Showing 3001 words to 6000 words out of 28383 words
Chapter 2 - MANYAN MATA BOOK 1 COMPLETE BY Hadiza Barau Gidan Iko.docx
/>
Huxu saura na Asuba suka iso gidansu, wanda ke a New Abuja, a cikin birnin taray
ya Abuja. Xaki Rose ta wuce ta faxa banxaki ta watsa ruwa ta faxa kan
Gado sai bacci, yayin da Deena da Beeba sai da suka sallaci Asubahi suka kwanta.
Washegari ranar ta kama Lahadi, inda Rose ta sheqa wanka da kwalliya tayi nufin ficewa coci. Beeba da Deena suna
break fast
ta dube su.
“Naje Choci sai na dawo.”
Deena ta magantu. “Zaman gaskiya a faxawa juna gaskiya, ya fa kamata ki gane addinin…”
Rose ta xaga mata hannu. “Saurara min don Allah Deena, wai lokacin da na zavi shiga Musuluncin kina ina? Ba mu fa san juna ba!
Kiristanci shi na gada, cikinshi aka haife ni, roman baka da kyautata zato a kan Musuluncin ya sani shigowa. To don me yanzu kuma na ce ban yi za ki nemi takura mini?
Bari in gaya miki wani abu da ba ki san shi ba daga ni, a kan xa namiji na zavi na bar iyayena, na bar dangina, na kuma bar gatana. Amma sai gashi mijin da na yi wa yayi min abin da ya sani yiwa Musulmai baqin maki, na shatawa addinin layi, naga gara in koma inda na fito saboda su ba su haka.
Kuma bayan haka ina da ‘yancin zavin abin da ya yi mini a rayuwa. Don haka haxiye maganarki ki kora da ruwa, ban ce ki baro addininki ki shiga nawa ba bare ki yaudare ni da wani zancenki wanda na daxe da jin wanda yafi shi garxi.
Na tafi don na rufe wannan (Chapter) xin ban da lokacin buxeta, xan makullin ma na jefa a Maliya.” Ta fice abinta ba tare da ta qara tofawa ba.
Suka maida hankalinsu a kan qatuwar
TV
(Plasma) wadda ke kafe a bangon falon inda ake labaran qasa a N.T.A.
Fuskar Shehu Usman Shehu ce ta cika allon
TV
xin, in da ake sanarwar mutuwarshi a kan kisan da aka yi mishi a otal (Hotel) xin (First Class).
Beeba taja tsaki inda Deena ta dube ta.
“Aikinki ne hala Beeba?”
“Uhmm!” Ta bata amsa.
Ai ko da yake an tavo ma su riqe da linzamin duniya, sai vavatu ake. To yanzu aka fara ma balle a gama.
“Uhum! Ai maza babu sauqi bare sauqaqawa
a tsakaninmu. Ai ko da ba a ce duk abin da namiji ya yi mace ma zata iya ba, to ni xin zan yi abin da yafi na namijin ma.
Ina baqin cikin in waiwaya baya a rayuwata in hango sanadi da takaici da baqin ciki wanda xa namiji ya yi min. ban san me yasa namiji ya zavi ya cusa min baqin ciki a kan ya bani farin ciki a rayuwa ba.
Nayi halacci ya yi min butulci, na so shi ya tsane ni, na xaga darajarshi ya qasqantar da tawa. Naqi kowa na so shi ya qi ni ya so wata. Na yarda da shi ya yaudare ni. Beeba me zai sa in yiwa maza sauqi
a rayuwa? Me zai sa ba zan qarar da mazan da ke duniya ba?
Namiji ko na tsuntsu ne na tsane shi, namiji ko na wane irin jinsi ne wallahi na tsane shi, matuqar ina numfashi namiji ya gama jin daxi ko na wane irin jinsi ne, har yau, har kuma gobe, ke har in koma wa Mai duka ba zan tava warke mikin da xa namiji ya yi min ba.”
Beeba ta ziraro hawaye.
“Deena namiji ya so ni ya qaunace ni, ina da tabbas babu irin qaunar a duniya, sai dai kash! Ban dace ba, ban dace ba. da zan iya da maza sun ci albarkacin qaunar namiji xaya. Amma duk da haka zan yi hukunci a kan takaici da baqin cikin xaya.”
Deena ta bita ido, inda ta miqe ta shiga xaki. Jim kaxan ta fito da wani hoto ta miqawa Deena.
Kyakkyawan saurayi me sanye da ka-ki na Xansanda, fari ne tas! Me dogon
hanci, sumar kanshi ta qayata kyanshi. Me faffaxan qirji, fara’arshi takan gigita ‘yanmata har su shagala da kallonshi.
“Mits!” Deena ta ja tsaki “Nasan da me ya ruxe ki har ki ke wani ajiyar hotonshi.” Beeba ta shafi fuskarshi, hawaye na zuba.
“Allah Yasa kana cikin Aljanna, Allah Ya yafe laifukanka. Ka tafi ka bar ni ina cikin garari wanda rashinka ya sabbaba min, a da ina ganinka a mafarkina me yasa ka guje ni?”
Deena ta zuba idanu, ganin irin kukan da take yi da sambatu. Ta ruqo ta “Ya isa Beeba.” Ta bi ta da ido. “Deena da mutumin nan yana raye wallahi tallahi da har in mutu ba zan tava yin kuka ba. Da yana raye da ban xorar da takaicin xa namiji ba. Da yana raye hawayena ko sun fito shi zai share min, ya kuma hana min kuka.
Rashin wannan shi ne qarshen baqin ciki a gare ni. Da ana fansar rai da na fanshi rayuwarshi da tawa rayuwar.”
Deena ta share mata hawayenta “Daina kuka Beeba, na soma fahimtar ki…” “Ta ya ya zan daina kuka Deena? Wallahi kuka yanzu na soma, zan yi ta kuka har a busa qaho, domin ko abin kukan ne ya same ni.”
Yini zungur Deena tana rarrashinta har Rose ta iso daga (Coci)
. “Oh God! Beeba what is rong?”
“Me ya faru?” T
a faxa tana cire
Head
xin kanta da zare zanqala-zanqalan takalminta masu maxauri. Deena me ya same ta?’ Ta faxa tana duban Deenar.
“
Me fa ya same ta, ban da waiwaye a kan xa namiji?”
“Ehem! Ehem!! Ni nasan za a yi haka. kin ga Beeba idan kina irin haka sai in ga kamar ba ki godewa Allah ba. ko kin manta tuggun da namiji ya shirya miki
?
So ya yi qasa ta lulluve idonki, kin manta in da tuggunshi ya kai ki? Kin manta so ya yi a kashe ki murus? To albishirinki ce min goro ban kuvuto mu ba don mu tsira daga sharrin da suka xana mana kawai ba, a’a na yi hikimar kuvuto da rayuwarmu
ne don mu maida martani a kan mazan mu na asali da suka cuce mu.
Mazan da muke wa ta’adi kuma laifin waxancan ne ya shafe su saboda sunansu guda kuma halinsu guda. Kusan Beeba da ke Deena na zavi na taimake ku ne saboda lurar da nayi muku tayi iri xaya da tawa, don mu haxu mu fidda A’i daga rogo.
Don haka share hawayenki ki xaura xamarar yaqar maza domin ko da akwai shirin da nake yi mana. Ni wallahi na matsu naji labarin Beeba wanda na tabbatar
ko rabin nawa ban kai ba a zalunci.”
Ta dubi Beeba, “Ina son sanin gaskiyar lamarinki Beeba. Duk da na lura wani namijin yayi miki halarci, wani kuma ya yi miki butulci. Ya ya abin yake ne?”
“Deena kiyi haquri ba zan iya sanar da ke komai a yanzu ba, saboda bana cikin natsuwata a duk sadda na tuna wannan komai kwance min yake. Amma nayi miki alqawari ni ce farkon wadda zan fara sanar da ku labarina kafin naji naki labarin da kuma Rose kafin muga irin shirin da Rose take mana.”
“Kin yi daidai Beeba, don haka ku tashi muje ‘SAHAD’ muyo
shopping
saboda kayan abincinmu sun yi qasa.” cewar Rose.
“Ga shi kuma gobe Litinin ranar Azumi ba.” Cewar Deena. “Ni dai kam gobe kam ba zan samu damar yin Azumi ba.”
“Eh ai naga me jan danja ya iso miki.” Deena ta tare ta da faxin haka. “Haka ne, sai dai mu haxu a ranar Alhamis.”
“To Allah Ya nuna mana.” In ji Rose. Suka xauki wanka na tashin sens, kowace fuskarta ta xauki kwalliya tamkar an varota daga qwai, shigarsu ma iri xaya ta dogayen riguna da guntun gyale wanda suka yi ma kansu
, akasin Deena da ta sagalashi a kanta wanda hakan ya bada damar ganin dogon wuyanta da tsarin qirjinta.
Kai tsaye suka doshi ‘SAHAD’ motarsu ta faka a katafaren filin fakin na farfajiyar super market xin ‘SAHAD’.
Suka fito, Deena da Beeba suka yi gaba, in da suka baro Rose tana xauko kuxi. Ta fito daidai da tsayawar wata mota kusa da ita. Mutumin ciki ya fito inda idonshi ya sauka kan fuskar Rose.
Gabanshi ya sara da qarfi, ya zare gilas xin idonshi ya bi Rose da kallo, yayin da take shigewa
‘SAHAD’. Ya zaro wayarshi ya doka wa Tukur Sambo waya.
“Tukur kana ina yanzu?”
“Sir, ina Legos wani abu ne?”
“Eh, tambayarka zan yi, ya sunan matar nan
da ta mutu a gidan Yari, wadda ka ce min ka ganta?”
“Kar dai kai ma ka ganta Sir?”
“Sosai, na ganta amma ina son sanin sunanta.”
“Sunanta Aisha, Sir! A ina ka ganta?”
“Na ganta a ‘Sahad’ a garin Abuja.”
“To Sir, ko mu qaraso?”
“A’a bar ni da ita kawai, idan da buqatarku xin zan sake kiranka.”
“To Sir, a dawo lafiya.”
Ya sauke wayar yana mai mamaki. Ya shiga cikin
Store
xin yana baza idon inda zai hangota
. Can ya hangota tana jidar abinda ya kawota, yayin da Deena take vangaren littattafan Hausa tana zavowa, ita kuma Beeba tana zavar
sweet
da
biscuit
.
Ya iso inda Rose take ya yi mata sallama. Tamkar ba ta san Allah ya yi ruwan shi a wurin ba. A zatonshi duk Musulmi ba ya qin karvar sallama.
Ya sake doko mata sallamar ta sake baiwa banza ajiyarshi. A da dai ta amsa sallama amma a
yanzu da sallamar da masu sallamar duk tayi wuri ta aje su.
Ya kai hannu a kan abinda tayi nufin xauka, tayi saurin kallonshi inda taji gabanta ya yi muguwar sarawa, amma sai tayi saurin basarwa ta janye hannunta. Ya zuba mata ido.
“Haba Aisha, ina ta sallama kin qi amsawa ko ba ki so ganina ba?”
“Wace ce haka kuma Malam?”
“Ke nake nufi mana, ko kin manta ni ne in tuna miki? To sunana Olu Kayode na gidan kason da ke garin Lagos qiri-qiri, nasan yanzu kin gane.”
“Uhm! A can ka sanni kenan?”
“Kinga idan ba za ki damu ba ina son mu zauna da ke, da akwai tambayoyin da ni ke so in yi miki, kuma ki amsa min su.”
“Ok, babu damuwa. Amma ka bani
Address
xin inda zan same ka saboda a yanzu ina cikin wani uzuri.”
“Ayi haka kuwa? Ke dai in jira ki ki gama sai muje.”
“Kar ka damu, ni na ce ka bani
address
xinka zan iske ka…”
“Zan jira ki kar ki damu.” Shima ya tare ta don yana zaton tsari ne ba zuwan zata yi ba.
“Ok, to babu damuwa.” Ta ci gaba da xaukar abinda take buqata, yana biye da ita a baya.
Deena ta qwalo mata kira.
“
Rose ga
turarenki ‘Amiril uhd.”
“Ok, to xauko min.”
Ya maimaita sunan a ran shi “Rose?” sai kuma ya bar mamaki domin ko hakan na iya faruwa a zuwan vadda sawu.
Deena da Beeba ba su kula da shi ba, yayin da shima xin bai kula da bin fuskokinsu ba, wata qila da ya dube su da kyau to da ya bar kokonton Rose ita ce ko ba ita ba ce.
Mamakinshi yana kan yadda Aisha ta kuvuto har ta sauya sunan Rose a tsarinta na vadda sawu. Suma gama siyan abinda ya kawo su suka isa wurin biyan kuxi.
Rose ta biya aka tsauna musu a mota. Sai a lokacin Beeba da Deena suka ankare da Olu Kayode da ke biye da su. rose ta miqa wa Deena makullin motar.
“Kuje Deena, ni zan ga wannan mutumin.” Ta nuna Olu Kayode da ke gyara fitowa da motarshi. Beeba tayi magana a hankali don kar ya ji me, ta ce “Rose wannan ai Gandiroban nan ne na Legos ko?”
“Shi ne Beeba, har ma yana gayyatata.”
“Na shiga uku Rose kar fa…”
“Kar ki damu fa Beeba, ai sun makara wallahi tunda har suka bari duniya da mutanen cikinta suka yi mana abinda muka yi wanka muka fita hantsi. Kuje gida in tayi ruwa Rijiya, in kuma ta qafe Masai.
Amma fa kar ku tashi hankalinku, nayi muku alqawarin duk rintsi duk wuya ba zan wuce awa uku zuwa huxu ba.”
Ta juya da sauri ta shiga motar Olu Kayode yaja suka hau titi.
Deena ta dubi Beeba.
“Anya ko ba mu yi sakacin barin Rose ta bi wancan mutumin ba Beeba?”
“Hankalina bai kwanta da ganin mutumin can ba Deena! Komai zai iya faruwa a kan Rose. Idan ta bayyana me ki ke tsammani? Gaskiya mu bi bayansu.”
“A’a in muka bi bayansu ne zai gane da wani abu a qasa.”
“Ina nufin mu ga inda zai kaita. Idan muka ga lokacin da ta xiba ya wuce ba ta dawo ba sai mu zo muga abin da ke faruwa.”
“Kar ki damu Deena, nasan Rose ba zata yi abin da zai vata ruwa ba, muje gida
.”
BABI NA BIYU
H
otel xin (Fist Class) Olu Kayode ya faka motarshi, ya kama xaki a qasa me lamba sha biyu. Rose tana biye da shi har cikin
xakin.
Yayi odar abin tavawa da na jiqa maqoshi. Ya dubeta da son ya ga razanarta amma sai ya same ta a dake, ko dama can ba ta da tsoro bare fargaba.
“Me za a kawo miki baquwata?”
“Uhum! Na gode sosai, cikina a cike yake.”
“Amma zan so ki sha ko abin sanyi ne saboda tattaunawar tamu tana da tsayi.”
“Babu komai wallahi na gode. A shirye nake da in ba ka haxin kai a kan abin da za ka buqata daga gare ni, na kuma yi maka alqawarin faxa maka abinda ka ke son sani.”
“Na gode Aisha. Amma zan so in san wanne ne sunanki na gaskiya tsakanin Rose da Aisha?”
“Sunana Rose kafin in zavi Aisha saboda faruwar wasu lamura da suka faru a baya, yanzu kuma na dawo da bara-bana, wato tsohon sunana Rose.”
“Da kyau Rose, idan na fahimta dai ke ce Bursunan nan da ta mutu a gidan yari ta dawo duniya?
”
“In ban da abin ranka ya daxe, ka tava jin wanda ya mutu ya dawo?”
“Sosai ma, ga ki na gani?”
“A’a ni ban mutu ba gaskiya…”
“To ya aka yi ki ka vulla a garin Abuja akasin inda na san ki a garin Legas, a gidan Yarin qiri-qiri?”
“To wannan tambayar kuma ina ga bani ya dace na amsa ta ba, mahukuntan gidan su ke da alhakin amsa wannan tambayar.”
“Na yarda, amma ina fatan ba ki manta da alqawarin da ki ka yi min ba na sanar da ni gaskiyar abin da na tambaye ki. Haka ne?”
“Haka ne. amma ka dubi shimfixar maganta in da naso nayi wasa da hankalinka sai in ce maka ba ni ce Aishar da ka sani ba, in tsaya a kan sunana Rose.”
Ya zuba mata ido yana kallonta, kafin ya xora batunshi “Na yarda da ke Rose, amma ina son tabbatar da shin ke ce wadda na sani a matsayin me laifi a gidan kason qiri-qiri?”
“Qwarai ni ce.” Ta amsa mishi babu tsoro ko fargaba.
“To ya aka yi haka?”
“Nima abinda ni ke tambaya kenan?” Ta faxa tana kallonshi.
“Ina son sanin shin sakinki aka yi ko ko guduwa ki ka yi?”
Tayi wani guntun murmushi.
“Bana jin yadda qiri-qiri ke da tsaro wani fursuna zai samu sa’ar guduwa, in ma ya gudun to ina ma’aikatan su ke? Ko kuma aikin me suke?”
“Rose lamarinki na kulle min kai, na rasa gane qullin voyen da ki ke min.”
“Uhum! Ranka ya daxe da Hausa fa muke maganar nan duk da kasancewar ba yarenmu xaya ba, ni Igbo ce kai kuma Bayarbe, amma ai muna fahimtar juna ko?”
“Haka ne, amma har yanzu ba ki bani amsa ta daidai ba, shin sallamarki aka yi daga gidan yarin ko ko guduwa ki ka yi?”
“To bari in baka amsar da zata gamsar da kai. Kamar yadda na wayi gari a gidan kason ba tare da na shirya ko na sani ba, haka na sake wayar gari a wajen shi ba tare da na shirya ko na sani ba.”
Ya dubi agogon hannunshi “Amma naso mu taqaita dogon bayanin da ki ke ja mana Rose. Gashi har lokaci ya ja.”
“Kar ka damu, bani da wani uzuri a yanzu sai naka, babu matsala ina saurarenka.”
“To ai kin qi faxa min abinda na tambaye ki.”
“Ban san me ka ke so na faxa maka ba bayan wanda na faxa maka.” In ji Rose.
Ya ce, “Da za ki taimake ni da kin gajarce min da cewa sallamata aka yi ko guduwa nayi, shi kawai nafi buqata da tuni na sallame ki.”
Rose ta ce, “To ni dai ban san an yi min abu xaya daga cikin abu biyun da ka zano min ba. Da ban yi alqawarin faxa maka gaskiya ba to da na kamfaci wata shareriyar qarya na shirga ma, saboda na kula kafi son in faxa maka abinda ba gaskiya ba…”
“Look Rose, na kula sai na biyo ta bayan gida kafin ki faxa min gaskiyar lamarin…” Ya faxa cikin xaure fuska.
Itama ta tari numfashinsa. “Amma ko bamu yi haka da kai ba. A kan me za ka biyo min ta bayan gida? A kan faxar gaskiyata? To ina
jira.” Ta miqe da shirin wucewa.
Yayi saurin fincikota. “Ai tunda ki ka yarda har ki ka amsa ke ce bursunan da ki ka yaudari mutane ki ka tsere ai kuma qarya ta qare
.”
Ta zuba mishi ido tare da faxin, “Me ka ke nufi da faxar haka?”
“Ina nufin riqe ki a matsayin mai laifi hawa biyu, kafin mu xora bincike a kan yadda ki ka tsere daga yarin.”
“Uhum! Me yasa ba ka faxa min manufarka a kaina ba sai da na biyo ka ka yaudare