Showing 21001 words to 24000 words out of 48171 words

Chapter 8 - BASO BANE CUTA CE BOOK COMPLETE BY Usaina B Abubakar.doc

gardama har sai da ta wuce ya saki tsak'i afili...


Jawahir tayi nisa a tafiya sai ta hango babbar mota a gaba ta, da duk kan alamu matsala motar ta samu dan a tsaye take cak kuma ta tare hanyar wuce wa, cike da jin haushi ta juya kan car din ta zuwa d'aya hannun bata ji zuwa wajen wani shan iska kawai sai ta kama yawo a unguwani daga wannan sai wannan tana ciki haka ne tayi wajejen 'yan shana da yake sabuwar anguwa ce yawaci filaye ne da ruwa sai dajiji ka dake gefen su, gida je kuma jefi jefi suke a barayin babu wani dogon tunani ta shiga anguwar tana ta kalle-kalle abin ta cike da nishad'i abinda bata sani ba tun farko taso war ta wata ba'kar car take bin ta...


Jameela tayi nisa ta hangi wasu garda-gardan samari sun sha gaban ta, ko wane su face din sa a rufe take da farko kamar ta bita takan su gani hanyar babu mutane a waje amma tunawa da abinda ya fito da ita sai ta tsayar da car din tana laik'owa tace"malam d'an matsa akan hanya."" tana fad'ar haka ta mayar da kan ciki motar gani bai da niyyar tsayawa sai abu ya b'ata ma rai cikin masifa ta fito..

Cak ta tsaya gani basu kad'ai bane har da wasu dake bayan ta ko wane akan mashin din sa gaba d'ayan su babu d'igon rahma a fuskar su...



Hanyar da jameela tabi nan Imran yayo yana ta dube-dube wani tunani yayi zaiyi wuya Jawahir tayo nan haka kawai sai ya juya kan motar sa da nufin bari wajen...

*Gaskiya na fara gajiya da rashin comment din ku, ya fara damu na in babu dama sai na ajiye kawai in na dawo daga tafiyar da zanyi na ci gaba in bakwa so haka ku kuwa?x? ?x? *


Comment
And
Shared
Please


Mrs Abubakar ce?x??
[8/19, 4:32 PM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*?x  ?xR?BA SO BANE ?xR??x  *
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYU DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*


1???1????~ 1???2???


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Mace ya hango tana tsala gudu tamkar zata tashi sama sai hannu take d'ago mai alamar neman taimako ido ya 'kura mata zuwa wani lokaci in ba ido sa bane gani yake kamar jameela bude motar yayi ya fita yana 'kara k'ura mata ido tabbas ita ce mamaki ne ya kama shi gani yanda take gudu tana waiwayen bayan ta...


D'aya daga cikin su ne ya ciro wayar sa game da kara ta a k'unne yace" madam mun kama ta me kike da buk'atar ayi mata ? "

Banji me aka ce mai ba ilama k'ashe wayar da yayi yace" yara yau fa dawa tayi nama madam tace muyi yanda muke so da ita.. " ya fad'a yana lashe lips kamar wani tsohon maye..

Cikin Jameela ya d'uri ruwa cikin kid'ima tace" ku bana so shashanci ku matsa mini a hanya na wuce. "

A tare suka she'ka mata da dariya kana su kayi kan ta, tashin farko d'aya yayi na nasarar zare mata d'an yalolon mayafin dake kan ta, jameela ta k'wala ihu cikin firgici tace" shegu matsiyata uban wa ya aiko ku waje na." ta fad'a cikin tsiwa...

Babban cikin su ne yayi mata dariyar mugunta kana yace"me hali bazai fasa ba amma yau sai mun nuna miki ke k'aramar marar kunya ce." ya fad'a game da yin kan ta gadan-gadan..

Da yake suyi mata k'awanya sai ta rasa ta inda zata sa kan ta, take ido suka furfuto waje cikin rawar murya tace"dan Allah kuyi hak'uri ku fad'a mini duk abinda kuke so zan baku ko menene amma karku tab'a mini martaba ta." tayi maganar hawaye na bin 'kuncin ta...

Dariya suka saka yace" a hakan ke har wani martaba gare ki ? dubi fa shigar dake jikin ki amatsayin ki na y'ar musulmai yau za ki gane kuren ki yarinyar.. "

Suka rufar mata a tare Allah ya bata iko tayi tsalle zuwa gefe ai bata jira komai ba ta saka gudu cikin d'imuwa da kad'uwa, suma suka rufa mata baya..

Tun daga nesa ta hange car din duk da bata san waye a ciki ba haka ta shiga d'aga hannu alamar neman taimako..

Suma gani mota a gaban su oga yayi musu ink'iya da ido aiko suka juya a guje zuwa wajen mashi nan su ko wane ya ara a kare...

IMRAN ya kama baki gani JAMEELA wujiga-wujiga ta zuba uban nishi tana zuwa jikin sa ta fad'a tana cewa" ka taimake ni dan Allah zasu wula'kanta ni.. "
Ta fad'a cikin kuka da sauke ajiyar zuciya.

Jikin Imran har rawa yake wajen rok'o ta yace" Jameela ke da waye ?" ya fad'a cike da mamaki.

Ai sai yanzu ta san a jiki wa take cikin tsananin murna ta d'ago da fuskar ta wace gashin kan ta yayi ma rumfa ta sa hannu ta janye shi gefe guda tace" Yaya Imran!! " kawai sai ta sake rungume shi kam tana saki wani marayan kuka...

Tausayi ta bashi dan haka ya shiga buga mata baya a hankali alamar rarashi...


Nabila dake can gefe nesa da su wani irin bakin ciki ya kama ta, kawai sai ta juya ta bar waje zuciyar ta nayi mata zafi dan sam bata so haka ba...


" Ya isa haka 'kanwa ta daga ina kike ? kuma me ya had'a ki da su ? "

Daga nan ta k'washe duk abinda ya faru ta gaya mai, take hankali sa ya tashi cikin hargowa yace" JAWAHIR !! .." ai bai sake jin me zata ce ba ya shige motar sa ya bar wajen cikin tsoro da fargar abinda zai same ta...

Ita ma cikin sauri ta koma inda car din ta take ta biyo bayan sa, sai gudu suke tsulawa akan titi...


Duk hanyar da yabi sai yake gani kamar ta nan Jawahir din ta wuce dan haka ya sake bada himma wajen bin hanyar, Imran kamar wanda akayi ma wankin ido duk inda ya sa motar sa Jawahir ta bi ta wajen a haka har ya isa 'yan shana, tsaya wa yayi yana ta kalle-kalle da tunane-tunane yanzu ina zai nufa kuma hannun damar sa ya shiga kai tsaye, tafiya yayi me nesa shine har 'yan hamar ya kara gaba kenan sai ya fara hango wata car daga can gefe shima nan yabi zuciyar sa nayi mai zafi a hankali-a hankali ya karasa wajen sabida yashin dake wajen, tabbas ko daga barci ya tashi ya san a wannan motar Jawahir ta fita d'azu tunanin sa ne ya tsaya lokacin da idon sa ya kan kan mayafin ta dake yashe a k'asa da sauri ya isa waje hannu shi har rawa yake wajen d'aukar sa...


" Kk'albi sai kin kadani da wannan k'waton mayafin naki, nace ki sako k'arami kin ki to muje.." ya fad'a lokaci da take k'ok'arin ya fa shi a jikin ta ya rufe mai ido..


Tunowa da hak da yayi yasa shi saurin yin baya kamar zai fad'i kana ya saki wani ingarma ihu game da rad'a mata kira "JAWAHIRR!!! " ya fad'a iya 'karfin sa..

Jameela ta iso wajen sa ita ma idon ta fal k'walla ta ma kasa magana...


A hankali ya tashi tsaye,


Tafiya su kayi me nisa amma bai ga ko alamar an bi ta wajen ba, har ya cire rai da samun ta kamar ance ya waiga sai ga d'an 'kunne ta wari d'aya har da gudu wajen d'aukar sa, nan ma ya sake shiga rud'ani ya kuma kara k'ami wajen bin hanyar har da gudu yake had'awa.


Abinda ya faru

Car din ta ce ta shige cikin yashi abinka da ba kwarariya ba, tayi iya yin ta amma ta kasa fita fitowa tayi a motar tana neman wa y'an da zasu taimaka mata, tana fito mutane uku nan na fito su ma wanda dama su suka shirya komai , Jawahir cikin ladabi tace" dan Allah bayin Allah taimako nake nema? "

" Na me fa?" " dama car din ce ta mak'ali a cikin yashi shine nake so ku taimaka mini.." ta fad'a har da gurini murmushi..

Basu sake cewa komai ba sai nufar ta da su kayi kamar abin kirki kye ta mik'a musu amma me sai kawai d'aya ya damk'e mata hannu kam, Jawahir tayi mai wani kallo kana ta kalle hannu ta da ya sha rik'o tace" lafiya ka kalau malam?"
gani yaki sakin ta yasa ta fara k'ok'arin k'wace wa a haka suka shiga kokawa dashi amma a banza d'ayan ne ya sa hannu zai janye mata mafiya tayi sauri d'auke shi da mari da d'aya hannun na ta, aiko kafi ta ankara d'ayan ya zafga mata mari me inganci wanda tunda uwar ta ta kawo ta duniya ba'a tab'ayi mata irin sa ba sai yau jin ta da gani ta suka d'auke, kafin ta dawo nomarl wanda ta mara ya tsige mata mayafin ta k'arfin tsiya...


Jawahir ta rundum ihu game da kiran MY!!!..

Haka tana ji tana gani suka raba ta da mayafin jikin ta duk ko da irin rok'on da take musu, dama su uku ne wanda ya mare ta yace" nan hanyar wuce wa ce ku shiga ciki da ita.." Aiko suka fara janta tana cije wa haka suka ringa jan ta ko tausayi babu dan ko fad'uwa tayi haka suke janta a k'asa dan-danan kuwa tayi tumu-tumu da ita Allah ma yaso wajejen babu duwatsu sai yashi a haka har kwalliyar jikin ta kaf ta cire kama daga d'an k'unne sark'a takallmi dadai sauran su...


Mun dawo

haka ya ringa gudu a hanyar yana tsintar abubuwan ta, kuka kam Imran yayi shi tamkar k'aramin yaro haka ya dawo...

Jameela ma kuka take gani yanda duk ya bi ya d'aga hankali sa kan Jawahir...


A haka har ya isa gindin wata bishiya darbaijiya cike take da ganyayaki gata k'watowa me reshe da yawa, da yake magariba tayi gari ya fara duhu hankali Imran ya sake tashi ya bude murya iya 'karfin sa ya k'walla Jawahir kira har sau uku..


Jawahir da ta jima da suma sanadin d'aurin da ta sha tamkar akuya tana nan jiki bishiyar da yake amma ita tana daga baya shi kuma yana gaba ga bakin ta ya rufe babu halin yin magana ko ihu dama su ajiye ta ne suje su dawo dan cika umarnin da madan din au ta basu..

Imran ya zube a waje yana sake fashe wa da kuka kana yace" ina suka kai mini ke ne Jawahir din na ya Allah ka sa kar su wutar mini da ita, Allah ka kare mini ita a duk inda take ya rabbi ka taimaka mana kan makiyya mu... " ya fad'a cikin mawuwacin hali...

Sannan ya tashi yayi gaba domin nemo ta, yana barin wajen Jawahir na bude idon ta sama-sama take jin kamar sautin kuka da tafiya yunkurawa tayi da nufi magana amma ina sai taji bakin ta a rufe take wani tsoro ya tsarga mata, ta shiga kici-kici ko zata samu wata dama amma ina a banza tana cikin wannan halin ne ta jiyo murya Imran yana kiran ta iya k'arfin sa..

Bata san lokacin da tayi wani murmushin dadi game da k'walla da suka subuce mata a lokaci guda ba, aiko ta shiga cewa " umm. Ummm umm g.a.n.i.n.a.n" amma ina muryar ta bata fita gashi wajen babu wani haske haka kafar ta takalmi d'aya ya rage kawai sai fashe da kuka me cin rai..

Jameela gani duhun dare ya fara tace" Brother bana jin Jawahir zata iya shigo wa har nan wajen me zai hanna baza mu koma da baya ba watak'ila mu same ta a can." ta fad'a hakan ko Allah zai sa ya yarda ta samu hanyar guduwwa gida..

Aiko babu gardama suka juyo duk da yana ji a jikin sa Jawahir na waje, hkaa suka kara lin'kowa zuwa baya yana tafe kamar mahukaci sai dube-dube yake bai kuma fasa kiran ta ba a haka har suka karaso gindin bishiyar nan..

Jawahir ta shiga motsi da duk kan 'karfin ta tana umm umm hmmm hmm had'in da saki nishi da k'arfi, ko Allah zai sa su jiyo ta amma me......



Allah na gaji kawai zan ha'kure sai na dawo din
Tunda ba kwa so,
Comment din ne ya gagare ku.?x???x???x???x???x??

Comment
And
Shared
Please


Mrs Abubakar ce?x ?
[8/20, 11:18 AM] Mrs Abubakar ?xR?: *?x ?DA BAZARMU WRITERS ASSOCIATION?x ?*

*~we are here to make you happy, smile, educate and to realized that we are best among all.... DA BAZARMU MUKE TUNKA'HO~*


*?x  ?xR?BA SO BANE ?xR??x  *
( *_CUTA CE_* )




*_STORY_ $*
*_WRITTEN BY_*
*HUSAINA B.ABUBAKAR*

*(Mrs Abubakar)*





LITTATTAFAN NA!

*'YAN BIYAU KYAUTAR ALLAH NE*
*HAD'IN ALLAH NE*
*KA MANTA DANI*
*KUN CUCE NI*
*BANYI DACE BA*
*BA SO BANE*...

*Book 2*

```Ina jin dadin comment din ku sosai BASO BANE GRP 1 ALLAH YA BAR K'AUNA```


1???3????~ 1???4???


BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM


Har sun gota wajen da take, dabara ce ta fad'o mata aiko ta zame ta'kalmin k'afar ta ta shiga bubuga k'afa tana turzawa game da sakin wani irin kuka har yanzu tana cewa umm umm hmm..


Cak Imran ya tsaya yana kasa k'unne jin kamar motsi a bayan su cikin sauri ya juya Jameela za tayi magana yayi saurin d'aga maya hannu, sauti yake ji kama a sama bishiya kan sa ya d'aga sama amma bai ga komai ba kawai sai ya juya zai wuce ya sake jin kamar kuka ake ai da sauri yayi wajen tana shafa bishiyar game da d'aga kan sa sama duk da babu abinda yake gani sai duhuwar ganyayaki, motsi yake ji sosai aiko ya fata takawa a hankali yana lai'kawa tsam ya tsaya gani mutun d'aure yayi futufutu da k'asa.


Jameela ta matso cike da mamaki tana kare mata kallo can tace" brother wanna kamar Jawahir ce ai.." ta fad'a da mamaki.

Imran ya ma kasa magana jikin sa sai rawa yake cikin sauri ya cire mata abinda dake bakin ta aiko ta shiga tari babu k'au-'kautawa jikin sa na rawa ya since mata d'aurin dake jikin ta yanayi yana share 'kwalla dake zubo mai, Jawahir da ta gama galabaita ai tana jin ta a sake ta fad'a jikin sa tana sakin wani marayan kuka...


IMRAN ya rungume ta da kyau a jikin sa shi ma k'walla na zubo mai na tsantsar tausayin kan su..

Jameela tayi karfin hali cewa" ya kama ta muyi mu bar wajen nan sabida a ko wanne lokaci wa y'anda suka ajiya ta zasu iya dawowa.."

Ba su sake magana ba Imran ya d'auki Jawahir tamkar jaririya suka wuce ko wane da abinda take sa'kawa a ran sa, a haka har suka isa inda motar su take Jameela ta shiga ta ta, inda IMRAN da JAWAHIR suka shiga car d'aya basu wuce ko ina ba sai gida har yanzu Jawahir ba tayi magana ba..

Bari su wajen babu jimawa Nabila da ma'karraban ta suka iso wajen cike da mumunan nufin su, sai dai abin takaici babu Jawahir babu dalilin ta wannan abun ya fusata Nabila nan take ta shararawa ogan cikin su mari cike takaici..


A cikin gida kuwa Adda mairo da Adda Samira a zaune ga khadija dake gefe sai iyaye maza dake d'aya gefen, duk wanda ka kalla a cikin su zaka iya fahimtar halin da yake ciki domin gaba daya fuskar su babu an'nuri ko wanne da irin tunanin dake ran sa...

Can Baffa Abdullahi yace" yaran nan ina ji a jiki ba lafiya domin sam ba sai kai wa irin wannan lokaci a wajen, abin mamaki kuma shi ne duk wayoyin su ba sa shiga gaba daya su ukun.." Ya fad'a hankali a tashe.

Baffa Adam yace" kuma ance ko wanne da car ya fita.."

Shi dai Baffa Nafi'u bai ce komai ba dan yayi zurfi cikin tunanin..

Suna cikin haka ne su IMRAN suka shigo ko wanne sa fuska babu walwala ga Jawahir a hannu kamar wata gurguwa, a tare suka mik'a Adda samir tayi kan Jameela tana rok'o ta tace" ke lafiya kuwa kuka shigo mana gida kamar wa yanda akan ma sane?" ta fad'a cikin tsoro da furgici...


Su Baffa kan IMRAN su kayi ko wanne da kalar tambayar da yake mai, baya da duba jikin sa da suke Baffa Adam ne ya amshe Jawahir dake hannu Imran yana cewa" ita kuma me ya sa me ta? " akan kujera ya sauke ta yana duba ta gani yanda tayi futu-futu da k'asa ga ido dake a kumbure sai ya d'ago da sauri ya kai kallon sa ga Imran yace" kayi magana ma me kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login