Showing 1 words to 3000 words out of 28383 words
Chapter 1 - MANYAN MATA BOOK 1 COMPLETE BY Hadiza Barau Gidan Iko.docx
MANYAN MATA
1
Na
Hadiza Barau Gidan Iko
(Maman Assibi,
Matar Aminu Idris)
08035191669 – 08078500055
Haqqin Mallaka (M) Gidan Iko
Copyright © Gidan Iko 2019
GODIYA GA ALLAH
Allah Ina godiya da baiwarKa marar a dadi a gare ni, ba ni da bakin godiya sai dai fatan in tabbata a cikin salatin Annabi, wanda na ba wa kyautar raina da rayuwata abadan da’iman.
KYAUTARWA
Ga duk inda masoya Annabi suke a faxin duniya, ina qaunarku saboda qaunar Annabi da ku ke, Allah Ka yarda mu so Annabi (S.A.W).
YABAWA DA JINJINAWA
Ga Nafi’u Salisu, jagoran tafa rubutuna ya fito rangaxaxau, Allah Ya qara qwarin ido, Amin.
TUKWICI
Ga Hadizatu ‘yar’uwata. Ina miki addu’a da fatan Allah Ya yarje miki, Ya lumunce miki saboda qaunar Annabi (S.A.W) da ki ke Maman Zee-zee.
SADAUKARWA
Ga matan da suke haquri da duk wani qalubale na ‘GIDAN AURE’, suka yi haquri suka jure, waxannan su ne ‘Manyan Mata.’
MANYAN MATA NE…
Ummi Sulaiman Sale (Aisha) xiyata ta kaina
, Zainabu M. Sani (Maman Jinior) mata ga Awaisu, Aunty Salima Lambobi (Sabuwar Marubuciya), Zainab Lawal Abdulqadir Lambobi, Aunty Binta Lariya (Maman Sister Mawaqiya), Hadiza Uwar-biyu (Maman Twins), Mariya Lawal Aja, Lubabatu Ali Mai Chanji.
KU NE MANYAN MATA…
Hajiya Abu (Maman Auta) Marubuciyarmu.
Malama ‘Yar Fatin su Idi (Marubuciyarmu)
Da dukkan Makarantanmu, da ma su (Renting) a cikin gidaje, da ma su shagunan littattafai.
GARGAXI
Ban yarda wani, ko wata ya juya min labari ba, ta hanyar wani abu ba da yardata ba. Haka ma ban yarda a watsa shi a
Social Media
ba. Babu mai son ya aje abin shi a xaukar mishi ba da izininsa ba, don haka a guji satar fasahar ‘yar Gidan Iko, domin yin hakan babban laifi ne a dokar qasa.
BUGAWA A COMPUTER:
NAFI’U SALISU
08038981211 - 08093248661
Shimfida
Kyawunta ya fi komai xaukar hankali
tamkar zinari ko madubi. Fuskarta ta sha
make up
irin na kanti.
Sanye take da doguwar rigar
Passion
ta yadin
Pear up
. Riga ce doguwa wadda aka matse qirjinta aka saki hannuwanta.
Kanta babu kallabi (xankwali) sai dogon gashinta da iska ke kaxawa. Kalar rigar
Pink
ne da
Yellow
, sai takalminta
Plat
na kamfanin (Win win), ‘IPAD’ ce mai girma a hannunta.
Tana tsaye bakin titin inda ta dubi ‘IPAD’ xin hannunta wadda agogon jikinta ya nuna mata qarfe 11:55 PM (sha xaya da minti hamsin da biyar na dare).
Ta xan ja tsaki tana duban titin da son ganin motar da zata taho, kamar daga sama wata qatuwar mota ta Kamfanin ‘FORD’ ta danno tamkar zata tashi sama.
Da sauri ta soma xaga mata hannu alamar
‘Wait! Wait!! Wait!!! Tamkar motar ba zata tsaya ba, har ta wuce sai kuma ta dawo baya ta tsaya daidai inda take tsaye.
Gilashin motar ya sauka qasa, kasancewar shi da tintak. Matuqin motar ya zubawa qirjinta da ke bayyane ido.
Ta sunkuya saitinshi tana murmushi wanda take siye zuciyar maza.
“Sannu Chairman.” Ta ce da shi.
Ya amsa da sauri saboda qamshinta da ya shaqa. Ya zuba mata ido.
“Ya ya dai Baby?” Ya tambayeta, idonshi a kanta. Tayi war da ido.
“Idan ba zan takura ka ba
,
I want lift with your car
.”
“
Oh, no problem, go ahead
.”
“Na gode fa.” Ta faxa tana qoqarin buxe murfin motar.
Ya fito da sauri yana faxin.
“A’a bari in buxe miki mana.” Ya faxi hakan yana son qare mata kallo, don ji yake tamkar ya haxiyeta. Ya buxe mata ta shiga ya rufe. Sannan ya kewaya ya shiga ya yi wa motar
key
ya harba ta titi tamkar zai tashi sama.
Qamshin turarenta ya game motar, sai ya bada wani kalar qamshi kasancewar shi ma nashi turaren mai qarfi ne, ga kuma
Air Freshner
xin motar.
Ya dube ta da murmushi, yayin da take latsa ‘IPAD’ xinta.
“Ina muka nufa ne?”
Ta dube shi itama da murmushin a fuskarta, ta faxa mishi.
“Uhum! Kadarko Estate zan je.”
“Ok! Amma me yasa ki ka fito ke xaya a irin wannan lokacin? Sha biyu fa!”
“Wallahi ban so haka ba, wanda nazo wurinshi ne ba ya nan. Nayi zaton bai yi nisa ba shi yasa na jira shi na kira wayarshi kuma a kashe, shi ne naga gara in juya kawai. Ni kaina tsoro nake ji.”
“Ki ce da kin iske shi da ban yi sa’ar ganinki ba kenan?” Ya faxa yana kashe mata ido.
Ta gama lura da shi xan hannu ne a harkar, sai itama ta kashe mishi idon.
“Uhum! Kusan haka ne gaskiya.”
“Ayya! Ki ce ni Allah Ya bani a sama kenan?”
“Uhum! Anya ko?”
“Eh mana, ba ki san kin fi
Diamond
qyalli ba?”
“Uhum!” Ta faxa tana danna ‘IPAD’ xin hannunta.
“Ba ki faxa min sunanki ba.”
“Uhm! Sunana Tsaiba!”
“Hahahaha! Har da zolaya kuma?”
“Ba ka yarda ba ne?”
“Gaskiya ban yarda ba. Haba dai Tsaiba, sai ka ce wata Bararoji.”
“Ai ko naga Tsaiba suna ne me kyau.” Ta faxa tana kallonsa.
“Haka ne. Amma don Allah faxa min sunan, ko ba ki yarda da ni ba ne?”
“A’a ba haka ba ne, kawai dai sunan ne yake da tsada.”
“To an zo wurin, har za a wuce wurin.” Rafar dubu xari ya xora mata a kan cinyarta.
“Au! Ban tambayi nawa ne kuxin faxar sunan ba? nawa zan qaro a kan wannan?”
“Wannan sun isa.” Ta faxa tana kallonshi.
“To shi kenan, ina saurare.” Ya faxa idonshi a kanta.
“Sunana Beeba!
Habiba kenan, amma ka bar kuxinka tunda kai ma kayi min
lift
.” Ta faxa tana xora mishi kuxin a kan cinyarshi.
“To na gode, amma ai bayan tiyar akwai
wata cacar. In roqi wata alfarmar za ki yi min?”
“Me zai hana?” Itama ta tare shi.
“Ina so in maye gurbin wanda aka zo wurinshi.”
“Wannan ai ya fi ruwa sauqin sha, muje.”
“Ok! To ba ni
account number
xin ki in yi miki wani karambani.”
Ta karanto mishi yana shigarwa a wayarshi. Take taji
alert
, tana dubawa taga kuxin da aka jero.
Ta dube shi cikin mamaki.
“Na meye wannan kuxin?”
Yayi murmushi. “Na kyauta ne, ko sun yi kaxan na qaro miki?”
“Sun dai yi yawa. Gaskiya ka rage.”
“To shi kenan bari in rage.”
Kawai sai taga ya qara turo wasu kuxin. A zuciyarta ta ce,
‘Maza kenan mayaudara!’
Ta dube shi kafin ta ce wani abu ya tare ta.
“Kar ki ce komai, ni in ina son mace ba ni da wayo, raina ma ina iya ba ki shi.”
“To na gode sosai
.” Ta faxa da murmushi.
“Ina ki ke so muje, hotel ko Guest House xina?”
“Duk in da ya yi maka muje kawai.”
“To muje hotel xin saboda sirri, kin san ni sanannen mutum ne wanda kowa ya sani, dole sai da sirri.”
Sai yanzu ta shaida shi, ashe fa Senator Shehu Usman Shehu ne na Babban Birnin Tarayya Abuja, me riqe da muqami biyu, wato Senator kuma jinin Sarauta.
Don haka sai ta bar mamakin kyautar da ya yi mata.
“Uhum! Sai fa yanzu na shaida ka, ina ta tunanin inda nasan fuskar ne sai yanzu na tuna.”
Shima ya yi murmushi “Kar dai ki ce min kema kinm sanni?”
“Waye bai sanka ba? ai ko yaron goye ya sanka, in bai san suna ba to yasan fuskar.”
Da haka suka iso Hotel xin
Fist Class
me tsadar masauki a garin na Abuja. Xaki me lamba sha biyar a hawa na biyu.
Qayatuwar xakin ya isa a bada labari, koda yake ma su abu da abun su, wai ‘Yar Garuwa taga hadari.
Gaba xaya ta gama kixima shi da kyawun fuskarta, zuwa zatinta, da surarta, musamman qamshin da ke fita a jikinta.
Ya zuba mata ido.
“An tava faxa miki kina da kyau?”
Ta kaxa kanta tana mai cewa, “A’a.” Ya numfasa sannan ya ce mata.
“To ni zan faxa miki duk da ban yarda ba
, kina da kyau na gaban a bada misali.”
Tayi murmushi ta ce, “Na gode sosai.” Ya riqo yatsunta
ya matsa, yayin da taji tamkar ta qurma ihu saboda tsanar da tayi wa maza.
Amma sai ta doje tana aika mishi da wani rikitaccen kallo wanda ya ida kixima shi.
Ya miqe, “Bari in watsa ruwa in fito sai kiyi min wannan kallon me shirin sanya ni suma.”
Tayi murmushi, shi kuma ya faxa banxakin inda ta bishi da wata matsiyaciyar harara cikin matsanancin baqin cikin da ya jima da xarsuwa a ranta.
Minti sha biyar ya fito daga banxakin, babu komai a tare da shi sai gajeren wando. Kallo xaya tayi mishi ta duqar da kanta.
Kyakkyawan mutum ne wanda ya fito daga qabilar Fulanin Yola, shekarunshi ba za su haura talatin da biyar ba. Ga kuxi ga mulki, ga kuma sarauta. Sai dai kash! Ya kusa zama tarihi shi da dukiyarsa da mulkinsa, domin ko ita xin ‘KARA DA KIYASHI’ ce xaukar marar sani.
Ya iso dab da ita ya zauna, ya zuba mata ido. “Uhum! My Beeba, kalle ni mana.”
Tamkar ta rusa ihu, musamman da ta kalli qirjinshi taga gashin da ke kwance luf! Wanda ya tuno mata da wani shuxaxxen al’amari.
Bata ankara ba taji shi a fatar bakinta yana kissing xinta. Duk da tsoron da ya mamayeta sai da ta nuna mishi itama xin gwana ce a harkar duk da ba gwanancewar tayi ba.
Tana dai so ta cika buri da alqawarin da ta xaukarwa kanta na son qarar da duk wani namiji a duniya. Kai kaf xin mazan duniya sai ta kashe su, wallahi sai ta kashe mazan duniya.
A take ta gama kama shi ya zo hannu, duk da ba qaramin yaqi tayi da zuciyarta ba. kanshi a kan qirjinta yana riqe da hannunta, xayan hannun kuma yana wasa da dogon gashin ta, yayin da ya maida hasken xakin ya koma
deep night
.
Hasken
ya ragu sosai inda tsoro me tsanani ya shigeta saboda
jin yana son rage mata kayan da ke jikinta, wanda in dai har hakan ta tabbata to ko shakka babu zai yi nasarar ganin bindigar da ke soke a gefen qwivinta, wanda bata fatan ya gani.
Da sauri dabara ta faxo mata, ta kai bakinta a nashi tana
kissing
xinshi wanda hakan ba qaramin tasiri ya yi ba.
Gaba xaya ya sallamawa, abu xaya sai yadda tayi da shi. A lokacin ne lamarin ya ke shirin faruwa, ko ma ya farun.
Cikin kissa irin ta macen da tasan kanta, ta zaro bindigar daga qwibinta ta sakar mishi harsashi uku a jere a cikin cikinshi, kafin tasa filo ta danne kanshi da qarfi.
Duk da babu haske a xakin, hakan bai hanata ganin jinin da ke vulvulowa a cikinshi ba, ya ci gaba da mutsu-mutsun neman agaji har ya ce ga garinku nan.
Jin ya daina motsi yasa ta janye filon daga kanshi ta kuma kunna hasken xakin ta zuba mishi
ido tana kallon gawarshi, kafin taja tsaki ta xauko bindigar ta wulwula ta a yatsunta ta soke a kwivi.
“Kai ne namiji na ashirin da uku waxanda suka shigo layin burina, kashe mazan duniya ban ma soma ba. Nayi alqawarin kaf xin mazan duniyar nan sai naga bayansu, matuqar ina numfashi tasa ‘IPAD’ xinta ta xauki hoton gawar kafin tayi sauri ta bar Hotel xin.
Shin me karatu za ka so jin abin da maza suka yi wa wannan kyakkyawar budurwar? To biyo ni a sannu a cikin littafin ‘MANYAN MATA.’
**
BABI NA XAYA
T
a saki ‘IPAD’ xin a kan kujera ta zauna javar! Tamkar an saki kayan wanki. Ta dafe kanta.
Deenar ta dubeta, “Ya ya dai Beeba?” Ta ce, “Lafiya qalau Deena, gajiya ce kawai.” Ta miqa hannu ta xauko ‘IPAD’ xin ta shiga duba hotunan ciki, ta soma dubawa xaya-bayan-xaya har ta gama dubawa, taja tsaki.
“Gaskiya
ba ki da qoqari Beeba, har yanzu fa ba ki yi qoqarin tankaxa qeyar maza hamsin lahira ba. Duba ‘IPAD’ xina ki gani sama da mutum xari da ashirin na aike da su qiyama, ina jin dai kina yi wa maza sauqi ne, me yiwuwa ba su qunsa miki baqin cikin da ya kamata kiyi ta tankaxa su qiyama ba.”
Rose ta shigo da kofin Tangaran a hannunta wanda yake xauke da ruwan
Cofee
me zafi tana kurva. Ta bi su da kallo.
“Ya aka yi ne naga kun yi jugum?”
Ta maida kallonta ga Beeba.
“Ya aka yi ne Bibalo?”
“Babu komai Indo-Aisha.”
Ta faxa tana murmushi, saboda sanin Rose bata son sunan na Aisha, wanda tace tayi bankwana da amsa shi.
“Zan xurawa uwarki ashar Beeba. Bana so! Sunana Rose, ai tunda na gane ku xin Musulmi mayaudara ne na fice daga cikinku, na koma kiristancina.
Kuyi Azuminku, kuyi sallarku, ni kuma Lahadi tayi in fice zuwa coci na.”
Deena ta miqa mata wayar Beeba.
“Duba don Allah mutum ashirin da uku ta iya jarumtar aikawa lahira. Anya ko Beeba da gaske take a kan alqawarinmu na son ganin bayan kowanne namiji?”
Rose ta karvi wayar ‘IPAD’ xin tana kallon hotunan. Ta aje kofin
Cofee
.
“Da gaske take mana Deena, in ba da gaske take ba ai ba za ta yi wannan qoqarin ba. Ina zaton dai kamar yadda aka biyo aka yaudareta ne itama take bin hanyar don maida martani, ko Beeba?” Ta faxa tana kallon ta.
Ta xaga mata hannu alamar jinjinawa. “Da kyau Rose, kin fahimta ashe!”
Deena ta dube su “Haka ne, ina jin a duk duniya babu wanda ya kai ni shiga haxarin xa namiji, shi yasa nafi me kora shafawa. Da na mutu ko da an kashe ni da ba qaramar asara nayi ba. Shi yasa ni ke jin zan ginawa maza Jahannama a duniya.”
Rose ta miqe tsaye tana duba agogon hannunta, biyu da rabi na dare.
“Kin ga Zubaida uwar surutu tashi mu wuce dare na tafiya, tunda Beebar ta iso.”
Suka miqe a tare suka sauya shiga da wasu baqaqen dogayen riguna, tare da voye fuskokinsu da fuskar roba (mask). Rose taja motar suka harba a Titin tamkar zata tashi sama saboda gudun da take.
Kai tsaye suka doshi dogon gidan me bene. Rose ta gyara fakin ta yadda da sun fito za su arce.
Deena ta fito da wasu makullai ta doshi
Gate
(babbar qofar) gidan, ta soma zura makullin. Cikin sa’a ta buxe suka xure ciki.
Beeba ta ce, “Don Allah Deenar dubi gidan nan tamkar ba za a mutu
.”
“Yo ba dole ba Beeba, sun handame kuxin talakawa sun baro mahaifarsu sun zo Abuja suna gina Gidaje da kuxin talakawa.”
“Aiko dai ki ga maza, ni da matan duniya za su mara min baya ai da sunan xa namiji ya vace a duniya bare kamanninshi. Amma dai muje zuwa, wallahi sai na cinye qwanjin xa namiji na taune qashinshi koda zan zamo ni xaya tal babu me mara min baya! Bare ma gani ga Indodo.”
“Za ki ci ubanki Beeba, matuqar kina liqa min sunan da na ce na zave shi a da na kuma qi shi a yanzu..!”
“Wai kun mance abin da ya kawo mu ne ku ke surutu kamar kuna gidan ubanku?”
“Eh, masu gidan mu ke so su zo su marabce mu su kuma san da zuwanmu.” Cewar Deenar. Ita ko Beeba cewa tayi.
“Lallai matan gidan nan watan shiga takabarsu ya tsaya tunda yau Rose ta ziyarce su.”
“Uhum
! Ai mu ba ma faxa da mata koda ko suna yankarmu. A yau in da babu maza to da muma muna
one side
!”
Suka miqe a tare suka danna kansu cikin gidan tamkar dai sun san ta kan gidan, kasancewar shi me sashi-sashi da yawa.
Rose ce a gaba kasancewarta marar tsoro. Kamar daga sama suka jiyo kukan qaramin yaro irin me rigimar nan a tsakar dare. Kai tsaye suka doshi inda kukan ke fitowa. Uwar yaron ta farka
da son sanin abinda yake so, inda ya sanar da ita
cornflakes
yake so.
Ta soma rarrashinshi tana haxa mishi
cornflakes
xin, kawai sai ganin mutanen uku tayi fuskokinsu voye a fuskar roba. Ta xauki salati a tsorace tana kyarma.
Deena ta dafata da faxin “Sorry Madam, kar kiji tsoro ba wurinki muka zo ba, jagora kawai za ki yi mana inda turakar maigidan take…”
“Wallahi-tallahi Maigidan ba ya qasar nan…”
“Ina yaje?” Rose ta tare ta.
“Ya je Sweezland, yau kwananshi sha biyu.”
“Oh my God!” Rose ta faxa “Kai mu ma’ajinshi.” Da sauri matar ta nufi wucewa inda Deena ta tsayar da ita. “Ji mana.” Ta dawo da sauri jikinta na ta vari. “Ya ya sunan yaron nan?”
Ta saita shi da bindigar dake hannunta, inda matar ta qanqame yaron.
“Don girman Annabi kar ki tava min shi.” Ta faxa hawaye na fita a idonta. Deena ta janye bindigar daga saitin yaron.
“Ai tunda ki ka ce Annabi na qyale shi, amma wallahi da sai dai ki sake haifar wani, don mu nan faxa muke da duk wani namiji koda ko yau uwarshi ta haife shi, saboda nan gaba zai zama xan kunama gara ya mutu.”
“Bar shi Deena, muje turakar Maigidan.” Faxar Beeba. Matar tana qanqame da xanta ta wuce gaba har inda sashin Maigidan yake.
Ta buxe musu ta kuma nuna musu ma’ajin shi na kuxaxe. Da sauri Rose ta soma jido daloli a
cikin (Ghana must go). Sai da suka jede su tas kafin su baro gidan.
Rose ta figi motar da qarfi ta harba ta kan titin, bayan Deena ta sanar da matar ba sata suka zo ba, Maigidan suka so gani, gani kuma ba na alheri ba.
Amma tunda ba su same shi ba to za su yi gaba da kuxinshi kasancewar shi shugaban Majalissar Dokoki ta Abuja.