Showing 24001 words to 27000 words out of 28383 words
Chapter 9 - MANYAN MATA BOOK 1 COMPLETE BY Hadiza Barau Gidan Iko.docx
ciki ne?”
Ya ce, “Gaskiya ban je gidansu ba, saboda ni dai aikina ya qare tunda aka xaura aure na manta
da wata halitta Husna, kuma idan naje gidansu in ce me? Ke ya kamata kije kiji abin da yake faruwa, nima nafi kyautata zaton ta gane abinda ki ke nufi…”
“Kai Shahid saurare ni ka ji! Gaya min gaskiya.” Ta faxa a zafafe. Ya ce, “Madallah, ni kuma zan faxa miki gaskiyar da ki ka nema, ina saurarenki.” Ya faxa da jiran jin abinda zata tambaye shi.
“A ina Husna ta ke?”
“Tana tare da ni!” Ya bata amsa.
“Uhum, sai yanzu na gane manufarka, kana so ka ce min son Husna ka ke?”
“Babu ko shakka.” Ya bata amsa.
“Hehehe!” Tayi dariya “Ka ce ka kwanto wa kanka ogas ka xauko ruwan dafa kanka wallahi, kana so ka ce min kishi zan yi da kai?”
Ya ce, “Ko xaya!..” ta ce, “Haka ne mana. To bari ka ji in faxa maka, bana tarayya da kowa a kan son Husna, zan rufe ido in yi maka abin da ba ka zata ba. Zan iya yafe maka yaudarar da ka yi min amma ba zan iya yafe maka son Husna da kayi a zuciyarka ba bare kuskure ya kai ka tava min ita. Shin ka tava min ita?”
“Qwarai kuwa.” Ya bata amsa.
“Za ka iya maido min ita?”
“Bana zaton haka gaskiya.” Ya bata amsa.
“To shi kenan, idan ka iya faxa sai in ce ka shirya, idan ko ba ka
iya ba sai in ce ka koye shi kafin gobe.”
“Qwarai ma kuwa na iya faxa, wanda ki ka sani da wanda tunaninki bai kawo miki shi ba. Bari in faxa miki wata magana guda xaya don ki hutar da kanki a kan son ganina, don gaskiya ko da kuxi ba za ki iya gano inda ni ke ba.
Na lura a duk duniya babu mutumin da ki ka raina wa hankali irina. Ta ya ya za ki maida ni kawali, kawalin ma irin na ‘yan maxigo?
Wallahi tallahi ban tava son wani abu irin Husna ba, kallon farko nayi mata na tabbatar da nayi mata. Mata kuma irin tagari.
A lokacin da ki ka tura ni ga Husna ta sanar da ni ba zata tava yin soyayya da ni ba, saboda ta rufe shafin maza ba kuma zata dube su ba, saboda wani ya yaudareta.
Na tabbatar mata da ni ba zan yaudareta ba, ba ma wannan ba a manufar da kika tura ni ga Husna matuqar na tabbatar da hakan to ina da yaqinin sai Ubangiji ya gina min Jahannamata ta
wani ko dai saboda laifina ya zarta wanda ki ke shirin aikatawa Husna.
Husna ba irin matan da za ki nema ba ce, Husna ba irin matar da za a yti sakaci da irinku su tava ba ce. Don haka ni ke ba ki haquri a kan hakan, matuqar ina numfashi babu ke babu Husna, sai dai ki faxi sunanta a baki, amma Husnata koda sawunta za ki kalla kiyi sha’awa to zan yi yadda nayi na kare sahunta bare ki kalle shi.
Ina kuma me tabbatar miki, Husna ko a mafarki ba za ki ga fuskarta ba bare jin muryarta ko ta bata sai anjima!”
Xit! Ya datse kiran, tabi wayar da kallo. “Lallai Shahid ya xauko Dala babu gammo.” Ba ta iya runtsawa a daren ba saboda irin yaudarar da Shahid yayi mata, babu abin da ke gilmawa ai idonta sai Husna.
Washegari ta nufi bincken in
da Shahid yayi masauki, sai dai
tayi
duk iyakar bincike
nta amma bata yi nasarar samun inda Shahid yake ba.
Tsayin sati xaya babu amo babu labari. Da dai ta tabbatar Shahid ya yi nasara a kanta sai ta kira wayar shi.
“Uhum! Xan samari Shahid ya ya Amarya Husna? Zan so bakinki ya daina ambaton sunan Husna, wallahi ba ki ji yadda nike ji ba idan ki ka kira sunan Husna.”
Ta ce, “To albishirinka Shahid, ka ce goro! Wallahi tallahi sai na cika burina a kan Husna, ai tunda na qwallafa raina a kanta to sai nayi nasara a kanta, koda zaman zaio kaimu tsawon shekara xari.
Kai ko mutuwa nayi sai fatalwata da kurwata sun dawo duniya sun biya buqatar su a kan Husna. Don haka sai ka rubuta ka aje Husna zata zo hannuna ko a xaxe ko a jima.
Kai kuma ina me tabbatar maka daga yau wannan shegiyar tsohuwar taka ta gama kwana a duniya. Dama an ce xan kuka shi ke ja wa uwarshi jifa!”
Ya ji maganarta har cikin yatsun shi, ya miqe tsaye a ruxe babu abinda yake so da qauna irin mahaifiyarshi. Ya kuma san Gwanar rawa zata iya yin komai a kanta.
Ya shiga tsananin tashin hankali da ruxewa, ya shiga safa-da-marwa a qofar gidan da sauri ya zaro wayarshi ya kira qanwarshi Maryam.
Sai dai wayar shi ya kira qanwarshi Maryam sai dai wayar a kashe. Ya soma kiran duk wani da yasan zai nemi xaukinshi amma rashin sa’a da kuma ajali da aka ce in yayi kira babu tsimi babu dabara.
Bai samu sukuni ba ko na savani, fatanshi ya smau wayar Maryam amma ina! Bai kwanta ba yana gaban Mai duka da son Allah ya kuvutar da mahaifiyarshi daga sharrin Fadila wayarshi ta xauki qara wadda ta taho da bugun zuciyarshi a jere.
In da yaga lambar makwabcinsu Zaidu Barmo inda yake sana’ar da shi yana ina wuta ta tashi a gidan su har ta lashe tsohuwarshi da qanwarshi?
Bai
i
ya ba shi
amsa ba ya zube a qasa yana maida numfashi. Sai hawaye ya shiga biyo fuskarshi, inda wayar ta sake xaukar qara a karo na biyu, inda yayi arba da sunan Fadila gwanar rawa.
Ya kasa kai hannu ya xauka bare yayi wani abu. Kuka yake me sauti don tunowa ya yi da Bash da mahaifiyarshi a duniya.
Aka yi ta kiran wayar ya kasa xauka. Can saqon kar ta kwana ya shigo wayarshi. Ya duba saqon wanda ya fito daga lambar Gwanar rawa.
Duk da idonshi dishi-dishi yake gani bai kasa shaida abinda ta rubuto ba.
“Da ka xaga kiran ma babu abin da zan ce maka illa in yi maka gaisuwar Gyatumarka, in kuma faxa maka yanzu ka xaura aure da tashin hankali har sai ka tako qafarka gare ni ka kuma kawo min Husna ka kuma bani haquri
.
Me yiwuwa in iya yafe maka, me yiwuwa kuma akasin hakan. Sai in ce sai na sake bugowa in yi maka wata ta’aziyyar…”
Qit! Ta kashe wayar
Washegari ya iso inda har wannan lokacin wutar ba ta mutu ba. ganin yadda yaga Mahaifiyarshi da qanwarshi yasa ya zube a sume bai farko ba sai a gadon asibitin.
Bai san yadda aka yi ya dawo gida ba kasancewar ba a garin yake da zama shi da Husna ba. Tsayin sati xaya yana a tsakanin rai da rayuwa, sai ga wayar Fadila inda take sanar da shi Yayarshi Jummai a kanta zata xora daga inda ta tsaya.
Wayar da wuqar da Fadila ta soka mata da nufin kasheta inda kuma asiri ya t
onu har aka gane ita ce tasa wuta a gidan su Shahid.
Wannan dalilin
shi ya kawo Gwanar rawa inda Shahid yayi rantsuwa me tsanani a qarshe ya xauki fansar abinda tayi mishi a kan Mahaifiyarshi.”
Itama xin tayi rantsuwar bata gama yi mishi nilla ba, sai ranar da ya kawo mata Husna haka kuma ta ce ko ta mutu sai ta yio fatalwa ta dawo duniya ta biya buqatarta da Husna.
Deena da Beeba suka zubawa Rose ido tamkar suna kallon
TV
, sun kuma kasa cewa komai. deena ta juyo
inda ta hango Gwanar rawa sai taka rawa take tamkar Ibada.
Ta zuba mata ido tana hango ta’addancin da tayi wanda kai ba ka ce zata iya ba. Tabxijan! Amma fa zan so in ga yadda wannan fim xin zai qare?” In ji Beeba.
“Ke dai bari Beeba, nima ina so in ga yadda za a haxu tsakanin Shahid da Gwanar rawa, da kuma Husna baiwar Allah.”
Ba ma wannan ba, idan Husna ta gane yadda aka qullo aurenta da Shahid me ki ke zato? Kai
haxuwar Shahid da Gwanar rawa shi ne gangar jikin labarin, don ba a ma soma ba.
Deena ta soma zuraro hawaye haxi da shesshekar kuka kafin ta rushe da kukan. Ai fa ke kin ji tsiyar ki Deena, labarin su Shahid fa bai qare ba bare kiyi tunanin wani yayi nasara wani ya faxi da har ki ke zubar hawaye.”
“Haba Rose! Ai ga wadda tayi nasara nan. Uwarshi fa da qanwarshi sun ci wuta.”
“To sai kuma ki ce Fadila bata yi nasara a kan shi ba? duk wanda ya kasance maka uku yafi kowa yin nasara a kanka, babu abinda za ka yi mishi kja rama, babu ranar da za ka daina baqin ciki?
Babu ranar da zaka daina baqin ciki babu ranar da hoton abun zai ba ce maka. Haba don Allah tuna fa wuta akan bankwa mata ta qone ita da ‘yarta qanwarsu.”
Ta soma share hawaye sai in ce Shahid ne ya soma shigar baqin
cikina a kan kashe mishi iyaye. Hakan ya tuno min da nima ranar da na buxi ido naga gawar iyayena.”
Ta soma kuka me cin rai, suka kasa rarrashinta har tayi shiru don kanta, ta juyo inda ta hango Gwanar rawa ta doso inda suke.
“Kai ‘yar madara kukan ki ke hala? Ke dai kam kin yarda da kuka ko
Cornflacks
ki ke so?” Ta faxa idonta a kan Deena.
“Bana buqatar komai a rayuwata da ya wuce kuka.” Cewar Deena. “Lallai kina jin daxinki, ni kam abinda na xauki kuka aikin raggaye masu zuciyar kabewa ko kankana. Ba komai ake wa kuka ba ni bana jin da akwai abinda zan yi wa kuka a duniya, babu shi.
Ni fa zuciyata tafi dutsi tauri, shi yasa bana barin idona ya yi hawaye, ko lokacin da ni ke qarama Mamana ko dukana take bana kuka, sai ma in tsaya ta dake ni ta gaji sai in ta gama in ce mata kin gama Mama?”
Ta ce, “Eh.” Sai in wuce kawai amma ke naga babu abin da ake miki ki ke wage baki kina ta kuka, me yasa? Me yasa ne?”
“Saboda zuciyata da taki ba iri xaya ba ce, ke an saba dukanki ni ko ba a saba dukana ba, ko hararata ba a yi a gidanmu
sai rarrashi.
Shi yasa ni ke kuka a kan abubuwa masu yawa. Me yiwuwa da nima gidanmu an saba dukana kamar ke wata qila da ban yi kuka ba. kin san ko faxa ba a ware qwanji ayi dukan faxa ba a a’a ga wanda ya san faxa da magana ko ka
kashe abokin faxanka ya daxe yana jin ciwon maganar da ka faxa mishi.
Amma shi duka ana jin zafinshi ne a lokacin da aka yi dukan, da anjima shi kenan ya wuce. Eh to, kin yi gaskiya ‘yar madara, bari in kawo miki madara ki sha ki huta yi mana kuk
a
.”
“Na qoshi gwanar rawa, na gode miki sosai.”
BABI NA TAKWAS
G
andireban ya shigo yana tambayar, “Wace ce Rose Ma’azi?” Rose ta dube
shi ta ce, “Ni ce Rose Ma’azi.” Ya ce, “Ki zo kina da baquwa.”
Gaban Rose ya faxi, baquwa? Shekarar ta biyar a gidan yarin babu wanda ya ziyarceta saboda wasu suna jin haushinta a kan baro Addininta da tayi ta shigo Musulunci.
Don haka take tababar qila dai ba ita ake nema ba. To waye ya zo mata? waye? Ta tambayi kanta. Ta dai bi bayan Gandiroban inda ta isa inda baquwar take zaune.
Ta dubeta inda suka rungume juna ita da Sintia qawarta ta amana. Hawaye ya zubo mata “Sintia ke ce ki ka tuna da ni?”
Ta ce, “Ban manta ki ba Rose, ban dai san abinda ya faru da ke ba sai da na shigo Legos na neme ki aka ce min ai kina tsare a gidan Kaso.”
“Uhum! Kin dai gani Sintia na neme ki ne aka ce min kin bar Legos gashi kuma bani da lambar ki, gashi kuma ba ni da lambar ki, gashi kuma kowa ya guje ne ni shi yasa babu wanda ke zuwa inda nike.” Ta faxa hawaye na bin idonta.
Sintia ta share mata hawayenta “Daina kuka Rose, ko kowa ya guje ki ni ba zan guje ki ba, ko kowa ya qi ki ni ba zan qi ki ba. Yanzu ina sauri ne amma ki faxa min abin da ki ke so ko zuwa gobe sai in kawo miki.
”
“Na gode Sintia da ki ka ziyarce ni ma ko ba ki bani komai ba.” “A’a ai kin fi qarfin komai a wurina.”
To na gode, duk abin da ki ka kawo min ina so! To ba damuwa. Sai gobe kenan. Suka miqe a tare inda Sintia ta zuge jakarta ta xauko rafar xari biyar biyar ta miqa mata.
“Ki riqe wannan kafin gobe ta zaro ido sun yi yawa Sintia…” Kar ki ce komai sai na dawo.” Ba ta jira komai ba ta fice. Rose ta bi ta da ido.
“Me Sintia take da har take iya bayar da kyautar dubu hamsin? Ta dai tattara mamakinta ta zubar a kwandon shara ta shiga ciki ta samu
Deena da Beeba ta sanar da su yadda suka yi da qawarta Sintia har ma ta nuna musu kuxin da ta bata.
Suka jinjinawa karamcin Sintia, inda ita kuma Rose take mamakin inda Sintia take samun kuxi
. Bata tsinke da lamarin ba sai washegari, inda Sintia ta iso da kaya na ban mamaki tamkar
za’a buxe shago, har da su kifin gwangwani da madara da abincikan gwangwani.
Gaban Rose ya faxi “Duk ni kaxai Sintia?
” Ta ce, “Qwarai ma kuwa Rose, ai ni ban xauki abota wasa ba, zan kuma riqa zuwa duk bayan wata saboda ina
busy
ne bana samun
time
sosai ne.”
Rose tayi godiya sosai suka yi bankwana da Sintia, sai ya zamo suma sun daina cin abincin da ake rabawa Bursunan, sai dai su ci me daxi su sha madara su kora da lemun roba.
Sai dai a gefe xaya Rose ta damu da son sanin me Sintia take tana samun kuxi haka? wane irin aiki take yi? Sai suka bar karvar wankin da ake kawowa a gidan yarin saboda gatan da Sintia tayi musu.
Duk kwanan watan duniya sai Sintia ta zo ta kawo ma Rose kayan masarufi, wani lokacin ma har da kuxi. Kuxi ko masu dama wanda idan kashewa zata yi ba za su qare a watan ba.
A sanin da tayi wa Sintia dai talaka ce tunda idan ba ta manta ba tasha agazawa Sintia da kuxi har ma da suturu. To qila kuma wani aiki ta samu me kawo mata kuxi.
In ko haka ne Sintia ta dace sai tayi mata addu’ar kada Allah ya haxa ta da sharrin namiji a rayuwarta. Tun tana yamaxixin tunani inda Sintia ke samun kuxi har ta watsar dare ya tsala sosai inda suke ta jan munshari saboda barci.
Deena dake barci sama-sama ta soma jiyo ana lalubarta. Ta miqe a tsorace inda
tayi arba da Fadila Gwanar rawa a kan gadonta.
“Ah! Meye haka?” Faxar Deena. Gwanar rawa ta soma magana qasa-qasa. “Haba ba ki san tun zuwanki gidannan nike qaunarki ba? tausaya min yau kaxai kin ji?”
Deena ta soma kaxa kanta “A’a’a ba harkata ba ce, bana yi. Ki fita daga harkata don Allah!” Ta ce, “Sau xaya fa!” Deena ta ce, “Allah Ya kiyaye ni, wallahi bana yi, ki kuma fita harkata in ba haka ba wallahi zan sanar da mahukuntan gidan, kin san dai idan aka kama me wannan laifin hukunci ne me tsanani
.”
Rose ta miqe da nufin zuwa fitsari. Da sauri Gwanar rawa ta koma gadonta. Tun daga wannan ranar sai ya zamo duk inda Deena da Gwanar rawa za su haxu to harara ce zata yi ta aunowa Deena.
Ko magana ta daina yi mata, inda Deena ta jinjinawa Gwanar rawa wai ita da aka yi wa laifi bata yi harara ba sai ita da tayi laifin.
Sati xaya da yin haka, cikin dare kawai sai ji tayi an rungumeta ana shafata. Da sauri ta ida buxe idonta inda tayi arba da Gwanar rawa har ta soma cire mata riga.
Da sauri ta diro daga gadon ta damqi wuyanta ta shaqe. “Wahayi aka yi miki da ni ne?” Ta faxa da qarfi. “Koda ki ka ganni a nan qaddara ce ta kawo ni ba ‘yar iska ba ce ni, wallahi sai na kashe ki, dama abokin tafiya nake nema. Da me zan ji?”
Ta soma kai mata duka a fuska, kokowa ta kaure inda hayaniyarsu ta tada sauran Bursunan da ke barci.
Rose da Beeba suka soma qwatar Gwanar rawa amma suka kasa qwatarta, duk yadda suka raina Deena ashe shegen qarfi gareta.
Da kyar suka qwaci Gwanar rawa, tana haki. “Me ya faru?” In ji Rose. Amma Deena tayi shiru don tana jin abin kunya ne ta ce Gwanar rawa ta neme ta.
Can wata ta bada amsa da cewa, “Yo ya wuce yarinya taga ana qoqarin yi
mata fyaxe? Abin fa ba a duhu yake ba
a bayyane yake.”
Ita dai Deena bata tanka ba bare Gwanar rawa da ta sha shaqa. Kasancewar kowa ya sani yasa aka rufe babin.
Washegari Sintia ta iso a wannan karon ita da wani Inyamuri suka zo, wai ya zo ya duba Rose xin. Rose ta iso inda tayi arba da sangamemen Inyamuri marar kyawun duba.
Suka gaisa inda Sintia ta gabatar da shi a matsayin ubangidanta. Rose ta sake gaishe shi, ya amsa yana washe baki. Kaya masu yawa Sintia ta dire mata inda shi kuma ubangidanta ya bata rafar dubu xari.