Showing 12001 words to 15000 words out of 28383 words

Chapter 5 - MANYAN MATA BOOK 1 COMPLETE BY Hadiza Barau Gidan Iko.docx



Bisa dole kuxin suka fito ta aljihun Tukur Sambo. Ba kuma fitar kuxin ne yafi damunshi ba

irin yadda ta qulla mishi sharrin da bai da ruwan wanke kanshi bare abokan aikinshi suga haskenshi. Takaicinsa xaya, yadda za a riqa kallonshi da abinda bai tava kawowa zuciyarshi aikatawa ba, lallai ya yarda babbar mace ce. Lallai sai a gaida manyan mata.

Sai da ta kwana biyu kafin ta gyagije, inda aka xora a kan inda aka tsaya. ‘Yan Jarida na ta rawar jikin xaukar rahoton wadda tayi kisan Kayode, a cikin kwana na uku ne aka miqata ga kotun da ke riqe da ragamar

case

xin kisan Kayode, wadda bata ko ja ba ya yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan an karanto laifinta na baya

wanda idan aka haxa su ta ko ina ba sauqi.

BABI NA HUXU

“N

i fa dama jikina bai bani ba, ban yarda da Xansandar nan ba wallahi. Da Rose ta biye ni da bata xaga wayarshi ba, bare ta taka taje in da yake. Bana ko tantama ‘Gadar Zare’ ya shirya mata, ta kuma afka.”

Deena ta dubi Beeba bayan ta dire maganarta. “Sai yanzu na gano mugun qullin da ya kwance a kan Rose, wannan Xansandar duk yadda aka yi ya san fuskar Rose a matsayin

Criminal

, me yiwu wa a kisan Kayode, me yiwuwa a matsayin ‘yar gidan Yari. Wadda ya biyo ta hanyar da ba za a gane ba, wato bariki. Inda yayi amfani da hikimarshi ta aiki ya kira ta ta taka da qafarta ta kai mishi kanta.”

Beeba ta xora da nata batun. “Babban tashin hankalina da Rose tayi nasara a kan mutumin can to da bata yi daxewar da tayi ba. Shirunta yana nufin shi ne ya yi nasara a kanta. Bana jin ta makomar mu nafi jin ta yadda za a yi mu maidawa Rose halaccin da tayi mana irin wanda take buqata a yanzu.

Meye abin yi Deena?”

“Kar Allah yasa hakan ma ta kasance Beeba, mu qara jinkirtawa mu gani, me yiwuwa ko Rose

xin ta nufi wani wurin wanda ya sa ta daxewa…”

“Matuqar da ta gama da tsinannen mutumin can to da ta dawo gida. Amma mu kyautata zato a kanta da kawunanmu.” Suka yi jugum suna jimami tamkar an yi musu mutuwa. Koda yake a yadda suke a yanzu ba su da kowa sai kawunansu, duk wanda zai mutu ma ba damuwarsu ba ce, in dai ba a kansu ba.

Don haka suke jin shirun Rose ya fiye musu jimami a kan mutuwar mutanen duniya. Suka yi tsit kowacensu da abin da take saqawa a ranta. Ko ruwa suka kasa kaiwa bakinsu. Deena ta miqe ta isa kan

Centre Table

ta xauko wayarta ta doka kiran wayar Rose.

Sai dai wayar a kashe, ta sake kiran don tana zaton ko matsalar

Network

ne, amma shiru ta sake babu ralabari. Ta dubi Beeba, “Kin ji wayarta a rufe.” Beeba ta bita da ido “A rufe ki ka ce?” Ta ce, “Wallahi ru fe take. Wayarta a cike take da chaji bare ko ace ya sauka. Shi kenan ta faru ta qare. Shi kenan mun shiga uku Rose ta shiga hannu.” Ta faxa a kan kujerar yavar jiki a sanyaye.

Beeba ta zabga tagumi aka rasa me tsinkawa. Idonsu buxe da son ganin Rose xin, kunnensu buxe da son jiyo amon qarar takalminta amma ina! Ba su yarda ba sai da qarfe taran dare ta doka babu Rose babu labarinta. Da sauri Deena ta miqe tsaye ta suri makullin mota, ta dubi Beeba.

“Tashi muje, ai na tuno inda ya faxa mata zata same shi, wato Sheraton otal.” Da azama beeba ta miqe, sai dai kowacensu ta voye fuskarta da niqaf. Haka suka fice daga gidan suka doshi Sheraton.

Sai dai ba su da dabara ko azancin sanin inda masaukin su yake. Idonsu a kan masu shige-da-fice, fatansu bai wuce yin ido huxu da Rose ba. sai dai ba su ganta ba.

Can xaki me lamba ta sha biyu taga wasu maza sun fito sun shiga motarsu sun fice. Daga kansu ba su sake ganin wanda ya fito ko ya shiga ba, sai dai wani da ke ta hidimar kawo abin da oganshi ya aike shi kawowa.

Ba su bar harabar otal xin ba sai sha biyu saura, inda suka tabbatar da aikin gama ya gama. Suka dawo gida inda kowacensu ta xaura alwala dama su xin gwanayen tsayuwar dare ne. haka

kuma gwanayen Azumin Litinin da Alhamis

, sai fa wadda baqonta ya zo ta sha.

Amma babu Litinin xin ko Alhamis, don haka suka xaura alwala suka tada sallah koda wai ba su runtsa ba sai da suka sallaci Asubahi. A kan gadon Rose Deena taga bindigarta, wadda ta manta saboda sauri.

Ta ce cike da mamaki, “Haba! Ni dai na san ayi haka!” Beeba ta juyo “Mene ne?” Ta ce, “Kin ga bindigar Rose ta manta ta, wadda bana ko shakka

rashinta ya ida jefa ta a shiga uku. Don da ta tafi da ita to da bata shiga halin da ta shiga ba.”

Beeba ta sauke ajiyar zuciya. “Wallahi Deena barcin nan bana jin shi, zan dai kwanta ne in samu damar tunano yadda za ayi mu lalubo yadda Rose ta vata. Babbar matsala da ba mu san in da take a yanzu ba. Ban da tabbacin idan Rose ta sake komawa a hannu a yanzu zata kuvuta, domin ko abin ya zamo

Double

.”

“Kar ki damu Beeba, riqe Rose yana nufin zamu ware qwanji ga maza. Wallahi tallahi riqe Rose yana nufin saukar annoba ga hukumar duk da tayi ruwa tayi tsaki a kan kamun Rose. Mu bar wa gobe har mu samo mafita.”

Haka suka kwanta da saqar zuci a ransu, maganar barci ba ta ma taso ba. Washegari Deena ta gama yanke hukuncin abin yi. Ta dubi Beeba “Kin san abinda na yanke Beeba?” Ta ce, “Sai kin faxa.” Ta ce, “Wancan D.P.O xin da ya yaudari Rose, na gane D.P.O ne na yankin Suleja, don haka ina ga zanje in samo yadda aka yi Rose ta vata. Zan je Suleja in nemo shi don na san ba zai yi wahalar samuwa ba.”

Beeba ta ce, “Deena ba ki gudun allura ta tono Garma?” Ta ce, “Bana shakka Beeba, koda allura zata tono abin da yafi Garma, to na shirya. Rose bata cancanci mu zuba ido ta shiga matsala irin haka in dai ana maida alheri da alheri, kin manta ne Beeba in tuna miki…?”

“Ban manta ba, ba kuma zan manta ba Deena har in komawa Mai duka (Allah), ba don Rose ba da muna Kurkuku a xaure a matsayin xaurarru, ba don Rose ba da ba mu samu ‘yancin da muka samu a yanzu ba. Rose ita kaxai ce gatanmu a wannan duniyar da mazaunan cikinta ba su da adalci, bayan iyayenmu Beeba ba mu da kamar Rose a soyayya! Don haka mu tashi Beeba abin duk da Rose ya sama mu ma ya same

mu, in daxi Rose ke sha mu sha tare da ita, idan wuya ma take sha mu sha ta tare

.

Amma ba zan bari Rose ta sake faxawa wani bala’i ba a rayuwarta. Ke ni na zavi in fansar da raina da rayuwata a kan Rose.” Beeba ta dafa kafaxar Deena ta ce, “Nayi miki alqawari Deena zan iya yin duk abinda za ki yi ko ma fiye da ke, matuqar hakan zai nuna maida alherin da Rose ta yi mana.

Don haka ina ga mu bar wa gobe Litinin kasancewar yau Lahadi babu aiki, me yiwuwa ba zamu samu ganinshi ba saboda hutun qarshen mako. Ko ya ya ki ka gani?” Ta ce, “Wannan shawarar yaki tayi Beeba, mu bar wa goben. Amma kafin nan xebo kuxi muje muyi sadaka da niyyar Allah ya bamu nasara a kan niyyarmu, dama mun kwana biyu ba mu je gidan Marayu da masu tavin hankali ba, sai muje yau ai.”

Beeba ta xebo kuxi na Naira dubu suka miqi hanyar gidan marayu, inda suka kai tallafin kuxi. Dama sun saba zuwa har sun yi sabo da wasu yaran, haka ma ma’aikatan. Sai manyan mata in ji wata ma’aikaciyar gidan. Kuxi sosai suka bayar kafin suyi sallama da gidan, inda wasu

matasa suka iso suna faxin “Sai manyan mata, Allah Ya ba ku abinda ku ke so.”

Deena ta watsa musu dubu-dubu masu yawa, suka bi suna wawaso. Har da tsofaffi suma sai jinjinawa manyan mata suke suma sun sami nasu kason. Deena taja tsaki. Beeba ta dube ta ta ce, “Ya ya dai Anti Deena?”

Ta ce, “Uhum! Anti Beeba matsalar ai bata shige maza! Ban da muna kamun qafa ga Ubangiji da son cika buri me zai kai ni ba maza kuxina? Ai har tsaffin can ba zan iya basu sisina ba. Amma ba komai, Allah ya karva buqata kuma ta biya nufi.”

Beeba ta ce, “To amin. Amma fa maza sun yaudare mu hawa-hawa. Ai Allah dai ya fiddo mana Rose lafiya, ita ce wadda taga yaudara bayan wadda aka yi mata da farko, shi ne tsinannen D.P.On can ma

ya yi mata wadda ta sata a shiga uku!”

“Uhum! Ai ko dai bari Anti Deena, ai dab ni ke da ganawa maza azaba a duniya.” Da haka suka isa gidan masu tavin hankali. Abin ban tausayi, mutane ba su cikin hankalinsu. Wani abin kokawa wani abin darawa, kai Allah Gwani ne a kan komai.

Suka ba da taimako da addu’ar samun sauqi ga marassa lafiyar suka juyo gida. Qarfe tara suna a falo inda

TV

ke ta vavatu

, ba don suna fahimtar abin da ake faxa ba. Deena ce ke cin jalof xin taliya wadda taji tsanwan wake da qwai da hanta, yayin da Beeba ke zuqar madarar shanya.

Kamar daga sama aka nuno fuskar Rose a cikin allon

TV

, inda take sanye da sarqoqi hannu da qafa, ana ta shelanta ita ce wadda ta kashe Olukayode, inda dama can tsohuwar mai laifi ce wadda Kayoden ya tabbatar da kamunta, inda ta aika da shi qiyama daga qarshe dai an yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya!...

Su duka biyun suna gaban

TV

tamkar zasu yi jarumtar finciko Rose xin daga cikin

TV

n. “Qarya ne wallahi! Wallahi qarya ne Rose ba zata mutu ba, ko za ta mutu to mutuwar Allah ba sanadi ba. Maza ba za su tava yin

nasara a kanmu ba. Sai Rose ta xauki fansar abin da aka yi mata ko zata mutu!”

Ita ko Beeba kasa cewa komai tayi saboda fargaba. “Me ya dace muyi Deena?” Ta ce, “Komai ma! Don ganin mun kuvutar da Rose a ciki, ke har da tada yaqi a garin Legos me

yiwuwa a maimaita yaqin Biyafara a Lagos. Na rantse miki da Allah xaya, Beeba ba zan tava bari a yi wa Rose rauni ba bare aje ga fitar rai.

Ba za mu tunkari inda aka aje Rose ba sai dai mu bibiyi labaru da jaridu don tabbatar da ranar da suke ikirarin rataye Rose. To a ranar za a gane me qarfi tsakanin mu da su! Amma Rose ta dawo gida ta gama har mun xora daga inda muka tsaya.”

Hakan ko aka yi, suka bibiyi Jaridu da labarun N.T.A News, inda suka gano wai ranar Asabar me zuwa (nan da kwana shida) kenan. Qarshen tashin hankali sun gama shigar shi, amma duk da hakan bai hana su yin shiri na sosai ba.

Na gama tsara yadda abin zai tafi Beeba, kina ji na?” Ta ce, “Ina saurarenki Deena. Matsala xaya nake ga zamu fuskanta, ita ce rashin sanin inda zasu yi ratayar…”

Beeba ta katse ta, “Wannan ba matsala ba ce. Ni nasan inda ake yin ratayar, kema kin san shi ba ki dai san nan ne wurin ba. Ina wurin da muke kai bahaya a gidan kason qiri-qiri?” Ta ce, “Eh na gane shi fa.” Ta ce, “To nan ne. In da kin lura

da akwai wasu qugiyoyi biyu a cikin dajin sune ake sagale mutum.”

“To Alhamdulillahi, ko me zai zo da sauqi. Abin da na tsara kuwa shi ne

zamu je dajin mu voye motarmu a cikin ciyayi, mu kuma yi kwanto a cikin ciyayin. Motar da zata zo da Rose zamu kafawa tarkon qusoshi wanda idan ta taka su a hanyar zuwa wurin ratayar dole zata yi faci.

Idan kuma tayi faci dole za su sauko su qarasa zuwa a

q

asa

. Ta haka ne zamu soma yi musu xauki-xai-xai, ko ma mu buxe wuta

har mu samu nasarar guduwa da Rose, ina fatan hakan yasa muyi nasarar ko kina da taki shawarar?”

Beeba ta jinjinawa Deena da wankakkiyar qwaqwalwarta. “Kin gama komai Deena, sai dai fatan Allah ya bamu nasara. Lallai a gaida manyan mata.”

“Uhum! Beeba ai ba mu zamo manyan matan ba tukuna sai mun ji yadda muka rayu da irin yadda muka haxiyi takaici, muka mayar da martani shi ne muka

zamo manyan mata.”

“Lallai kam! Mu jira yi fitowar Rose kafin mu farkewa juna layar mazan mu don ina xokance da son jin yadda Deena ta rayu da

mijinta, da yadda Rose ta shigo musulunci a kan namiji ta kuma fita a kan abin da ya yi mata…



Ni kuma naki ni ke

so in ji.” in ji Deena. Ta ce, “Kar ki damu Deena, an kusa zuwa wurin har ma a wuce wurin.” Da haka suka yi ta tattauna batun, da kuma shiri na musamman a kan yadda za su tunkari ranar Asabar, da kuma Dajin na garin Legos.

Zuwa ranar Juma’a sun gama shirya komai, sai dai tsumayin wayar garin gobe Asabar, in da suka shirya yin sammako don isa da wuri. Sai dai me? Misalin qarfe goma da rabi na dare qararrawar da ke nuni da baqo a waje ta xauki qara carrr!

Suka yi saurin dubar juna a tare, suka saurara don tabbatar da shin qararrawar ta gidansu ce ko ko ta maqotansu ce? Can qarar ta sake xaukar amo, inda suka tabbatar da cewa ta gidansu ce ke qara. To waye?

Deena da tafi Beeba rashin tsoro ta zura hijabinta ta doshi hanyar waje…da sauri Beeba ta riqota tana faxin. “Kar ki je Deena, ba mu da alaqa da kowa bare ya neme u, ke kaxai ki ka rage min, me ki ke zato idan wani abu ya faru da

ke? Rabu da duk me danno qararrawar, can ya qaraci nacinshi yayi gaba.”

Deena tayi murmushi ta ce, “Babu abin da zai faru sai alheri Beeba, ba zan fara buxewa ba sai na leqa naga me dana qararrawar, idan ban yarda da shi ba zan rabu da shi.”

Beeba ta ce, “Yauwa, to haka nafi yarda da shi, ke muje ma tare don ba zan

tava bari ki kuvuce min ba.” Ta faxa, itama tana zura hijabinta tabi bayan Deena

.

Sai da suka leqa ta taga don ganin me son ganinsu. Abinda idonsu ya hango musu ne yasa suka qurma ihun qara a tare. Suka nufi

Gate

xin da gudu har suna shirin yin karo da juna.

Deena ta zura

key

xin ta buxe

Gate

xin kafin ta ida buxewa Beeba ta fice a sukwae inda ta rungumeta tana hawaye. Da sauri Deena ta ce, “Wa ni ke gani?” Tayi murmushi a wahalce “Ni ce dai ki ke gai Deena.” Ta kamo hannunta da sauri suka shigo ciki ta maida

Gate

xin ta datse

da

key

.

“Wacce irin godiya zamu yi wa Allah?” Ta faxa bayan ta durqusa a gabanta. Sai a sannan ta lura da ciwukan da ke jikinta. Ta ce, “Ah! Rose

me ya ji miki ciwo haka?” Beeba ta rungumo ta “Garin ya ya?”

Ta dube su ta ce, “Kuyi haquri, ina buqatar hutu. Mu shiga ciki.” Xaf suka xaukota ba su bari ta taka qasa ba, suka aje ta a kan

three seater

, ta kwanta jikinta na raxaxin ciwon da ke jikinta.

“Amma kar ki yi barci Rose, bari in kawo miki

Tea

me zafi ki sha tukuna.” In ji Beeba. “Ai ko na gode Beeba, kamar kin san ina buqata kam.” Da sauri Beeba ta shiga

kitchen

ta haxa mata shayi me kauri, kafin ta xora mata jalof xin makaroni wanda ya ji kayan haxi, irin su waken Gwangwani, da Alayyahu, da qoda.”

Deena ta shiga xaki ta xauko ruwan ideen da shanshanbale, ta shiga goge mata jinin da ya soma bushewa a jikin ciwon da ke kan dokin wuyanta da kafaxunta, da kuma bayanta.

Sai a kan goshinta, da kumatunta, wanda alamu suka nuna karkacewa ce.

“Wash! Wash!! Deena ba ki da Imani fa, wallahi da zafi sosai.” Deena ta ce, “Imanin kenan Anti Rose, ba ki san tarairayar ranki muke tamkar qwai a kan

tiles

ba?”

Ta ce, “Uhum! Ai dama nasan haka, ina can ina tunaninku a raina. Da ace na samu waya da na kira ku in ce kar ku tashi hankalinku a kaina, don ni da kaina ai na san ban shirya mutuwa ta silar wasu tsinannu ba, sai ta Allah tayi.

Ai an yi sake da aka bari wannan duniyar da mutanen cikinta marasa adalci suka bari na zama qwallon shegiya.

Yanzu zan soma ta’adi, yanzu rayuwar zata fara, yanzu ne maza za su shiga uku, musamman da maza biyu suka qaru a cikin waxanda suka yaudare ni.

Shegen D.P.O na Suleja da kuma Tukur Sambo.” Deena ta ziraro hawaye. “Mun shiga tashin hankali ba kaxan ba

Rose a kan rashin dawowarki kan lokaci, har muka yi kaicon barin ki fita bayan Beeba ta hana ki fita.

Ba mu ida shiga tashin hankali ba sai da ki ka kwana ba ki dawo ba, muka nemi wayarki a kashe, Bindigarki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login