya shigo babu kowa a falon, da k'arfi yace" K'ALBI!!!..." sai kuma yayi part din su a hargitsi...

Kwance ya same ta cikin jini, tamkar matacciya haka take, hankalin sa ya kai k'ololuwar tashi, d'aukar ta yayi a hargitsi ya fice da ita, bai tsaya ko ina ba sai asibiti an amshe ta cikin gagawa domin ceton rayuwar ta...

Anyi nasarar dai-daitowar numfashin ta, nan aka kai ta d'akin masu jinya, kan ta d'anne da farin kyali..

IMRAM tsayawa yayi daga bakin kofa Yana hangen ta daga na, zuciyar sa cike da tausayin ta, daga bisa ni yaje wajen doctor a nan yake mai bayin buguwa tayi shi ne dalilin zubar jini ta da jin raunika ta, sai ciwon ka me tsananin dake damun ta..

IMRAN ya fito yazo d'akin da take bakin gadon ya zauna yana kallo yanda take fitar da numfashi a wahale take wani Sabon tausayin ta ya sake kama shi, bai san lokacin da hawayen bakin ciko suka zubo mai ba haka suka dinga d'inga aka face din ta, hannu su na sark'e waje guda..


Abdullahi ya duba a goggon hannu shi yaga lokacin ya kusa kurewa, gashi har yanzu IMRAN bai iso ba bayan shi yace mai gashi nan akan hanya, ya saki siririn tsaki domin mutane shi kad'ai ake jira...

A k'unne yayi wa Adam magana, mik'e wa yayi ya fita daga waje sannan ya Kira wayar IMRAN, hankalin sa baya jikin sa dan haka wayar sa na mota bai d'auka ba, haka baffa Adam yata Kira amma shiru babu amsa gajiya yayi ya koma ciki ya sanar musu, jikin kowa babu yayi sanyi haka taro ya watsi...

Ran su baffa ya b'accci sosai da rashin zuwan IMRAN waje haka suka wuce office din su ko wanne zuciya babu dadi..

" Eyye!!" suka fad'a a tare game da taffa tamkar sa'anin juna suna dariya farin ciki...

Adda Samira tace" to aikin ki yayi kyau Naz shirts ki fice kafin su dawo, kin san halin babaki da shegin say idon tsiya yanzu zai ce kece..". ta fad'a tana wuce a d'akin.

Jameela yau tana cikin farin cikin d'an haka cikin k'ank'ani lokaci ta bar gidan gaba d'aya..


Mik'e wa yayi zai je ya d'auko wayar sa, har ya kai 'kofa ta farka cikin murya masu jin jiki tace" M y!! zata kashe ni.." ta fad'a rarabe..

A su'kwane ya dawo inda take yana sake kamo hannun ta yace" K'ALBI bude idon ki gani a kusa dake, me ya same ki?? ". ya fad'a a rud'e..

A hankali ta bude idon ta tana kallon shi can kuma ta mayar ta lumshe, barci me k'arfi yayi awan gaba ita, domin allurar da akayi nata ta fara aiki...

Fasa tafiya yayi ya koma ya zauna yana ta kallon ta, zuciyar sa na k'ara mai wutar son ta da k'aunar ta game da tausayin rayuwar su, tunanin sa ne ya tsaya akan waye yayi mata haka??.. gani barcin ta yayi nisa dole ya tafi ya d'auko wayar sa, baiyi mamaki gani miss call din baffa nashi ba, kiran su yayi d'aya bayan d'aya, ya fad'a musu abinda ke faruwa bai boye musu komai ba..

Babu wanda hankalin sa bai tashi ba a cikin su, haka su kayo asibitin hankali a tashe, sai da suka so ne ma suka ankara dashi kad'ai ya kawo ta nan suka shiga tambayar sa mutanen gidan..

Bai boye musu akan shi baiya kowa ba, sunyi mamaki da tunani Ina kuma suka tafi har haka ta faru..?

I zuwa yamma kaf 'yan gida sun zo a sibitin, haka kuma sun cika d'akin, IMRAM yana mak'ali a jikin gadon yanzu ya dai na kuka sai da aukin sauk'e a jiyar zuciya da kuma tunanin mafita...

Motsi ta fara da hannun ta zuwa can kuma ta bude idon ta a hankali, d'ishi-d'shi take gani kowa na d'akin lumshe ido tayi, game da dafe gefen kan da d'aya hannun tana ya mutsa fuska..

IMRAN ya kura mata ido sosai, can yace" sannu k'albi , kai ne yake miki ciwo ?" yayi maganar yana dafa mata kai..

Hannu shi ta kama a hankali idanun ta suka bude tar a kan shi, cikin murya marar sa lafiya tace" My! dan Allah ka d'auke ni daga gidan nan na gaji wallahi tunda na taso nake gani abubuwa da dama, har zuwa girma na, ka taimake ni ka rabani da gidan nan ko zan samu salamar rayuwa.." ta fad'i maganar hawaye na bin kuncin ta..

Babu wanda bai rud'e ba da jin wannan furicin nata, amma ban da IMRAN wanda shima tunanin sa kenan..

Cikin wata murya yace" kwantar da hankalin ki K'albi dole ma mu bar shi, ko dan samun farin cikin ki.." ya fad'a yana shafa mata gefen fuska..


A cikin su baffa ko Adda babu wanda yayi magana sai ido kawai da suke zarewa..


Suna cikin haka doctor ya shigo ya sake duba ta da kyau, gani babu sauran wata matsala yasa ya basu sallama, haka suka dawo gida ko wanne su jiki a sanyaye..

Dare nayi yace mata bari yaje ya dawo, akwai abinda zai duba tunda juyen duniya yayi da ita akan ta fad'a mai wanda yayi mata haka tak'i, da ya matsa mata sai ta sanya mai kuka, dole ya hak'ura zaje ya dawo ya gani da idan sa..

Yana fita ta tashi duk da bata jin k'warin jikin ta sosai haka ta wuce d'akin sa, laptop din sa ta hanga akan table cikin d'an sauri ta isa wajen bata wani sha wuyar cire password din ba, dube-dube ta fara aiko taci sa'a abinda taje nema cikin gagawa ta goge tass sanna ta mayar da ita inda ta ganta ta fice a d'aki tana suke a jiyar zuwa, maganar Jameela ta k'arshe na dawo mata, ita kuma baza ta so a cutar mata da IMRAN din ta ba...


Yana shigowa d'akin sa ya wuce shi ma laptop din ya d'auka, yazo nan kusa da ita ya zauna yana duba wa, mamaki ne ya kam shi gani tunda ta fita bata sake shigo d'akin ba, tunanin sa ne ya tsaya kan to ya akayi shi ya same ta a d'aki? duk yanda akayi Jawahir ta goge, aiko ran shi ya b'accci ya d'ago yana kallon ta yace" JAWAHIR me yasa kika d'aukar mini laptop har ki kayi mini goge-goge ?"

Ta kalle shi cikin shagwab'a tace" no ni bam shiga d'akin ka ba, tunda muka dawo Ina nan a kwance.." ta fad'a tana ya mutsa fusaka..

B'accci rai ya hanna shi magana domin ya sa kaf gidan babu wanda ya san da CC camera sai ita, haka kuma babu wanda ya san password din shi sai ita, tsaki yayi ya tashi ya bar mata wajen...

Jawahir ta lumshe ido a fili tace" mudin zaka kasance cikin jin dadi ni zan iya komai dan gani na kub'utar da kai My! bazan iya jure ganin ka cikin mugun yanayi ba.." ta fad'a tana share k'wallar ta da tsananni bakin ciki, ba dan komai ba sai dan gani 'yar uwar ta ke neman rayuwar ta, yanzu dama duk k'aunar da jameela take nuna mata dama *BASO BANE CUTA CE* lallai duniya cike take da abubunwa alajab'i, inko haka ne ba makawa akwai mai d'aure mata gindin, kuma yanzu ita ma zata tsanan ta bincike, wasu hawaye suka zubo mata...


IMRAN dake d'aki yana kallon ta tausayin ta ya kama shi, haka ya d'aure zuciyar sa shi ma ya fito inda take, da kan shi ya ta rarashin ta har tayi shiru..

Adda mairo ce ta shigo part din su bakin ta d'auke da sallama, duk da sun jin shigowar ta hakan bai sa IMRAN ya janye JAWAHIR daga cikin sa ba, sai ma k'ara k'ank'ame ta da yayi haka ita ma tayi lak'ur a jikin sa, kusa da su ta zauna tana kallon su da fusakar tausayin tace" Jawahir ya jikin naki ?" ta fad'a tana kallon su, zuciyar ta tanayi mata wani iri..

IMRAN yace" da sauki sosai tunda yanzu ba kamar d'azu bane.."

" Ok yayi kyau Allah ya sauwak'e, Jawahir ki d'aure ki gaya mana wanda yayi miki abun nan, domin hankali mu ya tashi sosai da Ina cikin gidan nan da duk haka bata faru ba, amma abun mamakin a nan shine Addanki nan domin lokacin da zan fita na bar su ita da jameela a falo, to ban sani ba ko bayan fita na ita ko ta fita tunda tace bata san anyi ba, abun dai da mamaki gaskiya yarinya gaba d'aya tunda kika taso abubuwa sai faruwa suke akan ki ke d'aya, gaskiya lamarin akwai rud'ani a cikin sa, JAWAHIR ko da tsoratar dake akayi kika k'i fad'a ?" ta jefa mata tambayar cikin bazata..

Jawahir tayi saurin mi'kewa tana cewa" a'a-a'a babu wata maganar tsoratar wa kawai fad'ar ne bai da amfani, domin baka sani masoyin ka na gaskiya har sai wani mumun abu ya faru da kai a nan ne zai nuna kan shi, wane masoyin kuma rik'id'ewa yake ya koma makkiyi ko kuma ya nuna maka duk duniya babu ya kai Ashe duk ba haka bane ban tab'a tunani *ba so bane CUTA ce* sai yau na tabbar da hakan da ido na, amma na say Rai na ko zaa kashe ni bazan tab'a fad'ar ko waye ba mudin da rabon a san shi, to asirin sa zai tuno kowa ya ganshi, ni na bar mutun da Allah in babu a nan ai akwai can, haka kuma abinda kayi mai 'yar wani to kai mai za'ayi was taka insha Allah, wanna ba fad'a ta bace a rubuce yake, duk Wanda ya zalince ni a matsayi na na marainiya, Allah ya saka mini ko waye kuwa na barshi da malincin mu, Allah ne zai isar mini da isar say insha Allah..." ta fad'a cikin kuka..

Adda mairo har wata zufa take ji tana neman d'igo mata, amma da yake makira ce ita ma, sai ta k'washe-sheb'e fuska, tace" haka ne yarinya ta Allah ba azalimin bawan sa bane dama, Allah ya taimake mu baki d'aya ya tsare gaba, ni zan koma sai da safen ku.." ta fad'a tana wuce wa..


IMRAN ya juyo da ita saitin sa yana kallon ta yace" ina alk'awarin da kika mini na duk abinda ya faru da d'aya matsawar d'aya baya waje to dole d'aya ya sani, yanzu dama har akwai ranar da irin wanna abun zan faru dake ki gagara gaya mini, anyya JAWAHIR kina jina kamar yanda nake jinki kuwa ? idan har kina jina kamar haka bazaki ji shakar gaya mini damuwar ki ba ko Wanda yake k'ok'ari turaki kiyyama lokacin baiyi ba, bazan ta kura ki ba akan ki fad'a mun ba, duk lokacin da kika shirya sanar mini ni a shirye nake da na saurare ki.." ya fad'a yana shafa gashin kan ta..

JAWAHIR ta sake k'ank'ame shi cikin kuka tace" kayi hak'ura My!! bazan iya ka kallon cikin mugun yanayi ko hali ba, bazan bari a tagaiyar rayuwar ka ba, zan iya fanssar ka haka kuma zan iya jure komai akan kai, dan Allah ka sa ran ka babu abinda ya faru dani na muni ko nak'i, ko da nan gaba kuwa kak'iji kak'i gani My heart dan Allah kuma bana so ka tsawai ta bincike.."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login